Showing 135001 words to 138000 words out of 286946 words

Chapter 46 - Fulani Book 1 Hausa Novel Complete

20 Dec 2024

963

mike tsaye.

“Akwai inda zan je, ki zauna a nan har Momy ta dawo, ni zan wuce”

Ta daga masa kai b tare da ta dago ba, sai yai murmushi ya dauki keys dinsa ya nufi kofa, sai da ya kusa fita sannan ta juyo ta kalleshi, kamar yasa magana take son mishi sai ya juyo shi ma ya kalleta.

“Na gode”

Yayi mata murmushi kadan sannan ya bude kofar ya fita. Sai da ya fice sannan ta daga kanta tana karewa falon kallo, ciki har da katon hoton mijin Momy dake manne a falon.
Falmata na zaune falon har kusan awa daya sannan ta ji an sakawa kofar falon key ana kokarin budewa daga waje. Hankalinta ta tattara gaba daya ta maida gurim kofar har sai da aka bude kofar Momy ta shigo tana sauke gajiya.

“Oh na barki kina da jira ko? Wallahi jirgin ne be tashi da wuri ba”

“Sannu da zuwa”

Falmata ta fada, sai Momy ta zauna tana amsawa.

“Yauwa sannu dai, na barki ke kadai ko?”

“Ya tafi yace yana da aikin da zai yi”

“Ya fada min, abu na biyu kuma Sirleem ya fada min abubuwan da suka faru, maganar gaskiya ni bana bukatar yar aiki saboda aikin gidana ba wani aiki ne mai yawa na, kuma mijina yana Abuja gurin uwargidansa, saboda a can yake zama, ni kuma na zabi zama a nan saboda aikina da kuma yan'uwana, sai an dan kwana biyu ne yake zagayo ni ko kuma ni na tafi, sai dai hakan ba zai hana na daukeki aiki ba saboda halin rayuwar da kike ciki, and Sirleem ya roki idan ma bana son aikinki na barki ki rika wuni a nan idan lokacin zuwanki yai zai samo wanda zai rika kai ki gida, idan wata yai zai biya kudin aikinki, so from now on zamanki ya dawo a nan, zaki wuni a nan ko da baki yi aiki ba, abun da nake son ki da shi shine rikon amana da kuma tsabta”

“Inshallah zan kiyaye Hajiya”

“Ki kirani Momy, baki da wani suna bayan Falmata ne?”

“Mamana tana kirana da Fulani, amman dai sunana na kwarai Fatima”

“To zan rika kiranki da Fulani daga yau Inshallah”

“Na gode”

Falmata ta fada tana jin wani irin dadi a ranta.



_________
Ina mata matan kwalisa Matan da suka ansa sunansu na Mata? Ina wadanda ke cewa mun yi mun yi bamu ga amfaninshiba? Hmmm to ku zo ga Yar gidan Maifata ta zo maku da Al ajabu, dan tsugunno, gumba da tsimi da Zuma daban daban, maganin sanyi na maza da Mata. Ga kuma garurruka irinsu mallakau sabuzu kuwa, sa bahaushe saibi, Dan hubbare kafi malam aiki, ke kadai ke da miji, dahuwar kaza, tattabara, ciccibi da dai sauransu. Ba anan kayanmu suka tsaya ba, muna hadin amare na musamman turaren sutura turaren tsugunno turaren wanka da na daki da na jiki duka 4amare nasu na musamman ne, amma ga tsuhuwar da ke son komawa yarinya itama zata iya zuwa ahadata kai abundai sai wanda ya gani, dan haka karkubari abaku labari, domin neman karin bayani zaku iua nemana ta wannan number  09029891757 ko 08169311410, muna aikawa ko'ina a fadin kasar nan har waje kasar nan muna aika kaya.
Address: Nasarawa Samaru Area gurin masallacin mai sola Gusau Zamfara state Nigeria.
34

*Littafin nan na kudi ne biya ki karanta cikin aminci. Pay 300 to 0314795884 Abubakar Hadiza Gt bank, then send the evidence via 08036126660*


UNCLE AA POV.

“Hankalina ya tashi babu inda ban je nemanka ba tun jiya, saboda baka saba wuce 10 baka dawo gida ba, yau ma sai a wayarka yarinyar take fada min an kama ka, ni da su abokanka babu police station din da ba muje ba, ashe kana nan, Ahmad miye amfanin rashin jin magana?”

Anti Rabi da kira shi da sunansa kai tsaye tana kuka.

“Kaddara ce Wallahi, ban isa na wuce abun da Allah ya rubuta min ba, kuma abun da suke zargina da shi ban aikata na Wallahi Anti, dan Allah ki yarda da ni”

“Na goye ka a bayana, na san abun da zaka iya da wanda ba zaka iya ba, na san ka na san halinka, n yarda da kai Sardauna, amman da ace ka ji magana da haka be faru ba”

Shiru yai ya kasa cewa komai, daman can tashin hankalinta yake gudu, satar da aka laka masa ma ta kasance a haka ina ga ya labarta mata cewar za a juyar da case din zuwa kisan kai, ba zai iya labarta mata haka ba.

“Dan Allah kamin ka aikata abu ka rika tunawa da halin da zan shiga, zuciyata ba komai take dauka ba, kuma ba ni da walwala matukar baka cikinta, zan siyar da gidana na fara biya kudin sarkar, in ya so daga baya sai mu cika”

“Haba Anti wane irin gida kuma? Dan Allah karki yi haka, gidan nan fa gadon su Khaleel ne su su yi yaya?”

“Yayana ba su fi kanena muhimmanci ba, gidan ne kawai abun da nake da shi, kuma zan siyar na biya wani abu daga kudin sarkar, nawa ne kudin?”

“Ba fa cewa sukai a biya kudin Sarka ba, sarkar tana hannun mai ita, kawai dai sun aje ni nan ne saboda wata manufa da ban san ta micece ba, kar ki yi gagawar yin haka ki jira har sai mun ga abun da suke nufi tukuma”

“To, bari naje na samo maka wani abu ka ci, ji yadda duk suka buge maka fuska da jiki Uncle AA baka jin magana”

Ta fashe da kuka. Shi kanshi ya san ya ji jiki, domin ba a taba masa irin dukan da akai masa jiya ba. Fita tai daga gurin wanda hakan ya bawa abokansa damar shigowa suna gaisawa da shi, su kansu sun yi mamakin abun da aka zargeshi da shi domin sun san waye Sardauna, ba zai taba daukar abun wani ba. Har daya daga cikin abokinsa yake cewa ya ja hakkinsa.

“Kai wa zai iya ja da masu kudi? Wuya kawai zai sha Wallahi, Allah dai ya sar masa kawai”

Cewar abokinsa Abdul, AA dai be ce komai ba sai kunyarsu yake ji, duk da yana da tabbacin ba su yarda ya dauka ba, sai dan nauyin abun da aka zargeshi da shi. Anti bata dade ba ta dawo rike da takeaway irin wanda masu shinkafa a hanya suke zubawa masu tafiya da shi, sai kunun aya da ruwan sanyi.

“Gashi ka ci”

“Ba zai ci ba sai kin fara ci Hajiya”

Wani dan sanda ya fada, haka ta bude abincin ta ci kadan ta bude kunun ayar shi ma ta sha sannan ta mika masa.

“Na gode Anti da ba ni da ke da na shiga uku”

Ta furta yana jin wani irin son yar'uwarsa fiye da kima.

“Zan je na fadawa su Kawu, anjima zan dawo na kawo maka wani abincin, kai ta addu'a ka ji, Allah yai maka mafita”

“Amin Anti”

Sai da yai sallama da abokansa sannan ya sake yi mata sallama, abun ka da mace sai ta fashe da kuka, domin jin take kamar ta ja hannunsa su tafi gida amman babu hali ga kuma dukan da suka masa gwanin ban tausayi. Sai da ya gama cin abincin sannan aka bada umarnin maiyarda shi cikin cell din. After like one hour da maida shi aka sake kiran sunansa ya taso.

Police din daya fito da shi yana gaba, AA na baya har suka fito reception din.

“Ka yi free yarinyar ta yafe ma”

Police din dai handling case din ya fada yana rubuta a wani  littafi, kamin ya duba abubuwan da aka kama shi da su ya fara mika masa abun sa, zube agogon hannu tufafinsa biro sai kuma yan canjinsa da suke aljihu. Kamar almara haka AA ya rika ganin abun, da dai daya ya rika karbar komai nasa har ya saka tufafinsa ya saka komai nasa.

“To sai a kama hanya, gobe ma ka kara sata a bikin manya, Allah ne yai maka gidar dogo Wallahi ya takaita ma Wahala da sai ka gane shege ma da ne”

Shi dai be ce komai ba, ya nufi kofar fita yana jin wani iri, domin kalmar da police din ya jefeta da ita wato sata ta muzanta shi fiye da kima, sai da ya fito waje ya ji yana shakar iskar yanci, kamar wanda ya shekara a cell din haka yake jin kansa, sai a lokacin ne ya ji yana kyamar kansa, irin warin da cell din ke yi ga mutanen ciki kowa kalarsa daban, ya dan ja rigarsa ya shinshina kai kace da ita ya kwana a cell din.

“Wallahi Allah ya isa, Allah ya isa, daga police din har ita bakar Hajiyar da duk mai hannu a ciki har ma wanda ya jidadin an kama ni, Allah ka wulakantasu, Allah ya tsinewa arzikin Hajiyar albarka, kuma Wallahi sai ta gani tun da ta tana marayan Allah, bakar muguwar mata kawai, kuma na rantse Nana ba zata auri danta ba, kut”

Yayi kwafa yana huci kamar mai yi da wani, da hannu ya tare dan achaba ya fada masa unguwar da zai kai shi.


ZAINAB POV.

Tun da suka kamo hanyar zuwa cikin garin Katsina Zainab take hawaye har suka isa, yar rayuwar da su kai da Auwal cikin kankanen lokaci ne ta tsaya mata a rai. Zuciyarta ta kasa daukar rashin masoyinta, ta kasa aminta cewar Auwal ya tafi ya barta. Harabar gidan Hajiya Amutu suka faka motar ta bude purse dinta ta dauko 20k ta mika musu, da murna suka karba suna godiya, ita kam bata kula su ba domin hankalinta ba a nan yakr ba, su Hajiya ma da suke falo, tana amsa sannu da zuwan da suke mata ta wuce dakin da kayanta suke, gaba daya jin tai tana bukatar komawa Yola, kamar wanda aka cewa idan ta koma Auwal zai dawo, cikin gajiya da rashin kuzari ta rama sallah magariba sannan ta gabatar da isha'i, babu komai a addu'arta sai nemarwa masoyinta yafiya da rahamar Allah, tun tana yi tana jirewa har ta fashe da kuka.

“Ashe Allah be kaddaro mu yi rayuwa ba Auwal, ashe ganin da nai maka na karshe ne”

Ta furta tana jin kamar tai tsuntsuwa ta ganta a Yola cikin daren nan, online ta shiga domin siyen ticket din Jirgin da zai tashi zuwa Yola daga kt, cikin rashin sa'a ta samu babu wanda zai tashi zuwa kt sai dai zuwa wasu guraren, na Yola zai jibi, jin tai ba zata iya jira har jibi ba, hakan yasa ta siye na Kaduna, ganin JIrgin da zai tashi daga Kd zuwa Yola nA safe ne yasa ta yanke shawarar bin mota zuwa Yola daga Kaduna. Kamin safiya ta waye har ta masu, tun cikin daren da shirya komai nata, sai 10 jirgin zai tashi amman ko da 8 tai tana airport din. Jirginsu be daga ba sai goma har da yan mintuna. Suna sauka Kaduna kai tsaye ta nufi tasha, shata ta dauka ta zuwa Yola daga ita sai driver, ko kadan Zainab bata son tafiyar mai tsawo a mota saboda zama, amman yau duk ta manta da wannan, haka suka kama hanyar Yola tafiyar awa 10 da mintuna yaran ga mai gudu, sai da suka isa wani kauye da direban ya tsaya sallah sannan ta fita ta siyo lemu da ruwa da biscuit ta saka a cikinta.
Bayan dirban ya dawo su ka cigaba da tafiyar, sallah ce kadai take tsayar da direban, be shiga yola ba sai tara da mintuna 37 da yan dakiku, be san wacece ita ba har sai da ya shiga cikin masarautar a lokacin ne ya kara tabbatar da cewar yar manyan mutane ya dauko, bayan sallamar da tai masa a tasha sai da ta kara kyautata masa sannan ta fita ta nufi cikin gidan kanta na mata mugun ciwo saboda zaman mota da kuma tunanin Auwal daya hana ta sukuni.
  A ka'ida idan tai tafiya ta dawo falon Ammy take fara shiga ta sanar mata ta dawo sannan ta wuce dakinta, amman a yau sai ta samu kanta da son wucewa dakinta kai tsaye, key dinta ta saka ta bude kofar ta shiga saman gado ta sauke komai sannan ta shiga bandaki ta watsa ruwa tai alwala ta fito ta gabatar da sallah, bayan ta sallame ta dauko wayarta ta kira kawarta Imaan.

“Imaan kin ji Auwal ya rasu?”

“Eh Wallahi haka na ji, yau kwana biyu gobe ake sadakan uku, kin je?”

“Aa bana gari yau na dawo amman dan Allah ki zo gobe da safe ki rakani mu je”

“Okay Allah ya kai mu, Amina an yi rashin miji Allah sarki Allah yai masa rahama”

Sai da Zainab ta runtse ido hawayen dake idonta suka zubo sannan ta bude tana masa mata da.

“Ameen”

Ta sauke wayar bayan ta katse kiran, tana jin wani sabon kuka na taso mata, domin ba kawarta kadai tai rashin miji ba har da ita. Shigowar Iya dakin yasa Zainab ta mike tsaye ta isa gaban tissue ta yaga ta goge hancinta da idonta. Iya ta zauna bakin gadonta tana kallonta ko bata fada ba ta san ba wai wuce kuka mutuwar Auwal ba.

“Ban yi zaton na waje ya raina ni ba ke ma kuma ki raina ni taya zan ce kar ki yi abu, amman ki tsalle ki tafi ki aikata”

“Iya dan Allah mu bar maganar nan, ina cikin damuwa a yanzu”

“Damuwar me? Damuwarki ta kai ta wa damuwar ne?”

“Iya Auwal ya rasu...”

Da sauri Iya ta rike kai.

“Kai wayyo Allah na, mugun abu ya bi dare, yaushe?”

“Yau ake kwana ukunsa, ya tafi ya bar matarsa daya da yara uku, Allah be kaddarar mu yi aure ba”

Ta fashe da kuka.

“Allah ya jikansa da rahama, ai kara matarsa da yayansa, ya tafi ya bar musu dukiya nan da kwana biyu za su manta komai, shi ne abun da nake nuna miki kema kin kasa ganewa, jiya akan matsalarki kadan ya rage Hajiya bata mareni ba”

Iya ta fada sai kuma ta fashe da kukan munafurci, Zainab ta share hawayenta tana kallon Iya.

“Miya faru?”

Cikin kuka Iya ta labarta mata gaskiya abun da tai wanda har ya saka Ammy tace kar ta sake shigar mata a falo. Cikin muryar kuka Zainab tace

“Haba Iya miyasa zaki yi haka? Na fada miki bana son Shattima ni ban taba masa kallon miji a gare ni ba, a kullum ina masa kallon dan'uwa ne kuma abokin shawara, zuciyata bata taba raya min son sa a matsayin miji ba”

“Amman saboda haka kawai sai Ammy ta zabi wulakanta ni? Saboda ta maida ni ba kowa ba? Har makaskanciya tace min, har tana fadin wai mun kusa barin gidan nan, duk abun da nake Zainab saboda ke nake, ina son ki samu rayuwa mai kyau, ina son ko da zan mutu ya zama na tafi na barki a cikin farinciki kuma a inda za a iya kula da ke, baki da kowa sai ni ni ma bani da kowa sai ke, kin tashi babu uba, ina miki fatar samun miji mai kula da ke, yanzu haka zaki saka ido kan abun da Ammy tai? Ta wulakanta mahaifiyarki a gaban jama'ar Annabi”

Kalaman da Iya tai wa Zainab sai yasa ta ji tausayinta kuma ta kara jin kaunarta a zuciyarta, tabbas ko wace uwa tana son ganin danta cikin jindadi da kulawa, sai a yanzu ta fahimci me Iya take nusar da ita.

“Be zama lallai sai na auri Shattima zan samu rayuwa mai kyau ba, zan samu wanda nake so soon, maganar gida kuma? Ba sai an yi nisa ba, ki fara shirin barin gidan nan daga yanzu gobe, ba zan taba zama gidan da aka wulakanta mahaifiyata ba, har kika zubar da hawayenki, zan mu bar gidan nan bari na har abada, tabbas be dace Ammy tai miki haka ba, har Shattima be kamata ya kyale Ammy ta fada miki haka ba, zamu bar gidan mu koma gidana da yake million quarter's”

Iya ta kalli Zainab hankali tashe, domin ba tai tsammanin Zainab zata kawo wannan tunanin ba na barin gidan, ta fada mata haka ne saboda Zainab tai zuciya ta janyo soyayyar Shattima.

“Aa ai ba korarmu tai ba, ta bar mu mu raba ne, ni bana son barin gidan”

“Idan ke ba zaki tafi ba, ni zan tafi, daman ba ni da kowa sai ke, idan kin guje ni zan zauna ni kadai, daman na rasa Auwal miya rage min to?”

Ta fashe da kuka, Iya kam sai duk ta ji babu dadi, domin ba barin gidan tare so ba, gashi kuma kilu ta ja bau.




SHATTIMA POV.

Ya saki labulayen falon tare da juyowa yana kallon Ra'ees.

“Baba Waziri yayi hakan ne kawai saboda kyautatawa, ban isa na ce masa aa ba, yarinyar ma dazun ta kirani tana kuka wai ita tana so na amman akwai wanda suka dade tare, kar na raba su dan Allah nace na fasa”

Ra'ees ya sauke ajiyar zuciya yana kallon abokinsa.

“Tana tsoro ne kawai, kuma tana da gaskiya, ni da zaka yarda da ka je an maka qukiya, ba zaka rasa aljana mai aurenka ba Shattima”

Shattima yayi murmushi.

“Ko maciji bana jin zai iya rabar jikina saboda addu'ar da nake balle kuma wani aljani ko aljana, ni abun da yafi damuna ma transfer nan”

“Gaskiya kam zamu yi missing, amman ni shawarata ka nemo wata kawai idan baka son Maijidda”

Ya dawo saman cushion ya zauna tare da daukar ruwan dake cikin gora ya zuba a kofi ya sha.

“Ni yanzu ina da zabin wacce nake so ne? Kasan lamari ne fa sai dai wacce zata taimaka ta aure ni kawai, and zan nemi transfer din, sai na sulale nai tafiyata, hutu zan dauka na bar kasar nan for a while, kamin na dawo na san Baba Waziri yayi fushi ya fasa zancen aure, sai na ci gaba da aikin a can Yola kamar yadda ya bukata, domin bana son saka yar sa a matsala Wallahi”

“Gaskiya kam dan lamarinka azimun ne Shattima, ni Wallahi har tsoro nake”

Shattima ya kalleshi yana murmushin kasaita.

“Baka fada min ni kaje nemawa aure ba, kana ta boye boye Ammy ta fada min ai”

Ya karasa still smiling, sai kuma ya kalli ceiling kamin ya sake kallon Ra'ees yana murmushi.

“But ka san me? Yarinyar nan ta burge ni, bata da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login