Showing 87001 words to 90000 words out of 286946 words
motar ya rufe masa motar. Reverse Shattima yai sannan ya hau titin unguwar har lokacin murmushi ne a fuskarsa zuciyarsa cike da nishadi. Sai da ya kama hanyar airport sannan ya kalli Fadime ta madubu har lokacin kuka take da gaske gasken domin ko kadam bata jidadin rasa Ra'ees da tai a rayuwarta ba.
“Me kike yi ma kuka?”
Ta dago jajayen idanuwanta ta kalleshi hawaye na mata zuba kamar ruwa.
“Ba kaji me yace ba, nai hakuri ya fasa fa kenan”
Samun kansa yai da wani murmushin yana kallonta ta madubun gaba sai dai ita din bata sani ba idonta be ma kai kan madubi ba kuka kawai take, ta dayan bangaren tana blaming Wasim domin shi yaja mata komai tun farko. Kirciya da rauta kawai Shattima yake gani a fuskarta domin yana da irinta, kuma kana kallonta kasan yarinya ce tsawon kafafuwa ya soma janta.
“Zan bi ta airport na dauki kanwata sai na kai ki tasha, amman ki daina kukan”
Ya fada yana jin kukan da take rerawa yana damunsa.
“To”
Ta amsa daker tana hade kukan, Fadime bata taba ganin airport ba sai a lokacin, a nan da nan ta manta da kuka tana ta kallon mutane da kuma manya motoci da suke kai kawo a harabar. Sai da ya faka motarsa sannan ya ciro wayarsa ya aikawa Zainab da sako cewar yana waje yana jiranta.
“Idan za a je wani kasa ake suwa Airport a shiga jirgi ko?”
Ta tambaya tana jin sanyin ac na ratsata, shi dai be ce mata komai ba, sai kallonta yake ta gaban madubin, a nan ta tuna da Inna tace tai addu'a kuma ba tai ba ta fito, sai ta duke kanta kasa ta karanta abun da ta iya sannan shafa a hankali dan kar ya gani, zuciyarta na raya mata ko dai siyar da ita zai yi ya samu nama a arha a banza, duk abunda take Shattima na kallonta.
Cikin kankanen lokaci Zainab ta iso gurin motarsa daman tun a lokacin da ta kirashi tana airport din zaune, duk da irin ciwon kan da take ji bata isa ta sake kiransa ba tasan ransa zai iya baci yace ta matsa, ba isa kuma ta tari texi ta tafi ba dan ta san zai zo idan ya zo be same ta ba ransa zai bace. Ta buga bayan motar sai ya bude mata boot boot bayan ta saka jakarta ta rufw ta zagayaon ta bude front ta shiga ta zauna.
“Welcome to KT”
Shattima ya fada bayan ta kalleta kadan ya dauke kai.
“Thank you Wallahi kaina ke ta ciwo da gefen bayana”
“Maybe zaman jirgi ne”
“Tun kan na taso nake jin ciwo”
Shattima be ce mata komai ba sai tukin motar yake. Fadime dai ya gidan bayan tana ta tunani ai ance idan masu fillar kai suka kama mutum baya iya magana right okay then bari tai magana ta ga idan zata iya.
“Barka da yamma”
Ya gaishe da Zainab sai Zainab ta juyo da sauri ta kalleta Fadime ta sakar mata murmushi yake, Zainab ta dan yamutsa fuska tana mata kallon wata yar kauye can kuma ta kali Shattima.
“Who is she?”
Kafadunsa ya daga alamar be sani ba yana murmushi.
“She's so comedian”
“I'm not a comedian”
Fadime ta amsa masa kai tsaye, daga shi har Zainab kallonta su kai, never thought tana jin turanci balle ma har ta iya maidawa.
“Can you speak English?”
Zainab ta tambaya, sai ta daga mata kai.
“Yes da kin je kauyenmu kika ce Fadime yar gidan Bapppa kowa ya san ni ce daya kawai, saboda ni na iya turanci idan aka kawo wasika a garin gurina ake zuwa na karanta, idan wani bako ya zo ni ake kira na masa turanci idan baya jin hausa, duk garin Bandalo babu yarinya mai jin turanci irina, Bappa ya sani makaranta tun ina karama kuma yana biya kullum idan zai je Kaita da ni yake zuwa idan mun tashi sai na jira shi ya gama cin kasuwa sannan mu dawo, har aka fara barayi sai aka rufe makarantarta gaba daya, yanzu mun daina zuwa amman ban manta komai ba na iya ina jin komai”
Tun da Fadime ta fara bayani bata tsaya ba sai da ta kai aya, irin yadda ta ga duk sun kalleta yasa ta jidadi ba abun da take so a duniya kamar aji ta iya turanci ita ma. Zainab ta saka hannu biyu ta dafe kunnenta.
“You are so talkative.. Haba.... ”
“Let her be she entertained me”
Shattima ya fada yana murmushi, yana ganin ganin lokacin da Fadime ta murgudawa Zainab baki ta hararenta kasa kasa, tana daga ido suka hada ido ta madubin sai zaro ido alamar ta ji kumya tai saurin rufe fuskarta da tafin hannayenta. A nan ma Shattima murmushi yai he don't know why take burge shi? It's because ta saka Ra'ees ko kuma because she's silly girl? Har yanzu ya kasa daina murmushin abun da Ra'ees yai, and she's pretty kana ganinta ka ga fulani shi kuma yana son haduwa da yarensa, daman can ya san yaran fulani akwai wauta. Ba tare da ya kalli Zainab ba ya ce
“Gidan Hajiya a Mutu zan kai ki”
“No bana son zama gidan Hajiya a Mutu ka sani”
“Ba zai yiyu na kai ki gidana ba”
Ta kalleshi.
“Why?”
“Kin san ba zai yiyu na zauna dake a can ba daga ni sai ke”
“Amman saboda na sauka a inda kake ne yasa na fada maka na zo, if ina son zama a gidan Hajiya Matu zan sauka a can ne kai tsaye”
Uffan be ce mata ba ya cigaba da tukinsa. Fadime kan mamaki ya ishe sai tunani Zainab take a ranta
‘Daga gani yar iska ce shiyasa tace tana son ta kwana a gidansa, Allah sarki shi na kwarai ne shiyasa babu ruwansa’
Tana kallon ya faka motarsa gefen titi kusa da wani mai siyar da kaji ta hade yawu. Mutumen ya zo da sauri.
“Guda biyu daban daban”
Mutumen ya juya ya koma da sauri ya cire biyu da suke kan wuta ta sarasu ta saka a leda dabam dabam ya nufo Shattima. Kamin ya karaso Shattima ya sauke gilashin baya ta inda Fadime take ya masa nuna da ya bata. Cikin girmamawa mutum ya mika mata Shattima ya mika masa 5k sannan ya matsa gaba daya yai horn mai shagon ya zo da gudu.
“Kana da yoghurt?”
“Eh akwai ta Alhaji”
“Kawo daya babba”
Mutumen ya juya da sauri be dade ba ya dawo da yoghurt din a leda nan ma Shattima gilashin baya ya bude aka mikawa Fadime.
“Na gode Allah ya biyaka”
Ya fada tana karba da hannu biyu, sannan ya rufe gilashin ya juyo ya kalleta.
“Ina ne garinku?”
“Bandalo”
Ya dan yi shiru alamar tunani kamin yace.
“Ina ne Bandalo?”
“Yana cikin Kaita”
Zainab ta juyo ta kalleta sai kuma ta kalli Shattima.
“Garin da zanje ne fa, yana cikin Kaita ai, a kusa da garin akwai wani Kauye ma da nake son zuwa Garuk”
Fadime ta zaro ido
“Na san garin ai ina da... ”
Har zata ce saurayinta sai kuma ta tuna.
“Dan'uwa a can dan'uwana ne, mutanen garin ma basa saka tufafi”
“Yes yes yes and garin ku akwai bukkoki ko?”
“Eh kowa yana da bukka ma a cikin muke kwana, har da shanu ma ni ma ina zuwa kiwo ai, daga can garin muka zo neman wani tare da kishiyar Inna ta, amman wai sai wasu mutane suka ce wai mayyace wai ta kama yaro, suka fara mata duka”
“To yanzu ina take?”
Zainab ta tambaya
“Tana can na barta hannunsu ni gudu mai kar ace nima mayya ce, na yi karya na ce ban santa ba naji ana cewa mijin matar police ni kuma na gudu nace ni ma ban santa ba, kar a laka min Maita”
A nan ma Shattima murmushi yai, Zainab tai fuskar mamaki.
“Minene maita kuma?”
Fadime tai shiru, ita ma dai taji ana cewa maita ko mayu bata san minene shi din ba if ma zata fada bata san yadda zata bayyana ba.
“How old are you?”
Nan ma bata cewa Zainab komai ba, sai hadiyar yawu take tiririn kaza na sauka a cinyarta.
“Zaki kai ni garin na ku har ma da can garim Garuk din?”
“Eh Babana shine sarkin fulani yankin yamma na Bandalo”
Murmushin jindadi Zainab tai dan ya kwana mata gidan sauki, ga yar gari ta samu wacce zata mata jagora.
“Sunana Zainab, I'm photographer daman zuwan da nai a nan zan dauki hotona ne kin san masu daukar hoto suna daukar abubuwa kala kala saboda samun Cigaban sana'arsu, an fada min mutanen garin Garuk ba su yarda da cigaba ko wane iri, ku kuma kuma da bukkoki wanda ba kasafai ake samun ba, wannan dalilin yasa na zo tun daga Yola dan na dauki hotuna”
Fadime ta gyada kai alamar gamsuwa.
“Ashe ke ma kina da surutu”
Ba karamin haushin maganar Fadime Zainab taji ba, amman ba zata iya nuna mata ba tun da tana son ta taimaketa. Shattima kan murmushi kawai yake yana kallon Fadime cike da burgewa, sannan ya juya ya ja motar suka hau titi.
“To yanzu ya zamu yi?”
“Ki bini muje garinmu sai na kira shi ya kai ki har garinsu daman ban taba zuwa ba”
“No ki kwana a nan gobe sai muje garin na ku”
“Aa na san hankalin Inna zai tashi idam bata gan ni ba, ni gida zanje, kuma Bappa na ai zai iya dukana ma”
“Okay zaki bani addirenshi idan na shirya sai na same ki a gari?”
“Eh”
Zainab ta dauko wayarta ta rubuta address din da Fadime ta fada mata sannan ta aje wayar ta bude jakarta ta dauko 2k ta mika mata.
“Gashi na gode”
Fadime ta bude ido.
“Da gaske?”
“Yes take it”
“Thank you”
Ta fada tana karba cike da far'a. Har tasha Shattima ya kaita ya ciro 5k ya mika mata.
“Za ki iya gane garinku ai ko?”
“Eh kai ina ganewa fa”
Ta bude motar ta fita cike da murna ga kazarta har biyu a leda da yoghurt ga kuma 7k hannu. Ta nusa kai cikin tashar ta nemi motar Bandalo, cikim sa'a ta samu har ta kusa ciki sai dai a motar akwai yan kaita akwai yan kuma wadanda za a kai Bandalon kai tsaye. Sai da motarsu ta tashi sannan ta fara tunani ko Amo ta wuce ko kuma tana can? Kila ma ta riga ta isa gida gashi har kwayar manshanun nata an fasa.
AA POV.
Yawon gararanba yai ta yi da ita cikin gari har lokacin tashinsu daga makaranta ya kusa sannan ya faka gaban wani karamin restaurant dan siyen abun da zai sakawa cikin ganin yunwa na kokarin hanashi sukuni.
Har ya fita sai kuma wani tunanin ya zo masa sai ya dawo cikin motar ya kalli Nana.
“Zan ranta kudi na siyo ma kaina abinci idan mun koma gida sai ki bani”
Nana ta watsa masa harara.
“Lallai ma kato da kai zan ciyar da kai, dan can da wake baka abinci?”
“Amman kin san yanzu karkashinki nake aiki ai, haba karki canja daga halinki na kirki mana, Allah kadai ya san irin ladar da kike samu na wannan aikin da kike ni fa maraya ne ki tuna wannan, Manzon Allah yasa wanda ya taimaki maraya ni da shi kafada da kafada zamu shiga aljana ba kya son wannan ladar ne?”
Yadda ya marairaice mata sai ka rantse da Allah kuka zai yi, yadda kasan wanda ya rasa gabas ya rasa yamma haka ya marairaice mata fuska. Sai duk taji tausayinsa ya kamata.
“To je ka siye”
“Na gode Allah ya saka miki da alheri”
Ya fita ransa fes ya shiga restaurant din ya siyo rabin kaza da jalop mai kyau da lemu sai kuma ruwa kusan 7k ya kashe sannan ya fito rike da takeaway din ya bude motar ya shigo ya zauna.
“7k na kashe”
“Ba matsala”
Ta fada tana tunanin hanyar da zata bi ta samu kudi. Jan motar yai suka shiga wata sabuwar unguwa dake kusa da gurin wacce babu mutane sosai sannan ya faka motar da yake jinta kamar tasa ya bude abincin yana ci.
“Allah dai ya biyaki Hajiya, Allah ya kara miki lafiya da imani kuma ya kara miki tausayina”
“Amin”
Ta amsa tana kallon gefen titin gana daya hankalinta yana wajen yadda za a yi ta samu kudi. Gashi Hajiya Karama ta yi tafiya yau balle ta roke ta kudi Shattima kuma be nan ko ma yana nan Baba Waziri ya musu fada cewar karsu sake bata kudi. Mafitarta a yanzu Sirleem ne ko Hajiya Babba.
Sai biyu har da yan mintuna sannan ya dawo da ita gida, bayan ya faka motar a inda aka saba ajeta ya juyo ya kalli Nana.
“Hajiya nace zan iya daukar motar na shiga gari da ita? Ba kullum ba irin wani lokaci haka kin san akwai mahassada saboda su gani su ji zafi”
“No ba a bari”
Yayi shiru yana kallonta har ta bude motar ta fita, sannan shi ma ya fita ya rufe motar ya kama hanyar gida, yana ta tunanin dalilin na kin son makaranta bayan kuma ya san karatu shine gaba da komai musamman yayan manya basa wasa da karatu amman ban da ita why? Can kuma wata zuciyar tace masa ko ma dai minene ina ruwansa tun da an dauke shi aiki sai a lokacin ma ya tuna ya kamata yai mata maganar kudin achaban da yake hawa idan zai zo da kuma komawa, dan ba zai yiyu ace shi yake biyawa kansa ba.
“Wallahi yarinyar nan shi ake cewa tsuntsu daga sama gassashe, Wallahi bata da wayo”
Ya fada yana dariya tunawa da ya ranta mata kudi ya siye abinci a dazun.
**
Jaka rike a hannu ta shiga falon Ammy sai dai ta tarrarda da ita da baki hakan yasa ta na gaishesu ta shige dakin Ammy ta rufo kofar ta aje jakarta da sauri ta nufi dorowar da Ammy take aje kudi ta bude, bata ma tsaya kirgawa zarowa kawai tai ta saka a jakar makarantar ta juyo ta fito daga dakin. Da ido Ammy ta bita har ta bi corridor da zai sadata da dakinta, ko ba a fada mata ba ta san wani abu ta daukar mata dan bata shigar mata daki haka nan kawai bayan kuma gata a nan zaune, yanayin yadda ta fito ma kadai ya isa ya sanar mata cewar akwai abun da tai a dakin.
Sai kusan uku Ammy ta sallami bakinta, sannan ta tashi ta shiga dakin, kai tsaye gurin durowar ta nufa tana budewa ta daga littafin dake sama ta gane Nana ta taba kudin, wani abu ta ji a tsoketa a kahon zuciyata ba dan kudin da ta dauka ba sai dan halin bera da ta tsirarwa kanta.
Hajiya Babba ce ta shigo falon cikin wani irin taku na kasaita da isa sai kallon hadiman dake falon Ammy take a hankade kamin ta kalli Falmata wacce ke tsaye goye da Luma tana kallon tv. Kowa ya gaishe ta ban da Falmata wacce hankalinta ke kan tv gashi bata ji sosai balle tace taji suna gaisheta har ta san da shigowarta.
“Ita wacan wace isasar ce da ba zata risina ta gaishe ni ba?”
Hajiya Babba ta fada tana watsa mata wata banzar harara. Jekadiya ta ce.
“Bakuwa ce sabuwar mai rainon su Labib ce, bata ji sosai ayi mata afuwa Hajiya”
Jekadiya ta mika hannunta ya ja zanen Falmata tana nuna mata Hajiya.
“Falmata gaishe da Hajiya”
Da sauri Falmata ta sirina tana gaishe ta amaimakon ta amsa sai ta dauke kai ta nufi hanyar dakin Ammy hannayenta rumgume a baya tana wani irin taku kamar wacce ba zata mutu a rufe da kasa ba. Bakin kofar dakin ta tsaya tana dan saurare ko zata ji Ammy na wata magana bata ji komai ba sannan tai knocking.
“Shigo”
Ammy ta fada muryarta a sanyaye kana ji ka san akwai damuwa a tare da ita. Hajiya ta tura kofar ta shiga cikin jindadin yadda ta samu Ammy da damuwa duk kuwa da kasancewar bata san minene matsakarta ba, amman tana jindadin ta ganta a damuwa ko cikin kunci. Sai da tai Bismillah sannan ta zauna tana kara kallon Ammy da kyau dan fahimtar damuwarta.
“Ya gidan?”
“Al-hamdulillah”
“Daman na zo ne akan maganar auren Rukaiya”
Ammy ta dago kai tana fuskantarta jin ta ambaci yar minitan aiyuka da za a aurar.
“Na san kusanci Alhaji Nasiru da na Mai Martaba kusanci ne sosai wanda da ace Mai Martaba yana da lafiya shi zaije da kansa ya bada auren yar aminsa, amman haka Allah ya tsara shine nake tunanin Talba sai wakilce shi yaje yai komai kamar Mai Martaba”
Wani kallon mamaki Ammy take mata.
“Wane irin Talba kuma? Ga Waziri ga Jarma ga Ubandoma ga Lado duk a rasa wanda zai wakilci Mai Martaba sai Talba? Aiko ko Shattima yai karanta balle kuma Talba da yake kannensa”
“Ai dan na ga Shattiman baya nan ne yasa na yanke shawarar kanensa ya wakilce shi”
“To gaskiya ba zai yiyu ba, mun riga mun gama magana da Waziri shi zai je ya wakilci mai martaba”
Ammy ta fada kai tsaye, daman can haka take duk abunda akai a gidan wanda take ganin be dace ba zata fito tai magana idan kuma shawarace Hajiya ta kawo ko wani shi ma idan ta ga be yi ba zata hana ko tai magana, wannan dalilin ne yasa Hajiya take mata ganin tana mulki mallaka a gidan kuma ta mallake Mai Martaba, domin lokuta da dama zata kawo shawara idan Ammy ta ga abun be dace ba zata hana ko kuma ta kawo tata shawarar kuma sai Mai Martaba ya bi, domin yana son Ammy sosai kuma yana kyautata zaton ba za yi wani abun na son kai ba. A can baya babu yadda Hajiya bata so akai Rima kasar waje karatu ba amman Ammy ta hana saboda kula da wasu halaye na banza da Rima ta tsira tun a nan, take ganin idan aka kaita can karatunta zai lalace ne haka ma rayuwarta kara dai tai karatun a nan inda ake ganinta ake saka mata ido kuma ayi mata fada idan tai ba daidai ba tsabanin can da babu mai tsawarta mata. Sai dai wannan abun ya tsayawa Hajiya a rai duk kuwa da kasancewar an kai Jurry sai take ganin kamar Ammy bata son cigabanta ne ganin ita ta haifi biyar ita kuma tana da biyu shine take mata hassada.
Dan murmushi