Showing 3001 words to 6000 words out of 286946 words

Chapter 2 - Fulani Book 1 Hausa Novel Complete

20 Dec 2024

889

mata kudi ba, ba wai duk abunda aka ba ki za ki bata ba, albashin ma rabi za ki bata ki boye rabi, dan alherin idan kin samo karki kuskura ki bari ta gani, ke abinci wannan ma da ki kawo mata Wallahi kara ki ɓarar dashi a akwata"

Har wani yatsine fuska Khadija take tana jin kamar ace ita ce a matakin Falmata take da step mother kamar Tumba da Allah kadai ya san irin sherin da zata kulla mata.

"Mahaifina yace idan ban mata biyayah ba be yafe min ba, ko da ace bata san yawan kudin aikin ba zan bata dika balle kuma ta riga ta sani, idan ma na hana ta zata iya duka ko taja Baba da kansa ya doke ni, ba ni da wani yanci a gidan nan Khadija kin sani"

"Hmm ai har da ke Wallahi da kike biye mata, ke ko yar ketar nan ba ki iya ba, Wallahi da ni ce da sai ta sha wuya, shiyasa na tsani shegiyar matar nan bakar Tumba kawai"

Falmata da dai bata ce mata komai ba, ta cigaba da tafiyarta, sanin kanta ne idan zata ce Khadija ta daina kiran Step mom dinta gatsasa sau hansin sai Khadija ta aikata sau dari biyu.

"Ki duba ki ga fa saboda ki Wahala ta tura ki aiki a gidan, ga yayanta, kuma wai dan tsabar zalinci tace ita zata karbe albashin, bayan babu abunda take tsinana miki"

Tafiya suke Khadija na jifar Tumba da kalamai marasa dadi, Falmata dai bata ce mata uffan ba har suka raba hanya, kowa ya dauki hanyar gidansu. Da sallama ta shigo cikin gidan amman aka rasa mai amsa mata kamar masu gaba da ita ko kuma wadanda ba su ji sallamar ba.
Ko kadan hakan be dame ta ba, inda da sabo kusan ta saba da wannan rayuwar. Kallo daya tai ma Naja ta dauke kai ta hade wani abu daya tsaya mata a makoshi, yar gata kenan masu yin yadda suke so a gida ba kamar ita ba, wacce aka hana wanke surfen da ruwan da ita da kanta tai aikin jigilar debo su da safe, an bar yar gaban goshi tana wanki da su.

Sai da ta sauke ruwan sannan ta nufi gurin da surfen yake ta dauko ta wanke, ragowar ruwan ta juye a karamin bokiti ta shiga bandaki tai wanka, dakinsu ta nufa ta shafa mai abun ka da mai son kwaliya sai ta dauko ragaggin kayan kwaliyarta ta tai kwaliya har da su jan baki. Ta yi kyau sosai duk kuwa da kasancewar ta baka sai dai bakin be rage ta da komai ba daga kyaun sura kwarjini ta halitta da kuma cikar sura da zati irin na ya mace. Baka ce amman ba mummuna ba, baka ce kyakkyawa irin kyau ne mai shining. Bakinta mai kyau ne wanda ya kara fito da manyan idonta kuma farare tas, sai dai bayan ido da hakora da tafin hannunta da na kafa babu sauran wani gurin da fari ya bayyana a jikinta. Yana daya daga cikin dalilin da ya saka Falmata bata sha'awar saka bakin kaya, domin ganin take ita da tufafin za su saje ne.
Bayan ta gama shiryawa ta mike tsaye tana cigaba da kallon kanta a madubi kamin ta maida dan karamin madubin a mazauninsa da ke cikin kayan kwaliyarta.
Tsakar gidan ta fito ta nufi kitchen dinsu ta dauko abinci da ke rufe a langa (Kwano) ta zauna jikin kitchen din ta soma ci tana ta kallon awakin gidan da ke ta aikin kuka suna fada da junansu, sun ɓata turkensu sun masa kacha-kacha kamar ba dazun ta gama gyara shi ba. Can kuma ta maida dubanta gurin mayan shanun da ke daure guda biyu a gafen garken awakin.

"Idan kin gama ki taso ga surfen masarar nan ki surfa ko tiya daya ne"

Kam ta gama cin abinci Tumba tai mata furucin, a take yanayinta ya canja tai narai narai da ido kamar ta fasa kuka.

"Umma ba kin ce sai gobe ba?"

"To masu masarar yau suke son abunsu, kuma da safe ai sai dabobi su samu abunda za su ci"

Kalma daya idan ta kara fitowa daga bakinta ta san ba zata sha da dadi daga hannun Tumba ba.
Bata da wani zabi da ya wuce ta gama cin abinci ta taje tai surfen kamar yadda ta umarce ta. A hankali tai ta cin tuwon marar har ta gama ta tashi ta nufi gurin butarda ke gindin ice ta wanke hannunta sannan ta nufi gurin da masarar take ta dauka ta bude turmi ta fara surfawa. Tsakanin fara surfen da sallamar Maman Baby makociyarsu ba zaka iya tantance wanda ya riga wani ba. Tumba da ke tsakar gidan ta amsa sallamar tare da kallon Falmata da sauri.

"Kina da son wahalar da kai Fulani, ina ke ina surfe da tsakar ranar nan? Dan Allah ki aje har zuwa anjima ko kuma idan Naja ta gama wanki sai ta surfa"

Kallonta kawai Falmata tai ta sadda kanta kasa ta cigaba da surfen.

"Aa zan iya"

Sai kuma ta fada kasa-kasa idanuwanta na cika da kwalla, haka take mata a duk lokacin da wani ya shigo gidan ko kuma idan a gaban mahaifinta ne. Kowa a unguwar ya shaidi Tumba akan kaunar da take nunawa Falmata agaban idanuwansu, wani lokacin har da ita ake bada kwacen matar uba wacce ta rike yar kishiya da amana.

"Oh Tumba ikon Allah, ke dai ba ki kaunar ganin Falmata tana aiki"

Cewar Maman Baby tana dariya.

"Mahaifiyarta amana ta bar min ita, idan ina ganin tana wata wahalar sai na rika ganin kamar na ci amanar mahaifiyarta"

Daga inda Falmata take tsaye tana surfen ta dago manyan idanuwanta masu kamar madara ta kalli Tumba wacce ta shantake da makociyarta suna fira ta sadda kanta kasa ta cigaba da surfe idonta tab da kwalla...!

FADIME POV.

Katsina State...

Shanun na gaba ita kuma tana biye da su a baya tare da karenta, hannunta rike da yar karamar sandarta ta dukan shanun, tana sanye da tufafin riga da zane na fulani gashin kanta a cinkushe. Sosai hankalinta yake akan ko wace shanuwa da ke gabanta, zuciyarta cike da fargaba da zullumi irin wanda ya saba ziyartar a duk sa'in da ta fita da shanun. Ba ta natsu ba har sai da ta isa da shanun a gurin da ta saba tsayawa da su, sannan ta nemi guri ta zauna saman wani karamin dutse ta zuba musu ido.
Haka take wuni a cikin tashin hankali da fargaba a duk lokacin da mahaifinta ya tura kiwo, ba tsoron kiwon take ba, ba dan bata saba ba, sai dan fargabar abunda zai samu shanu a duk lokacin da ta fita da su.
Ba kasafai take zuwa kiwo ta dawo da shanun lafiya ba, wani lokacin a hanyar tafiya wata zata mutu, wani a hanyar dawowa wani sa'in ma har sai ta iso gida.
Tun shanun suna arba'in da uku har sun dawo sauran goma sha bakwai.
   Mikewa tai tsaye tana kallon wata bakar mage mai jajayen indanuwa, wacce ke tsaye saman dutsen da ke gabanta, ba yau ta saba ganin magen ba, kusan kullum idan ta fita kiwo sai ta ganta, tun tana tsorota har ta daina, sai dai su yi ta kallon kallo ita da magen, sai dai a duk lokacin da tai arba da magen sai tsigar jikinta ta tashi, tsakanin ita da magen aka raba mai daukewa wani ido, ba m kamar magen da ke kyakar hakora.
  Can dai Fadime ta nemi guri ta zauna ta dauke kanta daga kallon magane da take, ta maida hankalinta gurin shanunta.

WASIN RAU POV.

As usual, yau ma sai da hasken rana ya fara haska kyakkyawar fuskarsa sannan ya bude idonshi a hankali yana kallon birds din dake saman icen suna rera masa waka kamar yadda suka saba a ko wace safiya.
Lumshe ido yayi sai kuma murmushi ya biyo baya mafarkin da yai yake kokarin tunawa, jinke hannunsa yai gam yana maida numfashi a hankali tare da dantse hakoransa.
Kamar an tsikareshi sai kuma yai saurin bude idon yai hanzarin saukowa daga kan icen ya doro kasa, jikinsa ya girgiza har sai da kowace gaɓa ta jikinsa ta motsa.
Babu riga a jikinsa sai dai hakan be hana shi jin zafi ba, duk kuwa da irin tsananin sanyin da ake kasancewar yanayin safiyar yau a akwai hadari da ya karade ko'ina a sararin samaniya.
For the first time a yau yaji a kasa yake sha'awar yin busar sarewa abunda be taba ba, a kowace safiya a saman dutse yake yin busarsa mai dadi saurare da kawarda duk wata damuwa. Jingina yai jikin icen ya ciro sarewarsa ya kafa bakinsa ya soma busar cikin kwarewa da shauki, a take duk dajin ya dauka, yanayin haduwar hadarin da kuma busar sarewar, da iskar da ke kadawa sai ya bada wani kalar yanayi na musamman wanda ko wace irin halitta zata so kasancewa a ciki. Sai da yai busar ya gama sannan ya kai hannunsa a gefen walkin da ke jikinsa ya kwance wata yar karamar jakar tsaba ya bude bakinta ya zubo hatsin da ke cikin jakar a hannunsa ya watsawa tsuntsaye a kasa, a take suka sauko kasa suka baibaye gurin suna ta cin tsabar har wasu na hawa kan wasu, kallomsu yake suna cin abinci har sai da idonsa ya gundura da abincinsa sannan ya juya ya kama hanyar shiga cikin burninsu.
   Safiya ce amman kowa hada hadarsa yake, kai tsaye ya wuce cikin fadarsu, gaba dayan mutane da suke cikin fadar babu mai tufafi kowa walki ne a jikinsu, fuskarsu babu annuri kamar sun yi arba da mutuwa.
  Kafarsa ya kai kasa dayar kuma ya gurfana da ita ya sirinar da kansa ya gaishe da mahaifinsa. Da mafecin da ke hannunsa ya daga ya dora masa a kai alamar ya amsa gaisuwar sannan ya mike tsaye ya nufi cikin gidan sarautar mai kamar wani karamin burni.
  Ta wani bangaren ruwan korama ne ke da guduna ga shukoki a gefenta daga can nesa da shukokin kuma wasu manyan itatuwan ayaba ne, idan ka tada kanka ka kalli gabanka kuma ginar kasa ta zakanin da irinnta kaka da kakkanin, wacce aka kawata ta da fatar damisa wani gurin kuma an kawata shi da gashin tsuntsaye kalakala da suke cikin dajin.
  Masarautar GARUK babban masaurata ce mai karfi tsafi, tun daga kakannin har jikoki su ba su yarda da cigaban zamani ba, a duk inda za su je a duniyar nan sai dai su taka a kasa ko su yi tsafi ko su hau wani abun hawa daga dabbobinsu ya kaisu, fita su bar garin ma abu me mai wahala, ba kasafai yam garin ke nesa da garin ba saboda yanayin rayuwarsu da kuma suturarsu, kamar yadda ganganci ne wanda ba dan garin ba ya kawo ziyara a garin ba tare da sanin wani a garin ba. Yawancin abincin mutanen garin yayan itatuwa ne sai alkama danyar kwakwa.

ZAINAB HAJIYA KARAMA POV.

Yola...

Kadan ta kurba tea da ke gabanta ta aje karamin kofi a hankali sannan ta tattara dukannin hankalinta da natsuwarta ta maida akan laptop din dake gabanta.
Hotunan da ta dauka jiya take kokarin gyarawa, tunanin yadda zata banbanta su da sauran take, domin a halin yanzu bata da wani buri da tunani da ya wuce ganinta a matakin da kowa be taba kaiwa ba, tana bukatar sabuwar idea.
Tunani take tana wani tsuke karamin bakinta, tare da dora kafa daya saman daya. Wayarta ta dauko  ta kunna data, ba da niya ba ta shiga whatsapp, da gangan ta duba sakonin da ake aiko mata na dan ta bada amsa ba, ta saba halinta sai ta bude sako ta bar shi a bude ba tare da ta mayar da amsa ba, ji take ta isa da hakan, kuma ra'ayinta ne dole kowa ya bi.
  Kai tsaye ta nufi status, sai da ta fara duba adadin mutane da suka duba nata status din wanda ta saka sannan ta fara duba na mutane.

“Wow.......”

Ta furta tana kara zooming wani hoto na wani namiji tare da matarsa da yayansa biyu.

“Amman mijin nan na ki ya hadu fa”

Ta kara duba hoton da kyau da sauran hotunan da suke biye da shi duka na miji wani guri da yaran wani gurin ita da shi wani gurin kuma shi kadai, sai a lokacin ta lura da matar ta goge hoton ma, sai ita a gurinta be gogu ba saboda tana using GB whatsapp.

“Happy anniversary dear zan zo cin cake”

Ta rubuta mata sannan ta shiga wani sashen tai saving hoton. Wata Dattijuwar mace ce ta shigo dakin tana daure da zane kanta kuma ya yafin atamfa kalar zanen da ke jikinta.
  Ganin matar yasa Zainab kara relaxing akan kujerar tana wani lankwafar da kai.

“Iya..... ”

“Kyakkyawa, kowa yana can yana karyawa ke kina nan”

“Iya inata tunanin abunda zan yi this week na haska duniya, kuma na amsa sunana na photographer, ina da mabiya miliyan uku da rabi a media, ina yan hamayya ya kamata ace na hara kura na daga musu hankali, kin san mu photographers kullum burinmu mu dara kowa”

Ta karasa tana kai kafarta ta tana wata karamar camera dake gabanta da kafartata. Iya ta yi murmushi irin nasu na manya, sannan ta lasa bakinta ta dan daga jajayen idanuwanta kadan tana kallon Zainab tace.

“Na fada kullum idan kina bukatar wani abun, ki rika kiran yayanki, shawara kike bukata ko wani taimako ki rika fada masa”

“Iya kin san baya son waya mai tsaye ne, kuma baya gari balle na same shi mu yi magana”

“Yana gari be dai shigo gidannan ba”

Da sauri ta tashi zaune tana kallon mummunar fuskar Iya.

“Ya akai kika sani?”

Iya ta yi dariya.

“Kina wasa Zainab, sirrin masarautar nan a hannuna yake, sai ki rika abu kamar a nan aka haife ki ba, ni na fada miki Omar yana cikin garin Yola”

“Idan hakan ne, ba shi da amfani tun da baya bukatar shigowa cikin gidan nan....”

“Kira shi ki fada masa dansa Labib, be da lafiya”

“Ba zai jidadi ba idan nai masa karya”

Ta fada tana dan turo baki tare da komawa jikin kujerar ta kwanta.

“Ni kuma mahaifiyarki sai nace ki yi karya? Da gaske ne dan sa be da Lafiya, bari na dauko miki shi yanzu nan”

Iya na fadar hakan ta juya ta fice daga dakin, sauka tai kasa gaba daya downstairs, ta nufi wani bangare na masarautar, a tsakanin bangaren da ta nufa da kuma wanda ta baro yayi nisa wata karamar unguwa zuwa wata.
  Da kanta take tafiya hadiman gidan nata aika mata gaisuwa ita ko tana amsa musu baki har kunne, haka take da kowa fatfat kusan ta fi kowa far'a gidan.
  Sai da ta fakaici idon mutane sannan ta shiga garken dawakai tana tambayar mai gadinsu.

“Yau ka duba su kuwa?”

“Ranki ya dade duba su kuma ai dole ne tunda shine aikina”

Ta yi murmushi.

“Hakan na da kyau bari na duba dokin Babban mutum.... ”

Haka take kullum sai ta fake da sai ita da kanta zata duba dokin ba dan komai ba sai dan ta samu damar shiga ciki, cikin gurin ta shiga tana takawa ahankali tana duba dokuna kamar mai duba lafiyarsu, har ta isa gaban wani farin doki wanda ake kebe can shi kadai aka zagaye shi da katako, bude gurin tai ta shiga, ta kai hannu ta shafa dokin wanda kusan ya saba da ita, sannan ta duka kusa da shi ta fara tonon kasa, wasu abubuwa da fiddo guda uku dane a cikin zare, na tsakiyar ta matsa sai kuma taja zaren da karfi.
  Daga inda take ta jiyo kukan Labib a kunnuwanta, da kuma maganar Nana wace ta tsorota da yadda yai kyalowa ta nufo shi tana ambaton Allah. Cikin saurin ta mayarda kulolan ta rufe ramen ta nade hannunta cikin zanenta gudun kar a ganshi da kasa sannan ta fito daga gurin.

SHATTIMA UMAR....

YOLA...

Kofin tsamiya ne a hannunsa, dayan hannunsa kuma rike da lemun tsami yana matsawa a karamin kofin, farar singilat ce jikinsa sai farin tawul din da ke daure a ƙugunsa, fafaren kafafuwansa kuma sanye da takalminsa na bedroom.
Sai da ya gama matsa lemun sannan ya saka tea spoon ya garwaye lemun tsamin da tsamiyar suka hade jikinsu, a take ya daga kansa sama ya hanye, a gurin ya dire kofin ya mike tsaye ya nufi bathroom, he spent more than thirty minutes a bathroom din yana jika kansa da ruwa sannan ya fito rike da wani karamin tawul yana goge kyakkawan jikinsa, gaban madubi ya tsaya yana goge gashin kansa. Fari ne kyakkyawan gaske, irin kyau nan mai daukar hankali, bafulatani gaba da baya amman idan ba sani kai ba sai ka rantse da Allah baasbine ne ko shuwa, ko'ina na jikinsa yana amsa sunansa na namiji kamar yadda muryarsa da siffar zatinsa take haska surarsa. Wani farin mai, mai sanyi ya dauka ya shafa a hannunsa ya murza sannan ya shafa shi a jikinsa, kana ya ware hannayensa yai mika, wacce ta sanarwa dukan jikinsa.
  Wayarsa da ke kan gado ce tai ringing, sai da ya kwance tawul din jikinsa sannan ya nufi wayar ya dauka.

“Nana”

“Na'am Labib ba Lafiya yana ta ihu”

“Waya taba shi?”

Ya tambaya sanin cewar daman can ba lafiya ta isheshi ba.

“Babu ina ma dakin, sai kawai na ji yayi kyalowa ya fashe da kuka, jikinsa ma duk yayi zafi”

“Ku kira Doc”

“Ammy ta kira shi”

“Gani nan zuwa”

Ya fada yana sauke wayar daga kunnensa, kiran Nana na sauka na Muhseen ya shigo wayarsa, da murmushi Omar yai picking call din.

“Shattima kana gurin Ammy? Ko kana Kaduna”

“Ka shigo gari ne?”

“Yeah ina Yola yanzu haka”

“Wow gani zan je fada yanzu”

“Okay mu hadu a can”

Daga haka ya sauke wayar yana murmushi he can't remember when last ya ga Muhseen mutanen Abuja.
  Daukar tawul din yai yaaje shi a muhallinsa sannan ya bude wardrobe ya dauko farin jean and blue t-shirt ya saka, a gagauce ya shirya ya saka agogon hannunsa ya fesa turare ya dauki abubuwan bukatarsa ya fice daga dakin.
 
“Baba Adamu.... A tashi mota yanzu nn zamu

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login