Showing 282001 words to 285000 words out of 286946 words

Chapter 95 - Fulani Book 1 Hausa Novel Complete

20 Dec 2024

964

da kai ba a banza ba ne, na san kana som Mama a yadda ka lake sai ka dawo kusa da ita kadai ya isa ya sanar da kowa ba da son ranka ya bar gidan ba, amman na san shirrin na Umma ne”

Ya daga kai.

“Haka ne ni kaina ina ji a jikina kamar ba a banza ba, saboda na saka zuwa neman mahaifiyata, bayan kuma tana cikin rai a kullum, na yi sa'a a lokacin da na bar gida, na yi nisan zango ban san inda zan je ba kawai dai na ji ina bukatar nisa da gidan ne, Allah yasa na hadu da abokin Daddy shi ya dauke ni ya kai ni gida gurin Daddy, tun daga lokacin sai na fara fuskantar wata wahalar daga gurin Inna Kulu (Uwargidan Daddy) a kullum ina mafarkin Mama ina ji kamar zata nemi inda nake amman shiru, na sha wahala kamin Allah ya budewa Daddy ya zama babban mutum kamar haka, sai kuma na kara samun wata sa'ar na aurin Momy da yai mace mai hakuri da sanin ya kamata, ganin irin wahalar da nake sha a can yasa Daddy ya maida mi hannun Momy saboda bata da yara kuma tana nuna tausayi da kulawa a gareni sosai, Matar nan ta rike ni kamar ita ta haife ni, ban san zafin rashin uwa ba saboda ita, sai dai hakan ina fatar wata rana zan ga mahaifiyata, ashe lokaci ya kure min”

Ya fashe da kuka.

“Da Mama tana raye, ta ga yadda ka zama da ta yi farinciki”

Sirleem ya rumgume matarsa dake ta kuka yana lallashinta.

“Yadda Allah ya tsara abu haka yake kasancewa, kin ga da Allah ya so sai yayi ki a gidan masu hali inda ko ciwon kai kika yi sai an shiga damuwa, Allah yana da iko da power da zai iya haka amman be yi ba, sai ki fahimci akwai hikima a cikin lamarin, ku yarda da kaddara ku gode Allah da yai muku tsawon rai har kuka gane junanku”

Sirleem ya fada sai Ameer ya girgiza kai yana murmushin da yafi kuka ciwo.

“Haka ne, ni kaina na san Allah ne ya tsara min haka, sai kuma ya kawo min Momy kalar yadda ya kawo miki dauki a yanzu bayan abubuwa da yawa sun faru”

Ita ma kan ta daga masa tana cigaba da kuka da yaki ya tsaya mata. Sai da Sirleem ya tabbatar ta daina kukan sannan ya tashi ya basu guri sun yu maganganu da yawa masu taba zuciya da tuna baya, Falmata tana fadar yadda Mama take yawan maganarsa. A gidan ya ci abincin tare da Sirleem da Falmata abincin da kanwasar Falmata ta girka, duk da kasancewar baya cikin walwala saboda abun da ya faru sai dai kana ganin fuskarsa kasan yana cike da son yar'uwarsa ko'ina tai binta yake da kallo irin na kauna da mamakin yadda ta zama jininsa lokaci daya, sai a yanzu yake ganin yanayinta yana yin kama da na Mamarsa.

***
Rayuwa da ciki a gurin mace ba abu ne mai sauki ba, musamman cikin fari kuma ga mai kananan shekaru kamar Falmata, sai dai kasancewar mai juriya da hakuri ya bata damar iya daukar nauyin cikinta cikin ma Sirleem yana hana ta yin abubuwa da dama gudun kar ta wahala, domin har ya fita kula da rawar kafa dan abu kadan zai yace zata gajiyar masa da baby ko tana son ta ja masa babynsa ya wahala. Sai da tai da gaske sannan ya barta ta tafi bikin kawarta Khadija domin ko fita baya son tana yi wai ciki ya tsofa tana ta wahalar da abun ke cikin, idan ya fita komai ya gani sai ya siyo mata idan kuma yana gida kullum tana jikinsa shi kuma hannunsa ko kansa na kan cikinta, har mamakin yadda yake ta zumudin cikin take wata kila. Saboda be taba yi ba ko kuma saboda an kawo gunsa ne, domin wani rawar kafar dai bata taba gani ko jin irinsa ba sai da aka kawo gunsa, haka dai akai ta fama Allah ya kai ta shiga watan haihuwarta, a nan ta gane ashe abun ba sauki sai ga wanda Allah ya kawo wa, asibiti ta haihu tana dakin haihuwa tana nakuda Sirleem ya waje cikinsa na murdawa kamar shi zai haihuwa daman tun kamin nakuda ta kama ta ya fara nashi zazzabin da ciwon kai.
  Sai yamma ta haihuwa cikin nasarar Allah, take Sirleem ya fadi yai ma Allah sujuda yai godiya. Kamin dare hotunan baby sun cika Media kasancewar mijinta sanannen mutum ne.



FADIME POV.

Zuwa tai ta tsaya gabansa ta mika masa hannu.

“Miko min kofin can”

Ya dauke kai daga laptop din dake gabansa ya kalleta.

“Shi kofin?”

Ta turo baki gaba.

“Eh”

Sai yai murmushi ya kai hannu ya dauka ya mika mata, haka take masa ita ala dole tana da ciki ba zata duka ba, musamman idan ta san yana cikin gidan ko wanka za tai sai dai ta rage tsawo a hankali har ta kai kasa saboda cikinta kamar wata mai tsohon ciki, babu ranar da bata bude cikin tai ta kallo tana shafawa, har tana cewa wai bata ji motsinsa ba wai ko ba shi da lafiya ne ko kuma dan tana yawan cin abinci mai yawa ne, hakan yasa ta rage cin abinci mai nauyi kuma da yawa wai kar ta cutar da ciki, wani abun idan tana yi Shattima sai yai ta dariyarta yana mamakin yadda take wauta sosai. Ya fada ciki sai ya kai wata hudu yake fara motsi amman bata yarda ba, kullum sai ta masa complain.
Haka akai ta shan rainon cikin kamar akanta aka fara ciki a duniya ko numfashi ba ta yi da karfi, sai dai duk abun da take tana yi idan tana ita kadai ko kuma ita da Shattima, bata yi a gaban mutane musamman idan suka leka masarauta hakan yasa Shattima ya gane shagwabar har da shi ake yi ma. Daman kuma shi dan nema ne domin shi ya fara nuna mata tun farko ita kuma sai ta samu guri, haka zata tashe shi cikin dare ta ce zata ci abu, idan be nemo mata ba sai kuka kamar karamar yarinya, wani lokacin lallabata yake da sunan zai nemo mata sai ya samu tai shiru har bachi ya dauke ta, wani lokacin kuma fitowa yake da sunan zai fita ya nemo mata sai ya dawo falo ko dakinsa ya zauna sai ta yi bachi sannan ya koma ciki.
Ba ma kamar da cikin ya tsofa a lokacin ne yake son ta motsa jikin sai ta tsaya kai ta fata ta ce ba zata yi komai ba, sai fadar take cikin ya mata nauyi wani lokacin idan ta shiga bandaki fitsarin ma a tsaye take sakinsa, sai dai ta saka ruwa, domin idan ta duka zata ji kamar cikin zai fito mata ko kuma ta gagara tashi, hakan kuma baya hana ta fita cikin mutane da cikin saboda shegen son yawo, idan yace zai hana ta wata rigimar ce zai takalowa kansa. Yau ma ta kama weekend Shattima na gida amman hakan be hana ta shiryawa da sunan zuwa Walimar wata cousin dinsa da ake ba. Yana zaune falo ta sauko da shirinta karfin hali har su jaka. Shi dai kallonta kawai yake har ta sauko.

“Da gaske zuwa zaki yi?”

“Eh ni dai ina son zuwa”

Ta fada tana dan turo baki gaba, so kawai take yace mata ba zata je ba ta fara masa kuka tana cewa ba zata ji abinci ba saboda ta san yadda yake shiga damuwa idan bata ci ba. Murmushi yai ya mike tsaye ya nufi dakinsa, be dade ba ya fito ya shiga dakinta ya sauko inda take tsaye tana jiransa ya cire gyalen dake jikinta ya mika mata Hijab.

“Ki saka wannan zaki fi rufe jikinki”

“Ni nauyi yake min”

“Daure ki saka haka nan haba baby na dan Allah”

Ba dan ta so ba ta saka Hijab din sannan ya aje gyalen akan kujera ya rika hannunta suka fita daga falon, ya riga isa gurin motar ya bude mata ta shiga ta zauna sannan ya zagaya mazauninsa yai ma motar key.

“Allah ya taimake ni karki min raki gurin haihuwa”

“Wallahi sai na yi haka kawai waya ce kai ciki waya ce? Mutum cikin mutum kuma zai fito a ciki mutum ace ba zai yi raki ba? Lallai fa”

Yayi dariya.

“Kina da gaskiya fa, mutum cikin mutum ko?”

“Eh mana, kuma ni zan sake haihuwa ba ma daga wannan idan na haihu yar mace mai kyau”

“Kamar ni?”

Ta yi dariya.

“Ke da kika ce twins kike so? Ai mutum biyu ne zai fito a jikinki yarinya”

“Ni dai da na ji wani abu ka kaini asibiti”

“Aa asibiti? Ga asibiti a gida? Wa zai kula da ke kamar mijinki?”

“Ai kai ta yaranka za kai”

Ya kai hannu ya taba kumatunta.

“Kamin na ga yaran waye na fara gani?”

Ta mika masa bakinta sai ya maso da nasa tai masa kiss.

“Ni ka fara gani”

“I love you”

Ya dora hannunsa a kan katon cikinta yana murmushi.

“Kin san dai kina saurin jin yunwa ko? Ki daina zama baki ci ba yunwa tana damunki”

“To zo ka bude min”

Ya fita daga side dinsa ya zagaya dayan side din ya bude mata ta fito sannan ya rufe ya fita da kallo har ta shige cikin falon shi kuma ya shigo motarsa ya dawo gida, bayan yayi sallah azahar ya kwanta be farka ba sai 4 shi ma alarm din wayarsa ne ya vmuslim app ya farkar da shi,  bathroom ya shiga yai alwala ya fito ya sauko yana hamma ga mamakinsa sai ya ganta zaune saman kujera tana kallon plasma dake falon.

“Hajiya yaushe kika dawo?”

Juyowa tai ta kalleshi da idanuwanta da suka mata ja tsabar kuka.

“Tun dazun, kaje kana ta bachi wai ni kuma ina ta daukar nauyi, kai ba ruwanka tun da ba a jikinka ne ba”

Zaunawa yai kusa da ita, ya san kullum abun kuka take nema, but abun mamakin kar dai ace dan yana bachi take kuka, ya hana ta bachin ne ita?

“Shi ne kike kuka?”

“Eh mana, kuma mutane sai cewa suke a a ashe ciki ya tsufa mai ciki mai ciki suna ta ce min haka....”

Ta kara fashewa da kuka domin a yanzu babu abun da ta tsana kamar ace mata mai ciki, daman tana ta daurewa a can amman a gida dole ne tai kuka saboda abun ya mata ciwo, gashi kuma tana zuwa ta tararda Shattima yana bachi abun shi. At first dariya ce ta zo masa sai yai saurin gintseta ya ja jikinsa ya rumgume.

“Na san kina fama da abu, shiyasa na ce ki daina shiga mutane amman kin ki, da kina nan ai ni ma ba zan fara yi bachi ba, balle har su rika ce miki Mai ciki Mai ciki Mai ciki Mai ciki... ”

Dagowa tai ta kalleshi.

“Cewa kake yi kai ma?”

“Aa ni ai ba zan fara ba, ina fadar yadda suke fada ne, Allah ya ba ni hakuri?”

“Ya baka?”

“Ya baki”

Yayi saurin gyarawa yana maidata kirjinsa sai dariya yake amman yaki bari ta gani.

“Fada min waya kawo ki?”

“Direban gidan”

“Ya kyauta, tashi ki yi sallah ni zan tafi masallaci”

“To”

Ta daga jikinsa shi kuma ya mike tsaye yana sumbantarta.

“Se na dawo”

Ta bishi da kallo tana jin haushinsa daman tun da cikin ya tsofa take ta jin haushin mutane, ko ido aka kura mata sai ya zama laifi, sai kuma takalar cikin take idan bata ji motsinsa ba sai ta hannu ta rika laguda tana takalarsa, idan kuma ya motsa mata da karfi sai tace ya taba mata hanji ta fara kuka tana cewa ciwo.
Haka dai Shattima yai ta fama har ta wuce kwanakin haihuwarta da kwana biyu sannan ta fara nakuda, a nan ta gane ashe wacan ciwon duk sharar fage tai yanzu ne na gaske yake tafe, idan marar ta murda mata sai ta ji kamar ba a duniya take ba, tun kamin ta shiga watan haihuwarta Shattima ya shirya mata komai na haihuwa a gida, har sai idan abun ya garara tukuna ya tafi da ita asibiti, sai dai baya barinta ita kadai idan zai fita hadimai za su zauna da ita saboda bukatu na yau da gobe da kuma gudun wata matsalar.
Ihu babu kalar wanda batai ba tun tana da kuzarin ihun har ta koma ta na ambaton Allah, tana fadin ba zata sake haihuwa ba.

“Ba zan sake haihuwa ba har abada, har abada ba zan sake haihuwa ba”

Shattima ya zo kusa da ita ya kwanto yana shafa kanta

“Pushhhhh”

Sai ta buge masa kai.

“Ba zan yi ba, pushing din ba, ai duk kai ne kai yi kai ka ja min, wayyo uwata wayyo ubana, Wallahi ba zan sake haihuwa ba”

Ya tsorata sosai a lokacin da ya ga ta daina unkurin yin nishin gudun kar ta kashe masa abun da ke cikin cikinta. Sai da yai da gaske sannan ta ni wani karfi ya zo mata daga gurin Allah yai nishi dai yunkuri sai ga kai ya fara fitowa, tanayin na biyu sai Shattima ya saka hannunsa ya janyo baby yana murmushi da hawaye a lokaci daya, ya saka alkamshi ya yanke cibiyar, ita ma a lokacin ne ta samu damar yin kuka mai hawaye domin a can da kukan kawai take ba hawaye, sai ta ji wani shauki yana ratsata babyn dake hannun Shattima sai kuka take tana jin kuka har cikin ranta, Shattima ya lullube ta da zane sannan ya sumbance ta ya kwantar mata da ita a jikinta.

“I love you so much”

Ya fada yana kissing din Fadime, hawaye na sauko masa, ita ma hawayen take tana murmushin da bata san ta ina yake zuwa mata ba, saboda joyful na uwa.

“Wa ta biyo? Mace ce ko Namiji?”

“Mace”

Ya fada yana shafa fuskarta, a tunaninta shikenan tun da ta haihu duk zancen da Shattima yake mata cewar yan biyu ne bata yarda ba a tunaninta yana mata wasa ne saboda ya san tana son yan biyu, sai da ta ji wata nakudar ta taso mata ta musamman, sannan Shattima ya fita ya bada Babyn wa mutanen da suke falo aka fara karba karba ana yabawa, shi kuma ya shiga wani sabon aikin, da taimakon Allah ta sake santalo danta yana kuka kamar yadda mace take. Za ku ga murna gurin Shattima kamar yanzu ne ya fara samun haihuwa.

Sai da ya gyara matarsa ya kwashe komai sannan ya shiga bandakin da ita ta gyara jikinsa ya fito ita kuma Jekadiya ta shiga yi mata nata aikin na kula da jikinta.
Da kansa ya buga ya fadawa Ammy da Inna cewar Fadime ta sauka, Inna sai ta ji kamar tai tsalle ta tafi, tana ta mamakin yadda akai Fadime tai iya karfin halin haihuwa domin ta san yarta da raki, gashi bata da halin zuwa domin Fadime kamar yar fari take a gurinta kuma kunya da al'adarsu ta fulani ba zata bari ta tafi ba, sai dai kenanta aka tura da wata yar uwar Bappa.
   Hankalinta be kwanta ba har sai da ta ji muryar yarta a waya tana labarta yadda akai ta haihu.

“Inna da kaina na haihu Wallahi, amman akwai wuya ba zan sake ba, Inna haka kika ji kema”

Inna ta yi murmushi idonta na cika da kwalla. Sai kuma Fadime ta fashe da kuka farinciki.

“Inna na zama uwa... Nima na zama uwa....”

Inna ta lumshe ido hawaye na sauko mata.

“Allah ya baki ikon tarbiyantarwa, ya raya miki su yasa masu jinkanki ne”

“Amin Inna, ke ma Allah ya saka miki da alheri dawainiyar da kika yi da ni da rashin da na yi miki Allah ya biyaki da aljanna”

“Ameen”

Shattima ya shafa fuskar matarsa yana jin kamar ya hadeye ta tsabar kaunarta da yake. Gurin ba da nono sai ido ya raina fata ashe a nan ma akwai wani zafin ba haka nan kurun ake bawa yaro nono ba, sai an yi da gaske sannan take shayar da yaran.
  Wani irin kula da tarairaiya ake bata kamar akanta kadai aka fara samun jika a masarautar, domin kwananta daya aka rabota da gidan Shattima aka dawo da ita masarautar, duk yadda Inna ta so ta ki zuwa bata samu hakan ba domin Ammy ta matsa mata kuma ta aika musu da komai na zuwa, ganin Ammy an wuce wannan karnin da ake cewa uwa tana kunya sosai da har zai hanata zuwa bikin yarta, bayan kuma babu abun da ya tafi so a wannan lokacin kamar gatan mahaifiyarta.
  Irin wulakancin da akai ma nera a ranar suna sai ka rantse da Allah daga sama ake jefo musu kudi, domin bidi'ar da kai a gurin sunan ba ayi irinta ba a gurin aurensu, namijin aka saka masa sunan Mai Martaba Abdallah, mace kuma ta ci sunan Inna Aisha, sai dai dukansu ana musu lakani da Ameer da Ameera.


ZAINAB POV.

bata dauka da gaske Wasim yake ba har sai da ya fada kuma suka amince masa cikin sauki, ganin cewar ba tafiya zai yi gaba daya ya bar garin ba, zai tafi a inda zai fi jindadin rayuwa ne fiye da nan, kuma ya karbi addinin da zai fi samun natsuwa da shi fiye da wacan na kakanni da iyaye.
  A lokacin da za su bar garin ita ta rika jin kewar garin da mutanen cikinsa, shi kan be ji komai ba domin ya saba yin nisa da garin dama kuma ya san ba wai tafiya ce ta har abada ba. Sai da be nuna musu zai aje tsafinsa ba wannan ya bar shi a zuciyarsa ne kuma a tsakaninsa da Zainab sanin cewar Familynsa za su iya kin yarda domin sun fi girmama tsafinsu fiye da addininsu.
  Garin Sokoto shine gari na farko da ya fadowa Zainab tun a lokacin da take tunanin garin da ya kamata ta zauna, bata san kowa a garin ba, amman hakan be hana ta zuwa ba, sai suka sauka a Hotel, iya kar kokari ta yi na ganin ta kare mutuncin addininta hakan yasa ta kama musu daki biyu ko wanne daban dabam. The following day after ta samu ma'aikatan hotel din tana tambayar ko akwai inda zata samu


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login