Showing 93001 words to 96000 words out of 286946 words

Chapter 32 - Fulani Book 1 Hausa Novel Complete

20 Dec 2024

945

birni ta yi dawowarta, kana kallonta kasan babu alheri a irin kallon da take yi ma Fadime, da ace yau tana da dama da iko da Fadime ba zata kwana duniya ba, domin abun da tai mata yafi wanda mutanen can sukai mata.

“Har abada dan da bana ka be taba zama naka ba, Wallahi kin ji haushin rayuwa, ai ko cewa su kai na kashe rai be kamata ki yi min haka ba, ni na biya miki kudin mota saboda kawai na nemo miki miji kina zaune a nan sa'aninki suna can da samari amman ke babu mashinshini balle ma dauki shine zaki watsa min kasa a ido ko?”

Sai da Amo ta kai aya sannan Fadime ta kalli inda take tana dan turo baki.

“To kuma sai na yarda su dake ni bayan ban san hawa ban san sauka ba, kuma ni ai hankali bacewa yai ban san abun da ya faru ba”

“Ni ai na san hawa na san sauka, shiyasa suka lakkada min duka, gashi nan ina jinya, ki wannan yarinya an yi haihuwar banza”

Inna ta aje butar dake hannunta ta nufo Fadime tana fadin.

“Haihuwar alheri dai akai, ko ba anan na same ki ba? Ke ai ko ta banzan banga kin haifo ba sai yar riko, kuma Wallahi da wani abu ya samu Fulani yau da tashin hankalin da za'ayi na gari da gari ne ba ko na cikin gida ba, daman can ban so tafiyarta ba kika matsa kika saka ta gaba kika je da ita shine kuma zaki baro ta ki dawo dan ta hallaka a can ko?”

“Kuma daman nace bana son zuwa ta matsa min”

Fadime ta fada tana dan turo baki ganin yau Inna ta bude baki tana fada akanta abunda bata taba ba kuma bata saba ba. Amo kan wani kallon mamaki ta kara yi ma Fadime, kamin Inna ta gwatsaleta.

“Dalla can rufe min baki, da za a fita ai kina gana jiki na rawa kika bita ko kunya bakyaji, kwata kwata babu inda kika da halin Fulani, wai kije birni neman saurayi saboda kunya ta fita idonki”

“To ai gashi nan na samo kaza da yoghurt da dubu bakwai”

Amo ta wani kashe ido tana kallon Fadime wacce tai magana tana turo baki, wato ita ta biya mata kudin mota taje da ita tasha duka, ita kuma ta samo kaza da yoghurt da kudi, a take zuciyarta ta raya mata wata kila tayi arba da saurayin ne har ya siya mata kayan dadi ya bata kudi tun da kusa da gidansu Ra'ees ne abun ya faru

“Ai Wallahi sai na fada masa halinki dan kar ya kwashi mugun abu, ya kai cikin gidanshi”

Inna ta kalli Amo a fusace.

“Ni ban haifi mugun abu ba, miji kuma ki yi ta kaya tana zaune Allah zai kawo mata nata”

Inna ta ja hannun Fadime suka shige bukkarta, babu kalar fadan da Inna ba tai mata ba a cikin bukkar tun Fadime na daurewa tana shanyewa har ta fasa kuka. Sai da ta gama kukanta taja kazarta ta bude ta fara ci, sosai ta ci namanta rabon da ta ci kaza har ta manta, amman a yau ta mata cin kashu ba ma ita kadai ba har da Inna dake fadan miyasa ta karba.

“Inna na ma hadu da wata mace tace tana son ta zo nan tai daukar hoto, na fada mata idan ta zo ta nemi gidanmu zan kaita ko'ina ma”

Ta fada tana cika bakinta da nama, Inna ma da naman take ci ta ce.

“Wai ni Allah, wato gani sarkin gari ko? Wai ke kullum sai kin dauko abun magana”

“Aa wasa nake bance mata ba, daman can na ji abunda zaki ce ne”

Ta fada tana yar dariya dan tasan wani fadan Inna zata sake mata. Rowar Naman kazar Fadime ta kulle a ledar da yake ciki ta aje a gefen gadon karan Inna sannan ta fito tana sudar yatsun hannunta sai da ta kawo kusa da Amo tai gyatsa.

“Al-hamdulillah na koshi da kaza da yoghurt”

Amo kallonta kawai take, kamin ta mike tsaye ta shige bukkarta, tukunyar tsafinta ta dauko ta sake turawa Fadime wutar sannan ta fito ta zauna tana kallon yadda Fadime ke alwala hankalinta kwance ita kuma tana jinya. Sai da Fadime ta gama alwala sannan ta mike tsaye tana yar waka kamar ba alwala tai zata yi sallah ba, da gangan take yi wai domin Amo ta kara jin haushi, dan ta yi arba da irin hararar da Amo ke watsa mata. Dakinsu ta shige ta shimfida buhu ta soma rama azahar sannan ta gabatar da sallah la'asar. Tana gamawa bata ko tsaya yin addu'a ta cire tufafin jikinta ta dauko na gadonsu ta saka ta fito tsakar gidan ta dauki tulu.

“To Allah ya tsare ya miki albarka kuma ya shirya na natsar dake”

Inna dake aikin wanke hannu ta fada, sai da Fadime ta kalli Amo sannan ta amsa da amin, sai kuma ta aje tulun ta shiga dakin ta bude ladar kazar ta dauko cinya daya ta boye a zanenta ta fito ta dauki tulun ta fice.
Amo na ganin ta fice ta unkura cikin zafin ciwon da karfin hali ta shiga bukkarta ta dauko wani magani mai kamar laya ta saka a baki ta tauna, sannan ta fito.

“Kar wanda ya shiga bandaki ina ciki”

Ta fadawa Hajjo sannan ta sabi buta ta shiga bandaki. Ba komai za tai ba so take ta bi bayan Fadime ta ga abunda take idan taje diban ruwa da kuma yadda wutar take barin jikinta. Tana shiga bandakin ta fara karanta wasu abubuwa tana karkada halshe ta birkice ido, a nan da nan jikinta ya fara gashi sai ta fadi a kasa ta kafa hannayenta da kafa kamar yadda dabbobi suke, cikin kankane lokacin gashin kyanwa ya maye jikinta gaba daya sai ta soma kankancewa ta zama bakar mage sai jajayen ido. Tsalle daya tai ta tsallake zanar ta dira waje, ta bi hanyar dajin tana tafiya daker dan ba karamin duka ta sha ba jikin kuma be isa saki ba, tafiyar ma kadan kadan take yinta.


Fadime tana tafe tana tunanin abunda Amo ta fada cewar sai ta fada masa halinta.

“Ai daman yace ya fasa, shikenan sai na tsaya a dake ni gashi nan ma ana mata tausar tuwon kasa, waya sani ma ko mayyar ce da gaske”

Duk taji haushin abun da faru gaba daya, Ra'ees yace ya fasa gashi kuma Amo tace zata kara lalata abun, idan ma ta tuna da Wasim sai ta ji haushinsa dan shine yasa muryarta ta yi katuwa har suka gudu ba dan shi ba da yanzu komai be faru ba. Allah ya gani kazar nan ma ba dan tana son masa kuri ba da ba zata je da ita inda zai gani ba, amman tana son nuna musu kazar shi da Ma'u dan su san ba wai farinjini ne bata da shi ba.
Sai da ta fara isa gurin ruwan ta fara ciko da zimmar idan ta cika sai ta je gurin duwatsun tai magana da shi, sai jin takunsa tai a bayanta kasancewar gurin babu mutane domin yamma ta yi kuma ana fadar dibar ruwan yamma da kuma rana tsaka be da kyau. Da sauri ta juyo sai ya sakar mata murmushi, mikewa tai tsaye tana kallonsa.

“Munje birni dazu”

Jin be ce mata komai ba sai kallonta yake yasa ta cigaba.

“Na hadu da wani saurayi ya siya min kaza”

Hannunta ya rika sai dai be yarda ya taba tafin ba, yaja ta suka zauna kan wani karamin dutse dake gurin.

“Fada mim yace yana son ki?”

Ta yi shiru sai ta ciro naman kazar ta mika masa.

“Ga shaida nan ka gani”

Dan murmushi yai ya bude mata bakinsa.

“Ba ni na ci”

Ta zare ido.

“Kai idan aka gan ni ina baka abinci sai a fadawa Bappa, gashi nan kuma baka da riga sai ace wani abu ne”

Murmushi yai gyada mata kai, can kuma sai ta waige ta ga babu mai ganinsu ta balli naman ta kai masa a baki. Bude bakin yai ta saka masa babu wata kyama duk kuwa da irin kyamar da yake da shi, sai ya fara tauna naman sannan ya kai sannunsa ya cafko wutar bayanta.

“An sake saka miki wutar nan”

Fadime ta waiga da sauri ta kalli hannunsa dake ci da wuta, ba shiri ta jefar da naman hannunta ta mike tsaye.

“Kai ne dai kake saka min ita”

Ya kalleta da fafaren idanuwansa ya jefar da wutar.

“Ba ni ba ne”

“To waye? Miyasa ake saka min ita?”

Mikewa yai tsaye ya shafa kanta da babu dankwali.

“Saboda karki yi albarka, wannna wutar ta maita ce”

“To minene ma yasa mayun suke bina suna saka min wutar ne?”

Murmushi yai ya kai dayan hannunsa ya shafi gefen fuskarta, sai kallonta yake kamar zai cinyenta.

“Ana sakawa mutum ita ne saboda kar yai albarka, komai kike samu ko kika rika sai lalace, idan kana makota da maye ko kuma ya saka maka ido, to zai saka mata wutar ne tai ta binka tana cinye duk wani abu da ka mallaka, idan kuma be saka maka wutar ba zai saka maka ciwo har dukiyar dake tare da kai ta kare, shi ma idan ya gagara cinka ne, mayu suna da hassada basa son su ga wani yana samun wadata saboda mafi akasari su matalauta ne, masu siyar da kurwa ne kawai suke arziki wadanda basa ci sai dai su siyar ko kuma suna ci suna saidawa, ko baiwa ko basira maye ya gani a tare dake zai kwasheta ya jujuta miki kwakwalwa, idan maye ya ci mutum dubu sai ya zama sarkin mayu, daga lokacin ne mayen baya iya sake cin mutun sai dai su koma bada maganinsu saboda sun san lagonsu, mugun ya san makwancin mugu, idan kuma maita mutun ta gawurta, ko dabba ya kalla ya kwallafa rai zata mutu, ko gini kai idan maye baya so yana kallon ginin zai zube sai idan ka gagareshi, idan kurwarki tana gurin maye zai ta miki waibuwa yana saka ki kalar mafarkin da kike so, idan kuma suka aje miki aljani a daki to zasu rika jin inda kike neman magani da inda kike ajewa sai su bata shi ya gagara yi miki amfani”

Tun da ya fara bayani Fadime take masa kallon tsoro idonta a waje.

“Kai ma maye ne?”

Ya girgiza mata kai yana sake kai hannunsa ya shafa gashin kanta.

“Mu garin mu ba a maita, sai dai muna tsafi sosai, amman ba mu yarda da ayi maita ba, saboda ba ma yarda mu cutar da yan'uwanmu, idan mutum yai mata korarsa ake a garin ko da shi din sarkin garin ne, mayu har yayansu suke badawa saboda ana adashe tsakanin junansu, idan aka ci dan wannan idan za ayi kwasa na wani za a ci, duk irin son da kake ma dan dole ka bada, idan kuma aljanin maita ya bukaci ɗan ka da kansa dole ka cinye danka ko da kuwa kana kana son shi, mayu basa son tsagera, sun fi son matsoraci da mai yawan kyautata musu, matsoraci kurwarsa tana kwantawa ne guri daya har su samu nasarar kamawa babu wata hala, kama ma mai yawan kyautata kusu kullum yana tare da su, kamar kaza ne a cikin keji idan ka tashi yankawa cirota kawai zaka yi, tsarega kam yana musu wahalar kamu saboda kurwarsa bata zama a guri daya kuma baya shan inuwa daya da maye, wani mai aljanu ma wanda aljanunsa suka fi na maye a take zai tona musu asiri, sannan maye be son tsarguwa, idan kika matsa masa zai tashi ya bar miki guri, idan har makocinki ne, ko kuma ya baki maita ki ci a asirce bani sani ba ki kamu da ita, kowa kuma da yadda yake kama kurwa, wani lasowa yake, wani sai ya miki kyaface da hannu wani sai jikinsa na taba naki, wani sai ya baki abu kin ci, wani sai ya shiga innuwarki, wani sai ya baki abu kin karba ko kuma kin bashi a lokacin ne zai samu damar jan kurwarki izuwa gareshi, wani sai ya miki magana kin amsa, wani kuma da ido zai janyo kurwarki, akwai wadanda basa gashi, amana basa tsawa soyawa ko gasawa, irinsu sun fi hadari su da masu saidawa domin idan sun sayar yana da wahala wanda aka saidawa ya dawo da ita duk kuwa da irin azabar da za ayi ma wanda ya kama kurwar, wanda baya gashi kuma take daya kama yake yankewa ya cinye mutum ya mutum, irin su idan suka kama ba zaka wuce kwana daya ba ko wuni wani ma awanni zaka mutu”

Gaba daya jikin Fadime yai sanyi, tun dai tana gane bayanin nashi har kwakwalwar kanta ta fara kwancewa yanzu kam jinsa kawai take bata gane komai ba, sai dai abunda ya faru a dazun da Amo ya dawo mata a rai wata kila da gaske Amo mayya ce.

“To ni wa yake saka min wutar? Minayi?”

“Baki yi komai ba, ban fada miki maye yana da hassada ba? Idan ma suka gagara cin kurwarka suna mata duka su daddake ta mutun ya koma musaki ko mahaukaci ko wawa ko kuma ya koma kwance da rashin lafiya, amman daga yau ba za a sake saka miki wutar maitar ba, ba zan sake bari a cutar da ke ko yatsa ba zan bari wani ya nuna miki ba kowa kuwa”

Ya fada yana kallon cikin idonta fuskarsa na nuna alamar babu wasa a maganarsa. Juyawa yai baya ya kalli wata bakar mage dake labe cikin itatuwan masara tana kallonsu sai ya nufi inda take Fadime dai binsa kawai tai da kallo.
Amo na ganin ya nufota hankalinta ya tashi tana son ta gudu ta kasa, sai ta ji kamar ma yana kiranta yana nufota tana tunkararsa har ta kai kanta gurinsa ta duka ya kamata ya birkiceta ya nade hannunsa ya sakar mata kulli a ciki sannan ya saketa, kasa tashi magen tai a take ta fara aman jini Wasim na ganin haka ya juyo ya dawo inda Fadime take tsaye.

“Wannan magen ina ganinta idan ina kiwo tana bibiyata, har a mafarki wani lokaci ina ganinta”

Fadime ta fada tana nuna magen cikin wani irin tsoro har bata iya numfashi da kyau. Kafadunta ya fada ya kara matsowa da ita kusa da shi ya rumgumeta ya lumshe ido yana sauke ajiyar zuciya.

“Kin cika tsoro...”

Ya fada a hankali hana shafa kanta, kamar wacce ta tuna abu tai saurim dagowa daga kirjinsa ta leka mage sai ta hango babu magen a wajen, ta kalli Wasim

“Kai ma ai kana keta ka maida min murya katuwa kuma ka saka min maciji a tulu”

Murmushin yai ya risino kusa da fuskarta yana mata wani irin kallo kamar maye.

“Ai ke kika ce na miki dabon maciji kin tuna?”

“Amman ban ce ka maida min muryar katuwa ba”

Nan ma murmushi yai.

“Wannan kuma ra'ayina ne, amman ba zan sake maida miki murya katuwa ba na yi alkawari”

Yana gama fada mata haka jikinsa ya bashi cewar akwai wani mai nemansa a kuwa da shi, tafin hannunsa ya bude sai sunan Liya ya fito da sauri ya rufe hannun ya juya gurin wata karamar hanya ya fara tafiya.

“Zan tafi sai na sake zuwa nan”

Wannan karon bata daga masa hannu ba kamar yadda ta saba sai kawai ta bishi da kallo har ya haye saman dutse ya dago mata hannu ya juya ya sauka ta dayan bangaren. Sai ya wuce sannan ta juya ta koma gurin ruwa ta cigaba da cikonta tana tunanin wasu abubuwan daya fada mata, tana daga kai ta hango Liya tafe ta gefen gulbin, Fadime ta tsaya jiranta har ta kawo.

“Dan Allah ki taimaka ki dora min tulun nan a kai”

Kallonta Liya ta tsaya yi sannan ta karasa kusa da ita ta rika mata tulun ta dorata a kai, a nan Fadime ta hango gashin kazar dake kanta ta kai hannu ta cire mata.

“Gashin kaza a kanki”

Fadime ta fada bayan ta kai hannun ta cire gashin ta jefar, Liya bata tsaya komai ba ya kaiwa Fadime bugu a baki.

“Kam Bala'in nan”

Fadime bata san lokacin data jefawa Liya tulun kanta ba ta fara zaginta bakinta sai jini yake.

“Shegiya muguwa shegiya shegiya shegiya daga taimako, muguwa Azzamula, muguwa ban yafe ba Allah ya isa”

Liya ta duka ta dauki gashin ta maida a kanta ta ranta a na kare. Fadime ta fara daukar duwatsun dake gurin tana jifanta da su iya karfinta tana zaginta tana kuka a lokacin daya, domin ba karamin azaba ta ji ba, daman mutane garin Garuk indan suka daki wanda ba dan gari ba sai yaji zaba saboda dafin hannunsa domin su komai na su a tsafe yake, ko dangwarar mutun su kai indai sun yi da keta sai yaji ciwo.
Da gudu Liya ta haye saman dutsen tana dukewa dan kar jifar da Fadime take mata ta same ta, daman can neman Wasim ya biyo da ita ta nan kuma bata ganshi ta kwashi ruwan duwatsu a gurin Fadime.


*Littafin nan na kudi ne biya ki karanta cikin aminci. Pay 300 to 0314795884 Abubakar Hadiza Gt bank, then send the evidence to 08036126660*


Ina mata matan kwalisa Matan da suka ansa sunansu na Mata? Ina wadanda ke cewa mun yi mun yi bamu ga amfaninshiba? Hmmm to ku zo ga Yar gidan Maifata ta zo maku da Al ajabu, dan tsugunno, gumba da tsimi da Zuma daban daban, maganin sanyi na maza da Mata. Ga kuma garurruka irinsu mallakau sabuzu kuwa, sa bahaushe saibi, Dan hubbare kafi malam aiki, ke kadai ke da miji, dahuwar kaza, tattabara, ciccibi da dai sauransu. Ba anan kayanmu suka tsaya ba, muna hadin amare na musamman turaren sutura turaren tsugunno turaren wanka da na daki da na jiki duka 4amare nasu na musamman ne, amma ga tsuhuwar da ke son komawa yarinya itama zata iya zuwa ahadata kai abundai sai wanda ya gani, dan haka karkubari abaku labari, domin neman karin bayani zaku iua nemana ta wannan number 09029891757 ko 08169311410, muna aikawa ko'ina a fadin kasar nan har waje kasar nan muna aika kaya.
Address: Nasarawa Samaru Area gurin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login