Showing 186001 words to 189000 words out of 286946 words
saboda ba ni da tabbacin ke kika haife ni ko kuma wata dabam! A yau zan tambaye ki tambaya ta karshe, zan bukaci sanin wani abu daga gareki sani na karshe, abun da zan tambaye ki mai sauki idan kin saukaka shi, mai nauyi ne idan kin ki fada min, domin zan tattara komai na nawa na bar garin nan, zan tafi inda ba zaki taba jin labarina ba balle idonki ya sake arba da ni ba”
Iya ta dora hannu a kirji tana kallon Zainab cikin tashin hankali domin bata ga alamun wasa a tare da ita ba.
“Wannan wane irin magana ne haka Zainab”
“Da gaske nake Iya, ba zan iya zama da ke ina kwankwanton ke mahaifiyata ce ko kuma uwar riko na, ba zan iya zama kunnuwa suna jin ana jifarki da munanan kalamai ba, zuciyata ba zata iya daukar nauyin abun ba”
Iya ta dauke kai tana aje numfashi da karfi.
“Iya ki fada min wacece ni? Ina asalina? Waye mahaifina, miye alakarki da Wasim? Kuma miya sa kika baro garin? Miyasa kika boye min asalina?”
Iya ta runtse ido tana jin wani irin abu na taso mata na rashin dadi.
“Miyasa zaki so tuna abun da ya wuce, miyasa zaki zabi tuna min da garin d basu san yafiya ba, kuma saba karbar tuba? Miyasa zaki tuna min da asalin da bana son sani?”
Hawaye ya cika idon Iya, kamar yadda ya suko a fuskar Zainab.
“Saboda ni ma ina da bukatar sanin asalina, ina bukatar na hashakin iskar yan ci yanci na sanin waye kai kuma dame zaka yi alfahari? Na kasa samun aminci da cewar ke mayya ce, wata kila saboda ban san abun da maita take nufi ba, ko kuma saboda kaunar da nake miki ne, sai dai ina jin na tsangwama idan na tuna abun da Fadime ta fadawa Shattima, wanda na san a zuwa yanzu ta yadashi a masarautar nan, sanadiyar haka zai yadu a duniya”
Iya ta bude jajayen idanuwanta.
“Ba zan taba yafewa yarinyar nan ba”
“Amman da baki aikata ba, da bata fada ba da hankalina da na ki be tashi ba, na yarda tana da laifi na surutu amman idan bata ji komai ba ba zata yada ba, duk na san ta kara da karya amman idan ba ki aikata ba b zata samu damar fadar komai ba”
Iya ta sake rufe ido a karo na biyu tana jin wani abu kamar na tashin zuciya saboda tunawa da garin Garuk. Ganin hakan yasa Zainab ta sauko daga kan gadon ta zauna kusa da Iya ta kama hannayenta ta rike.
“Wata kila sun guje ki ne ko kuma sun kyamace ki, ina son ki sani komai kika aikata ba zan taba gudunki ba, ba zan taba kyamarki ba, zuciyata bata raya min na butulce miki ba, na san muna yawan samum tsabanin ra'ayi da fahimta, amman hakan ba yana nufin gudun juna ba ne, saboda kin labarta min asalina ba zai canja komai akanki ba”
Iya ta sake bude idon tana kallon kallon Zainab hawaye na sauko mata.
“Me kika gani a fuskata?”
Zainab ta kura mata ido tana kallonta kamar yau ta fara ganinta.
“Kauna da soyayya irin wanda ko wace ya take gani a fuskar mahaifiyarta...”
Iya ta lumshe ido hawaye na sauko mata, har cikin zuciyarta kalaman Zainab ke ratsata.
“Ba shi nake son ki gani ba, muni da tabon da ke a fuskata nake son ki gani, akwai tabo a fuskata ko bani gani ba?”
Ta fada sannan ta bude idon, Zainab ta hade yawun bakinta sannan ta ce.
“Na gani”
Zainab ta amsa tana kallon gefen fuskar Iya.
“Da shi na taso, mahaifiyata ce ta yi min shi, bayan muni na hallita sai ta kara min da wannan”
Iya ta yi shiru na wani lokaci sannan ta cigaba.
“Gidanmu gidan sarauta ne, garin mu garin matsafa ne, garin ne da ba mu yarda da ko wane irin cigaba ba, tun kaka da kakanin har zuwa yau, kin je garin ina tunanin kin ga wadansu al'adu da dabi'u na garinmu, a da, yara yayan sarakuna basa zuwa ko'ina kamar barin garin zuwa wani gari ko da da sunan ziyara ko gani, sai dai mu an barmu kamar yadda nake zaton ana kara barin wasu bayan mu, na tashi cikin gwangwama da tsana a gurin mahaifiyata, duk da kasancewar ni ce yarta ta uku, na farkon namiji ne wanda shi ne Sarkin garin Garuk a yanzu, sai kuma yayata Ayyalata, mu hudu kawai mahaifiyata ta haifa, amman ta fi tsanata, saboda na fi fitina, lokuta da dama Ayyalata zata yi laifi ni nai, maimakon a hukunta mu ko a tare sai ta yi min hukunci ni kadai, ko da kuwa ni nake da gaskiya, idan zata siya mana abu, sai yace bari a fara da Ayyalata, ni kuma zata min daga baya, amman ba zata min ba, a kullum tana tsauraramin a komai, sai tace ni ce karama, ya kamata na rika yi wa Ayyalata biyayya, ganin hakan yasa bawa Ayyalata damar musguna min son ranta, idan kuma na rama sai amin hukunci, gashi na taso da muni na halitta, kowa ya fi ni kyau fuska, ga kuma muni na zuciya, domin bana kaunar ganin wani ya fi a komai, idan ina tare da mutum ya samu daukaka ko wata tarba wacce ni ban samu ba, ko kadan bana son na an dara ni da komai, ina kishin wani ya samu wani abu wanda ya fi nawa, idan na yi mahaifiyata laifi sai ta rika ce mu mummuna wanda shi yafi komai yi min ciwon, haka yayata ma take ce min kanwata ma haka, dan'uwana ne kawai nake jin sanyi a gurinsa, idan an bata min yana kyautata min saboda na ji sanyi, farkon hukunci da mahaifiyata ta fara min shine kone na min fuska da murfin kushi saboda na yi fada da yayata na buga da kasa, sai ta zaureni a icen gidanmu, a gaban bayinmu ta bar ni a gurin na wuni har yamma, sai da mahaifina ya zo ya kwance ni, hakan be mata ba, sai ta saka murfin akushi a wuta ta saka a gefen fuska, daga lokacin ne na gane cewar zuciyar mahaifiyata bata da kyau, sai na fara nisantar kaina da yan'uwana, na fara yin nesa da dangina, daga lokacin na nemi izinin mahaifina na fita zuwa bayan gari cikin wasu al'ummar ta dabam da ba tawa ba, sai mahaifina yai mana izini ba ni kadai ba har da sauran yan'uwana mata gaba daya, da farko wajen gari kawai na ke fita ina ganin tsuntsaye da taunuka, a lokacin ne aka farfafa mana tsafin mu, mahaifina ya saka aka fasa hannuna aka saka min laya a ciki, wanda zata bani damar saffara duk abun da ake so a iya gwargwadon tsafin mu, kuma zata bani tsari kuma ta saka jikina ya zama mai dafi, a lokacin ne na fara yin nisa da garinmu, karon farko da na leka wani garin baya namu sai na zama abar kallo a cikin garin kuma na zama abar tsoro, suka zagaye ni suna min kallom wata halitta ta dabam, na ssha wahala sosai kamin na samu dawowa garinmu, a ranar n karbi hukunci gurin mahaifina shi da kansa ya saka aka zaga min gefen hannu”
Ta daga rigarta ta nunawa Zainab inda tabon yanka yake a jikinta.
“Ai maimakon mahaifiyata ta tausaya min, sai ta dora min da nata hukuncin ta saka yayata ta azzabtar da ni da karara, (Wani ice ya ne dake saka jikin mutum kaikayi) a ranar na kwana na wuni ina susar jikina, daga lokacin ne na gane bana da sa'ar rayuwa, amman na daure na zauna a masarautar ban sake sha'awar fita ba, rayuwa ta cigaba da tafiya a haka har ta kai yayata ta yi aure kanwata tai aure, aka bar ni sai abun ya fara min ciwo, yayana ma yai aure har ya haifi Wasim, idan na fita cikin yan mata yan'uwa sai na zama kamar abar tsoro ko kyama ba kowa yake son mu'amala da ni ba, hakan yasa zuciyata ta raya min daukar maita, ba dan komai ba sai dan na gusar da bakincikina da kuma kawar da duk wnda ya hau hanyata, duk wani dan garin Garuk yasan maita ya san miye maita kuma ya san yadda ake rabuwa da ita, ni da kaina na hada tsafina na hadiye kankarar maita, duwatsu ne kanana idan ka haye su, aljanin zai zauna a jikinka ya bude maka ido, bayan ido biyu da kake da su, maita tana karawa mutum wasu idanuwan guda biyu, ta yadda zai iya gani ta gefensa da bayansa, sai dai mutane ba za su ga wannan idon biyu ba, za su dai iya ganin biyu ne kawai, A lokacin da zan dauki maitar na dauka ne saboda biyan bukatata ba dan cinye kowa da kowa ba, hakan yasa ban dauki maita mai zafafa min ba”
Ta yi shiru kana ta cigaba.
“Daga lokacin ne na fara ganin komai a cikin jikin mutane, idanawa suka bude, na fara ganin kurwar mutane wasu kamar fara wasu kamar kaza wasu kamar kurciya, bana yi ma kowa komai sai idan ka taba, shi ma ba zan cinye mutum ba, sai dai na yi kama kurwar mutum na tsoketa da kaya, ni kuma daga lokacin ne asirin da mahaifina ya bani ya karye, saboda a garin ba a maita kuma ba a zama da maye, da sannu sannu mutane suka fara ganowa, sai suka samu mahaifina da maganar ganin cewa ni jinin sarauta ce, a lokacin Wasim yana hannuna ni nake kula da shi, A lokacin da labarin ya samu mahaifina, sai kakana ya fada masa cewar ya san komai, kawai dai yayi shiru ne saboda ni jininsu ce, ni kuma a lokacin na shirya amayar da kankarar maitar, amman hakan be samu ba, saboda mahaifiyata ta zabi a hukunta ni kamar yadda ake yi ma kowa”
Hawaye ya fara saukowa a idonta.
“A gari akai yawo da ni, ina kuka ina mana yafiyar kowa amman ba a kula ni ba, bayan an nunuwa duniya wacece ni sai kowa ya tsane ni, ni kuma daga lokacin ne na ce ba zan amayar da kankarar ba...”
Iya ta dago tana kallon Zainab fuskarta da murmushin takaici.
“Kin san wa na fara badawa? Mahaifiyata, daman idan ka shiga maita dole ne sai ka bada wani naka, a lokacin na zabi fada mahaifiyata saboda tsanar da take min, na sha wahala kamin na samu kama kurwarta, da na kamata ban tsaya komai ba saboda gudun kar a gane, sai na Yanketa, kamin a ankaro ta mutu na dauki Wasim na gudu na bar garin, zuciyata bata raya min ko'ina ba sai Yola, saboda gari ne na da yai nisa da wa garin, a lokacin ban san sunan garin yola ba, ban san ina garin yake ba har sai da kafata ta dira a garin, na samu mutanen garin masu karamci da son baki ba kamar sauran garuruwan da na wuce ba, ba su bani masauki ba, amman sun min taimako, a tasha na tare da Wasim, na kusan wata ina zama a nan, kamin mahaifina yai min aike cewar ba za su min komai ba, amman idan lokaci yayi za su min aike, na san abun da aikensu yake nufi aiken mutuwa kenan ban da ban san ranar da zai zo ba, kuma ya fada min cewar idan suka bukaci ganin Wasim za su kira shi, sun bar min shi ne kawai saboda sun san ba zan iya cinsa ba, a tashar na hadu da mahaifinki, yana taimaka min sosai sai dai a duk lokacin da ya taimake ni ya kan bukaci wani abu daga gareni, a garinmu kuma a gurina abun da yake bukata ba komai bane hakan ysa ban taba musun bashi ba, ganin shi din be nuna min kyama kamar mutanen garin mu ba, abun da ban sani ba, bayan ni yana da wasu a cikin tashar, a ranar dana gano sai na kama kurwarsa na soka mata kaya na sake ta, ya fadi da jinya a bayan hannunsa na dama, daga lokacin ne ya zama baya iya yin komai da hannun sannu sannu dafin ya fara masa yawa, ni kuma sai na dauki Wasim na bar tashar na tafi zuwa cikin garin neman gidan sarki, domin na san a wacan lokacin duk wani bako a gidan sarauta yake sauka, a lokacin da na isa sai na fada musu cewar ba ni da kowa mu yi gudun yunwa ne daga garin kamaru, da farko na sha wahala na wulakanta kamin karbe ni, sai aka min masauki a inda ake aje bakin sarki na wani garin ko kuma marasa galihu, ni kuma a lokacin ne idon ya bude a masarautar garin na fara neman wadanda suke da alaka da masarautar, sai na watsar da addini na bi addinin da na samu mutanen gidan suna na yi, wato musulunci, na kan yi sallah idan a idon mutane ne, kamar yadda na ga suna yin alwala su yi sallah tun ina kuskure har na iya, har wasu suke ganin ina da riko da addinin fiye da wasu, na zama na fi kowa shiga shigewa a jikin mutane, tun ana tsorona ana guduna ganin ni bakuwa ce, har aka fara sakewa da ni, a lokacin da na so daukakar, sai na kame wadanda suke kusa da jekadiya kaf da kaf na tura musu ciwo, kuma ni zan hada magani na ba Jekadiya cikin hikima, idan kuma akai amfani da shi sai na saki kurwa mutum ya samu sauki, da haka na samu shigewa jikin jekafiya har ta ke shiga da ni cikin masarautar, a lokacin na samu Ammy da Hajiya Bilki su, sai dai ganin kamar Mai Marbata ta fi jin Ammy yasa na fi maida hankali da neman shige mata a jikin sai dai ban samu haka ba, tun a wacan lokacin saboda Ammy macece mai wuyar sha'ani da yarda, sai da na shige jikin jekadiya na san komai a masarautar, sannan na fara azabtar da Jekadiya, a lokacin ina da cikinki tana kula da ni sosai har na haihu, a lokacin da na haife ki, sai na ga ke kyakkyawa ce kama babanki, sai na fara yi miki sha'awar samum kyakkyawar rayuwa, na rada miki sunan Ammy, ni da kai na yi miki lakani da Hajiya Babba saboda akwai wata Hajiyar abokiyar zaman Ammy, daga lokacin ne na kama kurwar Jekadiya na yanke, a lokacin ne na nemi Wasim na rasa, sai na fahimci an kira shi kenan, aka sake nada wata ita na kawar da ita, aka sake na sake kawarwa, ya zama babu wata jekadiya da za a nada ban cinye kurwarta ba, sai aka sake nada wata na bita na shige mata a jiki, na samu sa'ar sake shiga cikin masarautar, salona da iya mu'alama yasan kowa ya san ni ciki har da Ammy, bata sake min sosai amman a haka nake shiga jikinta, ina kame komai nai masa kanene kamar yar gida, sarautar garin babbar sarauta ce mai tsari da abubuwan burgewa ba kamar ta mu ba, a lokacin da Ammy ta fara sake min fuska har tana aminta nai mata wani aikin, sai na fara nuna mata kauna da kula a gurin Omar a lokacin haka ake kiransa a lokacin, shi kuma ya saba da ni fiye da kowa idan be gan ni ba har nema yake, ba ni nake kula da shi ba, amman shishigina yasa na zama kamar ni ce mai kula da shi, ta sanadinsa ne a samu shiga cikin fadar Ammy har na zama an bani daki a dakin dake kusa da bayin a maimakon dakunan wajen gidan da nake zaune, tasowar ki sai Shakuwa ta shiga tsakaninki da Shattima, kasancerwar a lokacin ba shi da wata kanwa mace, sai yayan Hajiya su kuma ba shiri suke ba, ta sanadiyar kaunar da Shattima yake nuna miki har na samu yin fadanci a gurin Ammy ta bukaci a kaiki makaranta, a lokacin na yi zaton makarantar kudi za a saka ki, amman sai aka sakaki makarantar talakawa bayan a lokacin ina miki buri da kwadayin samu rayuwa mai kyau, saboda masarautar ta shigar min a rai, daga lokacin ne na kullaci Ammy na gane cewar bata son talaka ya daukaka, sai na fara bin nata yayan ina kama kurwarsu, kamin Nana an haife Maza biyu, da mace daya duk ni na cinye su, Nana ce kawai na kyale ita ma dan na taba mata kwakwalwa ne. Rana tsaka Wasim ya dawo min, ya cigaba da zama tare da ni, sai dai zaman be dade ba aka sake kiransa.”
Ta hade yawun bakinta tana ta numfasa sannan ta cigaba.
“Na ci buri na ganin kin samu ilmi mai kyau saboda ina miki fatar samun, mai amfani saboda ina miki fatar auren Shattima, domin na san shi za a bawa sarautar wata rana, dagewata ce da kokarina da jajurce wata ce ta saka kika samu karatu mai kyau, saboda ina hango miki gobe mai kyau, shakuwar dake tsaninki da Shattima da kuma Nana yasa aka miki masauki a kusa da Fadar Ammy, saboda yaran basa zama a ko'ina sai kusa da ke ko ni, na dafa kitsen wata kurwa na lasawa Nana a baki, sai ya zamana idan ba ni ba ko ke bata jindadin daukar kowa, a lokacin da Shattima ya kai ya zama namijin gaske sai shakuwarki ta karo saboda kina masa kallon dan'uwa shi kuma yana miki kallon kanwa, ga Nana ma sai abun ya zama kamar ke ma yar wani ce a masarautar, sai dai aduk lokacin da wani abun ya taso Ammy bata mantawa da yi mana jawabi, ko kaskantar da mu a gaban kowa, na yi ta son kama kurwarta na zabatar da ita amman hakan ya gagara saboda tana da karfin addu'a, har yau ban samu dama ba”
Iya ta share gumin daya keto mata sannan ta cigaba.
“Matar farko da na fara ci ta shattima kyakkyawa ce kuma yar sarauta, kaf daya nai mata, haka ta biyu, haka ta uku haka ta hudu, sai a wannan kawai nai yi ma jikiri shi ma saboda tana da aljanune ta gagare ni ce, har sai da