Showing 231001 words to 234000 words out of 286946 words

Chapter 78 - Fulani Book 1 Hausa Novel Complete

20 Dec 2024

940

sallame mu, tun da tace jikinta ba ya mata ciwo komai yanzu zaman Asibiti ba dadi”

Ta fada tana gyara zamanta, wani irin zabura Maijidda tai daga cikin bachin da take ta matse hannunta tai wani abu kamar zata tuma sama daga kwance da take sai kuma tai lamooooo babu motsi.

“Subhanallahi jidda”

Hajiya Talatu ta fada tana mikewa tsaye ta isa gaban Maijidda din, hannu ta kai ta taba ta tana kokarin tashinta.

“Jidda Jidda...”

Haka Hajiya Talatu tai ta kiranta tana motsata, amman bata motsa ba, kuma ba ta amsa kiran ba, sai Hajiya Talatu ta kwantar da kanta jikin Maijidda tana sauraren numfashinta. Nan ma bata ji alamum tana numfashi a razane ta dago tana kallon Afra.

“Afra je ki kira likita yi sauri”

Sai tai rasa akan gaba domin tana rufe baki, likita ya turo kofar dakin ya shigo tare da nurse yana dariya da alama wata maganar suke. Tsakanin Hajiya Talatu da Afra sai ka rasa wane ya fi saurin sanarwa likitan abun da yake faruwa, da sauri likitan ya karasa inda Maijidda take kwance yana dubata, fita yai da sauri ya kira wasu likitocin biyu suka shigo cikin hanzari suka hau bata taimakon gaggawa amman ina mai kira yayi kira rai yai halinsa Maijidda ta bakunci lahira...
Dayan likitan ne ya fitar da Hajiya Talatu waje ita da Afra, sai ta tsaya bakin kofar tana kuka hankalinta a tashe, gaba daya ta rasa abun yi ko zama ta gagara yi. Bayan wadansu mintuna likitoncin suka fito ko wanensu fuska babu annuri hakan ya sanarwa Hajiya da Afra cewar sun rasa Maijidda rashi na har abada, Maijidda ta yi bachi da babu farkawa a duniya, ta tafi inda ko wane mai rai ke tsumayin zuwa.

“Hajiya... Ku yi hakuri”

“Ban gane na yi hakuri ba likita kamar ya na yi hakuri? Me kake nufi?”

Ta tambaya cikin kukan tun kan a sanar mata.

“Hajiya kin san duk mai rai mamaci ne, ki yi hakuri Allah ya karbi abarsa”

“La'ilaha illahu innalillahi, wayyo ni Allah na Maijidda”

Cikin wani irin fitar hayyaci da ihu da kururuwa Hajiya Talatu ke fadar hakan ta nufi dakin da Maijidda take ciki sai likitan ya riketa, Afra kuma ta zube a gurin tana ta borin iska, aljanunta na son tashin.



FADIME POV.

Misalin sha biyu na rana direban Mama Fulani ya isa da Fadime asibitin da Muhseen ke aiki. A harabar asbitin ya fara motar sannan ya fito ya zagayon bangaren da Fadime take ya bude mata ya rika hannunta ta fito, sannan ya rufe motar yaja ta su kai gaba, ita dai tafiya kawai take tana sauraren hayaniya da kuma irin hanyar da suke bi, idan ta ji wani tunanin zai zo mata sai tai saurin kawar da shi.

“Kai dan Allah duk kana ganin mutanen nan?”

Direban ya kalleta sai ya ji tausayinta ya kamashi sanin cewar bata ganin komai, a lokacin ne ya gane lalli ga ni da ji wani babban ni'imace da Allah ke ma bayinsa.

“ina gani diyata”

Sai tai shiru ta cigaba da saurare tana ayyana yadda surar kowa take a ranta, a haka har suka shiga office din da Muhseen din yake. Ba su tararda shi cikin ba hakan yasa dole sai da suka dan jira ya dawo.

“Sai yanzu tun dazun na ke ta jira fa, likitan ma ya kusan tashi”

Muhseen din ya fada yana karasa gaban teburinsa.

“Ina kwana?”

Fadime ta fada sai ya wara ido da mamaki.

“Wow gaisuwa dai?”

“Eh ita wannan da kace mamata ce ita ce tace na rika gaishe da mutane, wanda ka ce dan'uwana ne ya zo tace na gaishe shi, kuma na gaishe da matarsa duk na gaishe su, tace ina kwana ake cewa da safe da rana ina wuni...”

Kai tsaye ta labarta masa wannan tana kallon saitin inda yake tsaye kamar tana ganinsa, kara bude ido yai da mamaki, sai ya ji ta burgeshi. Ya kalli direban

“Am za ka iya tafiya, idan an gama zan maida ita gida ko na kira ka kawo ka dauke ta”

“To ranka ya dade”

Direban ya fada sannan ya juya da sauri ya fice daga office din. After ya fita Muhseen ya dauki wayarsa ya kira likitan ya fada masa ga yarinyar an kawo, yana dagowa sai ya ga tana kallonsa baki bude ta gwalo ido waje kamar zata yagasu, a hankali ya sauke wayar ya baro tebur din ya karaso kusa da ita yana yawo da hannunsa a fuskarta sai ya ga tana bin hannun da kallon sai kara fito da ido take. Wani irin ihu ta saka tai cikinsa ta rumgume shi da mugun karfi, kamin yai wani yunkiri ita da shi sun kai kasa...!



Ina mata wadan da suke son sayen kaya kamar su laces, atamfa, materials,shadda lace, normal shadda, atamfa lace, veil's, shoes and bags, da sauransu kuzo ga MAMAN AHMAD tazo dan tashare hawayenku kudai kunemeta ta wannan number 08032350261 banan kadai tatsayaba tanada kayan order kama dana kitchen,tufafi,kuma order ta Bata dadewa ,tana saida kayan gyara kamar su Al'ajabu,shu'umar humra wannan inbakida aure Bama saida maki,hadin kaza me yasin,akwai na mallaka wanda wannan ana rubuta shi atafin hannu ke zakiyi wannan,turaren wuta,kulacca,da sauransu
Mazauninsu nanan a samaru Gusau Zamfara state
Muna aika kaya kowace jaha da wajen kasar nan cikin aminci da yardar Allah kunememu kusha mamaki

https://wa.me/qr/MYY56BH3RMFDG1



56

*Khadeeja Candy*

Da farko ya tsorata sosai zuciyarsa ta raya masa aljanunta ne suka taso, a hankali ya kara karanta mata ayatul kursiyo yana tofa mata a kai a hankali, sai ta zabura ta mike tsaye tana ta kalle kalle baki har kunne can kuma sai ta rufe idon tana dariya.

“Yasmin?”

Ya kira sunanta a hankalin bayan ya mike tsaye, sai ta bude idon ta juya bayanta ta ga wanda ake kira da Yasmin din, ganin babu komai a bayanta sai gina yasa ta juyo kalletashi, sai ya sake kiranta.

“Yasmin”

A nan ma juyawa tai kamar dazun ta duba bata ga kowa ba, sai ta juyo tana ta taba jikinta da fuskarta, A tunaninta ko ta canja kamanin ne.

“A ina nake?”

Ta daga kai tana karewa dakin kallo, a nan ta fahimci asibiti take.

“Taba min idon akai? Ai dai Wasim yace kar a taba idon, yace idan aka taba ba zai bude ba har a bada na shiga uku”

Ta fara kirkira kuka, a tunaninta aiki akai mata idon ya bude, shi dai Muhseen kallonta kawai yake ba dan ya fahimci yarenta ba, ba wai hausar ce baya ji ba, no the way da take maganar ne be gane komai ba.

“Waye kai? Waya kawo ni asibiti?”

Ta tambaya tana jin kamar ta dade tana bachi. Ya nuna mata kujera.

“Zauna”

Sai ta zauna tana murzar idon dake mata kaikayi, kuma tana jin kamar haske ya mata tawa.

“Ya sunanki?”

“Fadime a kauye, a birni Fateema”

Dan mamaki ne ya kama shi sai ya gane da gaske a hayyacinta take, amman abun mamakin dawowar tunaninta da idanuwanta a lokaci daya kuma a take kamar abun aljanu.

“Ina ne garinku?”

Ta yi shiru tana kallonsa, sai kokarin tuna abun da ya faru take.

“Laaa na tuna daga na gama cin abincin zan wanke hannuna sai na gan ni a nan me ya faru to? Waye kai? Ina Shattima da Bappa?”

Ya daga kafadunsa yana mata kallon ban fahimce ki ba.

“Daga wani kike?”

“Katsina, a katsina a kaita, a kaita a garin, kaita a bandalo, amman wani sarauyina Wasim wadan yake a garin Garuk ya kawo ni a garin Yola gurin wata mayya yace ta ga ajiya nan na kawo miki idan kin ga dama ki cinye idan kin ga dama ki aje....”

Shi dai kallonta kawai yake ba dan ya fahimce wani abun ba, sai ta sake komawa can baya ta dauko asalin yadda komai ya faru ta fada masa har zuwan su Bappa da tafiyar da za su yi a gobe.

“So Shattima na Yola kike magana kenan? And Iya mahaifiyar Hajiya Karama kenan?”

“Aa ba Hajiya Babba ba, ita wacan Zainab ne sunanta ai”

“Eh haka ake kiranta”

“Kuma na je zan wanke hannu sai kawai na gan ni a nan, amman dai wani abun kuka min nai bachi ko?”

“Aa wani brother na ne ya tsince ki a titi yana tare da matarsa, Aliyu da Ataa”

“Minene Ataa? Tsuntsu ne?”

Ta tambaya a bakin gaskiyarta domin ita bata fahimce mutun ne Ataa ba. Muhseen be san lokacin da dariya ta zo masa ba.

“Matarsa ce, sunanta Aisha Ataa i think sunan buzaye ne”

“Okay to yanzu kenan ba waya kawo ni asibitin?”

“Ni ne”

“To ina Shattima?”

“Nan ba Yola ba ne, kina Abuja ne, and you got lucky Shattima is my cousin”

“Abuja kuma? Na shiga uku? Waya kawo ni Abuja kuma? Innalillahi Wa'inna Ilaihirraji'un”

Ta dafe kanta.

“To ko Wasim din ne ya sake kawo ni? Ina ne Abuja ma?”

Kamin Muhseen ya ce mata komai wayarsa tai ringing, sai ya nufi wayar dake saman tebur ya dauka, at first ya dauka Mama Fulani zata tambaye shi ya jikin yarinyar sai dai yana picking sai ya ji wani mummunnan labari.

“Muhseen yanzu aka kira ni, wai Maijidda ta rasu”

“Wace Maijidda?”

“Yar wajen Waziri Diyar Hajiya Talatu”

“Innalillahi Wa'inna ilaihirraji'un, yaushe?”

“Yau, ni ma yanzu Ammy ta kira ni sai kuka take”

“Allah ya mata rahama, yaushe za ki je?”

“Gobe tun da safe Inshallah”

“Allah ya kai mu, ni ma gani nan zuwa yanzu”

Ya sauke wayar cikin rashin jindadi daman can sanarwa mutuwa ba ta yi ma mai hankali dadi.

“Dan Allah ka kira Shattima ka fada masa ya fadawa Bappa ina nan su zo su tafi da ni”

“Rasuwa akai musu ba zan iya kiransa a yanzu ba”

“Waya rasu? Allah yasa ba Iya ba ce ta sake cinye wani”

Muhseen ya mata kallon tsaf ita ko ta sako masa ido tana son jin amsarsa idonta kamar za su yi magana.

‘It can be possible, kai no... Be kamata ya yarda da zancen yarinyar nan ba, daga ganin yadda take da surutun nan za ta yi karya’

Ya fada a ransa.

“Dan kawai kin ji labari haka sai ki ce Iya mayya ce kin san shekarunta a idan nan?”

“Ko ma dai wacece Wallahi mayya ce, kuma ka tambayi Shattima idan baka yarda da ni ba shi ya yarda da ni”

Be ce komai ba ya zauna yana ta kallonta wata zuciyar na raya masa duk yadda akai aljanu ne suke dawainiya da ita ko kuma ma aljanar ce maybe. Baya son kiran Shattima a irin wannan lokacin amman ya zame masa dole ba dan ya labarta masa komai ba sai dan ya tambaye shi. Few seconds wayar tai tana ringing ya daga ba tare da yace komai ba, domin har ga Allah yana cikin damuwar da idan ma ya dauki wayar be san abun da zai fada ba.

“Shattima”

“Muhseen”

Ya kira shi yana shafa fuskarsa cike da damuwa.

“I know mun rasa Maijidda be dace na zo da new thing ba yanzu, amman tambayarka kawai zan yi”

Shattima yayi shiru be ce komai ba, wanda hakan ke karantar da Muhseen cewar ya ba shi izinin magana kenan.

“Wata yarinya muka tsinta day before yesterday, tace sunanta Fateema kuma ta... ”

Muhseen be gama ba Shattima ya mike tsaye da sauri rike da wayar.

“A ina kuka ganta? Tana kusa da kai? Bata wayar”

Shattima ya fada har kalaman na hade masa, Muhseen ya saka wayar a speaker ya mikawa Fadime, sai ta ta so ta amsa ta kai a kunnenta.

“Hello Assalamu Alaikum”

Shattima ya lumshe ido tare da saka hannunsa yana taba hancinsa.

“Shattima Fadime ce...”

A hankali ya hade yawun bakinsa sannan ya ce.

“Fateema ina kika je?”

“Ni ma ban sani ba, shi wannan mutumen...”

“Muhseen”

Muhseen ya katseta tare da fadar sunansa.

“Muhseen ya ce wai ina nan Abuja kai ka kawo ni?”

“Ba ni na kawo ki ba”

“Amman ai yace shi dan'uwanka ne”

“Ba ni a kawo ki ba, nemanki kawai mu kai mu ka rasa but Alhamdulillah”

“Kuma idona ya bude ina ganin komai har wannan mutumen da ke tsaye gabana ina ganinsa”

“Da gaske?”

“Wallahi kuwa amman a asibiti muke, ban sani ba ko ya taba min idon ne, kuma Wasim yace idan aka taba min ido a zai bude ba”

“Hey... Karki sake maganar wani Wasim ko Hajiya Karama ko Iya, mutanen nan ina tunanin suna da hannu a abun da yake samunki, and now babanki yayi fushi ya tafi, sai kuma aka tsince ki Abuja? Wannan wane irin abu ne?”

“Bappa ya tafi?”

Ta tambaya tana shirin fashewa da kuka.

“Zan kira anjima”

Ya katse kiran wanda hakan yayi daidai da saukowa hawaye a idon Fadime. Muhseen ya karbi wayarsa yana kara yarda cewar ta san Shattiman da kuma labarin da ta ba shi na Iya da Zainab.
Fashewa tai da kuka marar sauti tana ta sharar hawaye, shi dai be ce mata komai ba ya fita ya barta a office din.
Sai da ya gama abun da zai yi sannan ya dawo ya dauki abun da zai dauka ya ce mata ta ta so su tafi.

Sai da ya ga tana bin hanya daidai sannan ya mara tabbatar da tana gani, ko a gurin motarsa ma ita da kanta ta bude ta shiga ta zauna, sai dai bata daina hawayen ba har ya fara tuki.

“Ki daina kuka idan aka maida ke gurin Shattima sai ya saka a kaiki gurin mahaifinki ai”

“To”

Ta share hawayenta, tana bin titin da kallo.

“A ina kuka tsince ni a kasa?”

Sama sama ya labarta mata abun da Aliyu ya fada masa, suna isa gidan Mama Fulani ta fara bude ido tana kallon katon gidan.

“Nan ne gidan ka?”

“Gidan Mamata”

Ya amsa mata yana bude motar ya fita, sai ita ma ta bude ta fito tana mamaki kato gida kamar wannan ga tsari da kyau kamar gidan minister. Yana gaba tana binsa sai kalle kalle take gaba daya ta zama bakauya har da kai hannu ta shafa fentin da take ganin yana ta wani haske. Bata kara raina kanta ba sai da suka shiga cikin falon, kamar yar gida haka ta zama domin ta riga Muhseen isa gurin kujeru sai dai bata zauna a kai ba ta zauna a kasa ganin manyan kujeru ne na alfarma, Muhseen kuma ya zauna a daya daha cikin kujeru kamin yai mata magana yace ta taso ta zauna akan cushion dina, har ta mike tsaye ita ta zauna akai tana kallon fuskarsa ta ga ko hanata zai yi ko kuma yace ta sauka, haka ta daga kai tana ta kallon falon mamakin duniya ya cika ta, irin gidan da bata taba gani ba yau ga ta a ciki.

“Ku nawa ne a nan gidan nan?”

Ta tambaya tana mamakin katon gida kamar wannan ace na mamansa ne, Muhseen ya nuna mata Mama Fulani da ke saukowa rike da tissue da alama hawayen mutuwar yar kanenta be tsaya mata ba har yanzu. Fadime na ganin Mama Fulani ta san ba irin iyayen nan ba ne masu daukar nonsense ga ta da jikin dake nuna arzikinta a fili tufafin jikinta ma kadai sun isa shaida. Saurin sauka tai ta zauna a kasa tana gaishe ta tun kan ta karasa saukowa.

“Sannu da zuwa Ina wuni”

“Lfy Kalau Yasmin”

Mama Fulani ta amsa sannan ta nufo kusa da Muhseen ta zauna, har lokacin bata kura Fadime na gani ba, domin hankalinta be kai kanta sosai ba.

“An dubata ta?”

“Ba zancen dubawa yarinya ta tashi”

“Kamar?”

Ya nuna mata ita, tana kallon Fadime sai Fadime ta sakar mata murmushi, Mama Fulani ta kalli Muhseen ta sake kallon Fadime.

“Tana gani kenan?”

“Ba gani kadai ba har komai ta tuna”

“Magani kuka bata?”

“Aa...”

Ba karamin mamaki ne ya kama Mama Fulani ba, da Muhseen ya labarta mata abun da ya faru, can kuma ya tsakuro daga labarin da Fadime ta bashi ya samman Mama Fulani inda be yi daidai ba Fadime ta gyara masa, daga nan ya sakar mata linzamin ta labartawa Mama Fulani komai. Kamar almara haka Mama Fulani ta ji abun mamaki da al'ajab suka rufeta lokaci daya.

“Ashe ita take cinye mana zuri'a? Ba sididi ba sadada daga gamon tsintsiya da zagga? Ban zumuntar uwa ba ta uba take mana wannan sherin ba duk abun alherin da aka mata?”

“Ita da yarta mayyu ne, har yar mayya ce”

Fadime ta fada tana tsina fuska domin ita har ga Allah ta dauka Zainab mayyace.

“Lallai kuwa ai biri yayi kama da mutum, tana zaune a gida tana cinye mana zuri'a ko wannan ma waya sani ko ita ta cinye ta tun da Waziri ya fada min ya bawa Shattima ita? Tabbas ita ce ita Ammy ma take ne Fisabilillahi? Wace iri mata ce wai? Ta san da wannan ta zuba bata yi komai ba? To Wallahi ba zata sabu ba bindiga a ruwa, Allah ya kai ni Yola gobe lafiya Na rantse da Allah sai Iya ta bar garin nan, ta koma can inda ta fito, ba dan ma guduna alhaki ba ba zan barta da rai ba”

“Ashe ma ba ma yar garin ba ce amman yarta har wulakanci take wa mutane tana cewa kar a hau mata a kujeru ta barin mutun ya kwanta ba ko abun lullubi”

Fadime ta fada tana tuna abun da Zainab tai mata. Sai Mama Fulani ta biye ta kamar mai fira da sa'anta.

“Ba yar nan ba ce, waya san ma inda ta fito wata kila maitar tasa aka rokota ta zo nan ta lake har suke mata gata, amman shi Mai Martaba ya san da wannan zancen?”

“Wai daman shi Sarkin yana da rai? Ai na dauka ya mutu saboda wannan matar Hajiya Babba ta tafi tace a kashe shi kashe Shattima...”

Fadime ta fada tana kallon Mama Fulani da ta mike tsaye tana nuna ta, Muhseen ma gyara zama yai yana mata wani kallo.

“Keeee idan kika min karya sai na saka an yankaki an daddatsa namanki an zubar ni nan Fulani ba uban da isa yai komai”

Fadime ta sako mata ido hantar cikinta na kadawa, Mama Fulani dai ba tai mata kama da mayu ba, duk da kasancewar gidan yana mata kama da na masu yankan kai, to amman me ya kawo maganar yanka da daddatsewa daga bada labari, ta fara kuka.

“Na shiga ukuna”

“Ba wani kin shiga uku fada min gaskiya, ta ya akai kika sani...?”

“Zan dafa miki qur'ane kuma na yarda ki kira Shattima ki tambaye shi Wallahi ba karya zan fada miki ba”

Maman Fulani ta koma ta zauna tana kallon Muhseen da ke kallon Fadime. Tun daga salsalar zuwa garinsu Wasim har zuwan su Hajiya Babba da duk abubuwan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login