Showing 234001 words to 237000 words out of 286946 words

Chapter 79 - Fulani Book 1 Hausa Novel Complete

20 Dec 2024

924

da suka yi har kawowa zuwanta gidan da yadda ta labartawa Ammy komai sai da ta fadawa Mama Fulani. Mama Fulani bata san lokacin da ta daki kirjinta ba ta sake daka har sau uku.

“Dan'uwan nawa za a kashe? Ita Hajiya Balki rashin imaninta har ya kai haka? Akashe shi a kashe Shattima? Yanzu ita Ammy ta ji duk wannan abun amman ta share take zaune ta saka musu ido? Ko kuma ita ma asirin suka mata da bata iya komai? Ba zan dauka ba, na san dai na yi rashin mutunci a baya ammn ban yi rashin imani kamar na wannan matar ba, mijinta na sunna? Saboda Sarauta? No wonder ciwo yai ma Mai Martaba yawa, Mata ta yi yan'uwa su yi jamar'ar gari su yi, ba ma wanda zai fi kamar n matarsa tun da dole ne ta bashi ya ci, ai dole ne gobe Mai Martaba ya ji wannan maganar kuma dole, za ki iya maimaita wannan maganar a gaban kowa ko?”

“Eh Wallahi zan iya”

Fadime ta fada with full confidence. Mama Fulani ta mike tsaye ta nufi upstairs sai bala'i take.

“Kuma Wallahi Nana ba zata auri danta ba, muguwar mata kawai mai bakar zuciya...”

Sai da ta wuce Muhseen ya baro inda yake zaune ya motsa kusa da Fadime ya kai hannunsa ya kama lebenta yana ja.

“Kin gani wannan bakin na ki, zai kai ki ya baro, daga ganin ki na san zaki yi surutu, i wonder how Shattima ya zauna da ke shi da baya son hayaniya, kin ga yanzu kin takalo wata fitinar Mama Fulani ba zata kyale wannan maganar ba, kuma at end idan karya kike kin jefa kanki a matsala ko ma da gaske ne, za su iya wanke kansu ke ki kwana a ciki, kin san waye Hajiya Babba kuwa? Wannan bakin na ki wata rana sai ya yanka ki, wata kila shiyasa akai miki wani asirin aka kawo ki Abuja aka mantar da ke komai”

Wani tsoro ne ya kama Fadime jikinta ya fara rawa.

“Kenan yanzu ni za a jefa a matsala?”

“Ban ce kuma, amman ki san irin maganar da kike fada, kin ga Mama nan bata saurarawa kowa kan nata, ina tunanin ma yanzu waya ta je ta kira, kin ga kin ta da rigima a gidan Sarauta, sai an zo gurin magana ganki yar ficika ba wani auki”

Fadime ta taba jikinta tana jin wata zababbbiyar yunwa na taso mata.

“Ni yunwa ma na ke ji”

“Wato har yunwa kike ji? Duk baki ga abun da kika yi ba hankalinki kwance ko?”

“To ni wai ina ruwana ba su suka je suka yi ba, dan na fada kuma sai ya zama laifi, ma na Taimakawa Mai Martaba ban ai sai a karramani”

Ta fada tana turo baki gaba, tsoro dai kam ta ji shi, amman sam bata ga laifi a abun da tai yi ba. Muhseen yayi murmushi yana kallonta kamar yadda take kallonsa da fararen idanuwanta.


SHATTIMA POV.

Shattima ya kalli Ammy bayan sauke wayar da yai a kunnesa.

“Fateema ce wai an ganta a Abuja hannun Muhseen”

Ammy ta kalleshi duba irin na mamaki duk da kasancewar bata cikin yanayin dadi, bata damu da hawayen da ke fuskarta ba ta ce.

“Wane Muhseen din?”

“Na Mama Fulani”

“A Abuja kenan?”

“Eh ina tunanin abun da nai ma Hajiya Karama ne yasa ta janye kudirinta a kan Fateema, ita kuma mahaifiyarta ta kashe Maijidda”

“Ba ka da tabbacin yarinyar ta bata ne saboda Zainab, sai na ke jin kamar babu sa hannunta a ciki, kuma be zama lallai dan Maijidda ta mutu ba ace Iya, domin Waziri ya fada min asibiti sun ce tafoit ce, amman na san mahaifiyarta da kowa kai zai zarga, idan har Iya ce ai ita sai ka aura suke mutuwa wannan kuma tun kamin ayi auren ta rasu”

“Mai son abun ka ya fika dabara Ammy, bana iya gane komai a yanzu, ba zan iya cire Iya daga zargi ba, kamar yadda zuciyata ta kasa aminta da Zainab”

“Ka tafi gurin jana'izar kar ayi ba kai”

A hankali ya sauke ajiyar zuciya, sannan ya fice daga dakin, Ammy ta share hawayenta ta mike tsaye ta nufi dan karamin dakinta dake gefen wardrobe inda take canja tufafi, wani yadi marar nauyi ta saka ta saka Hijabinta sannan ta fito, sai kuma ta zauna bakin gadonta ta dafe kanta, babu wanda take tunani sai Hajiya Talatu, da Waziri duk da kasancewar ta san Baba Waziri mutum ne mai tawakkali sai dai be zama lallai Hajiya Talatu ma tai ba daman can ba son ta take ba balle kuma yanzu da zata ga kamar saboda za a hada auren yarta da Shattima ne ta mutu. Ammy ta kusan awa daya a dakin kamar mai kunyar fita, tana tunanin mikewa tsaye ta fita sai wayarta dake gafen gadon tai ringing, Hannu ta kai ta dauka ganin number Mama Fulani be bata mamaki a tunaninta ko zata sake wata maganar ko kuma ta fada mata cewar tana tafe.

“Ammy...! Yarinyar ta fada miki abun da ta fada min?”

“Kamar na me?”

Mama Fulani ta labarta mata kadan, sai Ammy ta sauke ajiyar zuciya.

“Ta fada min”

“Amman kike zaune a nan? Har kina kallon Hajiya Balki? Kai ba ma Hajiya ba Balki zance, ta ashe miji da ta kashe miki miji ta tarwatsa rayuwarku?”

“Ba komai ya kamata na yarda da shi ba, domin babu hujja kwarara a kan haka, idan nai tunani sai na ga ita ma ai tana da yaya fiye da yadda na ake da su da Mai Martaba, to mai zai saka ta aikata haka? Ko da ma ace akwai Hujja, idan nai unkurin yi mata wani abun za a zargi ko dan tana kishiyata ce ina son na kashe mata aure ne, kuma idan yarinyar kadai bata isa shaida ba”

“To zauna nan kina jiran hujja, ai komai bincike yake so, kuma idan aka titseta dole wata rana a gano gaskiya, ke ma dai ina ganin sun dan taba ki kin zama wata Salahu zaune kawai kike a gida?”

“To Fulani ya zan yi? Mijina ba lafiya, duk wata dawainiyarsa da kula da shi akaina yake, ga yayana ma ba su cikin natsuwa Nana ma daga baya baya nan ne na samu ta natsu, ga jama'ar gari da yan'uwa, ga Hajiya Balki ita kanta, abubuwa sun min yawa kwakwalta a cushe take”

Ammy ta fashe da kuka tana jin kamar ta mutu ta huta.

“To ni tawa bata cushe ba, na kira wayar Waziri bana same shi ba, ki aika a fada masa na ce kar a kai Maijidda a kabari a kira Iya ta tsallakata”

“Tafiya kam Maijidda ta tafi Fulani, sai dai fatan samun rahama”

Haushi ne yasa Mama Fulani ta kashe wayar, Ammy ta mike tsaye ta saka wayar a jakarta sannan ta fito ta rufe dakinta. Ko da ta fito direbanta har ya faka mota yana jiranta, daman tun da ta saka Jekadiya ta fada masa yake jiran fitowarta, fitowa yai da sauri ya bude mata ta shiga, sai dogaran da suke dayar motar suka matso da motarsu gaba.

“Ka fada musu kai kadai zaka kai ni, gaisuwa ce bana bukatar rakiya”

“An gama ranki ya dade”

Ya fita motar da sauri ya isa gurinsu ya sanar musu sakon Ammy, sai suka ja motar zuwa inda aka saba ajeta, shi kuma ya dawo cikin motarsa ya shiga.

“Allah ya ja zamaninki ya kara miki lafiya”

Ammy dai bata ko kalli inda yake ba har suka isa gidan Waziri, a nan Ammy ta dauko mask dinta ta saka, daker suka samu gurin fakin a cikin gidan saboda motocin da suka cika gidan, haka Ammy ta fito ta ratsa cikin mutane tana sanye da hijabinta da kuma face mask ta wuce cikin gidan domin wajen gidan maza ne a ko'ina.
  Hankalinta be kara tashi ba sai da ta shiga bangaren Hajiya Talatu, baka jin komai sai dariyarta dariya bata wasa ba, irin dariyar da ake kyalkyaltawa wanda ake cewa bata da kyau ko a musulunci, mutanen da suke falonta kuma suna ta aikin kuka, kanen Maijidda da yayenta babu mai iya ba wa wani hakuri, Ammy bata san lokacin da hawaye suka fara saukowa mata ba, sai jikinta yai sanyi sosai.


HAJIYA BABBA POV.

Haka ta wuni ta kwana ba eh ba aa, bata cewa komai kuma duk abun da aka bata bata ci, sai dai tai ta kallon mutane, idan aka ce ci sai ta bude baki ta saka ta tauna amman ta kasa hadewa, haka take a ruwa ko tea ko ruwa duk abun da ta saka a baki ko yayanta suka saka mata sai ta kasa hadewa sai dai ya dawo mata. At first sun dauka ko damuwar abun da Sirleem ya aikata ne, sai dai ganin har an kwana an wuni bata canja ba gashi tsawon dare bata runtsa ba ya fara bawa Karima da Jurry tsoro. Sirleem kan tun da ya bar gidan be dawo ba sai washe gari misalin takwas a tunaninsa zuwa lokacin abun ya sauka a ranta ta dan huce. Ko da ya shigo dakin Kausar na zaune kusa da ita ta kama hannayenta ta rike sai kuka take.

“Hajiya ina kwana”

Ya fada da tunanin zata amsa masa ko da a cikin fushin ne, ko kuma ta kalli inda yake amman ba tai ko daya ba.

“Ba ta yi magana ba tun jiya, kuma komai aka saka mata dawowa take da shi, bata cewa komai kuma ba ta runtsa ba har garin Allah ya waye”

Sirleem ya mike tsaye da sauri ya karasa kusa da ita ya kama kafafuwanta ya rike.

“Hajiya dan Allah ki yafe min? Dan Allah ki yi magana, ki yafe min Hajiya”

Tana bude bakin da zimmar magana sai bakin nata ya juye ya bar muhallinsa koma gefe daya, wato gefen kuncinta na hadu.

“Innalillahi Wa'inna Ilaihirraji'un, Hajiya”

Ta kalleshi yawu na zazzago mata kamar wata musaka. Take Sirleem ya fashe da kuka.

“Dan Allah ki yafe min Hajiya, ba zan sake tsaba umarninki ba, kuma zan saki Falmata yanzu, zan auri Nana, Wallahi ba zan sake saba umarninki ba”

Ya juya ta sauri ya fice daga dakin, Kausar ma ficewa tai da gudu tana kuka. Sai ga Jurry da Rima sun shigo hankali tashe, su suka rikata ta mike tsaye da taimakonsu suka saka ta mota zuwa asibiti, suna isa abun ka da babbar asibiti kuma ga ta matar babban mutum sai su karbe ta da sauri suka shiga yi mata gwaje gwaje. Bata motsa ba sai da aka soka mata allura za a debi jininta.

“Washhhhhhhh”

Ta fada yawu na biyowa ta bakinta da yaki rufuwa. Duk iya gwanje gwajen da sukai ba su gano ciwom komai ba, domin da farko likita ya dauka ko hawan jini ne domin shi ya fi yiwa mutum haka, sai dai ya auna ba awo daya ba be ga hawan jinin ba.



SIRLEEM POV.

Driving yake hawaye na sauko masa kamar ba gobe, ko a lokacin da ya rasa mahaifinsa be yi zubar hawaye masu zafi kamar yanzu ba, domin a yanzu yana ganin idan Hajiya ta mutu shi ne sila, domin be taba ganinta a hali makamancin wannan ba, be taba tunanin abun zai taba ta har haka ba.

“Hajiya dan Allah ki yafe min”

Ya fadi haka yana tukin ya fi a kirga, jikinsa sai rawa yake, kukan da yake ya saka zuciyarsa sai zafi take, kuka yake bana wasa ba, kuka irin na mace hawaye sun sama sa'ar lalata masa fuska, sai da ya iso gidan Momy sannan ya ciri tissue ya goge fuskarsa, rabonsa da gidan tun jiya da ya shiga ya ga Falmata sai dai be yi maganar komai da ita ba ya fito, be kuma koma gurin Hajiya Babba ba sai ya wuce gidansa ya kwana a can. A harabar gidan ya faka motarsa, ya bude gurin da yake aje paper, ya dauko diary ya dauko bironsa, sai ya dora kansa saman sitiyarin motar ya yana hawaye yana jin zuciyarsa kamar zata rabe gida biyu. Sai dai ba shi da zabin da ya wuce haka, sai dai har ga Allah baya son sakin Falmata. Dago kansa yai ya runtse ido ya cige bakinsa hawaye na cigaba da sauko masa, daker ya bude idon ya bude diary ya dora hannunsa dake rawa yai rubutu a jiki, sai ya fashe da kuka kamar ba namiji ba. Sai kuma yai sauri zarar tissue ya goge fuskarsa ya cire paper da yai rubutun a jiki ya bude motar ya fita. Brown jallabiya ce jikinsa kana ganinsa ka san yayi kuka ba kadan ba domin idonsa da farar fuskarsa ya nuna, sai da ya sauke ajiyar zuciya ya fi a kirga sannan ya nufi entrance din ya fara takawa har ya isa gaban kofar falon, wasu hawayen ne suka cika masa ido sai yai saurin sharewa ya danna door bell din. Babu bata lokaci Momy ta bude masa kofar daman tana zaune falo cikin shirinta na tafiya office domin duty safe take.

“Sirleem Lafiya?”

Sai ya kasa kallonta kuma ya kasa ce mata komai har ta ba shi hanya ya shigo cikin falon.

“Ina Falmata?”

Ya tambaya daker tana danne numfashinsa dake fisga.

“Tana sama, wai me ke faruwa ne? Tun jiya bata ci komai ba ko tea da na kai mata da safen nan bata sha ba, ni ban gane komai ba kuma...”

Kamar zata labarta masa zancen Ameer, sai kuma tai shiru ganin kamar be dace tai maganar ba a irin wannan lokacin da damuwa da samu muhalli a fuskar Sirleem. Be ce ma Momy komai ba ya nufi upstairs din zuwa kamar baya som tafiya, Momy dai ta bishi da kallo har ya haye sama ya shiga dakin Ameer inda Falmata take.
Yana shigowa Falmata ta mike tsaye da sauri tana kallonsa, shi ma kallonta yake sai hawaye suka samu hanya a idonsa, tana ganin haka jikinta yai sanyi sai ta hade hannayenta guri daya nata idanuwan suna ma hawayenta lalle marhabun. Takawa tai ya karasa kusa da ita yana kallonta sai kuma ya rasa abun da zai fada mata, ita ma kallonsa take tana hawaye daman ta dade da raya cewar Hajiya zata cilasta shi ya sake ta.

“Ka sake ki Sirleem matukar sakina zai saka Hajiya ta yafe maka, ka sake ni matukar sakina zai shirya tsakaninku da Hajiya...”

Ta fada ararrabe saboda kukan da ke cinta. Kansa ya daga sama ya kalli pop tare da jan numfashi ya sauke, sannan ya sauke idonsa a kanta, cike da nauyin kafa ya cira ya taka zuwa inda take tsaye sai ya rumgume ta tsantsan a kirjinsa kamar zai sakata cikin jikinsa, hakan da yai sai ya bata damar fashe kurjin kukan da da ya girma yai kumbura a zuciyarta, ta dago hannayenta ta rike rigarsa saitin kirjinsa tana ta kuka kamar ranta zai fita, shi ma hawayen yake sai daya jika dankwalin kanta.

“I love you, Sirleem Love you so much”

Ya furta cikin muryar mai karkarwar kuka, sannan ya hade yawun bakinsa ya sake ta ya kama hannunta ya danka mata takarda, karba tai tana wani irin dauke numfashi tana kallon fuskarsa tai baya baya sai ya juya da sauri domin ba ya son hada ido da ita, cikin hanzari ta kai hannunta ta kamo hannunsa.

“Sirleem karka bar ni dan Allah, idan ka tafi ban san ya zan kasance ba, kai ka kadai ne gata a yanzu kai ne rayuwata...”

Ta fada tana jin wanin irin yanayi da bata taba jin kanta a ciki ba, idonta har wani hayaki suke.

“Ni kuma mahaifiyata ita ce rayuwata, ba zan iya jabar ki na bar mahaifiyata ba, ban taba ganin Hajiya a irin halin da na ganta a yau ba, ba zan jama silar bakincikinta ba...”

Ya saka dayan hannunsa ya banbanre hannunta da ta rike hannunsa na dama da shi, ya fice daga dakin cikin sauri. Faduwa tai kasa tana wasu kalar hawaye masu zafi da kona fuska sai ta matse jikinta ta rumgume kanta tsantsa, ta sauke idonta akan hoton mahaifiyarta.

“Ma... Ma... Ma... Mama...”

Ta furta daker muryarta na rawa, wani irin abu ta ji kamar zuciyarta zata kone mata kirji, faduwa tai durkushe ta kasa yarda Sirleem ya rabu da ita a lokacin da ta fi tsananin bukatarsa. Mikewa tai tsaye ta fita dakin da gudu, yadda ta sauko downstairs din ma sai da ya ba Momy tsoro kamar zata tashi sama haka ta nufi kofar falon ta bude, ta bi motar Sirleem dake kokarin fita gate tana wani irin kuka tana kiran sunansa.

“Sirleem.... Sirleem.... Sirlee....”

Bata karasa sakamakon shakewar da muryarta tai sai ta fadi a harabar ta fashe da matsanaicin kuka. Momy ta fito da sauri ta yo kan Falmata ta kamata.

“Lafiya?”

Kamar mai jira sai ta juyo da sauri ta kama hannayen Momy ta rike gangam.

“Momy ya sake ni, Sirleem ya tafi ya bar ni dan Allah Momy ki ce ya dawo...”

“Innalillahi Wa'inna Ilaihirraji'un”

Momy ta furta cikin rudani da rashin fahimta. Sirleem ma tukin yake yana hawaye yana jin jikinsa kamar ba shi ba numfashinsa har kokuwa yake da shi.



Ina mata wadan da suke son sayen kaya kamar su laces, atamfa, materials,shadda lace, normal shadda, atamfa lace, veil's, shoes and bags, da sauransu kuzo ga MAMAN AHMAD tazo dan tashare hawayenku kudai kunemeta ta wannan number   08032350261  banan kadai tatsayaba tanada kayan order kama dana kitchen,tufafi,kuma order ta Bata dadewa ,tana saida kayan gyara kamar su Al'ajabu,shu'umar humra wannan inbakida aure Bama saida maki,hadin kaza me yasin,akwai na mallaka wanda wannan ana rubuta shi atafin hannu ke zakiyi wannan,turaren wuta,kulacca,da sauransu
Mazauninsu nanan a samaru Gusau Zamfara state
Muna aika kaya kowace jaha da wajen kasar nan cikin aminci da yardar Allah kunememu kusha mamaki

https://wa.me/qr/MYY56BH3RMFDG1
57

*Khadeeja Candy*

Tana yunkurin ta tashi sai ta ji cikin ya mata nauyi kamar an jefa mata katon dutse a ciki, da farko ta yi tsammanin ko dan ta cinye naman ne duka duk da ta san bata saba haka ba, ko mugun ci tai yana da wahala ta gagara tashi. Jinginawa tai da gadon tana dan hutawa na mintuna kamin ta sake yunkura ta ji ya fi na dazun nauyin gashi ba ciwo yake mata ba. Kallon cikin tai da mamaki yana da da girmansa kamar da, amman ya mata nauyin da bata isa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login