Showing 171001 words to 174000 words out of 286946 words
mutum nake bibiya, na cinye masa mata yanzu kuma yayansa na ke bibiya, kaga kenan mayya ce ko?”
Shiru Shattima yai yana tunani rage gudun motarsa.
“Waya fadi haka?”
“Ita wannan tsohuwar mai magana kamar gere kyankyankyan...”
Fadime ta kwaikwayi muryar Iya tana matse baki kamar tsohuwa. Shattima yayi murmushi duk da kasancewar yana cikin rudani da tunani. Sai a lokacin tunani ya zowa Fadime, what if shi ma danta ne? Ko Kuma yana da alaka mai karfi da ita?
“Wannan tsohuwar mamanka ce?”
“No”
“Kakarka ce?”
“No”
“Kanwar mamarka ce?”
“Oh...No”
“To miye alakar da ita?”
“Tana zama a gidanmu ne kawai kamin ta dawo nan”
“To yarta fa? Ita ma baka da alaka da ita?”
“Yes”
“Ko dai budurwarka ce?”
“No kin cika tambaya”
“To ina zaka kai ni?”
“Ina na sani, kin zame min kaya”
Can kuma ya kalleta yana murmushi yace.
“Bakin titi ki yi bara”
“Lalala ai ni ba makauniya bace makafi da nakasassu sune suke yin bara Allah ya tsare ni nikam”
Shattima ya faka motarsa gefen titi yana tintsirar dariya kamar ba shi ba.
“To ke micece?”
“Ai ni ba haka aka haife ni ba, kuma idona zai bude, kuma maganar nan ta min zafi”
A take idonta ya cika da kwalla domin har ga Allah ta ji zafin da ya kirata da makauniya har ta furta kalmar bara a gareta.
“Duk matar nan ce da ja min shiga wannan hali, da bata je garin ba da ban bita ba, ni Wallahi yanzu idan na ga wani zai je ma hana shi zan yi, duk bakina na yaje min nace mata na san wanda zai kaita, salo gareni Allah yayi min shegen salo (Banbandanci)”
Shattima ya jingina da jikin kujerAR motar yana dariya.
“Wace mata kuma?”
Ta fara bashi labarin abun da ya faru tun daga farko har karshe.
“To ai ita ce wannan matar wacce muka baro gidanta yanzu, ba a motata kuka hadu ba kika ce mata kin sa gari”
“Haka ne haka ne...ita ce?”
Ta daki kirji.
“Har take min wannan wulakancin? Har take ce min na sauka a kujera? Har take min tsawa? Har take min fada? Lallai dan adam butulu ne, lallai wannan matar ba zata ga annabi ba, mayya kawai yar mayya, masu bakin hali da mugun nufi, Allah yasa idanuwana suna budewa nata su rufe, amman ba zan taba yafe mata ba, ai wannan zallumci ne, ko tausayina bata gani? Wayyo Allah”
Kuka take sosai tana jin zafi abun da Zainab tai mata.
“Allah ya saka min a gareta da duk wanda yai sanadiyar haduwa ta da ita”
Shattima ya dago ya kalleta.
“Har da ni kenan?”
Ba dan tana tsoron kar ya sauke ta a hanya ba, da ko amsa masa ba za tayi ba.
“Aa bacin rai ne ya kawo haka, na yafe maka”
Ta fada cikin kuka, ba dan ta yafe masa a zuciyarta ba. Murmushi yai ya ja motar suka koma kan titi. Maganarta ta dazun ce ta dawo masa a rai, cewar wani mutum take bibiya ta cinye matansa kuma tana bibiyar yayansa, me hakan yake nufi? Baya son ya munana tunaninsa, amman har ya fadada tunaninsa mutumen daya fada ba yi kama da kowa ba sai shi! And lastly Ammy ta fada masa cewar ta talla Zainab, miyasa bata ji tsoron kar Zainab din ta mutu ba?
“Bayan haka kin ji wani abu?”
Ya tambaya yana kallonta, sai ta girgiza masa kai domin ba zata iya amsawa ba saboda kukan da take na bakincikin abun da Zainab tai mata.
“Wallahi da na san ita ce, ko tace na sauka a kujerar nan zan ce mata ba zan sauka ba, idan tace matsa can n ace ba zan matsa ba, hala ba saboda ke na samu matsala ba? Wallahi na fita iya iskanci yar daba ce ni idan bata sani ba, har ta isa?”
Shattima ya saka dariya, yana mamakin yadda ta rike abun a ranta ta kasa sakinsa.
“Dan Allah ki bar ni nai tunani, i need to think”
“To think Mr thinker...”
Ta fada cikin kuka, sai yai murmushi ya kai hannunsa yaja dogon hancinta.
“I like you idan ba ke ba ba zai miki haka duk a garin Yola?”
Ya saka dayan hannunsa ya dauki wayarsa ya nemo number Jekadiya. Bugu daya ta dauka tana rangada masa kirari.
“Jekadiya, dan Allah a nemo yariyar nan gobe”
“To an gama ranka ya dade”
Ya aje wayar kamar yadda ya saba ba tare daya kashe ba. So yake yayi ma Falmata wasu tambayoyi he need to confirm something. Ya kalleta har lokacin kuka take.
“Baki gajiya da kuka?”
“Baka san yadda nake ji ba, na taimaki matar nan amman shi ne zata saka min da haka? Ai ko bata san ni ba be kamata tai min haka ba, dan'adam yana da daraja, mu mutanen kauye ba mu san mu wulakanta mutum ba”
“Bata kyauta ba, sorry amman ba ganina nan ba? Zan kai ki gida gobe inshallah”
Ya zari tissue ya dora mata a cinya.
“Share hawayenki da wannan”
Ta dauka ta share ta goge majinar ta mika masa.
“Gashi”
“No kefa shi can”
Ya sauke gilashin motar na side dinta.
“Ina?”
“Gefenki ta gurin da kike jin iska”
Ya mika hannunta ta jefar.
“Ina zaka kai ni?”
Ya daga kafadunsa alamar be sani ba duk da ya san bata ganinsa, not knowing where to take her, yadda take da yawan surutu ba zai iya kaita masarauta a yanzu ba, domin zata je ta basu labarin maita na Iya, and if Ammy ta san yaje gidan Zainab she won't be happy. Bashi da zabin daya wuce ya kaita gidansa kamin gobe, ya sake dauko wayarsa ya kunna data da kansa dan siyen ticket din mutum biyu, shi da ita na zuwa Katsina gobe.
FALMATA POV.
Sai da tai kamar ta koma cikin gidan ta fadawa Jekadiya cewar tana son ta cigaba da aikin kamar yadda ya bata dama, sai kuma wata zuciyar ta hanata, sai ta nufi gate din kai tsaye da zimmar ficewa, a tunaninta cigaba da aikin karin wata barazanar ce a gurinta, domin zata iya shiga wata matsalar kuma bata san abun da zai kara biyowa ba, wata kila ma yafi wanda ta shiga a baya. Bata karasa gate din ba motar Sirleem ta kunno kai cikin gidan, yana kawowa daidai ita ya tsaya ya sauke gilashin motarsa, bata lura da shi ba har sai da ya kira sunanta.
“Falmata”
Ta kalli motar ganin shi ne yasa ta tsaya ba tare da ta ce masa komai ba, hannunsa ya mika ya bude mata dayan side din.
“Zagoyo nan”
Ba musu ta zagaya tana dingishi, shi kuma ya bita da kallon tausayi har ta shiga motar ta zauna.
“Rufe”
Ta mika hannu ta janyo ta rufe.
“Ina wuni?”
“Lafiya kalau miya samu kafarki?”
“Faduwa nai”
“Wannan ba faduwa ba ne, karya kuma ba halinki ba ne, Teema...”
Ta dago ta kalleshi ji irin sunan da ya kirata da shi.
“Baba ne ya dake ni”
“Saboda me?”
Bata boye masa komai ba, bata rage ba balle ta kara. Ajiyar zuciya ya sauke idonta ya cika da kwalla, for the first time ya ji ya tsani Babanta.
“Teema akwai wani abun da zan iya miki? Kina son naje na fadawa babanki baki son auren mutumen? Ko kuma kina da wanda kike so na je na yi magana da shi?”
Ta girgiza masa kai hawaye na zubar mata.
“Aa, ka min komai na gode”
Ya lumshe idonsa ya bude ya kalleta.
“Me kika zo yi nan?”
Ta fada masa.
“Bari na kai ki duba Momy ta duba kafarki”
Ta yi shiru bata ce komai ba sai hawaye take, ribas yai ya juya da motar suka fita, tafiya suke bata ce da shi komai ba shi ma be ce mata ba sai kallon fuskarta yake.
“Na rasa dan'uwana, 3 days back shi ne kadai dan'uwa namiji da nake da shi ya rasu sanadiyar hatsarin jirgin sama, ni kaina tun ranar dana bar ki a gidan Momy ban sake zuwa ba”
“Allah ya jikanshi”
Ta furta tana share hawayenta, yayi shiru be sake cewa komai ba, sai dai har ga Allah yana jin sauka hawayenta a zuciyarsa.
A harabar gidan Momy ya faka motarsa, sannan ya bude ya fita tana ganin haka ita ma ta bude ta fita, ta bi bayansa, knocking yai after few seconds aka bude masa kofar falon, sai yai ma Falmata alama da hannu cewar ta fara wucewa.
Bata masa musu ba ta saka kafarta cikin falon tana dingishi.
“Subhanallahi wani abun ne kuma?”
Momy ta fada tana kallon kafarta, Falmata ta mika mata gaisuwa ba tare da tace komai ba.
“Wannan Step Mother din ta ce ta gano an koreta daga aikin shine tasa Babanta yai mata wannan dukan, and lastly wai ta ji yana maganar zai maida aurenta nan da sati daya!”
“Auren wa?”
Momy ta daki kirji tana kallom Sirleem da yai mata maganar. Sai da zauna ita ma ta zauna sannan ya labarta mata zancen auren kamin ya biyo mata da abun da ya faru.
“Mai napep din ya dawo ya fada min ya daina ganinki zai je ya tsaya ya jira amman ba zata fito ba, yana fada min haka na raya cewar wata kila sun gano ne, ko kuma kin fada musu, na so na kira ka sai ga labarin rasuwar Talba ya same shi shiyasa da naje gaisuwar ban maka magana ba, yanzu miye mafita?”
“I don't know, na tambaye ta idan akwai wanda take so, tace babu”
Sirleem ya fada yana dagowa daga jikin kujerar da yake zaune. Momy ta kalleta wani irin tausayin Falmata ne ya shiga zuciyar Momy fiye da da, bayan wannan wahalar da ake bata sai kuma ace za a aura mata tsoho? Wata kila shi ma mutumen banza ne, da zai zo yana azabbatar da ita.
“Ke baki da wanda kike so ne Fulani? Karki yarda a aura miki tsoho, karki yarda a aura miki wanda baki so, ki fada min idan akwai wanda kike so”
Falmata ta yi kasa da kanta kamar a zata ce komai ba, Momy da Sirleem suka zuba mata ido.
“Wanda nake so, ba so na yake d aure ba”
“Taya aka yi kika sani? Ya taba fada miki ne? Kuma idan ba son aure yake miki ba me zai saka ya zo yace yana sonki?”
Momy ta tambaya.
“Ai kin san akwai masu son mace da son banza, bana aure ba, musamman irinta da ake ganin kamar idan an tabata ba za ayi komai ba”
Sirleem ya bata amsa.
“Ke yanzu duk a cikin samarinki babu mai yi da gaske?”
Ya girgiza kai, alamar aa Momy ta sauke ajiyar zuciya, can kuma ta sake kallonta.
“Fulani zaki iya auren Ameer, yaron da kika gani ranar da kuka zo gidan nan wani baki haka?”
Falmata ta dago ta kalleta, Sirleem ma ya kalleta da sauri.
“Momy?”
Ta kalleshi.
“Na san me nake yi Sirleem i want to help?”
“Amman Ameer?”
“Yes”
“Ina da iko da Ameer duk da kasancewar ba ni na haife shi ba, kuma mahaifinsa ba zai musa min ba”
“Makaranta fa yake yi yanzu kuma baya ma kasar?”
“Na sani, na san abun da nake yi Sirleem, idan ba Ameer ba muna da wata mafitar ne akan yarinyar nan?”
“No Momy gaskiya a canja wata shawarar ba Ameer ba, Ameer yaro ne ba zai iya kula da ita yadda ya dace ba”
“Waye zai kula da ita yadda ya dace Tsoho?”
“Amman Momy ba ki yi tunanin kowa ba sai Ameer what if shi baya sonta?”
“Kai kana sonta? Zaka iya aurenta?”
Yayi shiru ya saka cewa komai domin tambayar ta zo masa kamar saukar aradu. Falmata ta kalleshi zuciyarta na bugawa da karfi tana jin kamar ya amsa da eh, duk da tasan bata da kwarji da haifar da zai so a jikintaz gashi ita ba yar kowa bace balle tace ko dan arzirkin gidansu ko sarauta wane ita.
“Ba ni da iko da kai Sirleem saboda Hajiya Balki tana nunawa kowa isa akan yayanta, ban isa na cilasta a ba saboda ita ko da kuwa ace ni din daga bangarenta na fito, balle kuma ina kanwar mahaifinka, kuma na san yadd Hajiya ta tsani talaka, ba zata saurara maka ba idan ka auri Falmata bayan ta zaba maka Nana a matsayin mata, ko da ace zan iya cilastaka Falmata ba zata samu jindadi a gefenka ba saboda Hajiya, zata ma iya cilastaka sai ka sake ta, yarinyar nn tana bukatar kula, mutumen da zai bata ilmi ya kula da ita, idan ta auri Ameer zata dawo karkashina ne”
A take Sirleem ya datse maganar yana duban agogon hannunsa.
“Momy daman na biyo da ita ne ta fada miki abunda ya faru saboda kar ki ga bata zo ba, bari na wuce akwai abubuwan da zan yi”
Wani kallon mamaki da rashin fahimta Momy tai masa, har za ta yi magana sai kuma wata zuciyar ta hana ta, ba tare da ta ce komai ba ta mike tsaye ta haye sama. Da kallo Sirleem ya bita sai da ta haye sama sannan ya kalli Falmata.
“Tashi muje”
Falmata ta mike tsaye ta ni bayansa har suka isa gurin kofar ya bude mata ta fara fita sannan shi ma ya fita. Sai da ya fara shiga motar sannan ta zagaya ita ma ta shiga yai ma motar key tare da danna horn tun kamin ya yi ribas. A wata kemis ka kaita suka duba kafar suka bata magani tare da yi mata allura sannan suka fito. Be shigar motar ba ya tsaya yana kallonta.
“Zai fi ki hau Napep da ace na sauke ki a gidanku, wata kila za a iya kara miki doka ko?”
Ta daga masa kai alamar eh. Sai yaja wani dogon numfashi ya sauke.
“Teema, ki yi hakuri da abun da zaki ji ko ki gani, kuma ki min afuwa ina son nai magana da mahaifinki gaskiya”
“Dan Allah karka yi maganar ka bashi da wani amfani a gurinsa sai ma kara jamin duka da zai yi, zan hakuri da duk yanayin da zan samu kaina, na yarda wannan rayuwar a haka ita ce kaddararta, kuma na san Allah be manta da ni ba, zai min mafita inshallah, na gode da duk wani abu da kai min, cikin har da saurarena da bani lokacinka, bayan taimako na kudi da gudumawa da ka bani Allah saka maka da alheri, ina son na bi zabin mahaifina, wata kila auren tsohon shi ne kwanciyar hankalina, na gane yadda rayuwata take tafiya, ba zan taba samun abunda nake so ba, kuma na hakura da komai zan rumgume kaddara”
Sirleem ya kasa ce mata komai sai kallonta yake yana jin wani yanayi marar dadi. Ta share hawayenta.
“Ba zan taba mantawa da kai ba, babban mutumen sananne yayi hidima da ni, ya taimaka min yayi mini gata kamar uba, Allah ya saka maka d alheri Sirleem kuma ina maka fatan alheri sai wata rana”
Ta sauke kanta kasa hawaye na zuba.
“Ba zaki sake fitowa ba ne?”
“Bana jin za a sake barina na fito, sai dai na san ba za a hanani kallonka a waya ba ko a tv, ba zan manta da kai ba, na gode kuma dan Allah kai min godiya gurin Momy ita ma ta rike kamar ya, babu kyama babu nuna tsangwama”
Sai da ta share hawayenta sannan ta juya ta fara tafiya wasu hawayen na sauko mata tana jin kamar ta fasa ihu domin ta san ba zata sake ganin Sirleem ba sai a hoto. Da kallo ya bita ya rasa tunanin da zai fara? Maganar Momy ko kuma ya kyale ta tabi zabin mahaifinta kamar yadda ta ayyana? Kalamanta sun ratsashi, sun shiga zuciyarsa sun dada masa tausayinta. Sai da tai nisa sosai da inda yake sannan ta tari Napep ta shiga tana fada masa inda zai kaita. Tun da ta shiga cikin napep din sai ta ji kamar ta samu gurin da zata fasa kurjin damuwarta ta ji sanyi, damuwarta ta soma mata aiken hawaye babu kakkautawa.
“Allah ka kwanar min da hankalina, ka saka min natsuwa a cikin zuciya da ruhina, na tuba ka yafe ni ya Allah”
Shine kawai abun da take ta maimaitawa tana kuka sosai har Mai Napep din sai da ya juya ya kalleta, daidai inda aka saba aje ta ta bukaci ya sauke ta, ta fita ta zaro dubu daya cikin kudin da Shattima ya bata ta mikawa mai napep din ya cire kudinsa ya bata canjinta, ta karba ta kama hanyar gida, tana tafe tana dingishi dayan hannunta rike da ledar maganin da Sirleem ya siya mata, hawaye kuma be fasa mata zuba ba, kirjinta sai zafi yake tana jin zuciyarta kamar zata rabe gida biyu.
_________
Ina mata matan kwalisa Matan da suka ansa sunansu na Mata? Ina wadanda ke cewa mun yi mun yi bamu ga amfaninshiba? Hmmm to ku zo ga Yar gidan Maifata ta zo maku da Al ajabu, dan tsugunno, gumba da tsimi da Zuma daban daban, maganin sanyi na maza da Mata. Ga kuma garurruka irinsu mallakau sabuzu kuwa, sa bahaushe saibi, Dan hubbare kafi malam aiki, ke kadai ke da miji, dahuwar kaza, tattabara, ciccibi da dai sauransu. Ba anan kayanmu suka tsaya ba, muna hadin amare na musamman turaren sutura turaren tsugunno turaren wanka da na daki da na jiki duka 4amare nasu na musamman ne, amma ga tsuhuwar da ke son komawa yarinya itama zata iya zuwa ahadata kai abundai sai wanda ya gani, dan haka karkubari abaku labari, domin neman karin bayani zaku iua nemana ta wannan number 09029891757 ko 08169311410, muna aikawa ko'ina a fadin kasar nan har waje kasar nan muna aika kaya.
Address: Nasarawa Samaru Area gurin masallacin mai sola Gusau Zamfara state Nigeria.
43
*Littafin nan na kudi ne biya ki karanta cikin aminci. Pay 300 to 2451879008 Hadiza Abubakar Zenith bank, then send the evidence via 08036126660*
Bakin gate din gidansa ya tsaya yai horn sau biyu, mai gadin ya fito da gudunsa ya bude masa gate, a hankali ya shiga da motar ya faka a yalwantaccen parking space din dake gidan. Sannan ya bude motar zai fita.
“Ina zaka?”
Ta tambaya tana kokarin kai hannu ta taba shi, be kula ta ba ya fita ya rufe ya zagaya side din da take ya bude mata.
“Fito mun kawo gida”
Ta mika masa hannunta alamar ya rikata ta fito, samun kansa yai da kallon hannun ya yan dakiku sannan ya mika mata nasa hannun ya riko nata, tafin hannunsa na shiga cikin nata sai ta tsaya cak ta fasa fitowar tana sauraren sanyi da take jin yana ratsa hannunta, a hankali ta zame hannunta tai wani sukuku kamar ba ita ba, can kuma ta fara lalabe ta ta yunkura zata fito sai kanta ya bugu da motar.
“Careful...”
Yana kokarin taimaka mata ta fito,