Showing 102001 words to 105000 words out of 286946 words
“Heyy.... ”
Ya fada yana taba ta a hankali, sai ta bude ido ta farka a firgice, si ya kai bakinsa saitin kunnenta.
“Ina ne unguwarku ma?”
Ta fada masa, sai ya gyada mata kai. This time around ita ce take ta kallonsa har suka isa cikin unguwar da be taba zuwa ba sai yau.
“Ina gidanku yake?”
“Ina gidanku yake?”
“Yana can ciki mota bata shiga”
“Okay, bari ruwan ya rage sai ki sauka”
Daga haka ya kunna wutar motar ya soma nuna mata yadda zata sha maganin.
“Na gode Allah ya saka da alheri”
“Gobe misalin uku na rana ki dauki permission a gurin aikinki sai ki same ni a gidanmu na kai ki Momy ta duba kunnen ai kina so ko?”
Ta gyada masa kai alamar tare da dagowa da sauri.
“Eh ina so sosai”
“Okay gobe ki musu magana sai na kai ki asibitin da take aiki a duba ki”
“Ina ne gidanku?”
“Gidan da kike aiki, amman b bangaren Ammy ba bangaren kishiyarta”
Shiru tai kamar mai tunani, sam bata dauka Ammy na da kishiya ba, sai yau.
“Oh ki fito bakin gate din ku ki tsaya idan uku na rana yayi zan same ki a gurin okay”
“Tau...”
Ta fada tana kallonsa sannan ta shiga kokarin bude motar.
“Ba zaki bari ruwan ya gama sauka ba”
“Zan iya tafiya a haka, idan aka fadawa Babana an ganni a mota zai iya kasheni”
Kallon tausayi yai mata sannan unlock din motar ta bude ta fita sai kuma ta duko ta mika masa rigarsa.
“Gashi na gode”
Ya mika hannu ya karba, ita kuma ya juya ya nufi hanyar da zata sadata da gidansu jikinta sai kamshin turarensa yake.
HAJIYA BABBA POV.
Ta kasa zaune ta kasa tsaye sai tunanin yadda zata bullowa lamarin Falmata take, ba Falmata kadai ba har Fadime da Sardauna so take ta sani, ganin abun da mutanen suka fada ya fara tabbata yasa ta fara jin tsoron.
Wayarta ta dauka ta kira amiyarta Hajiya Talatu, bugu daya ta dauka da far'arta, sai da suka gaisa sannan ta labarta mata halin da take ciki.
“Kin san me Hajiya? Mataki zamu dauka tun yanzu, waya sani ma ko wani hadin kai ne da ita Ammyn?”
Hajiya ta dan yi shiru tana nazari.
“To ni yanzu ya zanyi? Tsoro nake kar mu mata asiri ta tona mana asiri”
“Ai dole shi za'ayi idan ba haka ba taya zamu koreta a gidan? Dole sai da asirin nan”
“Kika sani ko abun da zai saka aikinmu ya wargaje kenan? Ni fa tsoro nake ji, ki samu lokaci ki shigo gobe mu yi shawara abun da ya kamata wannan maganar bata waya bace”
“To kenan Hajiya zan shigo gobe idan Allah ya kaimu”
Daga haka ta aje wayar, zuciyarta na raya mata yi ma Falmata asirin da zata bar gidan ta dayan bangaren kuma tana jin tsoron kar ya zama na ko tana da aljanu da za su tona mata asiri su fadi abun da tai. Mikewa tai tsaye ta fara safa da marwa, tunanin yadda zata bullowa lamarin take, wannan karon sai da ta kai karshen dakinta sai kuma ta juyo da sauri ta dauki wayarta number yarta ta lalabo ta aika mata kira, Jurry dake kwance saman gadonta ta mike tsaye tana kallon kiran mahaifiyarta.
“Hello Hajiya”
“Juwairiyya kina ina?”
“Dakina, lafiya dai”
“Dakina lafiya dai?”
“Ba lafiya ba, zo ki same ni yanzu nan”
“Okay”
Ta aje wayar tare da mikewa tsaye gaba daya ta fito daga dakinta ta nufi dakin mahaifiyarta, daf da zata shiga dakin Sirleem ya turo kofar falon ya shigo tufafinsa a jike shakaf da ruwa.
“Ya Sirleem ina ka fito haka?”
Ta tambaya ganin yadda ya jike bayan ta fi kowa sanin yayan nata baya son ruwan sama ya taba shi.
“Somewhere...”
Ya amsa mata ba tare da ya kalli inda take ba, ya nufi corridor da zai sada shi da dakinsa. Tsayawa kallonsa tai sai da ya shige sannan ta tura kofar dakin Hajiya Babba ta shiga. Bakin gado ta samu Hajiya zaune tana ta faman sauke ajiyar zuciya.
“Hajiya lafiya dai?”
“Ina fa Lafiya? Juwairiyya muna cikin matsala, abun da mutanen nan suka fada ya fara tabbata”
Jurry ta zauna tana yi ma mahaifiyarta kallon rashin fahimta.
“Ban gane ba...”
Sai da Hajiya ta tunasar da ita abun da bokan nan ya fada n cewar Falmata Fadime and Sardauna za su lalata musu shiri sannan ta dora da..
“Kuma yarinyar nan tana cikin gidan nan tana aiki, ita take rainon yaran Shattima...”
“Bakuwa ce amman ko?”
“Nima haka nake tunani bata dade da fara aikin ba”
“To yanzu ya kenan?”
“Mafita nake nema na rasa yadda zan yi, gana daya kaina ya kulle, tsoro nakr kar na shiga malamai ta tona min asiri ban sani ba ko tana da aljanu ne, gaba daya hankali ya kasa kwanciya, gashi a ba a bangaren nan take ba balle na koreta”
Hajiya ta karasa tana dauke numfashi kana ganinta kasan a tsora ce take sosai.
“Ko ba a nan take ba, zamu iya yin abun da zai saka a koreta mana”
“Me zamu yi me zamu yi Jurry ace mun saka ido akan yarinyar da bangarena take ba? Daga nan ai wani tsonon asirin ne kuma”
“Ni na san abun da zan yi Hajiya, yanzu yarinyar tana ina?”
“Tana bangaren Ammy zaki ganta wata baka haka bata ji sosai ba zata wuce sa'ar Nana ba”
“Bana shiga bangaren Ammy amman zan ganta gobe inshallah, na san abun da zan yi”
“Me zaki yi?”
“Na san me zan yi Hajiya ai ba komai ne za'a tsaya ace sai an yi asiri ba, sometimes we need to work with our brain”
“Kar ki yi abun da zai kara jefamu cikin matsala fa”
“Ki yarda da ni Hajiya bari dai, na fara ganin yarinya yanzu”
Hajiya ta sauke ajiyar zuciyata ba dan ta natsu da abun da Jurry take fada ba duk da bata san abun da zata aikata din ba.
SHATTIMA POV.
Ya sauke wayar daga kunnensa yana jin wani iri, he don't know why Baba Waziri ke son ganinsa, ya san mo ma minene Magana ce mai muhimmanci tun da har ya bukaci ganinsa, kamar yadda ya kira shi a yanzu ya sanar masa cewar yana dakin Ammy yana jiransa. Mikewa yai tsaye yana busar da iskar bakinsa, iskar backyard din da yake tsaye yana bugunsa yana ratsa ko'ina na jikinsa. Juyowa yai ya turo glass door din ya shigo cikin falon, kai tsaye ya nufi hanyar da zata sadashi da dakin yayansa, he just want to make sure suna lafiya kamin je ga kiran da Baba Waziri yake masa, a hankali ya tura kofar dakin ya shiga, sai ya samu wutar dakin a kashe sai bedside lamp dake haska su, ac kuma an kunna shi kadan ya lullube su kamar yadda yake bukata, karasa yai kusa da su yai musu addu'a ya sumbance su sannan ya mike tsaye a hankali ya fito daga dakin. Kai tsaye ya nufi dakin Ammy gabansa sai faduwa yake, sai da ya kwankwasa sannan ya tura ya shiga, Ammy na zaune kan prayer mat Baba Waziri kuma na zaune a saman kujerar dake facing din gadon Ammy. Sai da ya gaisa da Baba Waziri sannan ya zauna kusa da shi yana kallon fuskar Ammy, domin ta fuskarta yake gane komai idan irin wannan ta taso a tsakaninsa da Baba Waziri ko da Mai Martaba, sai dai wannan karon ya lura kamar Momy ma da kanta bata san komai ba. Baba Waziri yayi gyaran murya sannan ya ce.
“Shattima dalilin kiran abubuwa ne guda uku, masu muhimmanci a gare ni kuma a gareka, ban fadawa kowa wannan ba, ciki har da mahaifiyarka, ni na yanke wannan shawarar da kaina, kuma bana fatan zaka saba min”
Shattima yayi sunkuyar da kansa yana sauraren Baba Waziri. Shiru Waziri yai na wani lokaci sannan ya cigaba.
“Abu na farko, ina son ka yi aure, domin zaman ka a haka ba zai yiyu ba, ba zamu zuba maka ido kana babba a cikin gidan nan ba, kuma ace kana zaune babu mata”
Da Sauri Ammy da Shattima suka kalleshi, kamin Shattima ya maida dubansa gurin Ammy.
“Amman Waziri kasan matsalar Shattima ba tun yau”
Cikin bacin rai Baba Waziri ya daga mata hannu.
“Karki sake min wannan maganar, ya kike kokarin maida shi ya zama wani abun tsoro, kai kana da wacce kake so?”
Baba Waziri ya karasa yana kallon Shattima da yai mutuwar zaune a gurin.
“Aa ba ni da ita Baba”
“To kaje gidana ka duba, Jayyada ko Maijidda gidan daya daga cikinsu tana maka”
“Baba ka san matsala ta fa, ni kaina yanzu tsoron kaina na ke”
“Idan baka son su ka fada min yarinyar da kake so, ko yar waye ce zan nema maka aurenta, idan kuma nemowa zaka yi zan baka dama”
Cewar Baba Waziri with serious face. Shattima ya aje numfashi a hankali sannan yace.
“Baba babu matar da zata yarda ta auri a halin da nake ciki, da dai mun dan jira n wani lokaci”
Kamin Baba Waziri yace komai Ammy ta ce.
“Jayyada ai ta yi kankanta Nana ma ta girme ta ai, sai dai Maijidda kuma bana tunanin Hajiya Talatu zata yarda a aurawa ƴarta Shattima”
“Talatu ke da ikon Maijidda ko ni? Ya in magana kina kawo min wata magana Ammy? Ni nai ra'ayin aurawa Shattima yata, ko ke baki isa ki hana ba, balle kuma Talatu da take karkashina, idan kika ga abun nan be yiyu ba, Shattima ne da kansa be amsa tayi na ba, amman ni haka nai fata”
Baba Waziri ya karasa da muryar dakd amsa sunansa na cikakken namiji mai magana daya. Shattima ya hade yawu a hankali ba tare da yace komai ba, ya san yadda Hajiya Talatu ta tsani Ammy balle kuma ace yarta ta aure shi bayan idan mace ta aureshi mutuwa take, da ma ace abokiyar zamanta ce Hajiya Mairo, duk da yasan ita ma ba zata so rasa yarta ba, shi kansa ya san karfin hali ne kawai irin na Baba Waziri b dan bayan son Maijidda ba balle kuma Jayyada da take karama.
Ammy ta aje carbin hannunta ta fuskanci Baba Waziri.
“Ba ina son hana hada auren Maijidda da Shattima ba ne, ina duba makomar Maijidda ne, lamarin Shattima kullum gaba yake ba baya ba, ko a kwanaki baya sai da na tutube abokinsa Ra'ees daya nema masa aure a can Katsina ko da yar kauye ce ba tare da sanin Shattima ba, amman abun ya gagara karshe kirana yai ya fada abun da ya faru na rashin dadi kuma yace shi ya cire hannunsa a ciki”
Baba Waziri yayi mata wani kallon Mamaki.
“Har yaushe ke da kanki zaki. zauna kina chaf danki? Wallahi da ba ke bace kika fada min wannan maganar a yau akan Shattima jinina Wallahi da sai n baki mamaki, wannan dai umarni ne B shawara ba, dole ne Shattima ya sake aure”
Shattima da uffan be ce ba, sai tunanin Fadime ya fado masa a rai, daman shi aka je nemawa aurenta? Ita kuma ta zo tana ta neman Ra'ees, shi kuma yana ta boye, sai ya yanzu ya tuna maganar Ra'ees na cewar wani abokinsa yaje nemawa aure. Ban ankaro ba ya ji Baba Waziri na dora masa wani umarnin.
“Abu na biyu zan mu kara fitar da Mai Martaba waje, domin a kara duba lafiyarsa ba mu san abun da Allah zai yi ba”
“Bana son na shiga tsakaninka da dan'uwanka, amman shi kansa baya son fita yanzu, kuma na dora shi akan magani da mun jira muga abun da Allah zai yi, kuma na ga an fitar da shi ba sau daya ba, amman kamar yafi samun sauki a gida”
“Kai kwararen likitan zuciya ne, mu bari kwararen likitan kwakwalwa ya ganshi pls, idan ina maganar dan'uwana ku daina saka min baki, ni kadai na san me nake ji akan ciwon nan nasa, kullum da abu na ke bachi nake tashi, be kamata mu saka masa ido haka ba”
“Haka ne ni kaina abun na damuna, kuma ina son ka saka har saukar qur'ane ayi masa, ba a san inda rabo yake”
Cewar Ammy cike da damuwa. Sai Baba Waziri ya amsa mata da cewa.
“Duka za ayi da yarda Allah”
Ya sake fuskarta Shattima yana fada masa abu n karshe.
“Abu na uku kuma na karshe, dole ne ka nemi transfer ka dawo nan da aiki, ba zai yiyu ka zauna a can ba bayan kai ne babba a masarautar nan, Ammy na bukatarka Mai Martaba na bukarta, wasu abubuwan za su iya tasowa sai ace sai na jira ka ka zo ko kuma ace kana ina ace Katsina kake aiki? So this one ma Umarni ne dole ka dawo garin nan da aiki”
Shattima ya kalli Ammy wacce ke murmushi dukan abubuwan da Baba Waziri ya fada sun mata 100% musamman dawowarsa a nan daman ta dade tana son ya nemi transfer sai yace mata baya son yana kusa da masarautar nan saboda abubuwan da suke faruwa. Ko kadan umarnin Baba Waziri ma dawowa garin Yola da aiki be yi ma Shattima dadi ba, amman be isa yace a a ba tun da har ya furta masa cewar umarni ne.
“Zan iya baka dama kai tunani akan yarinyar da kake so, domin ba zan maka dole ba, ban ce dole ka so yar wajena ba, amman aure dole ne you can go...”
Shattima kamar mai jira ya mike tsaye da sauri ya fice daga dakin yana cikawa bakinsa iska.
FADIME POV.
Washe gari tun da farar safiya Fadime ta dauko littafin da biro, duk abun da ya faru sai da ta rubuce shi tsaf sannan hankalinta ya kwanta. Bayan ta gama ta fito waje tana lekon dakin Amo, sosai take jin kamar ta labarwa wani a sanadinta komai ya faru kuma tana tsoron kar Bappa ko Inna su ji, kusa da Inna ta zo ta tsaya tana gaishe ta kamar ba ita ba.
“Inna naje na debo ruwa?”
“Eh amman kamin ki fita ki yi addu'a dan Allah”
Inna ta amsa mata da halshen fulantanci, da sauri Fadime ta nufi inda tulun yake ta dauka tana fadin.
“Ai na yi addu'a kuma idan zan fita sai na sake yin wata”
“Wai ina tulun jiya?”
Fadime ta zare ido sosai.
“Ai da naji tana cewa ita Mayya ce sai na jefar da tulun na gudu, sai ya fashe”
Ta tsuke fuska kamar wata tsohuwa, Inna ta dauke kai bata sake ce mata komai ba, Fadime na ganin haka ta nufi hanyar waje da saurinta ba abun da take son gani kamar Wasim, so take ta labarsa masa abun da ya faru so kuma ta nuna masa jindadinta. Kamin ta karasa gurin har da gudunta zuciyarta sai wani zillo take kamar zata fito, ko gurin ruwa bata je ba ta doshi inda ta san zata ga Wasim, ta kuwa ta ki sa'a domin ta same shi a jikin dutsen tsaye yana jiranta. Nesa da shi ta aje tulun ta karasa inda yake da sauri.
“Ina kwana”
Be amsa ta ba sai yawo yake da idonsa a fuskarta, fuskarsa dauke da murmushi zuciyarsa kuma cike da shaukin ganinta.
“Jiya ashe wannan magen Inna Amo ce kishiyar Inna, tana ta rawa tana ta ihu”
“Da gaske?”
“Wallahi kuwa na rantse da Allah”
Amsa mata da yai yasa ta jidadin bashi labari har da nuna masa yadda yake tana rike ciki. Tun yana murmushi har ya fara dariya, yadda take nuna masa Amo ta yi sai tai wani irin burgeshi har yake jin kamar ya hade ta ta zauna a cikin cikinsa.
“I like you...”
Ya furta cike da shauki. Sai ta tsaya cak yana murmushin mamaki.
“Me kace? Ashe ka iya turanci?”
Ya dauke kansa yana dan murmushinsa mai kyau.
“Me kika ji na ce?”
“You say you like me!”
“Ba kiji da kyau ba, yanzu dai shikenan kin huta ai babu mai sake miki komai”
“Amman wannan kawun nata yace na saurari sakamako na wai”
Matsawa yai kusa da ita ya ture hular kanta ta fada baya ya shafa gashin kanta.
“Babu wanda zai sake taba ki ina nan Fadime ki yarda da wannan! Ba ki cuwa ga kowa duk wanda ya zabi cin ki to ya ci mutuwa”
Ya yi murmushin jindadi tare da mika masa hannunta.
“To taba min hannuna”
Ya kalli tafin hannun.
“Idan na taba kika ji sanyi fa”
“Shikenan na huta”
Ta fada tana zare manyan idanuwanta da suka karawa fuskarta da far'arta kyau. Yayi murmushi.
“Idan kuma baki ji ba fa?”
Ta yi shiru tana dariya kamar yar 4 years.
“Ni kuma ba zan yarda ba”
Ya fada yana daga mata gira idonsa cikin nata kamar zai cinye ta.
IYA POV.
Mamakin karfin Halin yarta Zainab ya hana ta sukuni, sam batai zaton yadda ta sakar mata ciwon kai da baya zata iya tafiyar nan ba.
“Idan kin san wata baki san wata ba”
Ta mike tsaye ta daga carpet dinta ta walware kurwarta ta jefata sama sai abu ya tashi kamar tantaba yai saman dakin kamin ya bat ya bata. Sannan ta nufi gurin da take aje kayanta na tsafi ta dauko tukunyarta ta kai bakinta jiki tai magana ta kara tukunyar a kunnenta, sannan maida ta aje ta nufi karkashin gadonta ta dauko wata kwarya ta fiddo wata karamar wuka, ta maida kwaryar ta dawo gurin carpet dinta ta janye dorowar dake sama ta daga carpet din ta dauko kurwar Auwal ta nufi bandaki da ita, sai davta rufe bandakin sannan ta warware zaren jikin sai ga wata yar tsoka mai kamar lakka, kafarta ta daga ta saka tsokar a kasa, a take tsokar ta zama zakara, irin marar lafiyar rakazan nan da basu da kuzari sosai kafafuwansa ta danne ta saita wukar saitin wuyansa ta yanka sai jini.
“Sai ki dawo da hujja!....”
Ta furta cikin bacin rai tana jin wani irin bakinciki na tafiyar da Hajiya Karama tai.
HAJIYA KARAMA (ZAINAB) POV
Cikin rashin kuzari ta gama shirinta, sakon da Auwal ya turo mata cewar baya jindadi ya tayar mata da hankali sosai, har take jin kamar ta koma Yola. Tana zaune a dakin kiran Shattima ya shigo wayarta. Kamar mai jira sai tai saurin picking.
“Hello”
Yana jin muryarta ya san bata cikin walwala.
“Hey Hajiya Karama Lafiya dai?”
“Wallahi Auwal ne ya turo sako wai ba ya jin dadi sosai, kuma ina ta kira be daga ba, so ina ta tunanin ko na koma ne”
“No pls har kin riga kin je, ki dauri kawai zuwan na zama na banza, ai ba zaki dade