Showing 27001 words to 30000 words out of 286946 words

Chapter 10 - Fulani Book 1 Hausa Novel Complete

20 Dec 2024

900

karasa kusa da ita ta zauna bakin gadon sai Hajiya ta kwantar da ita jikinta.

“Garin ya hakan ya faru daughter?”

Irin karyar da tai ma su Ammy ita tai ma Hajiya.

“Amman an kore shi ko?”

“Yes Ya Shattima ya kore shi”

“Da ba a sallame shi ba, da sai na saka an hukunta shi sannan na masa korar wulakanci”

Hajiya ta fada cikin bacin rai, wanda hakan ba karamin dadin yai ma Nana ba. Babu abunda ta rage bata fada mata ba akan abunda Baba Waziri yai mata jiya har da hawayenta. Hajiya ta shafa kanta tana murmushi

“Haba daughter kar hakan ya dame ki, ba dai ina raye ba babu wanda ya isa ya taba ki, nan da kwana biyu zan maida miki duk wani abu da Waziri ya cire a dakinki, ni kaina ya min magana wai ni da Sirleem mu daina ba ki kudi ko siya miki wani abu, amman kin san ba zan yi haka ba ko? Domin ni ina kaunarki sosai”

Nana ta rumgume ta.

“Na gode Hajiya, za ki rika ba ni kudi?”

“Sosai ma, duk lokacin da kike bukatar kudi ki zo ki min magana, amman fada min me kika masa?”

“Ni ban masa komai ba, ban san miyasa yai min haka ba daman can shi baya so na ai”

“Mu ai muna sonki, bari na kira Sirleem ya zo ya kai ki wata asibitin a duba ki”

“A a Ya Shattima ya Kora Doc Deen ya duba ni jiya”

Ta mike tsaye jin maganar asibiti, domin zuwa asibiti da allura sune manyan makiyanta a duniya. Hajiya ta mike tsaye ta nufi wardrobe dinta ta bude ta dauko kudin da za su kai 20k ta juyo ta dawo kusa da Nana ta mika mata kudin.

“Karbi wannan ki siye wani abu”

Da sauri Nana ta saka hannu ta karba tana murmushi.

“Na gode”

Murmushi Hajiya tai mata a respond ita kuma ta saka kudin cikin aljihun wandonta ta juya tana dingishin ta fita daga dakin, Hajiya ta bita da kallo tana murmushi. Hakan da Hajiya tai mata ba karamin dadi yai mata ba, daman can ta san babu mai sonta sai Hajiya domin ta fi kowa sakar mata kudi ita da Hajiya Karama. Sai da ta fito daga bangaren Hajiya gaba daya sannan ta fiddo kudin ta karga 20k ne cif ta maida a inda ta saka dazun sannan ta nufi hanyar da zata sadata da bangarensu.


“Imagine Muhseen ya tafi be min sallama ba”

Cewar Zainab tana mamakin tafiyarsa ba tare da saninta ba.

“Yana busy daman Mama Fulani kawai ya kawo, any problem?”

Shattima ya fada ba tare da ya kalleta ba.

“No kawai na ji tafiyar ta sa a ba za ta ne, ita ma Mama Fulani ban ganta ba ai ko tare suka tafi?”

“Tana cikin garin gurin yan'uwa”

Ya bata amsar still be kalleta ba sai aikin taba System dinsa yake, ita kuma tana shafa wani mai a fuskarta jikinta sanye da sleeping dress wando da riga. Suna haka Nana ta shigo falon ta nufo inda suke tun kamin ta zauna Zainab ta ce.

“Ammy na nemanki”

“Me nai?”

Zainab tai murmushi

“Sai kin yi wani abu Ammy zata nemeki? Haba Baby ta shiga dakinki bata ganki ba na fada mata kin tafi bangaren Hajiya, tace idan kin dawo na turo ki”

Ta juya ba dan ranta ya so ba ta nufi dakin Ammy, a kasan carpet ta samu Ammy zaune rike sanye da hijab hannunta rike da carbi. Ta karasa ta sauna bakin gadon tana turo baki tana kin kallon mahaifiyarta. Ammy ba ta bi ta kanta ba ta kalleta a natse ta ce

“Ya jikin na ki?”

“Da sauki”

“Na shiga dakinki ban same ki ba, Zainab tace kin je bangaren Hajiya Balki me kika je yi?”

“Naje na fada mata duk abunda Baba Waziri yai min”

“Da kika fada mata sai ta miki maganin me?”

Turo baki tai ta mike tsaye ta nufi hanyar fita sai da Ammy ta daka mata tsawa.

“Nana....! Ina magana zaki tashi ki fita?”

Ta juyo tana turo baki amman bata dawo ta zauna ba.

“Daman ai na san ba so na kike ba, gidan nan daga Ya Shattima sai Hajiya Karama sai Hajiya Babba kadai ke so na, sai Mai Martaba....”

Mikewa tsaye Ammy tai ta karasa inda Nana take ta fisgeta iya karfinta ta jefar kasa sai da kanta ya bugi gadon dakin. A take Nana ta bude baki ta fara ihu daman kukanta na kusa, da gudu Zainab da Shattima suka shigo dakin, Zainab ta nufe ta da sauri ta rika ta.

“Ban mata komai ba ta jefar da ni kasa”

Ta fada cikin kuka tun kan Zainab ta tambayeta.

“Okay tashi muje room dinki”

Da taimakon Zainab ta mike tsaye suka fice daga dakin. Shattima ya zauna kusa da mahaifiyarsa yana karantar yanayinta.

“Ammy ki rika dagawa Nana kafa she is still young, ba isa tai irin wayon da kike so tai ba”

Ammy ta kalleshi.

“Wata yarinya kamar ta tana da hankali da tunani, wata yarinya kamarta ta san ciwon kanta, Nana ban isa na ce kar ki yi ba ta bi umarnina, ban isa na hana ta ba ta hanu, bata san komai ba sai a bata kudi ayi mata kaza, abunta ya fara yawa ace Nana idan ta ga kudi sai ta saka hannu ta sata?”

“Nonono Nana ba zata taba haka ba In-Sha-Allah, Ammy ki daina mata wannan fatan, tana dauka ne saboda tana ganin a gidansu ne, kuma wannan halin da ta yi wayo zata daina”

Ammy bata ce komai ba ta sauke ajiyar zuciya. Jin muryar Hajiya Babba yasa Shattima mikewa tsaye ya fito falo. Cikin girmamawa ya gaisheta ta amsa mishi da far'arta kamar ko yaushe tana kare masa kallo.

“Hajiya Zainab tana ciki?”

“Eh tana ciki”

Binsa tai da kallo sai da ya isa gurin system dinsa sannan ta dauke kai ta tura kofar dakin Ammy ta shiga. Daga bakin kofar dakin ta tsaya tana kallon Ammy.

“Hajiya Zainab kin kyauta kenan?”

Ammy ta mata kallon rashin fahimta.

“Me ya faru? Karaso mana kika tsaya daga bakin kofa”

“A a bar ni a nan da ina da muhimmaci a gareki ai da kanki zaki aika min abunda ya samu Nana, ko ba komai Nana yata ce kuma surukata ina hakkin sani”

Surukata yafi komai yi ma Ammy za fi domin har ga Allah bata son hadin nan na Sirleem da Nana, sai dai babu yadda ta iya tun da sai da aka tambayi Nana da kanta tace tana son shi sannan akai musu baiko. Murmushi karfin hali Ammy tai tana kokarin maida abun ba komai ba.

“Haba dai, dan ɗan wannan sai ace sai an tashi hankalinki, garin shiritarta ne taje ta ji ciwo kuma ba wani rauni ne sosai ba, kin dai san halin Nana da raki shi ne kawai”

“Uhmm ko da ace ba ni na haifi mijin da Nana zata aura ba, na ga dai nima uwa ce a cikin gidan nan, ko ciwon kai Nana take ya kamata a fada min, abunda kike yi sam ba yi ba ne, yau idan Mai Martaba ya fadi ya mutu haka zamu tai zama cikin rashin hadin kai? Idan yau kika fadi kika mutu ni zan rika Nana ya kamata dai a gyara...”

Tana fadar hakan ta juya ta fice daga dakin rai a bace sai dai bacin ran na iya fuska ne be kai zuci ba. Ammy kuma ta ja dogon numfashi ta sauke ta lumshe ido. Ba tun yau indai ta hadu da abokiyar zamanta sai ta fada mata wata maganar marar dadi, me ya kawo maganar mutuwar Mai Martaba ko nata a nan? Kan abunda be kai ya kawo ba?


Sai da ta fice daga bangarensu sannan Shattima ya mike tsaye ya rufe system dinsa ya dauke ta ya nufi dakin Nana. Zaune ya same su ita da Zainab suna ta kyalkyalar dariya bakin kofar ya tsaya yana kallonta yana murmushi.

“Ya Shattima zo nan”

Ya karasa ya zauna dayan side dinta da ta nuna masa da hannunta.

“Me kuke kallo?”

“Comedy”

Ta amsa masa tana karbar wayar daga hannun Zainab ta mika masa. Kadan ya kalla ya mike tsaye.

“A sha kallo lafiya”

Ya juya ya fice, ita ma Zainab din ta mike tsaye.

“Bari naje mai wanka kamin na shirya kin gama”

“Okay”

Ta cigaba da kallon hankalinta kwance bayan Zainab ta fice. Shattima na fita daga dakin Nana ya nufi dakin da ya aje yaransa ya dauko su ya dawo da su dakinsu wanda Falmata tai masa tas sai kamshi yake.





FALMATA POV.

Kamar wacce zata sanarda mutuwar wani haka ta shiga cikin gidan cikin tashin hankali da fargaba ga tsoron da ya cika mata zuciya har ya bayyana a fuskarta. Tun daga sallamarta zaka fahimci akwai damuwa da tashin hankali a tare da ita balle kuma idan kai arba da fuskarka.
Kamar mai koyon tafiya haka ta karasa kusa da Tumba da ke aikin tsintar shinkafa ta risina kan ta ce komai hawaye ya fara isar da sakon abunda zata sanar.

“Umma dan Allah ki yi hakuri”

Umma ta aje tray shinkafar tana mata kallon uku saura kwata.

“Ban gane na yi hakuri ba, me kika min macuciya?”

Ta fara yarfar da hannu.

“Sun kore ni daga aikin”

A take Umma ta saka, sam bata kawo kora daga aiki Falmata zata fada ba, a daukarta wani laifin tai mata na dabam.

“Amman wannan Ya kin iya bakinciki, dan kudin da zan samu kike wa Hassada? Ni zaki yi ma cuta?”

Da sauri Falmata ta girgiza kai tana wani irin kuka mai ban tausayi.

“A a Wallahi ba dan shi ba ne”

“To me kika yi ma wai suka koreki? Taya za su kore ki haka nan kawai ba tare da kin musu komai ba?”

Bata boye komai daga abunda ta aikata ba wanda take kyautata zaton hakan ne yasa aka koreta, wato tofawa Luma Addu'a har mahaifinta ya gani.

“To uban waye ya kai ki yi musu addu'a ke ashibi yar neman yabo ko? Makira shegiya yar iskanka, ni za ki yi wa bakinciki? Bari Babanki ya dawo sai na miki wanda ya fi wannan”

Tana fadar hakan ta mike tsaye ta kai hannunta a kirjin Falmata ta fara murzar kirjinta iya karfinta. Wani irin kuka Falmata ta saka tana rike hannun Umma.

“Umma ciwo mutuwa dan Allah ki yi hakuri”

Bata saurareta ba har sai da ta murja iya yadda take cin zata cutarta da ita, tun da ta san idan aka murza kirjin burduwa mai tasowa ciwo take ji sosai. A rana Falmata ta wuni da kirjin nata kamar dutse yana ta mata ciwo bayan nauyin da yai mata. Bayan sallah isha'i tana zaune saman tabarma ita da Naja sai dariya take mata, ita kuma ta takure guri daya tana ta tunanin abunda Umma zata saka Baba yai mata sai ta ji sallamarsa, wani irin tashin hankali ta ji kamar ance mata ga mutuwarta nan. A yau Naja ce ta amsa sallamarsa taje ta karbo ledar hannunsa tana masa sannu da zuwa sai far'a take.

“Baba sannu da zuwa”

Falmata ta fada muryarta na rawa tana masa wani irin kallon tsoro dan ji take kamar ma Umma ta mata sherin ne. Sai akai sa'a yana kawowa daidai inda take tsaye Tumba ta fito daga dakinta tana fadin.

“To Malam sai ka san abun yi, Fulani dai so take ta lalace, kama ta nai a kofar gida ita da wani da ban san ko waye ba yana taba mata kirji”

A bala'in firgice Falmata ta mike tsaye tana kallon tana kallon Umma, a take Umma ta zaro mata ido.

“Ko karya na ke?”

Falmata ta girgiza kai da sauri.

“A a ba karya kike ba Umma amman Wallahi ba zan kara ba dan Allah kui hakuri....”

Tun kan ta karasa Baba ya wanke mata fuska da mari biyu masu kyau, yasa kafarsa ya shure kafafuwanta ta fadi kasa tana jin kamar babu naman fuska a fuskarta, ga kunnenta yayi wani dummmm jin tai yai dogon zango, kamar an aiko shi haka ya hau dukanta yana fadin shi zata kawa abun kunya, gaba daya ta kasa kuka komai ya zo mata kamar a mafarki ga shi bata jin komai daga cikin abunda Baba yake fada kamar mai dukan Namiji haka Baba ya rika shurin Falmata yana dukanta har da saka kafarsa ya danne mata ruwan ciki sai da tai amai sannan Umma ta rugo da gudu ta rike shi tana kuka.

“Haba Malam daga fada maka abun dan ka mata fada sai ka hau yi mata wannan dukan, idan ka kashe ta fa, yarinya marainiya zaka mata wannan dukan”

Kuka take riri tana fadin haka iya karfinta wanda hakan yasa makonta su shigowa suna tambayar ba'asi, babu abunda ta rage sai ma kari da tai cewar wani ta gani yana taba kirjin Falmata. A lokacin ne Falmata ta ji wani irin kuka ya zo mata da karfi ta shiga ambaton Allah tana kiran mahaifiyarta da bata raye.

“Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un, Mama Mama Mama Mama Mama, na shiga uku mutuwa zan yi, Bana jin komai Mama Baba Baba”

Ta unkura zata tashi ta ji ba zata iya ba, hakan yasa ta koma ta kwanta a kasan ta rike kunnuwanta tana wani irin kuka mai shiga zuciya. Tumba ta nufi inda take ta rika tana kuka kamar ba ita ta kitsa komai ba, kokarin dagata take amman Falmata ta kasa tashi sai kuka take. Mutane wasu na bata hakuri sai dai mafi yawa sun girgiza da jin dalilin dukan da mahaifinta yai mata, domin Falmata yarinya ce mai natsuwa da kamun kai wacce ake ganin kamar wata yarinyar matashi irinta a unguwar, wasu cewa suke sai dai idan saurayin ne yake son lalata amman Falmata ba halinta ba ne, wasu kuma sun yarda wanda hakan bacin suna a gareta da kuma tarbiyarta, a yadda kowa yakr ganin Tumba tana rikon Falmata tana mata gatan da bata yi wa Naja ma da take yarta sai suka yarda da abunda ta fada a ganinsu ba zata mata sheri ba.

Har aka ci aka shude Falmata na kwance a gurin tana kuka, bata jin abunda mutanen suke fada har sai idan sun yi da karfi, fuskarta ya kumbura sosai kafarta sai ciwo yake kamar an cire mata shi, sai da dare ya raba sannan ta rarafa daker ta shige dakinsu bata ko karasa kan shimfidarta ba ta kwanta a gurin a kasa tana kuka a hankali, babu komai a ranta sai kewar mahaifiyar ta kalaman da tai mata na bankwana.

“Zan tafi na barki ciki taradadi Fulani, Allah ya zama gatanki, na san za ki sha wahala kuma za ki ga banbanci da kiyayya, amman ki rike Allah shi sai miki gata, kuma kar ki yi wasa da addu'a”

Mama..... Ta kiran sunan mahaifiyarta a hankali tana jin kamar ace tana kusa da ita, sai kuma ta fashe da matsanaicin kuka.




__________

Falmata baiwar Allah Iya ta ja miki wahala yau 😭
Nana yar...... 🤔
*🐄🐄 FULANI 🐄🐄*


By Khadeeja Candy


*8*

Da wani irin zazzabi Falmata ta farka, fuskarta ta kumbura gaba daya jikinta sai ciwo yake idonta ma ya kumbura sosai sakamakon kukan da ta kwana tana yi.
Babu abunda ta fasa daga cikin aikin gidan da ta saba, ta sani sarai idan ta saka kuiya ko tace ba zata iya ba wani karin wahalar ne. Tana aikin tana kukan zuci har ta yi ta gama, ta dawo dakinsu ta zauna ta gefe daya dan bata iya zama daidai.

Tumba ce ta shigo dakin tana kare mata kallo.

“Ba za ki tashi ki je gurin aikin ba?”

Kallon Tumba tai kamar zata fasa kuka, bata jin abunda ta ce sai dai tana ganin bakinta na motsi.

“Ban ji komai ba Umma”

Ta fada muryarta na rawa kamar yadda jikinta ma yake rawa dan ganin take kamar dukanta Tumba za tai ko ta sake mata wani mugun sherin. Wani kallo Tumba tai mata.

“Ni za ki fara yi wani sabon siyasa?”

Ganin Tumba ta nuna kanta da yatsa yasa ta nemi duk inda wani kuzari yake ta tattaro shi ta saka a jikinta ta mike tsaye ta karasa kusa da Tumba dan jin abunda take fada.

“Wallahi ban ji me kika ce ba Umma bana ji sosai”

Ta fada kamar zata fasa kuka, Tumba ta san Falmata ba zata mata karya ba, ba zata mata haka da gangan ba, yanayinta kadai ya isa ya sanar da gaskiyarta.

Tumba ta dan tabe baki, sai a lokacin ne take girmama marin domin ba marin wasa Baba yai ma Falmata ta ba, gashi fuskarta har ya kumbura.

“Cewar nai ki tashi ki tafi aikin”

Tumba ta fada cikin daga murya ta maimaita mata ta yadda za ta ji. A take Falmata ta fara murza yatsun hannunta so take ta sake tuna mata cewar sun koreta amman sanin waye Tumba yasa dole tai shiru ta sauke kanta kasa.

“Ba za ki je, ki ba su hakuri ba?”

Wannan karon ta ji domin Tumba da karfi tai maganar.

“To”

Amsa tana motsa jikinta daker domin ba karamin tsami yai mata ba. Tumba ta juya ta fice daga dakin. Falmata ta nufi gurin da Hijabinta yake ta dauka ta saka ta fito. Da gangan Tumba ta kira ta karbi dumamenta ganin Baba na tsaye yana shirin tafiya.
Falmata ta nufi inda Tumba take da zimmar karba ba dan ta ji abunda tace ba sai dan ganin tana miko mata kwanonta. Ba dan tana jin yunwa ba domin komai ya fitar mata a rai, kan ta karasa Baba ya daka mata tsawa.

“Kar ki karbi abincin nan, ba za ki sake cin abincin gidana ba, tun da kika zabi iskanci....”

Cak Falmata ta tsaya ta kasa karasawa gurin da Tumba take zaune taka miko mata dumamen, ta ji abunda Baba yace saboda yanayin muryarsa irin mazajen nan da idan suna magana daga murya suke, balle kuma ita da baya iya yi mata magana a hankali.

“Haba Malam ba a horo da yunwa, na san Falmata ta yi laifi amman ka dubi girman Allah ka yi hakuri, ba a biye ta yaro”

“Ni dai na fada miki ban yafe a bata abincin gidana ba, ba zan ciyar da karuwa ba”

Ya fada kai tsaye sannan ya nufi kofar fita ko inda Falmata take be kalla ba. Baki sake Falmata ta bishi da kallo hawaye na sauko mata zuciyarta na mugun kuna, kamin ta kalli Tumba wacce ke kukan karya.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login