Showing 261001 words to 264000 words out of 286946 words

Chapter 88 - Fulani Book 1 Hausa Novel Complete

20 Dec 2024

1389

da yakr zaune ya dauki apple daya ya nufi windows din dake dakin.

“Ki fara siffanta ni da irin sifar da kike son ganina zan bayyana yanzu”

“Na san kai fari ne, ina son na ganka a cikin green din yadi, da bakar hula kana kamshin turarenka, kana murmushi kana kallona”

Murmushi yai.

“Gani nan zan taba ki...”

Saurin buden idon tai a zatonta da gaske ne, sai ta ga babu kowa a gurin.

“Ba ka iya ba, kawai kana canka ne”

Murmushi yai sauti.

“I can't wait to see you Fateema...”

Ta yi shiru tana murmushi.

“Idan na fada cewar kana kira wai ba a yarda da ni”

“Ba na ce ki daina fadawa kowa ba?”

“Kuri na ke yi ai”

“Kurin me?”

Ta yi dariya da yar siriyar muryarta, ba ta ce komai ba har na tsawon lokaci.

“Zan aje waya, amman kamin na aje fada min abun da kike so”

“Karatu dan Allah ranka ya dade, ina son karatu ka ga Bappa na yana jin maganar ka dan Allah ka masa magana ya bar ni na yi likita kamar kai”

“Hmmm miyasa sai likita? Why not lawyer ko wani dabam?”

“Aa irin na ka dai”

“To ai kin kusa zuwa nan sai a saka ki makaranta kawai”

“Waye zai kawo ni?”

Yayi shiru yana jin kamar yayi subul da baka.

“Yan'uwanki mana, very soon za a kawo ki”

“Tare da wa?”

“Yan'uwanki”

“Da gaske?”

“Na taba karya?”

Ta yi dariya har da kyalkyalawa ta rufe ido kamar yana gabanta. Shi ma murmushi yai he can't say bata son shi amman zai iya tabbatarwa duniya izuwa yanzu Fadimr bata da wanda yake saka ta nishadi da sauraren labaranta any how kamar shi, all her silly questions zai bata amsa be taba jin ya gundura ba duk da kasancewar ba mutum ne mai son yawan magana ko tambaya, but he can't tell why idan Fadime ce zai tsaya ya saurarenta kuma ya amsa mata, kuma be tana gajiya da kin kiran a waya ba, ita kuma da ta iya kullum za a jera masa filashin ya fi a kirga haka ma Bappanta da duk wanda take da number shi.
Bayan ya katse kiran ta koma cikin bukkatarta ta aje wayar da screen dinta ya gama cin ubansa a hannunta saboda faduwan da wayar take any how, fitowa tai ta nufo inda Inna take zaune tana gyaran shinkafa ta zauna kusa da ita.

“Inna wai zamu ta fi yola?”

Inna ta kalleta.

“In ji wa?”

“Ranka ya dade ya fada yace wai za mu tafi Yola”

“Eh”

“Gurin me?”

“Gurin Aurensa mana”

“Aurensa kuma?”

“Eh”

“Aure zai yi?”

“Eh ba kin ce ba ki son sa ba?”

Take idonta ya cika da kwalla gabanta yai mugun faduwa.

“Amman be fada min ba, Inna da gaske?”

“Eh mana ba kin ce baki son shi ba”

“Ni ban ce ban son shi ba, na dai ce ina son Wasim, kuma na ce garin ya min nisa, amman ai yana da kyau kuma yana da sarauta”

Inna ta kalleta da kyau.

“Ashe kina da hankali, har kin iya kwadayi Fulani?”

Hawaye ne ya sauko mata, har ga Allah a lokacin da Bappa yai mata maganarsa ba ta ce  bata son shi ba, tace dai ita tana son Wasim, domin har kusan dukanta Bappa yai a lokacin amman bata dauka aure yake nufi ba.

“Kuma ai cewa yai Fulani za ki iya auren ranka ya dade be ce yana so na ba”

Ta fada tana jin wani irin kololin bakinciki na ta so mata kamar ta hade zuciya ta mutu. Mikewa tai tsaye ta nufi bukkarta hawaye na sauko mata, if ta san Bappa yana nufin Shattima yana son ta ta ya za a iya cewa aa? Tana tana son Wasim amman shi ma Shattiman ai tana sonsa musamman a irin wannan lokacin da yake kawar mata da kewar Wasim, kuma yake yawan faranta mata rai.

“Kenan yanzu wata zai aura?”

Hawaye ya sauko mata, sanin cewar ba za ta iya fadawa Bappa cewar yanzu ta aminta ba, ko ma ta aminta ai ba a a fasa auren ba, amman shi be fada mata haka ba kuma be fada mata cewar zai yi aure ba.

“Yanzu ai zai dinga ganin na masa butulci...”

Ta fada kamar gaske irin na yan matan nan da suka dade tare da sarauya daga karshe suka yaudare shi.

“Daman ba ni da sa'a babu mai cewa yana so na, Wasim ne kawai ya ce haka shi ma kuma ya tafi ya bar ni wannan ma haka”

Ta dauki wayar ta jefar a kasa iya karfinta tana jin wani kololon bakinciki na taso mata, hakan be wadatar da ita ba sai da ta saka fada ta taka wayar tana hawaye.

“Bana son wayar bana son komai”

Ta fashe da kuka marar sauti tana jin cewar laifin na Bappa ne, da be fahimtar da ita ba har ta gane. Fitowa tai tana kuka ta zo gurin Inna tana fadin.

“Kuma Wallahi ba zan je bikin nan ba...”

Inna ta yi dariya ta soma mata magana da halshen fulatanci.

“Kishi kike kenan?”

“Ni bana kishi kawai dai ina jin bakinciki, kenan ni ba zan yi aure ba? Ba ni da farin jini... Ban san wa na gado ba”

“Ubanki kika gado, waya ce ki ce ba ki so? Ke wai har yanzu ba za ki daina halinki ba ko Fulani?”

“To a dawo baya a tambaye ni, ni ba cewa na yi bana so ba, cewa na yi ina son Wasim shi ma ai da ne, yanzu na rasa kowa”

Inna bata sake bin ta kanta ba, domin maganar cewa bata san wa ta gado ba ya batawa Inna rai kuma ta san da ita take.

“Inna dan Allah idan Bappa ya dawo ki ce masa a bar wacan maganar, amman karki ce ni na ce”

“Sai ki fada masa da kaki”

Tashi Fadime tai ganin da gaske Inna take zancen auren Shattima, daukar abun tai ta saka a rai kuka ta sha b dan kadan ba tana tunawa yadda tai ta fama a baya babu saurayi mai sonta, tun da ta shigr ciki dakin bata fito ba har akai sallah azahar sannan ta fito tai sallah, Inna na fadin ga abincinta bata kula ba ta koma ciki ita ala dole abun duniya ya isheta. Gashi sai tunanin Shattiman take yadda yake mata da kuma dan zaman da tai a can ta sabo da shi, bayan shi yanzu kan bata da wanda take ganin zai iya zuwa ya ce yana sonta ko ya so ma. Kuka tai sosai har sai da fatar idonta ta soma ciwo, Inna bata dauki abun da gaske ba har sai da akai la'asar ta ga Fadime ta fito ta yi alwala ta koma ciki ta yi sallah kuma bata fito ba.

“Fulani Fulani...”

Tana jin Inna na kiranta ta ki ta amsa, domin ta daura damarar kin cin abinci da sakewa saboda abun da Inna ta fada mata. Inna ta yunkura zata tashi kenan sai ga sallama wata bakuwar fuska tare da wata Lanti yar'uwar Amo, sosai gaban Inna ya fadi ganinsu a cikin gidan. Ta amsa musu a sanyaye tana mika musu gaisuwa cikin karfin hali zuciyarta na raya mata ko dai wani abu suka zo su yi ma Fadime ko ita ko kuma Amo suka maido dakinta.

“Sannu da zuwa”

Inna ta fada sannan ta nufi bukkarta ta dauko musu tabarma ta shimfida musu, ko kallon tabarma ba su yi ba suka ce.

“Aa ba zama ya kawo mu ba, ina maganar zama aure ya kare”

Inna ta ji gabanta ya fadi.

“Kaya mu ka zo kwasa?”

“Lafiya dai?”

“Allah dai ya kyauta idan Jauro ya dawo ai sai ki tambaye shi”

Lanti ta sake fada sannan ta bukkar Amo ta bude rufin da akai ta dage labulen zanen ta shiga ta fara to da kayanta, yan tsuman kara sai yan tarkacenta, wanda suke tare kuma tana shirya kayan tana kullewa a zane, ta dauka ta kai wajen mai yar gof din da suke tare yana sakawa har suka kwashe komai tsab Fadime bata leko waje ba, Inna kuma na tsaye tana kallon ikon Allah zuciyarta na raya mata abubuwa kala kala, sai dai fi tunanin mutuwa Amo tai duba da tsawon lokacin da aka kwashe ba amo ba labarinta.

“To Amo dai zama ya kare sai ki shimfida tabarma dakinta ki kara, ki biya bukanki bukatarki ta biya”

Lanti ta fada sannan ta sa kai ta fice, Inna na maida mata da martani.

“Ba ni da boka ba ni da malam sai Allah, komai aka min Allah ne mai kare ni kuma mugun abun ta ne ya koma kanta”

Kalaman da Inna take ne yasa Fadime fito tana kallon bukkar Amo da aka bude, tana jin lokacin da ake kwasar kayan amman ta ki fitowa sai da ta ji Lanti na fadin zama ya kare. Zuwa tai ta leka bukkar ta ga babu komai ciki sai dan abunda ba a rasa ba marar amfani.

“Kenan mun huta mun huta mun huta”

Ta fada tana rawa kamar ba ita ba.

“Allah yasa ma ta mutu can mugun abun ta ya bita, mun huta da dangin mayu”

Rawa take har da juyawa jamar ba ita ce ta gama kuka ba, Inna dai sai kallonta take domin idomta ya nuna kuka tai amman yanzu tana murna an saki Amo.
  Bappa be dawo a sai yamma kamar yadda ya saba, tun kamin Inna ta labarta masa abun da ya faru ya fahimci sun kwashe komai domin alamu ya nuna haka, kuma daman can ya san za a rina tun da ya aika mata da takardar sakinta, domin har yanzu ciwon be barta ba sai an kwantar sai an tayar bata iya komai.
Inna har cikin ranta ta jidadin labarin da Bappa ya bata cewar ya saki Amo, daman can kullum tunaninta da zulluminta kar wata rana Amo ta dawo da zama a gidan, sai dai bata nunawa Bappa ba sai ta nuna masa bata jidadin hakan da yai ba.

“Haba Malam tana cikin ciwo kuma sai ka kara mata wannan? Da ma ka hakura har ta samu lafiya tukuna”

Uffan be ce mata ba ya dauki redio sa yana kamo bbc domin 8:30pm ta yi, bayan ya kama tashar ta aje redio ya dauko tuwon shimkafar da miyar kuka ga uban manshanu Inna ta labta masa abun ka da masu abu, ya bude ya dauki ruwan da ke cikin kofin ya wanke hannunsa ya fara cin, Inna sai gyara masa fitila take tana jinta kamar wata Amarya. (Na ce Ashe su Inna ba a son kishiya 🤣).

“Na yi magana da Sani mai jakkai na fada masa ya fara kawo mana yashi”

“Mashallahu aiki ya tashi kenan?”

“To me ake jira, tun da komai ya mallaka, Shehu ma ya ce abokansa zai dauko yan birni su yi aiki”

“Allah ya taimaka, ai haka yayi kara da ka siyar da wacan gidan ka dawo nan ka gina mana na zamani”

“Eh komai za a saka Inshallahu, na fada Shehu gida mai kyau kuma gina mai kwari na ke so, yace ko gidan Mai Garin ba zai kai nawa ba, yace har da tistis za a saka”

Fadime ta kyalkyale da dariya daga can cikin bukkar da take.

“Bappa tiles ake cewa ba tistis”

Daga Inna har Bappa dariya sukai domin ba su dauka tana sauraren firar ta su ba.

“Ja'ira, to tilis din har shi za a saka Inshallahu”

“Allah ya nuna mana an gama komai cikin kwanciyar hankali da tsawon rai, shi kuma Allah ya saka masa da alheri”

Fadime na jin haka sai ta tuno da zancen dazun cewar Shattima zai yi aure, take ta koma ruwa tana kukanta kadan kadan ta yadda babu wanda zai ji. Inna ba ta fadawa Bappa komai ba har sai da dare ya raba ta tabbatar a lokacin Fadime ta yi bachi sannan ta labarta masa yadda sukai da Fadime dazun. Bappa yayi murmushi.

“Ai hakan da tai ya taimaka mana, ina tabbatar miki da ace ta san da maganar nan da yanzu an yi garkuwa da mu ance mu kawo kudi, amman a haka sai ya taimaka mana babu wanda ya sani sai dai kwatsan su ji an yi ma Fulani amre”

“Ai haka yafi, daman magana ta yi yawa akanta sai fadar ake bata da miji, ai Wallahi hakan ya min dadi Allah ya bata miji ba karami ba, dan babba mutum kuma babban mutum mai mutunci”

Bappa yayi murmushi jin dadi yana jin wata kima na kama shi zai yi sakuta da sarki.

FALMATA POV.

Hannunsa na lakkame da wuyanta tana karanta masa abun da ta rubuta.

“Mamana, Babana Kakana”

Ya saka yatsansa ya ja kumatunta na dama.

“Ina mijina?”

Ta yi dariya sai ta kalleshi.

“Mantawa na yi”

Yatsan nasa ya saka mata a baki ta fara tsasa kamar sweet.

“Yanzu ki rubuta sunanyen mutanen kuma ki manta da mijinki? Teem Teem?”

Ta yi shiru tana murmushin da har dimple dinta ke lasawa saboda yadda ta samu guri in 3 months jikinta ya fara kyau, daman can abinci mai kyau ne babu da kuma kwanciya hankali.

“Zan rubuta fa sai aka kira sallah shi ne na tafi sallah sai ka dawo”

Ya kai bakinsa saitin kunnensa.

“Ban san ki da karya ba”

Ta saka hannayenta ta rufe fuskarta, sai yai murmushi ya kai hancinss yana shinshinar gashin kanta da ya sha gyara sai kamshi yake.

“Karki sake bari a taba kiki kai, bana son mace da kitso, gashi yana kara min sonki”

“Kai ma karka sake yin aski”

Ya fada tana jin kamar ta kai hannu ta taba shi kuma tana jin kunyarsa har yanzu, shi din ne baya jin kunyar yi mata komai ko kuma yin komai a gabanta.

“Sirleem”

Dayan hannunsa ya saka ya buge mata baki a hankali ta yadda ba zata ji ciwo ba.

“Ban ce ki daina kirana haka ba?”

Dariya tai tana jin kunyar kiransa da sunan da ya rada ma kansa a kanta.

“To Baby...”

Ya amsa daker yana kai wannan karon halshensa ya kai gurin wuyanta yana mata zirya da shi.

“Hmmm”

“Dan Allah Baby, yaushe zan tafi gida?”

“Ba yanzu ba Babyn baby, sai kin shekara”

Ta dan bata rai, domin har ga Allah tana son fitar amman ya hanata kullum sai yace mata sai ta shekara.

“Dan Allah fa”

Ta fada a shagwabe kamar ba ita ba, sai ya dago yana kallonta fuskarta da kadan ya rage hancinta ya taba nasa.

“Idan kin je gida me zaki yi? You know i hate wannan matar dai ko?”

“Ai ba ita zan je gani ba, Babana”

Bakinsa ya saka ya tsose cinin hancinta tass sannan ya dauke bakinsa yana maida numfashi.

“Da dare zan kai ki ganshi, ni kaina ina son na kyautata masa amman wannan matar ke bata min rai, ta fa wahalar min dake, and ji yadda tai ma dan'uwanki”

Falmata ta kalleshi da sauri domin ta san bata taba labarta masa cewar Ameer dan'uwanta ba ne, kuma bata ce masa Tumba ta yi masa asiri ba.

“Wa ne dan'uwana?”

Hannunsa ya saka cikin rigarta yana shafa cikinta.

“Ameer mana, Momy ta fada min komai, kuma the way da take ba ni labarin kana ji kasan asiri akai masa, ta ya mutum zai gudu ya bar uwarsa kuma ya kasa nemanta, i wonder ya zai ji idan ya sani”

Falmata ta yi shiru tana tunani.

“Allah sai ya mana shari'a da matar nan, ta cutar da mu sosai”

“Har kike son ki je ganinta”

“Ba saboda ita zan je ba saboda Baba, komai yai min ai shi Babana ne”

Ya kwaikwayi muryarta har da wani juya kai kamar mace.

“To masu Baba zamu je anjima mu gaisheshi, daga nan sai Tumbin ta gan ni ko ya za ta yi?”

Ta yi dariya.

“Zata ce ya akai ka zama yaro, kuma Sirleem, mawaki”

Ya shafa kansa tare da cire hannunsa a jikinta ya mike tsaye.

“Da ne ai wannan, yanzu kuma mu da waka sai dai kallo, Hajiya ta hana kuma na hanu”

Ya nufi upstairs ta bishi da kallo.

“Ba cewa kai makarantar zaka je ba?”

“Wasa na ke miki, wane irin karatu yanzu ina cin amarci? Ki dai iya wanda nake koya miki idan kin haihu sai na saka ki wacan din”

Ta mike tsaye.

“Haihuwa kuma”

Sai ya juyo yana kallonta.

“Yes... Ko ba ki san kina da ciki ba?”

“Ba ni da ciki Wallahi”

“Ki daina rantsuwa ni na san abun da na yi, yan mata fresh irinki suna saurin daukar ciki idan sun hadu da mazaje irin Jaruman nan na gaske, kuma na san abun da na ke yi kullum Hajiyata”

“Ni ban gane ba”

Yayi dariya tare da juyawa ya cigaba da hawa stairs din.

“Anjima zan ganar dake Babyn Baby”

Da kallo ta bishi har ya haye sama sannan ta kai hannu ta taba cikinta.
As he said sai da dare suka shirya daga shi har ita cikin tufafi mai tsada shi yana sanye da shadda sky blue ita kuma lace ja sai mayafinta sky blue, ba karamin kyau tai ba ko ranar da aka kawota gidansa ba tai kyau kamar na yau ba, tufafin jikinta kadai sun isar da kyaut balle kuma kwaliyar da ta sha kamar wanda zata tafi gurin biki. Yana zaune falo yana waya ta soma saukowa da talkamin yan kwakwasa sai amsa amo suke na daukar hankali, dagowa yai yana kallonta sai gashi ya mike tsaye yana kokarin yanke wayar da yake.

“Fadil za su sake kiranka”

Ya katse wayar yana kallonta cike da so da kauna, kusan kullum kara kyau take masa.

“Wow Babyn Baby kin duba madubi kuwa? I swear kin yi kyau over”

Ta yi murmushi, kamin ta karasa saukowa ya iso ya daga ta sama yana juyawa.

“I love this girl, look at you ga pretty face, and heart of gold, ga beauty skin, kai Alhamdulillah”

Ta yi dariyar da ta bayyana hakoranta. Sai ya mika mata bakinsa.

“Kiss me kiss me”

Ya duko bakinsa ta saka cikin nasa, sai da ya tsotse bakinta sannan sauketa ya rumgume.

“Sweet lips”

Runtse idonta tai yana jin kunyar abun da tai, duk da kasancewar ya kusan zame mata jiki, domin kullum sai yayi kissing dinta at any time any how kuma yace shi ma tai masa. Wayarsa ya ciro ya juyo da ita ya soma daukarsu hoto.

“Mu fa komai ba mu yi ba, ko dan pre-wedding pictures din nan da ake ba mu yi ba, ba dan ma gurin bikin kamfanin mu na sanar ke a matsayin matata ba da har yanzu wasu ba su san na yi aure ba”

“Ai pre-wedding ba shi da kyau a musulunci”

Ta fada sai ya sumbancin kumatunta.


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login