Showing 123001 words to 126000 words out of 286946 words

Chapter 42 - Fulani Book 1 Hausa Novel Complete

20 Dec 2024

960

kuma ya karbe ta ba tona mata asiri ba ya dauki laifin a kansa bayan ya san ba shi ya aikata ba. Bata san lokacin data mike tsaye ba, zata fara tafiya sai Hajiya ta rikota daman haka take nuna mata son munafurci har take ganin kamar ta fi son ta da Ammy.

“Daughter tafiya zaki yi?”

Nana ta kalli Hajiya idonta tab da hawaye, ta yi shiru sai kuma ta tuna Hajiya mai share mata hawayenta ne a koda yaushe.

“Hajiya ina son magana da ke”

Hajiya ta mike tsaye tana kai bakinta saitin kunne ta Nana a zatonta maganar ta baki da baki ce kawai, sai Nana taja hannunta suka fita daga gurin, sai da suka isa gurin da AA ya faka motarsu sannan ta sake hannun Hajiya ta sunkuyar da kai kasa.

“Lafiya dai daughter fada min matsalarki”

Nana ta kalleta tana fashewa da kuka.

“Hajiya wanda aka ce ya saci sarkar nan ba shi ya sace ta ba”

“Ban gane ba”

Cewar Hajiya tana kallon Nana da mamaki, zuciyarta na cika fal da farinciki jin furuncin Nana ta san wata kila zata fadi cewar ita ta saci sarkar wanda shi zai fi komai yi mata dadi a yanzu, saboda Ammy za a zaga ita kuma yabe ta na ganin tana son hada auren Nana da danta.

“Ni na sata.... Amman ban san miyasa n sata ba...ban san mi zan yi da sarkar ba...”

Hajiya ta kamo hannunta.

“To ya akai yace shi ne?”

“Ya fanshe ni ne, amman ba shi ya dauka ba, ni na dauka Hajiya ki taimaka masa kar a masa komai dan Allah, Wallahi Sardauna ba barawo ba ne na yarda da shi”

Hajiya ta ji wani abu ya sauko mata tun daga saman kanta har cikin kafafuwanta.

“Ke wa kika ce?”

“Sardauna”

Nana ta maimaita tana kuka sosai, domin wata kalar nadama ce ke rabarta.

“Ke sake fadi na ji”

Hajiya ta sake tambaya baki saki.

“Sardauna, Hajiya Wallahi ba barawo ba ne, dan Allah ki taimaka masa kar su masa komai saboda da ni”

A take kallo ya koma sama, sai murnar Hajiya ta koma ciki, wani kalar fever ta ji yana sauko mata.

“Saurayinki ne?”

“Aa shine sabon direbana”

Nana ta fada har muryarta a shakewa, jikinta sai bari yake irin na wanda kuka yake cinta sosai. A take Hajiya ta saka salati.

“La'ilaha illala muhammadu rasulullah sallalahu alaihi wassalam, ki ce ni na siya da kudina”

Nana bata kula zancen ba balle har ta gane inda ta dosa, wani irin dogon numfashi Hajiya ta ja ta sauke tana kara nanata sunan.

“Sardauna...”

Jin hakan yasa Nana ta rike hannayenta.

“Hajiya dan Allah ki taimaka kar a masa komai”

Hajiya ta jata jikinta ta rumgume tana rarrashinta kamar gaske.

“Daina kuka yanzu zan kira Babanki Jarma na fada masa ya binka inda aka kai shi”

Tana fadin hakan ta saki Nana ta nufi gurin motarta, Nana ta bi bayanta da sauri. Direban Hajiya na hangota ya fito cikin motar ya bude mata gidan baya, kamar daman abun da take jira kenan tana isa ta shiga gidan baya ita da Nana shi kuma ya tashi motar. Nana ta kwanto jikin Hajiya hawaye a sauko mata, can kuma ta dago hannunta tana ta kallon tafin hannun ita kanta bata dauka bayan Ammy da Mai Martaba da take yi ma sata ba zata iya yin wata a public place like this, kuma sarka. Ta jimke hannun wasu hawayen a sauko mata. Ganin hakan yasa Hajiya ta ciro wayarta a jaka ta nemo number Jarma, sai da wayar ta dade tana ringing sannan ya daga.

“Hello Jarma”

“Hajiya barka da dare”

“Dan Allah yar wata muka samu, wani yaro ne yai sata a gurin bikin da muka zo na yar Faro Ambassador, shine police suka tafi da shi, to ina son ka saka a binciko mana wane police station aka kai shi”

“To yayi, amman kin yaron ne?”

Hajiya kamar tana jira ta amsa da karfi.

“Eh sunanshi Sardauna, shine sabon direban Nana”

Daga dayan bangaren Jarma ya amsa da kuzarinsa.

“Sardauna fa kika ce Hajiya?”

“Eh a taimakawa daughter na kar ta shiga damuwa, gani tare da ita, zan kira ka anjima”

Bata jira abun da zai ce ba ta kashe wayar tare da kai hannunta ta taba Nana.

“Ki daina kuka ai komai zai zo da sauki tun da na fadawa Jarma”

Nana ta rumgume Hajiya tana jin wani irin son ta a ranta, domin ta tabbatar da Ammy ce ba zata mata haka ba. Apartment din Hajiya direban ya faka motar, sai Hajiya ta fito rike da hannun Nana ta nufi cikin gidan da ita, har cikin dakinta ta kai ta kwantar.

“Kwanta a nan ki huta”

Ba musu Nana ta kwanta a gurin, Hajiya kuma ta karasa ciki ta aje jakarta ta fice daga dakin rike da wayarta. Tashi Nana tai zaune ta kunna Power button din wayar sai ta samu wayar a pattern da katon hoton AA a din daya cika screen din wayar, wani irin tausayinsa ne ya kara sauka a ranta, ji tai kamar bata da natsuwa idan bata san halin da AA yake ciki ba, hakan yasa ta mike tsaye ta bi bayan Hajiya.


Hajiya ta na fitowa daga dakin, ta shiga second room dinta ta rufe ta kira number Jarma, wannan karon bugu daya ya dauka.

“Jarma”

“Hajiya”

“Jarma a nemo inda yaron nan yake, maganar bokan ta tabbata sunanshi Sardauna”

“Hajiya ai ni abun ya bani mamaki, ace har kin san shi”

“Ni ma sai yanzu nake saninsa, amman ni na siye macijin da hannuna, domin ni na dauke shi aiki ba tare da sani ba, kuma ba tare da na yi bincike ba, ina cikin tashin hankali Jarma ka nemo yaron nan”

“Dole zan saka a nemo shi ai, ba ke dai ce a matsala ba har da ni”

Jarma ya amsa daga dayan bangare.

“Kuma idan an samo shi, ka fada min da wuri, a juyar da case dinsa daga sata zuwa kisan kai, a tura shi gidan kaso, ko nawa ake ashewa zan kashe, ka shigo da safe zamu yi, domin dole ne mu koma gurin mutanen nan kar abubuwan su kara mana yawa, ina murna Nana ta fara dan hali sai kuma abu ya juye min haka”

“Gaskiya kam ya kamata mu koma garin nan daga can ma sai su sanar da mu wacece Fadime ita ma kar ta ribance mu”

“Haka ya kamata, muna ta sanyin jiki abubuwa suna faruwa da mu, ya kamata mu yi maganin komai tun a yanzu”

“Wai daman Nana ta fara dan hali Hajiya”

“Hmm Jarma kenan, ai har abunda ya fi sata sai Nana ta yi, ba ni da buri sai na ganin kukan Ammy kuma sai ta yi shi indai ina raye, yanzu dai ka nemo yaron kuma ka san wanda aka hannatawa case din, gobe ka zo ka karbi kudi ayi komai tun da wuri, abun ai ya zo mana da sauki tun da har haka ta faru”

“Shikenan Hajiya zan shigo gobe inshallah”

“Yayi kyau sai anjima”

Ta fada tana sauke wayar, tare da sauke wata doguwar ajiyar zuciya.

“Dole ne na shirya jibi nai tafiyar nan, idan ba haka ba ban san me zai sake faruwa ba, ya kamata na tari Fadimen ita kuma tun kamin ta tare ni”

Line Hajiya Talatu ta nemo ta aika mata kira, ringing daya ta dauka kamar daman can jiran kiran take.

“Hello Talatu”

“Hajiya ina cikin tashin hankali, Waziri ya dage sai ya hada auren nan”

Ta amsa da muryar kuka wanda hakan ke nuna ta ci kukan har ta gode Allah.

“Nima ina cikin nawa tashin hankali, amman dai ki shigo gobe sai mu yi magana, be kamata mu kyale yarinya akaita ga halaka ba”

“Shiyasa nake son tun wuri mu tafi garin nan tun da aikinsu kamar yankan wuka ne, su wargaza komai tun abu be yi nisa ba”

“Hmm ke dai ki shigo gobe kawai”

“Tau Allah ya kai”

Hajiya ta sauke wayar tana jijjina lamarin bokayen nan sai yanzu ta kara tabbatar ba da wasa suke aiki ba, kuma dama ta dade tana son irinsu masu aiki kamar yankan wuka. A yanzu ne take jin ya zame mata dole ta je garin ko dan maganin matsalolinta.


**
Shirun da Nana ta ji ne ya tabbatar mata da Hajiya ta gama wayar da take, sai ta daga daga jikin kofar wasu sabbin hawaye masu zafi na sauko mata. Why Hajiya zata juyar da case din to kisan kai bayan tace zata taimake ta? Mi Sardauna yai mata? Anya ya cancanci haka? Da sauri ta ta bar kofar ta dauki hanyar da zata sadata da part dinsu hawaye na sauko mata kamar ba gobe, daman ta bi bayan Hajiya ne da zimmar ta sake rokonta sai ta tararda kofar dakin a rufe tana kokarin turawa ta ji sautin muryarta na tashi kadan-kadan hakan yasa ta kai kunnenta domin ta ji abun da Hajiya take fada, domin azatonta zata ji ko Jarma ya gano inda suke ne ko kuma wani abu sai gashi ta ji mummunan abu da bata taba mafarkin ji ba, kuma ba tai zato daga Hajiya ba.

“Miyasa ma nai satar to? Why?”

Ta tambaya cikin kuka tana jin haushin kanta. Ganin bata da mai taimakonta a yanzu wanda zai fito da Sardauna, bata isa ta tunkari Ammy da wannan maganar ba, daman daga Hajiya sai Zainab ne suke mata gata a gidan, sai kuma Shattima, sai dai ba zata iya fada masa ba, gudun kar Ammy taji ko Baba Waziri. Silently ta isa bangarensu ta shige dakinta ba tare da kowa ya sani ba. Maida kofar dakin tai ta rufe ta jingina da kofar ta fashe da sabon kuka tana kallon hoton AA dake gaban wayarsa. Haka ta shafe awa uku zaune a gurin tana aikin kuka abun da bata taba ba, idanuwanta da fuskarta suka kumbura, tun tana jin kuzarin kuka har ta nemi kuzarin ta rasa. Can ta mike tsaye ta cire tufafin jikinta ta dauki tufafin bachi ta saka ta shiga bandaki ta wanke fuskarta, sannan ta fito ta hau saman gadon ta kwanta ba dan tana jin zata iya bachin ba sai dan jin jikinta da take da rashin kwari. Misalin 10 da yan mintuna kiran Anti Rabi ya shigo wayar AA dake hannun Nana.
Second Mother shine rubuce a wayar dauke ta emoji din heart. Kasa daukar kiran tai sai kawai tai rejecting call din ta kashe wayar gaba daya.

“Innalillahi”

Ta furta, she can't remember when last ta furta wannan kalmar ma. Bata taba jin ta a tashin hankali irin yau ba, abun da ta ji Hajiya Babba na fada ya fi daga mata hankali fiye da halin data jefa AA. Sauka tai saman gadon ta bude kofar dakinta ta fito falo, babu kowa a falon an kashe kayan kallo wanda hakan ke nuna Ammy tana bangaren Mai Martaba ko kuma tana shirin tafiya ne. Dakinta Nana ta dosa tana taba kofar ta ji ta a bude sai ta tura ta shiga, duk wani tsoron kar Ammy ta ji da take da gudun fadanta ko dukan Baba Waziri sai ta ne meshi ta rasa, bata da buri a yanzu da ya wuce AA ya zama free. Daga bakin kofar ta tsaya tana kallon Ammy dake tsaye jikin wardrobe dinta tana daukar wasu kaya, ta jikin madubin wardrobe Ammy ta hango Nana sai ta juyo tana wani kallo fuska ba yabo ba fallasa.

“Ya akai?”

Nana ta kalleta hawaye na sauko mata, sai kuma ta nufi inda take ta karasa har kusa da ita.

“Ammy... ”

Sai kuma tai shiru hawayen na sauko mata.

“Ammy na san ni da ke don't get along, amman dan Allah ki taimaka min”

“Minene?”

“A gurin bikin da naje dazun na su Amal na saci sarkar gold ta kawar Amal, nasan be dace nai sata ba right? Na sani amman ban san miyasa nai ba, direbana sai ya karbi sarkar yaje ya maida shine suka ce shine ya dauka kuma Wallahi ba shi ba ne ni ce, shine suka kira masa police aka tafi da shi, dan Allah ki taimaka Ammy a fito da shi pls”

Ammy ta saki kayan hannunta sun zube kasa, tana yi ma Nana wani irin kallo kamar na tsoro kamar na mamaki, a take idonta ya cika da kwalla. Tassss ta dauke Nana da wani irin mahaukacin mari, cikin wani irin zafin nama da bata taba sanin tana da shi sai yau.

“Sa... Sa... Sa... Sata Nana?”

Ta furta daker hawaye na sauko mata, Nana kam tun da Ammy ta tsinka mata mari tai bata da sauri tana ma Ammy wani kallo tsoro domin ji take kamar babu fuska a jikinta.

“Na san be dace nai ba Ammy na sani....”

Ta furta a rikice tana girgiza ma Ammy kai. Sai kuma ta juya da gudu da fice daga dakin, Ammy ta bita da kallo baki sake, wani abu ta ji yana mata yawo a zuciya yana neman numfashinta, da sauri ta rike murfin wardrobe din ta jingina ta zauna a kasa tana numfashi daker.

“Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un”

Ta furta daker tana ta kokuwa da numfashinta.



FADIME POV.

Hannu biyu Wasim ya saka ya dauki Fadime ya ya nufi kofar fita, zaratan mazajen da suke fadar tsaye suka nufishi sai Sarkin ya daga musu alamar su kyaleshi. Zainab na ganin hakan ta bi bayansu yadda yake tafiya da gudu sai ka dauka biyo shi akai Fadime kam sai tari take hankalinta ya dade da barin jikinta. Duk inda ya nasa kafarsa Zainab sai ta nasa tata, har suka isa wani karamin gida mai dauke da dakuna uku, dakin farko ya shiga wanda shi ya fi ko wane daki girma. Yana shiga ya kwantar da Fadime gaban makahon bokan ya soma magana da shi da yarensu.

“Kaka ka taimaka mata ta daina tarin nan kar ta samu matsala”

Bokan ya mika hannunsa ya taba fuskar Fadime.

“Wasim miyasa ka aikata haka?”

Wasim be tsaya bashi amsa ba ya nufi inda bokan yake aje magani ya bude ya dauko wani garin magani ya cika hannunsa da shi ya zo ya zuba a bakin Fadime sannan ya dagata ya jinginar da ita jikinsa. Tana yin tarin garin maganin ya bi ta cikin makoshinta sai kaikayin yai kasa, haka ya rika sauka kasa kasa har ya daina mata gaba daya. Wani irin sanyayyiyar ajiyar zuciya ta sauke ta lumshe ido sai bachin wahala. Duk abun da ake Zainab na tsaye kusa da Fadime, yadda yake ta kula da Fadime sai abun ya burgeta duk kuwa da kasancewar rabin hankalinta yana gurin nama da ta ci be mata komai ba. Daukar Fadime yai ya kwantar da ita kan wata shimfida dake dakin, ana dakin bokan kuma kakansa kadai yake da tabbacin zai aje Fadime mahaifinsa ko wani be taba ta, domin be isa ya fitar da ita daga garin ba tare da izinin sarkin ba, gudun kar a cutar da ita daga baya. Hannun Zainab ya riko ya fito da ita daga cikin dakin ya zagaya da ita wani guri mai hudu.

“Zan kai ki gida yanzu”

“Okay”

Ta amsa da sauri daman abun da take nema kenan.

“Amman camera tana can mun baro”

“Ki tsaya a nan karki je ko'ina”

Ya fada yana yin baya baya, kamin ya fice daga gidan, ko minti uku be yi ba ta hango shi ya dawo rike da jakar tata. Yana isowa ya mika mata jakar.

“Rike ta da kyau ki rufe idonki karki yarda ki bude”

“Tau”

Ta rufe idon da sauri, sai ya rika saitin kunkurunta ya kai bakinsa saitin goshinta, yayi hakan ne ssboda kar ta bude idon, domin matukar bakinsa na kan goshinta ba zata iya bude idon ba. Wani irin tsam taji a hikinta, duk yadda ta so ta bude idonta Jin kamar tana kan wani abu sai ta kasa, har sai da ta ji kafafuwanta a kasa, sannan ta bude idon a hankali ta sauke su a fuskar Wasim da hasken fari wata ke haska fuskarsa. Nesa kadan da gidansu Fadime ya sauke ta, ya kai hannunsa jikin walkinsa ya tsinki wani ziri daya ya kama hannunta ya daura mata.

“Shaidar kin zo garin mu”

Ta kalli zaren sannan ta kalleshi.

“Yarinyar fa?”

“Zan kula da ita, ba zai yiyu ta dawo yanzu ba, ki yi tafiyar ki kawai karki bari iyayenta su ganki”

Ta daga masa kai tana binsa da kallo har sai da ta daina hangoshi sannan ta aje jakar ta dauko wayarta ta kunna, number police din ta kira, bata wani dade tana ringing ba ya dauka.

“Hello Hajiya”

“Karka bari mutanen dake tare da kai su san na kiraka, kai musu sallama ka Fada musu tun da ban dawo ba ku za ku wuce, sai ka same ni a gurin karfen sabis”

Ta fada tana daga kanta ta kalli karfen, sannan ta kashe wayar ta fara tafiya da kafa zuwa inda karfen yake, bata karasa ba sakon kar ta kwana wato sms ya shigo wayarta da line Auwal, jiki na rawa ta bude, sai tai arba da mummunan abu.

“Allah yayi ma Auwal Sa'ad rasuwa, idan akwai bashi a tsakaninku ki fada, ko ka fada a sauke nauyi”

Sai da ta karanta sakon sau ba adadi sannan ta yarda hausa take karantawa, bata san lokacin data saki jakar hannunta ba.

“Ya Allah........”

Ta furta da karfi tana jin wani irin kuka na taso mata.

“Allah kasa ba gaske ba ne”

Ya shiga neman line Auwal din sai ta ji shi a rufe, ta sake bugawa ta ji shi a rufe, hannu ta dora saman kai hawaye a sauko mata.

“How...”

Sai kuma ta shiga neman line matarsa kai tsaye. Bata dade tana ringing ba matar ta dauka.

“Assalamu Alaikum”

Ba karamin jihadi Zainab tai ba na danne kukanta ta amsawa kawarta.

“Wa'alaikissalam, ya gida?”

“Lafiya Kalau Zainab, sai kewa da bakinciki”

“Da gaske ne?”

“Ai ba a karyar mutuwa, Auwal ya tafi ya bar ni, na shiga liyin zaurawa yayansa kuma sun zama marayu”

Ta karasa cikin kuka. A sanyaye Zainab ta sauke wayar hawaye na bin fuskarka.

“Innalillahi Wa'inna Ilaihirraji'un”

Ta kashe wayar ta durkushe a gurin fuskar Auwal nata yi mata gizo, kamar daga sama ta ji wani irin kuka ya sauko mata.



***
Cikin hikima police din suka yi ma Bappa Sallama suka kamo hanya, ya bar su sun tafi ne kawai Saboda ganin su police ne, ba dan haka ba, da ba za su tafi ba yarsa ba ta dawo


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login