Showing 90001 words to 93000 words out of 286946 words

Chapter 31 - Fulani Book 1 Hausa Novel Complete

20 Dec 2024

934

Hajiya tai ta mike tsaye kamar ba komai.

“To Allah ya kyauta, ni zan koma bangarena”

“A huta lafiya”

Ammy ta amsa mata, sai da Hajiya tai mata wani kallon sannan ta dauke kai ta fice daga dakin tana mamakin yadda har yanzu Ammy take mallake komai bata son a san da danta a iyalin Mai Martaba.

‘Babu komai lokaci na zuwa, zaki wayi gari kina kuka da idonki, zamu gani tsakanin tawa da taki wacce zata zama karya’

Ta fada a ranta bayan ta fito daga dakin, arba da ta sake yi da Falmata ya tuna mata da sunanta na dazun.

“Falmata....”

Ta furta da muryar da ita kadai zata iya ji tana kallonta kamar a razane, tsaye tai cak tana kallon Falmata kamin ta karasa fitowa daga corridor.

“Jekadiya miye sunan yarinyar nan?”

“Falmata”

Jekadiya ta amsa mata tana kallonta Falmata dake tsaye.

“Falmata...”

Hajiya ta sake maimaitawa sannan tana kara kallonta da kyau, wani irin dogon numfashi taja ta sauke sannan ta nufi hanyar da zata fitar da ita daga falon, sai da ta isa bakin kofar sai kuma ta juyo ta kalli Falmata da mugun mamaki sannan ta juya ta fice.

‘Taya zata lalata mana shiri? Taya? Amman ga zahiri a fara gani, lallai Ammy tana mana milkin mallaka a gidan nan har a kawo wata sabuwar mai hidima ban sani ba? Na zama kashi kenan?’

A ranta take ta wannan sake-saken tana nufar bangarenta.

“Dole ne na kara mikewa tsaye, kar maganar nan ta tabbata”

Wannan karon a fili take maganar tana tura kofar katon falonta ta shiga. Sirleem na ganinta ya yanke wayar da yake da Mansura ya mike tsaye, dan ya san zai sha fada amman sai ya ga damuwa a fuskarta bata ko kula shi ba ta nufi dakinta, sai da ta shige sannan ya ciro wayar ya sake kiran line ta.

“Miyasa baki jin magana? Kin san yadda ake saka mana ido amman zaki biyo ni a nan?”

“Amman Sirleem kasan ba zan iya jure rashinka ba na tsawon kwanaki, ban san ranar dawowarka ba ba zan iya zama a can ba”

“Fine gani nan zuwa”

Ya sauke wayar tare da ajiyar zuciya, sannan ya nufi dakin mahaifiyarsa domin sanin dalilin damuwarta.


*Littafin nan na kudi ne biya ki karanta cikin aminci. Pay 300 to 0314795884 Abubakar Hadiza Gt bank, then send the evidence to 08036126660*
24

*Littafin nan na kudi ne biya ki karanta cikin aminci. Pay 300 to 0314795884 Abubakar Hadiza Gt bank, then send the evidence to 08036126660*

Cikin natsuwa Sirleem ya shiga dakin mahaifiyarsa, tana ganinsa tai saurin aje wayar hannunta.

“Ya akai?”

Kai tsaye ta tambaye shi abun da bata saba ba. Mamaki ne ya bayyana a fuskarsa.

“Na ga kamar kina ciki damuwa ne”

“Aa ba komai ka je inda zaka je waya na ke son yi”

“Amman kin tabbatar da babu wata matsala?”

“Na fada maka ba komai mana Sirleem ka tafi inda zaka je”

Ta amsa masa da dan fada domin ta matsu ya fita daga dakin. Juyawa yai cike da mamakin yadda Hajiya take masa ya fice. Mikewa tai tsaye ta isa gurin kofar ta saka mata key sannan ta dawo ta kira number Jarma, yana dagawa ta labarta masa komai shi kanshi ya cika da tsananin mamaki.

“Kin gani ba ni san mutanen nan basa taba mana karya”

“Ada can ina ganin abun kamar wasa, amman ganin wannan yarinyar ya bani tsoro kuma ya saka na yarda, yanzu miye mafita?”

“Mafita kawai a koreta daga gidan mana, babba ce?”

“Karama ce ba zata wuce warin Nana ba, ni abun ya bani mamaki ma, taya zata iya lalata mana aiki? Ko dai tana da aljanu ne?”

“Ko ma dai minene abun da nake ganin yafi kawai a koreta daga gidan, matukar tana cikin gidan nan zata bata maka lamari da tsari”

“To amman ya za ayi na koreta tun da bangarena take ba?”

“Haba Hajiya kamar ba mace ba, ki yi tunani mana, ni anjima zan shiga na gaishe da Hajiya dan na ga yarinya”

“Okay shikenan ai dole mu san abun yi kam”

Ta sauke wayar tare da sauke ajiyar zuciya tana tuna sauran abubuwan.

“Fadime Falmata Sardauna, wacece Fadime kuma? Waye Sardauna?”

Ya mike tsaye tana ta tunani.

“Sun ce akwai tafiyar da ba dawowa? Wace tafiya ce kenan? Wa zai yi? Mu ko kuma bangaren Ammy?”

Safa da marwa ta fara yi a dakin.

“Ina kyautata zaton yarinyar tana da aljanu ne wata kila zata fada ne, in ba shi ni ban ga ta inda zata iya lalata mana shiri ba? Kamata yai nai mata sanadi da gidan nan cikin ruwa sanyi ko kuma ayi mata asiri ta bar gidan gaba daya”

Sai kuma ta girgiza kai.

“No ai idan mu ka mata asirin idan tana da aljanu zata iya fadar gaskiya ta tona mana asiri”

Wayarta ta nufa ta kira Hajiya Talatu ta labarta mata abunda yake faruwa.

“Wannan maganar ba ta waya bace ranki ya dade zan shigo gobe da kaina”

Daga haka ta aje wayar, gaba daya ta rasa yadda zatai ta natsu, haka ta wuni cikin tunani kala kala ta kulla wannan ta kwance wacan ta saka wannan ta ga be yi ba, babu abun da yafi tsaya mata a rai kamar yadda Falmata zata lalata musu shiri as how kuma ta yaya? Lokaci bayan lokaci sai ta ambaci sunan Falmata Fadime Sardauna tana jinjina lamarin.


SHATTIMA POV.

A kofar gate din Hajiya a mutu ya faka motarsa duk kuwa da kasancewar Zainab ba son zuwa gidan domin yan uwan Hajiya Babba ne ita kuma ba wani shiri take da Hajiya Babba balle kuma yan'uwanta.

“Ina jin gobe zan je Yola, zan turo miki number police din da za su raka ki a can idan kin shirya kawai ki kira su zasu same ki har inda kike”

Zainab ta kalleshi.

“Amman Lafiya zaka je gobe? Ko ka sake samun hutu ne?”

“Baba Waziri ne yace yana son ganina, ya kira ni da safe yace idan zai yiyu mu hadu da a yau, nace masa sai dai gobe”

“Okay Allah ya tsare, ni ba zan dade ba, domin bana jindadi sosai kuma ina son na gama cikin kwana biyu koma”

Hannunsa ya mika ya dauko diary sa yai rubutu a kai ya cire paper ya mika mata.

“Ki ba wani ya karbo miki wannan maganin”

“Thank you”

Ta fada bayan ta karba, sannan ta bude motar ta bita, sai ya jira ta dauki akwatinta dake boot sannan yaja motarsa ya dauki hanyar asibitin, gaba daya wunin ranar daya tuna abun da Fadime ta saka Ra'ees sai yai murmushi, sai yana daf da tashi aikin sannan ya kira Ra'ees a waya bugu daya abokinsa ya amsa.

“Hello”

“Matsoraci”

“Uhmm Allah yasa kaji abun da naji, ba zaka gane ba ne Wallahi”

Shattima yai murmushi kasaita wanda ya karawa fuskarsa kyau da kwarji sannan ya sake magana a hankali.

“Gobe dai zaka yi duty na, zan leka Yola”

“Lafiya dai?”

“I don't know, Baba Waziri ke nema kuma tun har ya bukaci ganina kasan abu ne mai muhimmanci”

“Allah yasa alheri ne ya tsare”

“Amin”

Ya aje wayar har sai da Ra'ees ya kashe da kansa sannan ya mike tsaye ta hada komai nasa ya zuba a karamar jakarsa ta riko system dinsa ya fito daga office din.
Kai tsaye gida ya dawo daman can indai baya gida to yana gurin aiki dan kuma baya aiki to yana gida sai kuma idan wata fitar mai muhimman ta kama, domin shi ba mutum ne mai son yawo ba.
After sallah la'asar ya fito falon ya zauna yana kallon tv, be yi minti talatin ba ya soma jin laurarsa na son tashi, daman can indai zai zauna shi kadai a gurin yana tunani to zai haifar da kansa da matsala ne, cikin rashin kuzari ya mike tsaye ya shiga kitchen ya dauko cup ya ciro lemun tsaki a fridge ya yanka ya matsa a cup din ya jika Lipton ya hada ya shanye sannan ya fito ya hau sama zuwa bedroom dinsa. Wanka ya fara yi sannan ya kwanta saman katon bed din nan da nan bachi yai gaba da shi.
Be farka ba sai da aka fara kiran sallah magari, sannan ya unkura ya shiga bandaki a nan ma sai da ya sake watsa ruwa dan jin yai jikinsa ya masa nauyi sannan ya fito ya nufi masallacin unguwarsu. Ba dawo gidan ba sai after isha'i, daman can idan yai sallah magariba baya dawowa gida a masallacin zai tsaya yai ta azkar da tasbihinsa har a kira sallah isha'i.
Da wuri ya bi lafiyar gado saboda ya samu tashi da wuri domin jirgin da zai bi zai tashi ne by 7am.


(Ku ji tsoron Allah da ya hallacinku ku daina karantawa idan ba ku biya ba, ku guji hakkin wani dan Allah baya yafe hakkin wani akan wani, daka ci hakkin wani kara a ci naka, ko ba komai kasan kai ka bi shi bashi ba wai shi ya bi ka ba, kuma zai biyaka a inda ba a abiya da nera sai lada ko zunubi. Indai har za ki karanta ki karu ko kuma ki samu nishadi to miye na hassadar ko kyashin biya? Masu sharing ku cigaba da yi kowa yai na gari dan kansa, wata rana sai labari duk abun da ka aikata shi zaka gani, kuna ganin abun kamar ba komai ba ko? To Allah ya baku sa'a ya muku yadda kuke mana🙌😊)


FALMATA POV.

Bata koma ba sai kusan tara har da yan mintuna, taji tsoro sosai domin bata saba tafiyar dare ba da nisa haka sai a yan kwanakin nan da fara kaiwa dare, bata baro gidan sai yaran sun yi bachi ta kwantar da su sannan zata kamo hanyar gida.
Ta iso a gajiya sosai sai dai tararda Sani da tai a kofar gidan yana jiranta sai ya saka ta manta da gajiyar. Sai da ta fara shiga gida ta sanar da Tumba isowar ta.

“To kije waje wani na nan yana jiranki, sauran idan ya baki kudi ki boye ki shigo min hannu sake”

Falmata bata ce komai ba ta juya ta fice daga gidan, saman dakalin dake kofar gidan ta suka zauna duk maganar da zai yi sai dai ya kai bakinsa kunnenta ya fada mata, kamin ya kumna matar wata tsohuwar wakar M2, tana kallon video wani shauki na dibanta, har ta dago kai ta fada masa cewar ta hadu da M2 ba sau daya ba sai kuma wata zuciyar ta hana ta waya ni ko shi ma ya karyatata kamar yadda sauran kawayenta su kai. Sai goma har da yan mintuna yai mata sallama ya tafi be bata ko sisi ba. Da fargaba da shiga gida domin ta san ko ta fadawa Tumba ba a bata komai ba ba yarda za tai ba. Sai da tai ta mata rantsuwa kamar za tai kuka sannan ta kyaleta sai masifa take.

“Idan ya san baya bada komai ya daina zuwa, ki sallame shi kawai”

“To”

Falmata ta amsa sannan ta shige dakinsu jikinta na rawa. Washe gari ma kamar kullum sai da ta gama gyara gidan sannan ta shiga dakinsu ta dauki karamin qur'anenta na hadda ta saka hijabinta ta fito tai ma Tumba sallama ta kama hanya tana ta kallon Naja dake shirin makarantar boko. A zatonta yau ma zata hadu da Iya kamar kullum amman sai gata wayau babu Iya a waje har ta isa cikin gidan ta hau sama ta kwankwasa kofar babu bata lokaci aka bude mata. Sai da ta gaishe da duka hadin da suke falon sannan ta wuce dakin yan uku ta fara aikin.
Misalin tara da rabi ta gama komai sannan ta dauko yaran ta fito da su domin ayi musu wanka.

“Ba a fitowa da su Falmata ki koma dasu dakin, sai kije ki kira Iya tai musu wanka tun ni ban gama aikin ba, na san Shattima be son jira Ammy tace a gama masa komai kamin ya iso zuwan safe zai yi”

Falmata ta jin Jekadiya ne kawai ba dan ta fahimci waye Shattiman ba balle, juyawa tai ta koma cikin dakin ta aje yaran sannan fito.

“Ina ne dakin Iya yake?”

Jekadiya ta umarce wata hadima da kai Falmata a bangaren Iya wanda bangare daya suke da Jekadiya da wasu manyan hadima gidan. Hadimar na gaba Falmata na binta a baya sai karanto addu'a take, sai da suka sauka kasa, suka fita daga bangaren Ammy gaba daya sannan suka isa wani madaidaicin part.
Bakin kofar Iya hadimar ta tsaya ta kwankwasa mata kofar sannan ta wuce ta bar Falmata a tsaye.


**
Iya na zaune dakinta, tana mamakin karfin hali irin na yarta Zainab, ta san yadda Zainab take son jikinta sosai shiyasa ta sakar mata ciwo domin kawai ta fasa tafiyar amman sai da taje, har gashi yau kwana daya kenan. A yanzu bata da wani zabi daya wuce sake kurwar yarta ta huta. Tashi tai ta bude kasan carpet din ta kwance kurwar ta sake ta, nan da nan tsokar da zama kamar wani karamin tsuntsu tai sama ta bace. Kurwar Auwal ta dauko ta matsa matsi bana wasa ba, bayan ta masa ta sake saka kumbarta ta soka daga kasa, jin an buga kofar yasa tai saurin maidawa ta aje ta ta nufo kofar ta bude. A can har cikin tsakiyar idon Falmata tana kallon amman a yanzu bata kaunar ma ta hada ido da ita, sai wani tsam tsam take ji yana tashi a cikin kanta.

“Ya akai?”

“Ance ki zo ki yi ma yara wanka”

Falmata ta fada tana kallonta a yayinda ita kuma Iya ta kasa hada ido da Falmata, da sauri ta daga mata hannu.

“Gani nan zuwa tafi”

Ta maida kofar dakin ta rufe tana sauke ajiyar zuciya.

“Lallai wannan yarinyar ta gawurta, ashe akwai kurwar da zata gagareni kallo? Uhmmm dole na yi wani abun kar ta zame min kaya”

Ta fada sannan ta karasa bakin gadon ta zauna da mugun mamaki.



SHATTIMA POV.

Be shigo gidan ba sai kusan azahar duk kuwa da kasancewar ya sauka da wuri, sai dai ba a gidan ya sauka ba a gidansa ya sauka sai da ya huta sannan Baba Adamu ya tokoshi a mota ya shigo da shi masarautar. Ta bangaren Mai Martaba Baba Adamu ya faka motar sannan ya fito ya budewa Shattima, kamar wanda baya son motsa jiki haka ya fito cikin motar yana wani irin takum kasaita da jin isar sarautar. Sai da ya shiga ya bangaren Mai Martaba suka gaisa sannan ya fito ya nufo bangaren Ammy cikin farinciki domin ya samu Mai Martaba a falonsa tsabanin da da kullum a dakinsa yake zama. Babu kowa a falon na Ammy sai ac da kuma Tv da turaren wuta da aka kunna yake da kamshi kamar dakin sabuwar amarya. Dakin yaransa ya fara nufa a hankali ya tura kofar dakin, sai ya tsaya daga bakin yana kallon Falmata wacce ta saka yaran da suke ta wasa a gaba tana rike da qur'ane tana karanta musu Suratul Bakara duk aya sai ta tsaya ta tofa musu, sannan ta cigaba.
Wani irin farinciki ne da natsuwa suka kirkiri kansu a cikin kirjinsa, Falmata ta shiga zuciyarsa ta kwanta yaji ta burgeshi matuka. Kamshin turarensa ne ya sanar da ita cewar akwai wani a dakin hakan yasa tana kai aya ta juya ta kalli kofar suna hada ido gabanta yai mugun faduwa sai ta sauke idonta da sauri tana cigaba da jin faduwar gaban. Karaso yai cikin dakin ya duka gaban yaransa ya shafa kansu ya sumbancesu sannan ya kalleta sai ta dago masa hannu tana gaisuwa.

“Barka da rana”

Samun kansa yai da sakar mata da murmushin da kasafai yake yi ma kowa shi ba, domin har ga Allah ta burge shi, ko ba komai ta kula masa da yaransa ya dade yana neman irinta be samu ba.
Be amsa ta ba ya mike tsaye ya nufi kofa zuciyarsa cike da annashuwa. Yana fita daga dakin ya shiga dakin mahaifiyarsa sai ya same ta tana yi ma Nana fada.

“Na fada miki ba zaje ki je ba”

“To ai ban ce binki zan yi ba, kanwar amaryar kawata ce class din mu daya ita ce ta gayyace ni”

“Ni ma ba zuwa zanyi ba, Hajiya Babba ce zata je a madadina, kuma kin san dai ba zaki fara binta ki shiga cikin manyan ba ko?”

“Tawa tafiyar dabam zan yi”

“Allah ya tsare hanya”

Ammy ta fada tana dauke kai daga barin kallon Nana ta maida gurin Shattima.

“Barka da rana Ammy”

Jin muryarsa yasa Nana juyawa da sauri ta nufeshi ta rumgume.

“Oyoyo Ya Shattima baka fada min zaka zo ba?”

Murmushi ya sakar mata yana mata side hug.

“Ni ma zuwan kai tsaye ya zo min, yaushe kika dawo”

Nana ta yi yar dariya.

“Bari naje na duba assignment dina gobe zamu yi submitting”

Ta fice da sauri, Ammy ta girgiza kai.

“Allah ya kyauta wannan yarinyar, Wallahi naje kamar na bada sadakarta na huta”

Shattima ya zauna yana murmushi.

“Kurciya ce Ammy zata daina”

“Allah yasa, ya hanya?”

“Al-hamdulillah”

“Ma-sha-Allah ga abinci can na jiranka, ka ci kamin Waziri ya iso”

“Ammy kin san miyasa Baba Waziri yake nemana?”

“dan ya shigo zaka ji”

Ammy na fadar hakan ta mike tsaye ta nufi wata karamar kofar dake dakinta.




FADIME POV.

Tada tashar Fadime ta dauki hanyar gidansu, daman tafiyar babu wata doguwar tazara daga inda ake sauke mutum zuwa unguwarsu. Kazarta dai tun a cikin mota ta fara cin abunta yoghurt din ce dai bata sha ba, sai da ta doso gidansu sannan ta fara tunanin Amo, idan tana cikin gidan ko ya zatai? Ko kuma dai tana can birni oho. Lekawa ta fara yi cikin gidan sai dai bata iya hango ko'ina na gidan sai bangaren shanu da kofar dakin Inna.
Ba kowa take ji ba kamar Bappa tun da ba da saninsa aka je da ita ba. Kamar wacce zatai sata haka ta fara takawa ta shiga cikin gidan. Sai hango Amo tai kwance bakin bukkarta Hajjo na danna mata tuwon kasa a baya. Da mugun sauri Fadime ta dauke kai ta rika kallon sama dan kar idonta ya shiga cikin na Amo. Amo dake kwance tana ganin Fadime ta mike zaune tana mata wani irin kallo na bakinciki da kuma mamakin da ya kasa barinta har yanzu. Ga kuma fadan da suka yi da Inna yau duk akan ta baro Fadime a

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login