Showing 114001 words to 117000 words out of 286946 words

Chapter 39 - Fulani Book 1 Hausa Novel Complete

20 Dec 2024

943

rike da kaya a hannu dayan hannunsa kuma janye da wani gawurtaccen farin doki. Daga Fadime har Zainab mikewa sukai tsaye suna kallonsa har ya iso.

“Doki zamu hau?”

Fadime ta tambaya tun kam yace mata komai, sai ya daga mata kai alamar eh.

“Ni gaskiya ba zan hau doki ba, zai je ya jefar da mu ni ban taba hawa doki ba”

Ta fada a shagwabe tana kallon dokin da fuskar tsoro.

“Ni na saba hawan doki ba zan bari ya jefar da mu ba, a idan mu akwai dawakai”

Zainab ta fada tana murmushi daman can tana sha'awar hawan doki. Fadime ta kalleta tana aika mata tambayar da ta san ba lallai ne ta amsa mata ita ba.

“A can Yola kuna siyar da dowakai ne?”

“Aa suna gidan Sarauta ne”

Zainab ta kalli Wasim da sauri jin amsar da ya bawa Fadime. Fadime ta wara manyan idanuwanta tana yi ma Zainab wani irin kallon burgewa jin an dangantata da sarauta.

“Taya kake sanin komai a kaina?”

A maimakon ya bata amsa sai ya sakar mata murmushinsa mai kyau ya mika mata wata bakar rigar saki tare da gashin kaza.

“Je ki saka, wannan kuma ki laka shi a kanki”

Ta karba tana masa kallon mamaki, sai a yanzu ta kara tabbatar da cewar tsafin da ake fadar suna da shi ya wuce misali, daga ganinta har ya san komai a akanta! Juyawa tai baya ta fara tafiya zuwa bayan dutsen, sai da ta wuce sannan ya mikawa Fadime nata.

“Ki saka wannan”

Ta karba tana dubawa.

“Miyasa kuke saka wannan kayan da kuma gashin kaza?”

“Kayan saki muke sakawa ba ma saka irin tufafinku, saka gashin kaza kuma yana nufin marar aure, duk mace da kika gani da gashin kaza a kai to bata da aure ko da kuwa tsohuwa ce”

Ta kalleshi tana yar dariya.

“To su mazan da basa saka riga su ma ba su da aure?”

Dariya yai mai sauti ya juya mata baya.

“Canja kayanki”

“Ba zaka juyo ba?”

“Eh”

Ta shiga cire rigarta sannan ta kwance zanen tana yi tana kallonsa.

“Kar fa ka juyo”

Be ce komai ba sai murmushi yake duk kuwa da kasancewar bata ganinsa. Sai da ta cire tufafin jikinta ya rage daga ita sai dan karamin saket din ciki sannan ta shiga kokarin saka rigar, wanda hakan yai daidai da fitowa Zainab a inda ta boya tana saka tufafin, tun da ta doso inda suke yake ta kallonta har ta iso, ba karamin kyau rigar sakin tai mata ba, daman bakin abu ko a bakar fata yana kyau balle ita da take fara sol, sai ta fito sak kamar yar garin, ga gashin kanta daya sha gyara ya kwanta bayanta gwanin sha'awa. Rigar ta tsaya iya guiwarta ne kasancewarta doguwar mace, ba kamar Fulani ba da bata kaita tsayi ba abun ka da wanda be gama girma ba, ga kirjinta babu komai, sai dan abun da ba a rasa ba, Fulani irin yan matan nan da basa da cikar gaba sai dai hakan be rage ta da komai ba. Tsabanin Zainab da kirjinta yake cike gwanin sha'awa.

“Na gama”

Fadime ta fada tana kokarin laka gashin kazar a kanta, juyowa yai ya kalleta sai ya ga ta masa kyau fiye da ko yaushe, daman kullum cikin kayan fulani yake ganinta, yau kuma gata sanye da kayan saki da suka karbeta suka mata kyau suka kara fito da hasken fatarta.

“Kin yi kyau kyakkyawa”

Ya furta tare da kai hannu ya karbi gashin kazar ya laka a mata a kai, sai ta kara kyau sam ba zaka ganta ka ce ba yar garin ba ce domin babu abun da ya banbanta da su. Juyawa yai ya matsa kusa da Zainab ya karbi gashin kazar yana kokarin saka mata a kai. Kusantota da yai sai ta ji wani irin faduwar gaba wanda yake neman danne mata numfashi, har sai da ta lumshe ido, abun da bata taba ji ba saboda namiji ya kusance ta ko Auwal da take so bata jin faduwar gaba idan ya matsa kusa da ita. Bayan ya saka mata ya matsa baya gurin Fadime.

“Zaki iya hawan dokin?”

“Ina tsoro”

Ta amsa masa a shagwabe tana masa wani kallo da manyan idonta kamar zata fito da su waje, hakan da tai sai ya ji ta kara burgeshi.

“Zan hau na rike linzamin ke kuma sai ki hau bayana ki rike ni”

Zainab ta fada tana kokarin saka camera a jikinta, wayarta kuma tana cikin karamin aljihun wandonta.

“Kin yarda”

Ta tambaye Fadime, shiru tai kamar mai tunani sai kuma ta daga masa kai alamar eh ta yarda. Wuyan hannunta ya rika, ya nufi gurin dokin da ita, Zainab na ganin haka ta dauki jakarta ya bi bayansu, sai ya gyara sirdin sannan ya mikawa Zainab hannunsa. Kallon hannun tai ta sai kuma ta kalleshi sannan ta mika masa nata hannun ya rikata ta hau, a maimakon yai ma Fadime yadda yai ma Zainab sai ya cira Fadime da duka karfinsa ya dorata saman doken.

“Wayyo wayoo shiiiiii”

Ta fada jin ta a saman doki abun da bata taba ba kuma bata taba saka rai ba. Duka hannayenta ta saka ta rike Zainab gam kamar wacce aka cewa idan kika sake ta zaki mutu.

“Asssha esssh essssss ashhhhhhh”

Shine abun da take ta fadi ta rufe ido gam. Shi kam kallonta kawai yake cike da burgewa.

“Kai ina zaka hau”

Ta tambaya ba tare da ta bude idon ba.

“A kafa zan je”

Ta bude ido da sauri.

“To ai shi dokin be san hanya ba”

“To ni kai zan bi”

Ta fara kokarin saukowa.

“Ba zaki iya tafiya a kafa ba, ki zauna nan”

“Zaki iya ganin abun tsoro, ba irin tafiyar da kike tunani zan yi ba”

“Tau”

Ta fada cikin muryar kuka, sannan ta gyara zamanta saman dokin.

“Zan iya tafiya da jakata?”

Zainab ta tambaya tana nuna masa jakar dake kasa, amaimakon ya amsa mata sai kawai ya dauko jakar ya mika mata.

“Takak takak”

Ya fada yana kallon dokin, kamar jira yake sai ya fisgesu da mugun gudu kamar za su fadi. Wani irin ihu Fadime ta saka tana ta kyakya da muryarta mai shiga kunne ta rufe ido gam ta kankame Zainab. Da kallo ya bisu yana murmushi.

“Fateme”

Ya furta sannan ya kalli hannunsa ya sauke ajiyar zuciya. Tun da dokin ya fisgesu be tsaya sai gudu yake kamar zai jefar da su, ba su isa bakin kofar garin ba sai da aka kira sallah magariba. Wani abun daya bawa Zainab mamaki ganin Wasim bakin kofar garin yana jiransu bayan sun baro shi a can baya. Daidai shi dokin ya tsaya sai ya rika shi ya shafa kansa, sannan ya nufo inda Fadime take yana rikata ta fasa ihu domin har lokacin idonta a rufe yake.

“Shiiiiiiiiiii ni ne”

Jin muryarsa yasa ta bude idon, wuyansa ta rike har ya saukar da ita, sannan ya mikawa Zainab hannu a karo na biyu ta rika ta sauko tana karewa kofar garin kallo. Katuwar kofa ce da akai ta ta manyan itace an yi ma kofar kwaliya da wani abu mai kyali kamar zinari.

“Wow”

Ta furta tana kara kallon yadda mutane suke ta hadahadansu babu wanda ya kula da wani. Be ce musu komai yai gaba ita da Fadime suka bi bayansa, yawancin mazan garin dukansu suna daure da walki sai dai kalar na kowa daban, masu riga a cikinsu kalilan ne, matan dake wucewa kuma wasu suna sanye da gashin kaza a kai wasu babu. A zatonta karami gari ne da ba zai kai garinsu Fadime ba ma, sai ya zo akasin tunaninta ashe wata duniyar ce ta dabam mai zaman kanta, wani gurin kasuwa wani abun gidanjen kasa wasu gidanjen zana. Wani mai mangalar dawakai ne ya faka a gabansu, sai Wasim ya umarce su da su hau, ba musu suka hau har shi, dawakin sukai gaba da su, wata unguwar da dabam suka dosa Zainab dai sai rabon ido take. Daidai bakin wata rumfa mai kamar ta shago ya sauke su, Wasim ne ya fara shiga cikin rumfar sannan Fadime dake ta makalewa jikinsa kamar zata shige masa, yadda taga kowa ba riga yasa ta kara tsorata jikinta sai rawa yake.
A inda suke suna nesa da mutane sosai kuma ba kowa zai lura da su ba, kasancewar duhu ya fara dauka.

“Zaki iya daukar hotonki daga nan”

Wasim ya fada masa yana kokarin janye tafin hannunsa da Fadime ke son kamawa ta rike, domin jin take kamar wani ne zai zo ya sace ta.
Zainab ta fiddo camera ta fara daukar hoton, garin be kara burgeta ba sai da hudu ya soma sosai, a lokacin ne mutanen garin suka soma kunna wutar ice, wasu kuma aci balbal, sai ko'ina ya haskaka gwanin sha'awa, masu gida suka kunna wutar icen daga waje, ya haska kofar gidansu ga kuma hasken farin wata daya haska ko'ina, a kusa da su ma wani ya kunna, cikin natsuwa Zainab ta shiga daukar hoton, abun da yake nesa zooming take ta dauke shi hoto.

“Sauke camera ki”

Ya fada da sauri hango Liya ta doso inda suke, cikin sauri Zainab ta boye Camera, Fadime kuma ta kara matsawa kusa da shi. Daga Zainab har shi har Fadime kallon Liya suke har ta iso, tsayawa tai kallonsu, ba zata iya cewa ba yan garin ba ne kasancewar suna sanye da irin tufafinta, sai dai abun da bata taba ganin ba Wasim da mata, ita kanta da take yar'uwansa ba yawo yake so yi da ita ba. Ta san kuma be da budurwa a duk fadin garin, hakan yasa mutane garin suke masa kallon yana sonta cikin hai da mahaifinsa. Daya bayan daya take kallonsu kamin ta kurawa Fadime ido, bata taba ganin Zainab ba, amman tabbas ta taba ganin Fadime, ba zata iya shaidar inda ta santa ba, but tabbas ta taba ganinta, Fadime ma na ganinta ta gane ta.

“Ya akai....?”

Wasim ya tambaya da yarensu yana mata wani kallo wanda ya dauke annurin fuskarsa gaba daya. Kallonsa tai da sauri kamin ta ce komai Fadime ta ce.

“Wannan matar muguwa ce na taba ganinta, lokacin daya wuce ita kuma ta zo na ce ta dora ni da tuluna, sai na cire mata gashin kaza a kai shine ta fasa min baki”

Ta karasa tana kallon Wasim irin na yaro ya kai kara a gurin babba, domin ta fada ne da zimmar Wasim yai mata hukunci sai ta ga ya lumshe ido, kamar be jidadin maganarta ba, ita kuma Liya sai tai dariya marar sauti tai baya-baya tana kallonta.

“Liya...”

Wasim ya kirata, sai ta daga masa hannu alamar babu ruwanta tana ta tafiya da baya-baya sai murmushi take wanda ya bayyana duka hakoranta. Wasim ya kalli Fadime.

“Miyasa kika yi magana?”

“Ai baka ce kar nai magana ba”

Ta bashi amsa kai tsaye, Zainab ta mike tsaye daga dukena da take.

“Akwai matsala ne?”

Shiru yai ya sauke ajiyar zuciya.

“Ki saka camera da komai naki a jakar nan ki bar nan”

Kamar mai jiran Umarni tai saurin yin abun da ya fada.

“Gida zaka maida mu?”

“Ba zai yiyu na fita da ku a yanzu ba, saboda ta yi magana Liya ta gane ta, Fateme zata iya samun matsala...”

Yana fadar hakan cikin Fadime ya murda sai fitsari.

“Wayyo Inna, na shiga uku yau Bappa na can na nemana, yau kashina ya bushe...”

Ta fashe da kuka, sai yai mata alama da tai shiru.

“Shiiiiiiiii daina kuka kuma komai aka baki karki ci”

“Tau, amman dai na shiga uku, daman Inna tace kar na zo, ni ban ji magana ba”

Ta kara fashewa da kuka.

“Daina kuka”

“Dole ne nai kuka, ni kadai zan shiga ukuna, ita wannan matar data janyo ni ba zata shiga uku ba sai ni mai shegen surutu, dole nai kuka... Amman na yi shiru”

Ta amsa da karfi tana kokarin datse kukan, ta rufe bakinta jikinta har bari yake cikinta na ta kuka kamar wacce zawo ya cikawa ciki.
Zainab kam jin tai kamar kafafuwanta ba za su dauke ta ba hango wasu maza kusan su hudu su doso inda suke, rike da wutar ice a hannu.


FALMATA POV.

sai da ta kalli Sirleem ta sauke kanta kasa sannan ta soma magana.

“Sunana Fateema, ana kira da da Falmata ne saboda na ci sunan Kakata ta wajen uwa ne, amman Mama na Fulani take kirana, daga Mamana har Baba duka fulani ne, amman Mamana baka ce sosai sam ba zaka ganta kace ita Fulani ce ba”

“Ita kika biyo kenan”

Sai tai murmushi kamar yadda shi ma yake murmushin.

“Haka mutane suke cewa, domin mahaifina fari ne kamar kai”

Ta fada tana kallonsa sai ya nuna kansa.

“Ni fari ne?”

Ta sauke kanta kasa cike da kunyar kallon da yake mata. Duk abun da suke Shattima na tsaye jikin window yana kallonsu kuma yana jinsu.

“Go on cigaba, aikin mai babanki yake su waye kanenki?”

“Mahaifina dan kasuwa ne, yana siyar da kayan masarufi irin gero masara da shinkafa, a kasuwa idan ya fita baya dawowa sai dare”

“that's how step mother dinki ta samu damar azabtar da ke ko?”

Ta kalleshi sai kuma ta sauke kai.

“Da can yana so na sosai, komai zai ce Fulani na, a da mu uku ne, Mamana tana da yaya biyu mace da namiji da ta haifa da wani namiji kamin ta auri Babana, domin baba shi saurayi na a lokacin da ya aureta ita kuma ta taba aure, a lokacin ta fada min a kauye suke zaune shi kuma yana zuwa birnin yola yana sana'a yana komawa, ganin yan'uwansa sun dora mata tsana saboda ya aureta tana bazara da yaya biyu sai ya dauke ta ya kama gida nan ya dawo da ita, har da yaran da wacan mijin ya bar mata sai ta dawo tare da su, saboda mahaifinsu ya tafi abuja neman kudi kuma tun da ya tafi baya aike kuma baya zuwa dubasu, a lokacin data dawo nan ta haife ni, sai baba ya saka namijin makaranta ganin shi ne babba, ni ma a lokacin da ina karama ya taba fada min zai saka ni a makaranta, a lokacin dukanmu baban mu yana son mu har wadancan da b yayansa ba, Mama na bata da kawa kamar Umma (Tumba) domin a da gidan da Umma take aure yana kusa da na mu ne, komai a tare suke yi da mama ni ma Umma tana so na sosai a da kowa yana yabon halinta saboda tana da kirki da kima a gurin mutane, baba yana taimako mijinta sosai kamin ya rasu, a lokacin ne ma babana da mama da kowa suka rika mata abun arziki, abinci tufafi da komai ma, bayan ta gama takaba zata koma garinsu sai Mama da Baba suka hana, baba ya dauki nauyin ciyar da ita ganin irin kusancin dake tsakaninta da mamana, har yan'uwansu sun san junansu, ashe ba mu sani ba baba ya shirya aurenta ne, duka ba mu sani ba sai da aka daura auren aka kawo ta dakin da muke kwana ni da yayan mamana, tun daga lokacin komai ya canja, Baba ya daina son mu ya ce baya son yaya mama sai an maida su gida, da kansa ya dauke su ya kai su kauye, sai namijin ya ki ya zauna aka dawo da shi, Mama ta cigaba da rika shi, rana daya muka neme shi muka rasa, ba mu san abun da ya faru da shi ba, ba a fada mana inda yake, kuma har yau mama bata sake maganar shi ba, ita mace ance ta rasu tun da dadewa, a lokacin ina karama sosai”

Ta yi shiru, sai Sirleem ya rika kafadarta ya zaunar da ita a daya daga cikin kujerun dake gefensu, har ta zauna kamar wanda ta tuna wani abu sai ta tashi da sauri.

“Aa manya suke zama a nan”

Ganin hakan yasa shi ma ya mike tsaye, domin ya san duk yadda zai ce ta zauna ba yarda za tai ba.

“Fada min babanki ya saka ki a makarantar?”

“Aa be sani ba, amman ya saka Naja yar da Umma ta haifa da abokinsa Malam Usman, Umma tana da wasu yaya manya a kauye da sukai aure mata uku namiji daya, bayan ni Mama ta haifi yaya biyu maza su ma baba baya son su, yana yi ma Mama na fada sosai ko da kuwa ita take da gaskiya, wani lokacin a gabanmu Mama take kuka, wani lokacin kuma sai ta boya, kullum Umma ce mai gaskiya a idonsa kuma yana yawan fadar wai Mama bata tausayinsa sai Umma, ni ma idan muka yi fada da Naja ni yake duka ko da kuwa ni nake da gaskiya, har kudin cefa ne da abinci sai ya koma hannun Umma, sai abun da taga dama za a girka, gidan Mama bata da lafiya ni zan girka, wata rana nai girkin be yi kyau sai Umma ta zuba min tuwon a kafa”

Ta daga zanenta ta nuna mishi kafar, kasancewarta baka ya bawa kunar damar fitowa kamar an mata tabo. Sirleem ya kalli kafar da mugun tausayinta ta gama bayyana a fuskarsa.

“Kwana biyu da faruwar haka akai amai da gudawa a unguwar, a gidan mu an yi kowa ya warke ban da Mamana, tun tana iya tashi har ta kasa, karfinta duk ya kare kullum ni nake hadimar Baba ya daina kula mu ni da ita, idan ta fadawa mutane abun da Umma take mata sai ace Kishi take, saboda kowa yana ganin kamar Umma ba za tai cuta ba, mutanen da suka yarda da ita kalilan ne, ita da kanta ta saka na kira mata Umma, ta rika hannun ta saka a cikin na Umma tana fadin, Tumba ga amanar Fulani nan n baki, ki rike ta amana ki ji tsoron Allah kanenta ma na baki amanarsu idan kin cutar da su ke da Allah, a lokacin ne Umma ta saka fada tana cewa ita ba zata karbi amanar kowa ba, Mama ta kama hannuna tana kuka, tace Fulani ki yi hakuri zan tafi na barki cikin kunci, ki yi hakuri Allah yana tare da ke, ki kula da kanenki kuma ki yi hakuri da rayuwa, n yafe miki na yafe muku ku duka Allah yai muku albarka, karki watsar da tarbiyar dana dora ki a kai, kuma ki yi hakuri da rashin uwa wata rana zaki zama uwa ke ma, Allah yai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login