Showing 201001 words to 204000 words out of 286946 words

Chapter 68 - Fulani Book 1 Hausa Novel Complete

20 Dec 2024

931

sauko mata. Murmushi yai ya juyo ya rumgumeta.

“Kin cancanci fiye da haka Teema na”

Sakinsa tai tunawa da abun da tai da kanta na rumgumarsa abun da bata taba ba, murmushi yai ya fice daga dakin.

***

Hajiya ta sauke wayar tana kallon kular tuwon dake gabanta.

“Me yace?

Jurry ta tambaya.

“Baya jindadi a waje zai kwana”

“Okay”

Ta dauki plate din abincin da ta gama ci tare da mikewa tsaye har zata fice sai kuma ta juyo tana fadin.

“Yauwa Hajiya, na manta wai Kausar tace min lokacin da taje kai su Hajiyar Zariya Gaisuwa a gurin Ammy ta ga wata yarinya makauniya tana fadar a boyeta kar Iya da Hajiya Babba su ganta, ina son na fada miki sai na manta”

Hajiya Babba ta juyo tana kallonta.

“Yaushe? Wacece?”

Wallahi ni ma ban sani ba, ranar da aka kai su Hajiya dai su yi mata gaisuwa.

“Ko wannan yarinyar ce Falmata?”

“Ni ma haka nai tunani, amman kuma Kausar ai ta san Falmata”

“Kira min Kausar din”

Hajiya ta fada tana tashi zaune da sauri. Jurry ta amsa da to sannan ta fice rike da plate din. Bata dade ba ta sake dawowa dakin tare da Kausar tana dake ta danna waya suka zauna a kasa.

“Kausar”

“Na'am Hajiya”

Ya amsa mata idonta na kam waya.

“Kalle ni nan ki aje waya”

Kausar ta aje wayar tana kallon Jurry kamin ta kalli Hajiya a tunanin wani laifi tai.

“Wa kika gani a dakin Ammy?”

“When?”

Ta tambaya domin ita ta manta da zancen ma. Sai Jurry ta dafa kafadarta.

“Ranar da kika je kai su Hajiyar Zariya ba kin ce kin ga wata yarinya ba har tana fadar a boye ta kar Hajiya ko Iya su ganta”

“Oh Eh me aka yi?”

“Kin san yarinyar ne? Ko Falmata ce?”

Hajiya ta tambaya.

“Aa ni ban taba ganinta ba, kuma ita fara ce sosai har ta fini haske Falmata kuma ai baka ce, kuma wannan bata gani har tana cewa wacece ni”

Hajiya ta yi shiru tana nazari.

“Duk yadda akai yarinyar ta san ni, idan ba haka ba, me zai saka ta ambaci sunana? Ko kuma Ammy ce ta fada mata wani mummunan abu a kaina?”

“Maybe, to amman kuma ai har da Iya ta ambata. Hajiya kin san yadda za ayi? Bari na tashi na je na kaiwa Nana lace sai na dubata daga can”

Cewar Jurry tana kallon Hajiya. Sai Hajiya ta daga mata kai.

“Okay”

Jurry ta mike da sauri ta nufi wardrobe Hajiya ta bude ta dauko wani tsadadden lace sannan ta maida Wardrobe ta rufe ta nufi kofa.
Kamin ta isa bangaren Ammy har da hadawa da sauri kamar wanda aka cewa jeki gata a can ki gani, door bell din daya kamata ta danna sau daya ko sau biyu ta danna sau ba adadi kuma ta hada ta knocking. Cikin rashin sa'a Nana ta bude mata kofar, sai tai tsaye kamar hoto tana kallon Nana, Nana na ganin hakan ta juya ta dawo cikin falon hannunta rike da apple daman can ba jituwa suke da Jurry ba, dama dama Kausar ko Karima amman Jurry bata shan inuwa daya da Nana. Shigowa tai cikin falon kamar yadda ta saba ba tare da sallama ba, ta nufo kusa da inda Nana take zaune ta zauna tana ta rabon ido, babu kowa a falon sai Nana sai wata yar cousin din Ammy dake zaune dinning tana cin abinci. Tunani ne ya zo mata Rahila ce bakuwar da Kausar take fada ko kuma ita ta zo tare da wata? Amman a iya tunaninta ai Kausar ta san Rahila, kuma ta ce wacan makauniya ce.

“Rahila yaushe kika zo?”

Cewar Jurry a kokarin ta na tantancewa, daga Nana har Rahila da aka kir juyowa suka yi suna kallonta, domin Nana ta san halinta ganin mutum tai masa magana ba nata ba ne, sai idan kawayenta na na kusa ko kuma wasu na bangaren Hajiya, Jurry tana da wani irin hali na ji da kai ko ta sanka zata iya yin banza da kai ko kuwa ka mata magana ne.

“Yau Anty Jurry ina wuni?”

“Lafiya Kalau ya gidan ke kadai kika zo?”

“Eh”

“Owk Ammy na ciki?”

Ta tambaya tana kallon Nana.

“No tana bangaren Mai Martaba”

Nana ta fada sannan ta mike tsaye ta nufi dinning din.

“Am Nana ga lace in ji Hajiya tace a baki”

“Ki aje nan na gode”

Ta fada a cikin yanayin da bata saba ba, ada idan Hajiya tai mata kyauta da sauri take zuwa ta karba tana murna d tsalle.

“Kuma tace a kira ki wai kin daina zuwa bangarenta”

“Ki ce ina gaisheta, makaranta bata barina zama yanzu shiyasa”

Da mugun mamaki Jurry take kallon Nana, sai da ta isa dinning din ta zuba ma kanta abinci ta fara ci, sannan Jurry ta aje lace din ta fice.
49

*Littafin nan na kudi ne biya ki karanta cikin aminci. Pay 300 to 2451879008 Hadiza Abubakar Zenith bank, then send the evidence via 08036126660*


Jirginsu na sauka direban Shattima na isowa, duk inda suka bi sai an kalli Shattima dake cikin shiga ta manyan kaya ga kuma Bappa da Kawu dan iroro dake biye da shi cikin shigarsu ta fulanin kauye, kana ganinsu ka ga fulanin ruga. Kawu dan iroro sai washe baki yake ganin a jirgi suka sauko abun da be taba tunanin zai faru, tun kam su karaso gurin motar Baba Adamu ya fito ya bude ma Shattima gidan baya a tunaninsa baya zai zauna kamar yadda ya saba. Sai ya ga sabanin haka ta hanyar nuna ma su Bappa mazaunin baya.

“Bismillah Bappa ku shiga mota”

Shi kuma ya bude front seat ya shiga ya zauna, Baba Adamu ya fisge motar kamar yadda ya san Shattima na son tuki. Bappa be tabbatar da Shattima babban mutum be ne kuma dan Babba mutum har sai da suka shiga masarauta, a nan suka rika kallon kallo shi da Kawu. Shattima da kansa ya sa a kira masa sarkin gida, sai ga shi ya zo da gudu ya zube gaban Shattima yana kwasar gaisuwa.

“Allah ya taimake ka, Allah ya kara maka lafiya”

“Sarkin gida ba bakina nan a basu masauki mai kyau”

“An gama dan sarkin da yafi wani sarki, an gama babbar giwa, Allah ya kara maka lafiya rai ya dade yai karko”

Uffan Shattima be sake ce musu ba, ya wuce abunsa bangaren Ammy, Bappa da Kawu kuma suka bi bayan sarkin gida kowa ne fuskarsa dauke da mamaki.
Kamar wani bako haka Shattima ya shigo cikin falon Ammy ya zauna yana dagawa Jekadiya hannu alamar amsa gaisuwarta da tai masa. Sai da ya fara kallon tv kamin ya kalli dakin yaransa, a idan ya shigo sai ya fara zuwa ya duba su wani lokacin ma sakawa yake a dauko masa su a gidansa dake wajen masarauta. Ba karamin sosuwa zuciyarsa tai ba tunawa da babu yaran a yanzu. Mikewa yai tsaye ya saka hannunsa daya a aljihu ya nufi dakin Nana, kamar yadda ya zata haka ya tarar Fadime na dakin zaune kasa hannunta a plate tana cin tuwon alkama da miyar ganye, kana ganin yadda ta bata fuska kasan bata son cin abincin.

“Waye a nan?”

Ta tambaya kamar an mata dole tana turo baki gaba. Samun kansa yai da murmushi sai farinciki da annashuwa suka baibaye masa zuciya. Sakin kofar yai ya fara takawa zuwa inda take.

“Shattima”

Ta fada tana washe hakora, sai ya tsaya cak yana kallonta a tunaninsa ta ji saitin tafiyarsa ne.

“Ga kamshin turarenka nan Wallahi kai ne”

Ta fada da dariya. Hakan yasa shi dariya shi ma ya karasa kusa da ita ya zauna a kasa kamar ita.

“Me kike ci?”

“Yeeee na gane kai ne, ina Bappa?”

“Na saka a kai shi masauki ya huta a bashi abinci tukuna sai na sadaku”

“Aa dan Allah ka kai ni yanzu, dan ina son na ga Bappana”

“Gani?”

“No ji ina son na taba shi na ji”

“Yanzu muka shigo ki bari na huta su ma su huta”

“Aa dan Allah”

Ta fada tana kokarin saka masa kuka. Sai ya kura mata ido, daman ya san za a rina, wai an saci zanen mahaukaciya. Kamin yace komai har ta mike tsaye tana mika masa hannunta.

“Wanke min hannuna”

Ya daga kansa yana kallonta da dan mamaki irin mamakin yadda take masa abubuwa, wata kila soboda idonta na rufe ne ko kuma saboda halinta ne oho.

“Wa yake wanke miki hannu idan kin ci abinci?”

“Ni nake wankewa”

“Then why yanzu kika ce na wanke miki?”

“Saboda ka zo mana, kasan ai ina jindadinka”

“Really?”

“Yes”

“To je ki wanke sai na saka a kaiki”

Ta fara takawa tana lalebe, ganin hakan yasa shi mikewa tsaye ya kama hannun nata suka nufi toilet din Nana. Da kansa ya kunna fanfo ya tara hannunsa ya saka nashi hannun yana murza mata a hankali.

“Wannan gidan na ku mai kyau ne sosai ko? Fanfo har a bandaki mu a kauyenmu ba mu da fanfo ma sai rijiya”

Be ce mata uffan ba, har ya gama wanke mata hannun, sai ta mika masa dayan.

“Wannan ma ya taba tuwon”

Ya rika hannun ya wanke mata yana mamakin kansa, ko kadan baya son yi mata musu, baya son tai requesting abu ya hanata, sannan baya son ya ga ranta ya bace.

“Sarautar nan gidan Babba ce ko? Ko karama?”

Be dai ce mata komai ba, surutun da take ne yasa Nana ta bude kofar bandakin ta leko sai ta hango Yayanta rike da hannun Fadime yana goge mata da tawul. Tsaye tai tana kallonsa da mugun mamaki shi ma kallonta yake kamin ya kamo hannun Fadime su fito daga bandakin.

“Yaya...”

Nana ta fada tana masa kallon mamaki. Sai ya kalleta.

“Nana me kika gani?”

“No ban ga komai ba”

Ta amsa masa tana zaro ido, sai ya juya sai kuma ta sake kiransa.

“Ya na ga kana wankewa Fateema hannun”

Juyowa yai yana kallonta fuska ba yabo ba fallasa.

“Zan iya sirri da ke?”

“Ba zan fadawa kowa ba, i mean ban ga komai ba”

“Good”

Ya juya ya nufi kofa sai ta bishi da kallon mamaki har ya fice hannun Fadime na cikin nasa. Sai da suka fito sannan ya saki hannunta.

“Bi yo ni”

Saurarawa tai ta fara bin inda take jin takunsa har suka iso cikin falon.

“Jekadiya ki kai yarinyar gurin mahaifinta, sarkin gida zai fada miki inda yake”

Yana fadar hakan ya mike zuwa dakin Ammy. Jekadiya ta mike tsaye da sauri bayan ta amsa ta kama hannun Fadime suka fice zuwa neman Sarkin gidan, sauko suka downstairs tana rike da hannun Fadime har suka fita gate din zuwa inda ta san Sarkin gidan yana zama. Jurry na tsaye jikin motarta tana waya idonta sanye da bakin gilashi ta hango Jekafiya da Fadime sun wuce, da sauri ta sauke wayar ta cire gilashin idonta ta kwalawa Jekafiyar kira.

“Jekadiya”

Jekadiya ta juyo da sauri tana amsawa, juyowar da tai sai ta juyo tare da Fadime da take rike da hannunta, tun kam su karaso inda Jurry take hankalinta yai mugun tashin, ganin Fadime. Tana ganin fuskarta ta gane ta kuma ta tuna inda ta taba ganinta duk da kasancewar wacan mai gani ce wannan kuma makauniya.

“Ina Ina zaki je?”

Ta tambaya numfashinta na rawa.

“Ranki ya dade aike zan isar”

Fadime na jin ance ranki ya dade sai ta saka duka hannayenta ta kama hannun Jekadiya ta rike.

“Okay wacece wannan?”

“To nima dai bana ce ba, domin ko sunanta ban rike ba”

“Ke ya sunanki?”

“Fateema”

Fadime ya fada, sai jurry ta gyada kai.

“Owk Fateema kawai”

“Eh”

“Okay ku tafi kawai”

“Godiya muke”

Jekafiya ta fada sannan ta ja hannun Fadime suka wuce, Jurry ta juya da sauri ta koma cikin gidan tana gudu kamar zata fadi, kamin ta isa dakin Hajiya har hakki take idonta ya cika da hawaye saboda tashin hankali, da karfi ta tura kofar dakin ta shiga wanda ya saka Hajiya yi mata wani kallo na mamaki ganin ta yi abun da bata saba ba.

“Juwairiyya?”

“Hajiya na shiga uku na lalace, asirina da naki ya tonu, Hajiya na ga yarinyar nan da Kausar take fada, Hajiya ashe ita ce a gurin bokan nan, yarinyar da muka gani gurin bokan nan tana tare da wani saurayi da ba shi da riga a lokacin da muka je, Hajiya ita ce Fadime da ake fada, yanzu na ganta tare da Jekadiya na tambaye ta tace sunanta Fateema, na shiga uku Hajiya na shiga uku...”

Ta fadi kasa tana buga hannayenta kamar wata mai aljannu.

“Shiyasa take cewa a boyeta karki ganta Hajiya ta fada musu komai, ni ban ma gane kan wannan abun ba wayyo Allah na, na shiga uku idan Mai Martaba ya ji wannan abun tsine min zai yi, kuma masarautar ta karya da ni, garin Yola zai gagareni zama wayyon Allah na, ko mijin aure sai ya min tsaye Hajiya”

Hajiya ta kankance ido tana kallon Jurry, sai kokarin taro maganar take tana fassarawa da halshen da zata iya ganewa, domin yaren ya mata nauyi.

“Ban gane manufar wannan bokon ba, shiyasa be fada mana wacece Fadimen ba? Yarsa ce ko kuma me? And taya ta zo gidan nan? Ko kuma bokan Hajiya ne muka je gurinsa ba mu sani ba?”

Jurry ta kara fashewa da kuka.

“Hajiya ba lokacin yin wannan tambayar ba ne, dan Allah ki tashi muje wani gurin tun abun be gama girma ba”

Hajiya ta mika hannu ta dauki wayarta ta kira Hajiya Talatu, Hajiya Talatu na yin picking Hajiya Babba tace.

“Kina ina Hajiya Talatu?”

“Ina gida, lafiya dai?”

“Ba lafiya ba, asirinmu ya tonu, ki aika yanzu yanzu nan a dauko matar nan, gani nan zuwa”

“Innalillahi miya faru?”

“Ba maganar waya ba ce, sai na zo”

Hajiya ta katse kiran sannan ta sauka kan doguwar kujerar da take ta nufi inda mayafanta suke ta dauka wanda yai kala da tufafinta ta yafa.

“Tashi share hawayenki, ki shiga mota zan yi magana da Mai Martaba yanzu sai mu tafi gidan Hajiya Talatu”

Jurry ta zabura ta shiga bandakin Hajiya da gudunta ta wanke fuska ta fito tana gogewa da mayafinta ta fito falo a firgice, kana ganinta kasan bata cikin natsuwa jikinta sai rawa yake irin na barawo da mai kaya, tana isa gurin motarta tai ta bude motar ta shiga tai ribas, kamin Hajiya ta nemi izinin Mai Martaba ta fito har Jurry ta fara jikewa da gumi duk da kasancewar ac motar a kunne yake.
Gidan baya Hajiya ta shiga fuska a daure tamau kamar wanda akai wa bushara da shiga wuta, Jurry kam ido sai cika yake da kwalla, gaba daya ta bi ta rude, domin ta san wannan abun har ita zai taba. Kamar ta sato mutum haka ta rika gudu da motar tana sharar kwalla.

“Ki shiga natsuwarki mana, zaki tonawa kanki asiri”

“Asirina ya gama tonuwa Hajiya, indai har ta fadawa kowa to ba abun da ya rage min, kowa zai rika kallona a matsayin yar da take son ta kashe mahaifinta, kuma ace ina budurwa yar sarauta har na san bin bokaye? Wallahi babu wanda zai aure ni Hajiya kuma Mai Martaba tsine min zai yi”

Ta fashe da kuka tana duka sitiyarin motar da karfi, bata taba shiga tashin hankali irin na yau ba, duk wani abu da take tunani a da sai ya tarar na yanzu ya ci uban bata shiri ya zama har da tsonon asiri da bata suna da kuma lalata mata rayuwa gaba daya. Ta yi horn ya kai sau biyar kamin mai gadin gidan Baba Waziri ya bude mata gate ta shiga, part din Hajiya Talatu ta faka motarta ta bude ta fita, ta bar Hajiya a ciki, iyakar kokarin da tai na boye fuskarta ne ta wuce dakin Hajiya Talatu ba tare da ta yi magana da yaran Hajiya Talatu da suke falon ba, cikin har da Haroon wanda dawowarsa kenan daga Abuja, kallo daya yai mata ya dauke kai ya maida gurin Hajiya Babba wanda ta shigo rike da waya tana dannawa.

“Hajiya barka da wuni”

“Ah Ah Haroon sukar yaushe?”

“Ban dade ba, ya gida ya Mai Martaba da jiki”

“Jiki Alhamdulillahi”

Ta nufi dakin Hajiya talatu cikin taku na alfarma da kokarin danne damuwarta. Da waya makale a kunne ta shiga tana fadawa Kausar ta rufe mata dakinta ta manta ta fito bata rufe dakin ba. Tun kamin ta zauna Hajiya Talatu ta saka salati tana dora hannu a kai saboda abun da Jurry ta fada mata

“Mun shiga ukun mu, Allah ni kaina idan Waziri ya ji wannan maganar aurena ya kare kenan, ba zai dubi yaya ko shekarun da akai a tare ba, akan Mai Martaba da Ammy baya jin asss bale kuma ya ji zance har da neman kisa? Gashi na je nemawa Mai jidda maganin hana auren? Wallahi kenan nan tawa ta karewa”

Hajiya ta tabe baki.

“Ta mu ta kare zaki ce, ni kina tunanin idan Mai Martaba ya sani zama zai yi da ni? Korani zai yi ya barwa Ammy gida ita kadai, daman abun da take nema kenan, sannan na shiga a bakin duniya...”

Kamin Hajiya ta karasa Jurry ta jarba tana kuka.

“Ni kuma ba zan samu mijin aure ba, kuma Mai Martaba tsine min zai yi, na zama zakka a gidan nan”

Hajiya Babba ta kalli Hajiya Talatu zuciyata da mugun nauyi.

“Na fada miki ki aika a dauko matar nna yau yau ba sai gobe ba, ta zo nan ta yi mana duk abun da ya kamata, haka mu kai wasa a baya har Falmata da Sardauna suna mana tsaye a wuya, domin su na su duk mai sauki ne ba kamar wannan ba”

Hajiya ta ce.

“Ai kina kirana na kira matar da ta san gurin na ce ta bar abun da take ta dauki shatar motar kasuwa taje ta dauko ta, domin idan na aika tare da direba wani karin tonon asirin ne, amman gaskiya wannan bokan ya iya munafurci, ta ya zai mana haka? Daga neman taimako?”

Jurry dai sai kuka take Hajiya Babba kuma ta nutsa a duniyar tunani tana ganin abun kamar ba gaske ba.


FADIME POV.

Sai da suka wuce take tambayar Jekafiya.

“Wacece wanda ta tambaye ni?”

“Ba ki santa ba”

Jekakadiya ta amsa mata a takaice haka take mata a duk lokacin da ta tambaye ta, ba ma ita kadai ba har wasu da ba Ammy ko Shattima ba idan suka tambaye wani abun gudun laifi ko ace ka yi sai ta ba shi takaitacciyar amsa, hakan da Jekadiya tai ba karamin kufula Fadime yai ba, daman ta lura a duk lokacin da ta tambaye ta wani abun sai ta amsa mata kamar bata son amsarwa ko kuma ta takaita, cikin bacin rai Fadime ta bi ta har suka isa inda Sarkin gida yake ta gabatar masa da sakon Shattima, sai ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login