Showing 165001 words to 168000 words out of 286946 words
miyasa kake munanawa Sirleem zato ba, ko ba komai yar'uwarka yake so ba, be kamata kana haka ba, kasancewarsa mawaki be rage shi da komai ba sai daukaka da suna”
“Ammay ba ki san waye Sirleem ba, yaron nan har rumgumarta yai before na tafi”
“Yaushe ya santa?”
A take mamaki ya cika Ammy domin ta san ba Shattima ba zai mata karya ba. Nana ce ta shigo dakin sanye da uniform din na islamiya cikin ladabi ta gaishe da Ammy kamar ba ita ba sannan ta mikawa Shattima gaisuwa, ya amsa da mamaki, sai ya ji ta burgeshi, a tunaninsa mutuwar da akai ne yasa ta natsu.
“Ammy zan tafi islamiya”
“To Allah ya tsare”
“Amin”
Har ta juya sai kuma ta juyo.
“Ya Shattima ka san Hajiya Karama bata gidan nan?”
“Nana ina ganin kamar kin fara hankali, taya zaki masa wannan maganar a yanzu?”
“Ammy ba dadi gidan, na saba da ita kuma kowa ya saba da ita, be kamata ta tafi ba”
Shattima ya juyo yana kallon Ammy.
“Miya faru?”
“Zamu yi magana anjima”
Kai ya daga mata sannan ya kalli Nana da murmushin karfin hali a fuskarsa.
“Je karki yi latti”
“To, kuma Yaya ina son magana da kai idan na dawo”
“Okay”
Ta juya ta fita a natse kamar ba ita. Ba Shattima ko Ammy ta jidadin yadda yarta ta dawo mai natsuwa cikin yan kwanakin nan abun da ta dade tana nema.
“I think mutuwar nan ta taba Nana”
“Ba mutuwa bace tun kamin mutuwa ta koma haka, abubuwa da yawa sun faru baka da labari, marasa dadi, ina ganin natsuwar bata Allah da annabi bace”
“Miya faru?”
Sai da Ammy ta labarta masa abun da Nana tai sannan ta biyo masa da zancen Zainab. At first dariya abun ya bashi duk da kasancewar yana cikin yanayin marar dadi.
“What if Iya ta fara rudewa ne Ammy? Kin san dai Zainab ba zata turo ta ta fadi haka ba, i think tana da wanda zata aura ma ai”
“Na ji ance ya rasu ai, kuma idan ita Zainab bata nuna mata ba, iya ba zata zo ta same ni da maganar ba, kuma dan rainin hankali sai suka tattara suka bar gidan, ni za su nunawa isa da zuciya? Miye masarautar nan ba taiwa Zainab ba da Iya?”
“Amman da su akai amsar gaisuwa ai shiyasa ban gane cewar sun bar gidan ba”
“Suna zuwa ne dai”
“Bana tunanin Zainab zata yi haka, ta dauke ni ne kamar dan'uwanta, tana yawan fada min damuwarta da duk wani abu daya ta so mata”
“Sake mata da kai da yawa shiyasa har ta fara tunanin sonta kake”
Ya sake yin murmushi domin shi kam abun dariya yake ba shi.
“Wata kila tayi hakan ne saboda karamci, a halin da nake ciki yanzu ai ba ko wace uwa ce zata bani auren yarta ba”
“Haka ne”
Ammy ta amsa wani tunanin na zo mata, miyasa Iya zata kawo tallar Zainab a gurinsa bayan ta fi kowa sanin halin da Shattima yake ciki? Amma Waziri ma yana kokarin yin haka, wata zuciyar ta raya mata. Mikewa Shattima yai tsaye yana saka hannyensa aljihu ya fito daga dakin.
“Jekadiya a nemo yarinyar nan”
Jekadiya ta daga masa hannu da sauri alamar girmamawa.
“To za a nemo ta”
Ta amsa ba dan ta fahimci yarinyar da yake magana kai ba, kuma kwarjininsa ba zai barta ta tambaya ba.
“Yarinyar da tai renon su Labib”
Sai da ya kara gaba kadan sannan ya furta hakan ba tare daya juyo ba, yai ficewarsa abinsa. Yana fita Jekadiya ta fice ita neman Inna wuro.
Kasa ya sauko har lokacin mutane shigowa suke suna gaisuwa, hakan yasa shi zabar zuwa garden ya kebe kansa, a dya daga cikin kujerun da suke gurin ya zauna yana kokarin ciro wayarsa, arba da yai da hotunan yaransa da suke screem din yasa jin wani iri, kewa da wata sabuwar kaunarsu ta sauko masa a kirji, sai a yanzu yake kara jin bakinciki rasa su da yai, sai dai babu wanda ya isa yaja da hukuncin Allah yadda Allah ya tsara haka ke tabbatuwa. A hankali yaa sauke ajiyar zuciya lumshe ido ya bude ya busar da iskar bakinsa.
Ku yi hakuri daga yanzu sai dare zan rika posting inshallah saboda wasu uzuririka da suka sha gabana, ni kaina ba haka na so ba Wallahi. Ayi min a fuwa dan Allah🙏
41
*Littafin nan na kudi ne biya ki karanta cikin aminci. Pay 300 to 2451879008 Hadiza Abubakar Zenith bank, then send the evidence via 08036126660*
Yana zaune garden din har la'asar, sai da ya ji kiran sallah sannan ya mike tsaye ya fito daga garden din, a fanfan masallaci yai alwala kamar sauran mutane sannan ya shiga cikin masallacin ya daidaita sahu tare da sauran talakawan gidan.
Bayan sun sauke nauyin sallah la'asar ya addu'a sannan ya fito ya nufi bangaren Mai Martaba. Yau ma kamar ko yaushe yana zaune falo, sai dai wannan karon yana tare da Waziri ne da alama suna tattauna wata maganar ne. Da sallama Shattima ya shigo ya zauna a kasa yayinda iyayensa suke zaune akan kujera.
Sai da ya fara gaida Baba Waziri sannan ya mikawa Mai Martaba tashi gaisuwar.
“Omar ya hakuri?”
“Alhamdulillah Mai Martaba”
“Ayi ta hakuri, rayuwa tana zuwa haka daman, abubuwa biyu sun zo maka a lokaci daya, rashin dan'uwa da kuma yaya, amman idan kai hakuri sai ka ga komai ya wuce”
“Inshallah na gode Allah kara girma”
“Ameen”
Waziri ya amsa sannan yana murmushi, Shattima ya mike tsaye tare da yi musu sallama sannan ya fice. Sai ya fito ya saka hannunsa aljihu ya ji babu keys din motarsa sai a lokacin ya tuna da ya bar su a dakin Ammy. Ba dan yana son zuwa ba babu abun da zai maida shi part din daukar keys saboda mutanen dake shiga shi kuma ba mutum ne mai son hayaniya ba, da kallo. Gashi kuma bayan son kowa ya tuka shi da sai ya kira Baba Adamu, hakan nan ya daure ya koma bangaren Ammy din. Be kalli kowa a falon balle ya lura da mutanen da suke ciki duk kuwa da irin gaisuwar da ake mika masa, sai da yai knocking sannan ya tura kofar a hankali ya shiga. Wata kawar Ammy ya samu a dakin tare da Ammy suna gaisawa.
“Shattima ya aka ji da hakuri?”
Cewar Matar sai ya amsa mata a takaice.
“Alhamdulillah”
“Allah ya masu ceto ne”
“Amin na gode”
Har ya dauki keys din zai juya Ammy ta kira shi.
“Shattima”
Sai ya juyo ba tare daya amsa ba.
“Yarinyar da kace a kira tana falo”
“Okay”
Ya juya ya fita, har ya iso tsakiyar falon be daga ido ya kalli kowa ba.
“Jekadiya yarinyar ta same ni waje”
Ya fada ba dan yana da tabbacin Jekadiya tana wajen ba, sai dan ya san ko bata nan dole a nemota a fada mata sakonsa, sai kuwa aka yi sa'a tana gurin ta amsa da to tare da yi ma Falmata a lama data mike tsaye, Falmata ta mike tsaye daker tana dingishi ta bi bayan Jekadiya suka fita daga bangaren, daker da wahala ta sauko stairs din saboda kafarta da bata ko son motsawa, haka ma da zata hawa sai da tai ta wai wai sannan ta samu ta haye har ta shiga cikin falon ita da Inna wuro.
Iyakar inda zata iya hange sai da ta duba ita da jekadiya amman ba su ganshi ba, gasu tsaye a rana suna ta duban inda yake ba su gashi ba, shi kuma isa ta hana shi yi musu wata alama da za su ganshi, ya hakimce cikin motar sai kallonsu yake, Jekadiya bata sa ran yana gurin motarsa ba, idan ma yana can wace daga ciki? Can dai wata zuciyar ta raya mata taje ta duba ko yana gurin ko kuma Garden duk da ta san be cika zuwa gardn din gidan ba.
“Zo mu duba nan”
Ta nufi gurin Motacinsa da suke fake a dabam da sauran motocin gidan, ta hanyar kukan motar da ta ji a kunne ne ta gane cewar yana cikin bakar motar, sai ta ja ta tsaya ita da Falmata har sai da yaga dama ya sauke gilashin motar. Da hannu yai mata alama da ta tafi sai ta juya ta koma inda ta fito, Falmata kuma ta sirina a gaban ganbun motar idonta a kasa, gabanta sai faduwa yake domin bata san dalilin kiran ba.
“Me ya samu kafarki?”
Ya fada yana kallon saman kanta daga inda yake zaune cikin motar. A tunaninta be kamata ta fadawa kowa cewar mahaifinta ne ya daketa ba, ba kuma zai mata kyakkyawar fahimta ba.
“Faduwa na yi”
Yana son ya ce garin yaya ta fadi har ta samu rauni haka, sai dai yana jin nauyin bakinsa da ganin zai shiga safgar da ba tashi ba. Dauke idonsa yai ya maida kan wayarsa yana latsa kamar ba mutum ya bari a gurin ba.
“Fada min gaskiyar abun da ya faru”
Ya furta bayan ya dauki tsawon lokaci yana chatin da Ra'ees a wayar. Ko be fito fili ya furta abun da yake nufin ya faru ba, ta san satar da ake magana yake nufi.
“Ban dauka ba, ban tana sata ba, ta shirya min abun ne ta yadda ba zan iya fitar da kaina ba, ita ta kirani tace na zo na gyara kayan Hajiya, kamin na gama ta ba ni yan kunnen yara tace na kulle a dankwalina, bayan na gama ta bani wannan sarkar tace kar na nunawa kowa na boye a hijbina.....”
Har ta gama zana yadda abun ya faru Shattima be ji komai ba hankalinsa yana kam waya, sai bayan kamar minti uku ya dago ya sake kallonta.
“Ban ji ba”
Haka ta sake karanta masa abun da ya faru kamar dazun. Aje wayar yai yana nazari, mi zai saka Jurry tai haka? Saboda ta batawa Ammy suna cewa mai aikinta tana saka ko kuma saboda wani abun dabam.
“Kin taba shiga bangaren ne kamin nan?”
“Aa”
“Then what happen da Sirleem ya dauke ki ina ya kai ki?”
Tsoro ne ya ziyarce ta, wata kila idan ta fadi gaskiya zai jefa Sirleem din a matsala hakan yasa ta zabi yin karya.
“Gida ya kai ni”
Hannunsa ya kai ya bude gurin da yake ajiyar kudi ya dauko bandir din 500 ya mika mata.
“Gashi hakkin aikin da kika yi, and idan kina ra'ayi cigaba da aiki a nan ki fadawa wani sai a sanar da ni”
Ta saka hannu biyu ta karba.
“Na gode Allah ya saka da alheri, ya baka wasu yayan masu albarka, su kuma Allah yasa masu ceto ne”
“Ameen”
Ya amsa yana kallonta, sai ta mike tsaye ta fara tafiya da dingishi, binta yai da kallo kamin ya maida dubansa gurin Nana data doso inda yake da saurinta tana sanye da Hijabinta na islamiya.
“Har kun ta so?”
“Yeah yau wa'azi ake mana yau laraba ba a dadewa”
“Zagoyo ta nan”
Ya fada yana rufe gilashin motar, sai ta zagaya ta dayan side din ta bude motar ta shiga ta zauna ba tare data rufe ba.
“Ya dan Allah karka yi bushi da ni idan na fada maka gaskiya”
Ya tattara dukan hankalinsa ya maida a gurinta.
“Ina jinki”
Cikin kunya da badama ta labarta masa abun da ya faru, na satar da tai da kuma barazanar da tai ma Hajiya har da abun da ta ji Hajiya Babba ta fada. Ba karamin mamaki ne ya kama Shattima ba, baya son ya munanawa Hajiya zato duk da ya san basa jituwa da mahaifiyarsa sai dai shi yana daukar hakan ne a matsayin kishi kasancewarsu mata, amman be yi tunanin fitowar lafazi irin wannan a bakinta ba.
“Ammy ta ji wannan?”
“Bata saurare ni ba, tana fushi da ni saboda abun da na aikata sai da aka yi rasuwar nan ne ta sauko”
Shattima ya sauke ajiyar zuciya.
“Shikenan, karki fadawa kowa wannan maganar ko da Mai Martaba ne, zaki tada masa hankali ne kawai, kuma dan Allah karki sake aikata abu makamancin wannan”
“To Ya Shattima, daman Sardauna yace na yi masa alkawarin ba zan sake aikata ba, kuma zan rika zuwa makaranta kullum zan zama yarinyar kirki, kuma duk na masa yace ma na daina zuwa bangaren Hajiya kuma ko ta bani abu na daina karba, yace wai ita ba son gaskiya take min ba Ammy ce take so na, tun ranar ban sake zuwa bangarenta ba ma, kuma ina zuwa school both islamiya da boko, ko bana jindadi ina daurewa haka nan saboda na cika alkawarinsa”
Maganar take idonta na cika da kwalla, Shattima kam kallonta kawai yake yana karantar abun da ita kanta bata san tana tare da shi ba.
“Ya dan Allah kai wani abu ya dawo I miss him, kuma yana da kirki sosai”
Shattima yayi murmushi.
“That's good gashi ya sa kin fara natsuwa ai”
Ta yi murmushi domin be fadi karya ba ita kanta ta san ta canja cikin yan kwanakin nan.
“My little girl, ya kamata a saka masa da abun da yai miki daman ai”
“Eh yaya dan Allah kaje gidan kai magana da yayarsa sai ta bar shi ya dawo aikin nan”
“Aa zamu dai saka a nemota ba zamu je ba kam, zamu saka a nemosa dai”
“No Yaya he's important to me kuma yayar shi ba, amman idan ta ga ka tafi zata bari maybe”
“Waye za a cewa Yarima yana nemansa yace ba zai zo duk garin nan? Wa zan yi ma magana yace min ba zai yi ba? Ko ke aka ce kina kiransu dole ta zo, kuma idan kika fada dole ta ji, kira daga masarauta ba kira daga makota ba ne, ke kanki da ace kin natsu kamar sauran yayanki da bata isa ta musa miki ba”
“Amman yaya ba komai ne Zaka ce sai an zo maka ba, sometimes you need to go, musamman idan abun yana da muhimmanci a gareka”
Ya dan yi shiru yana kallonta.
“You're right, zan sam abun yi”
“Yaushe? Anjima?”
Ya busar da iskar bakinsa daman ya san halin Nana akwai zakuwa.
“Tomorrow Morning”
“Okay thank Youu”
Ya daga mata kai yana murmushi sai ta juya ta fita cike da jindadi zuciyarta har wani zillo take tsabar murna da jindadi kamar ance mata Sardaunan ya dawo gidan ma gaba daya.
Sai da Shattima yai ribas sannan juya kan motar zuwa gate, a hankali yake driving din har ya fice daga gate din suna daga mishi hannu. Da hannu daya yake driving dayan hannun kuma yana rike da wayar da yake ta amsa sakonnin gaisuwar da ake masa, domin ko an kirashi a waya sai ya dama yake dagawa, daman can baya son yawan magana, balle kuma yanzu da yake jin komai ya masa nauyi, hakan yasa most of his friends musamman wandanda suka san halinsa da kuma wadanda suke nesa suke aike masa gaisuwar ta chat. Maganar da Nana tai ne yasa shi daukar hanyar da zata kai shi million quarter's, ba kamar yadda yai niyar aika mata da sakon kira ba ta waya, sai dai a yanzu ya zabi ruwa ba dan yayi niyar hakan ba sai dan abun da Nana ta fada cewar sometimes you need to go... Daman kuma hanyar gidansa ne da yake son tafiya a yanzu. Gaban gate din ya tsaya da motarsa ya danna horn, daman ya san gidan tun a lokacin data siya, shi ne mutum na farko data fara fadawa kuma ta dauko masa hoton gidan da komai, kamin ta takurashi yaje ganin gidan a lokacin da aka gama gyara. Mai gadin ya leko ganin mota yasa ya fara zuwa gurin motar ya ga ko waye kamin ya bude, sai dai bakin gilashi ne, kamar yadda motar take baka, isowa yai gurin motar a zatonsa ganinsa zai saka mutumen dake cikin motar ya sauke gilashi, amman sai ya ga tsabanin haka, hannunsa ya kai ya kwankwasa gilashin, domin aikinsa sanin wanda ya shiga da kuma wanda ya fita a gidan a matsayinsa na Mai Gadi. Anan ma Shiru Shattima be sauke gilashin motar ba, ko dagowa be yi ya kalleshi ba, sai amsa sakonninsa yake, hakan yasa Mai gadin ya juya ya koma cikin gidan dan sanarwa masu gida.
FADIME POV.
Gajiya da tai da zaman dakin yasa ta mike tsaye ta fara lalaben hanyar fitowa zuwa falo. Ta fara sabawa da yanayin gidan, domin ta san inda bandaki yake ta san yadda zatai ta fita daga dakin ko kuma ta shiga, ta kuma san ta inda zata bi ta fita kofar falon, sai dai ta saka saboda da mutanen gidan, ta ki ta saki jiki da su, babu ranar da bata kuka. Tun da Wasim yasa kafa ya tafi Zainab bata sake kula Fadime ba duk kuwa da kasancewar ya fada mata ta kular masa da ita, bata mata komai sai kyara, idan ta zauna a kujera zata ce mata ta sauka kasa, bata taba saka hannu ta rikata da sunan kaita bandaki ba ko kuma dakin da take kwana wanda babu komai a ciki sai tile, balle har ta dauko abinci ta bata, kwata kwata Fadime bata kwanta mata ba, jininta be gadu da nata ba. Abinci sai dai Iya ta bata, bandakin ma Iya ce ta nuna mata inda yake haka ma dakin da take kwana duk aikin Iya ne, ita kuma tana yi ne saboda Wasim, kwana ukun da sukai suna zuwa gaisuwar Labib kullum a gidan take wuni ita kadai da yunwa, har sai sun dawo sannan Iya ta dafa wani abu su ci har ita.
Da lalabe ta fito falon har ta karaso inda kujerun suke ta lalaba karamar kujerar ta zauna, Zainab dake kwance a doguwar kujera rike da waya, ta cire Bluetooth din da yake dayan kunnenta tana shan waka tare da dakawa Fadime tsawa.
“Wai ke wace irin marar jin magana ce, bana fada miki ki rika zama a kasa ba? Tun da kika zo gidan nan baki yi wanka ba, kin bi sai lashe kujeru kike”
Fadime ta sauka da sauri ta zauna a kasa, idonta na cika da hawaye, ita dai bata sam Zainab ba bata taba ganinta amman ta fahimci ta tsaneta tun da ta zo gidan, bata mata komai sai kyara.
“Yunwa na ke ji, tun abincin safe ban sake cin komai ba”
“To ba a dora girki ba, ki ci wuta, ke dai kin cika damuwar mutane Wallahi Mtchssssssss”
“Yi hakuri”
Fadime ta bata hakuri a sanyaye, sai ta sake jan tsaki, ba tsanar Fadime ne kawai a ranta ba, har da gaskiyar data gano ta ita, duk da kasancewar har yau ba ta yi ma Iya maganar ba,