Showing 174001 words to 177000 words out of 286946 words
tsaye tai ta saka dayan hannunta tana taba goshin.
“Be yi jini ba...”
Ya fada yana kallonta, bata ce komai ba, gaba daya yanayinta ya canja.
“Waye kai?”
Be ce mata komai ba ya janye ta jikin motar ya rufe motar.
“A asibiti na ji irin wannan sanyin da wani ya taba ni”
“Sanyin me?”
“Sanyi a hannuna, Wasim ya fada idan na taba hannun namiji na ji sanyi to shi ne mijina...”
Wani kasaitaccen murmushi ne ya bayyana a fuskar Shattima, ya kalleta yana jin tana kara kwanta masa a rai, saboda kiriniyarta da yadda take abubuwa babu kintsi, sai dai ya lura iya gaskiyar take fada domin yanayinta ba bayyana.
“Ni ne na taba hannunki a asibiti, saboda batanki mahaifinki zai iya kaini kotu, saboda nemanki yake gobe gobe zan kaiki gida”
Ta yi shiru bata ce komai ba, sai murzar hannun take da dayan hannunta idonta ya cika da kwalla. Ganin hakan yasa Shattima fadada murmushinsa.
“Kin ga shikenan na kawo matata har gida”
“Aa ni bana son ka, Wasim nake so, shi nake son na aura”
Ya sake yin murmushi ya kai hannunsa a karo na uku ya riko hannunta har lokacin bata fasa jin sanyin ba.
“Dan Allah akwai wani namiji a nan ka kira shi na taba hannunsa? Ina son na tabbatar”
“Idan kuma wasa yake miki fa?”
“Sai na tabbatar, ina son Wasim ina son shi, bana son ka bana son wani mutum”
To ni nace ina sonki ne? Ya tambaya a ransa, a fili kuma sai ya ce
“Gashi kuma idan na aure mace mutuwa take, duk matan da na aura sai sun mutu”
Ya karasa yana janyo hannunta su nufi entrance har din.
“Taka a hankali”
Ya fada yana kokarin taimaka mata ta haura gurin.
“Kai baka jin komai?”
Yayi shiru be ce mata uffan ba, har su ka hau gurin ya kai keys din dake hannunsa ya saka ya bude kofar. Sai ya fara shiga sannan ya janyo hannunta ta shigo, yana kokarin tura kofar ya rufe ta fashe da kuka mai karfi.
“Miya faru?”
“Dan Allah ka kaini gida gobe, zan fadawa Bappa gaskiya zan fada masa komai”
Ya kura mata ido, hawaye take wasu na bin wasu babu tsayawa.
“Na fada miki zan kaiki gida ai, and dole ne zan fadawa iyayenki gaskiya saboda su binciki waye Wasim din”
“Mutumen kirki ne, ba mugu ba ne, yana so na yana min duk abunda nake so, zan fadawa Bappa wannan, zan fada musu gaskiya”
“Then share hawayenki, indai akan aurene, ba zan aureki ba domin ina da wanda zan aura a yanzu, ko da ma bana da ita, ba zan so kusa miki a rayuwa na datse miki jindadi da walwala ba”
Ya fada yana kallon fuskarta, maganar yake har a zuciyarsa, idan ace za a aura masa Fadime tabbas ba zai ki ba, domin har ga Allah yarinyarta ta masa kuma zai so zama da ita, sai dai ba zai so ya aureta ta rasa rayuwarta kamar sauran matansa ba.
“Wannan Wasim din ya dace, sai sha dariyarsa ya more, zai nishadantu da rayuwarki you cute”
Ya fada yana lakatar hancinta da murmushi a fuskarsa. Kalaman da yai mata ne yasa ta ji sanyi a zuciyarta har ta share hawayenta.
“Zo ki zauna”
Ya zaunar da ita a kujera.
“Kin ce kina jin yunwako?”
Ta daga mishi kai da sauri tana kara share hawayen.
“Okay zan mana order abinci yanzu me kike so?”
“Yogurt da kaza”
Ta fada har tana hade yawu. Murmushi yai yana tuna wacan lokacin daya kadeta tace ya siya mata kaza da yogurt. Ya juya ya nufi upstairs yana lasa wayar hannunta.
“Ina zaka je?”
“Sama”
Jin abun da ya fada yasa ta dan tsorata.
“Sama kuma? Nan inda nake a ina ne?”
Murmushi yai har yana daga kansa ya sauke.
“Seriously rabon da na samu kaina cikin nishadi irin wannan har na manta, ina da damuwa sosai a raina, amman haduwar da nai da ke a yanzu yasa kin mantar da ni komai, ina jin kamar babu abun da ya faru”
“Saboda me mi nai?”
“Baki yi komai ba, saboda ba intentionally kike yi ba, rayuwarki ce a haka, and i like it”
Ya fada yana kallonta daga inda yake tsaye zuciyarsa cike da shauki. Fadime ta gyara zamanta tana saurarensa domin ta jidadi da yace he like it. juyawa yai ya cigaba tafiya har ya haye sama ya shige dakinsa, Shaddar jikinsa ya cire ya saka kananan kaya sannan ya dauko wayarsa ya sauko kasa, ko da ya fito ya sameta tsaye a tsakiyar falon tana lalebe a hankali.
“Ina zaki je?”
“Ban jika ba ne shiyasa nake lalabawa”
Yayi murmushi ya karasa saukowa.
“Ya kamata a samo miki sanda ko? Ki huta da lalaben hannu”
“Aa bana son sanda ni warkewa zance, abun da mutum yake kira shi ke binsa, ni bana son muguwar sara, zan warke inshallah”
“Ni ma ai fatan warkewa nake miki ai, amman sandar zata taimaka miki ne wajen gane abubuwa da kuma tafiya kamin ki samu lafiya, na san likitan da zai dubaki ma sai ya bada wannan shawarar kamin idonki ya bude”
“Aa Wasim yace kar a taba min ido, idan aka taba min ido zai lalace ba aikin likita ba”
Shattima ya riko cinyar hannunta ya zaunar da ita.
“Shi wannan Watsin din aljani ne ko mutum?”
“Ba Watsin ba, Wasim ba aljani ba ne mutum ne, ba na baka labarinsa ba?”
Ya daga mata kai kamar tana ganinsa, ba dan ya tuna ba ko ma bata taba bashi labarin ba oho.
“Ina ka tafi dazun?”
“Sama”
Ya fada ba tare daya kalleta ba.
“Sama? Sama?”
Ta sake maimaitawa wanda hakan tasa shi dagowa daga kan wayarsa ya kalleta.
“Yeah gidana gidan sama ne, so na hau sama ne upstairs”
Ta wara ido har da jan numfashi.
“Irin gidan masu kudi ne ko?”
Ya daga kansa yana karewa katon falon dake ciki da kyalikyali duniya irin na masu naira kallo.
“Ba laifi”
Ya fada yana tabe baki, sai ta daga kai tana ji kamar ace zata iya ganin komai a gidan, abunda bata taba mafarki ta shiga gidan sama irin a masu kudi.
“To ina matan gidan?”
“Ni kadai ne!”
Ta bude baki sai dai bata ce komai ba, har sai da ta ji motsin mikewarsa tsaye.
“Ina zaka je kuma?”
“Kicin”
“Ruwa zan dauko”
“Daga ina kicin din yake?”
Be ce mata komai ba ya nufi kicin.
“Baka ji ba?”
Ya juyo kamar an amsa dole domin har ga Allah tambayoyinta sun isheshi.
“Ba zan maimata ba ai ka ji, shiyasa na ke son Wasim, da shi ne ba zai kyale ni ba, kuma ba zai tafi kicin ya bar ni ba”
Yayi murmushi.
“Wacan ai Wasim ne, ni kuma Shattima ne, Wasim yana Katsina right? Ni kuma ina yola kin ga da banbanci”
“Shattima?..”
Ta maimaita tana tunanin inda ta taba jin sunan. Be sake ce mata komai ba ya nufi cikin kicin din dan yi abun da ya kawo shi. Sai da ya dauko ya fito rike da cup guda biyu sannan ta sake aika masa da wata tambayar.
“A nan ina ne?”
“Yola?”
“Yanzu, Wasim har yola ya kawo ni? Ina ne yola ma?”
“Ba ki jin bachi? Idan kin ci abinci ki yi bachi idan an yi magariba zan tashe ki”
Ta ji gabanta ya fadi, bata sake cewa komai ba har aka danna door bell din kofar, sai ta mike tsaye da sauri jikinta na rawa.
“Na ji wata yar kara minene?”
Sai da Shattima yai kamar ba zai ce mata komai ba, sai kuma ta bashi tausayi saboda ya san bata gani dole ne idan ta ji bakon yanayi ko wani abun ta tsorata.
“Kofa ce aka bugawa, ba kin ce zaki ci kaza ba, da yogurt? Maybe shi ne aka kawo, zauna bari naje na duba”
“Ta”
Ta zauna ba dan ta natsu ba. Tana ta sauraren takunsa tana auna tafiyarsa da inda ya dosa da zuciyarta har ya isa gurin kofar ya bude. Leda biyu ce a hannun mutumen dake sanye da uniform din restaurant dinsu ya mikawa Shattima cikin girmamawa yana gaishe shi, Shattima ya karbi ledodin sannan ya rufe kofar ya juyo ya dawo gaban Fadime ya aje. Tana jin kamshin kaza da motsin leda ta hade yawu, tana jin wani irin dadi. Kicin ya shiga ya dauko mata plate ya zo gabanta ya aje ya bude ledar dake dauke da kaza biyu ya ciro dayar kazar da aka rufeta da paper ya zuba mata a katon plate din, sannan ya dauko cup din da ya aje dazun ya bude yogurt din daya ya zuba mata.
“Sauko ki ci”
Ta sauko da sauri sai ya matsar mata da su gabanta ya kama hannunta ya saka a kan kazar.
“Kai har da zafinta, Allah ya saka da alheri Allah ya biyaka”
Take ta fara aikin kazar tana tsude hannu idan ta kamo kabeji sai ta cinye ta kara da nama. Shi dai yana hakimce saman kujera yana kallonta yana murmushi, yadda take lalaben kazar ta dauka ta ci idan ta cinye ta aje kashin a kasa, duk sai ya ji ta bashi tausayi, makanta babu dadi ci kawai take ba dan tana ganin kazar ba.
“Har na tuna wata mata, lokacin da ina garin su Wasim ta zo tace tana son a mata magani, wai a kashe mijinta da dan mijinta, sunansa ma irin naka ne har da mai irin sunana”
Ta fada tana tauna kashin, daman tun da ya fada mata sunansa take ta tunanin inda ta taba jin irin sunan bata tono ba sai yanzu da ta ji naman kaza a bakinta dadinsa na ratsa kwakwalwarta. Shi dai be ce mata komai ba har ta ci ta koshi tai gyatsa.
“Ina Yogurt din?”
Tashi yai ya karasa gabanta ya dauki kopin ya kai mata a baki, ta fara kwankwada sai da ta shanye tass sannan ta janye bakinta tana lashi gefen bakin.
“Kai ba zaka ci ba?”
“Na koshi”
“Ka aje min ragowar har gobe ko anjima”
“Ga wata nan ma zan saka miki a firji da safe sai ki ci”
Ya kama hijabinta ya goge mata inda bakin ya bace da maski da yogurt.
“Zan kaiki ciki ki yi wanka sai na saka yarona ya shiga kasuwa ya samo miki wasu kayan, kin yarda?”
“Eh Wallahi, na yarda daman ina son nai wanka tun ranar da na zo garin nan ban yi wanka ba, amman ba zan saka sosonka ba, da sabulu kawai zan yi”
Yayi murmushi finally ya hadu da mai kyamarsa.
“Shikenan bari na kira shi”
Ya mike tsaye ya fara tafiya sai ta kira shi.
“Shattima...”
Ya juyo ba tare da ya amsa ba. Ita ma bata jira ya amsa din ba tace.
“Na gode sosai, da wacan Zainab ce ba zata min haka ba, bata taba bani nama ba, ko ranar da na zo ina jin Iya tana soya nama amman bata bani ba, ina ta jin kamshi, sai cewa take tantabarun nan suna da mai, amman bata ba ni ko man ba”
Shattima yayi murmushi ba tare da yace da ita komai ba ya haura sama, kudi ya dauko sannan ya sauko ya fita waje, Zubairu na ganinsa ya taso da sauri ya nufo inda yake.
“Ranka ya dade, Allah kara maka lafiya wani abu za ayi?”
“Yeah so nake na shiga kasuwa ka samo doguwar riga medium ta manya da hijabi, ba dole sai mai tsada ba”
Ya mika masa 30k din hannunsa, Zubairu ya saka hannu ya karba yana amsawa da.
“To an gama yanzu kuwa”
Shattima ya juya ya koma cikin falon, wannan karon ya samu Fadime tsaye a inda ya barta tsabanin dazun da take zaune a kasa. Karasawa yai kusa da ita ya kama hannunta suka nufi upstairs din.
“Sai kin taka a hankali”
“Tau bismillahi”
Ta fara takawa a hankali.
“Ban taba hawa gidan sama ba”
Be biye surutunta ba ya saka hannunsa ya dauke ta sama ya haye da ita. Rike shi tai sosai har sai da ya shiga cikin dakin ya sauke ta sannan ta sake shi.
“Cikin bandakin ne ka kawo ni?”
“Aa”
Yaja hannunta zuwa bathroom din ya bude ya saka ta ciki, ya kai hannunta a a inda zata aje kayanta.
“A nan zaki dora kayanki”
Ya dauki sabulun ya mika mata a hannu ya ya kunna mata shawa.
“Tau fita”
Ya juya kamar yadda ta fada sai ta kai hannunta tana lalaben bayansa shi dai ban da murmushi babu abun da yake har ya fita ta ji ta rika kofar ta rufe da kanta.
“Yi magana na ji”
“Gani a nan ba zan shigo ba”
Sai da ta tabbatar ta ji muryarsa a waje sannan ta juyo da lalabe ta karaso gurin da ya kaita ta cire tufafinta ta aje ta karasa gurin shawar ta tara jikinta tana ayyana yadda bandakin yake, sai da ta duka kasa ta taba tile din ta taba jikin bandakin sannan ta cigaba da wankan tana jin dadi ruwa na sauka a jikinta, abun da bata taba ba.
Sai da ta gama wankan ta dauki tufafinta ta saka ta maida hijabin sannan ta fara kiran sunansa.
“Shattima.... Na gama”
Ta fara takawa tana tafiya, har ta isa gurin kofar ta fara lalabe ta bude ta fito tana tafiya a hankali.
“Shattima...”
Ta kwara masa kira, sai ya amsa yana zaune kan gadon.
“Na'am”
Tsayawa tai a gurin bata sake ce masa komai ba, shi a be ce mata ba, sai tunanin karfin halinta yake yadda ya fada mata be da mata kuma ba kowa a gidan sai ita da shi amman bata jin tsoro ta sake jiki babu wata fargaba, gashi kuma ba gani take ba.
“Zo ki zauna”
Ta fara takawa ta nufi inda take jin muryarsa sai da ta karasa sannan ta lalaba ta zauna kan gadon.
“Sanyin Ac”
Ya kalleta tufafin ma a birkice ta saka su, ya dauke kai ya mike tsaye ya nufi kofar fita, tana jin fitarsa ba hakuri bata ce komai. After like 30 min ya dawo dakin ya warware rigar, ya kama hannunta ya saka mata rigar.
“Zan fita sai ki saka, inda kike jin stone nan ne gaba, wannan dankwalin ne, ga kuma hijab”
“Tau na gode”
Ta fada da murmushi a fuskarta tana jin dadi duk kuwa da kancewar bata ganin komai. Juyawa yai ya fita yana jindadin ya farantawa wani rai. Sai da ta ji ya rufe kofar ta kwala masa kira.
“Shattima”
“Na'am”
Ya amsa mata da karfi yana juyowa.
“To tafi daman dan na tabbatar idan ka fita ne”
Ta mike tsaye ta fara cire tufafinta, sannan ta dauki rigar ta saka ta saka hijabin. Be dawo dakin ba sai bayan sallah magariba. Yana shigowa ta fara tambayarsa wai ta yi kyau, da taimakonsa tai alwala ya shimfida mata abun sallah tai sallah.
Bata kwanta ba sai da ya sake bata naman na kaza ta ci sannan ta hau gadon ta kwanta ta.
“Amman ka kwanta a kasa, idan ka bar ni ni kadai zan ta maka ihu”
Yana kallonta yasan zata iya tsab.
“Kina firgita da dare ne?”
“Aa amman dai nan ina jin tsoro, ba zan iya kwana ni kadai ba”
“To ki yi addu'a kamin ki kwanta”
“To zaka kwanta a kasa din?”
“Ke ki kwanta a gado?”
“Eh mana, a ba zamu kwanta a gado daya ba Allah ya tsare, in Bappa ya sani zai ya kusa kasheni”
“Okay”
Ya fada yana murmushi, bargo ya dauko ya shimfida a kasa ya saka filo, ita kuma ta kwanta saman gadon ta zuro hannunta kasa ta yadda zata rika jinsa ta tabbatar a kasa yake kwance.
Washe gari da asuba ya farka kamar kullum bayan yayi sallah ya tasheta tai sallah sannan ya fasa sabon brush ya rika fuskarta ya wanke mata baki ya fito da ita ta dauko mata ragowar kazarta ta cinye da yogurt, shi kuma ya hada tea ya sha.
Bayan sun gama mai gyara ya shigo ya gyara ko'ina a gidan sannan ya fita.
“Zan biya dake ta wani gida, na yi ma Ammy sallama sannan mu wuce airport”
“Ammy kuma...”
Tana ta tunanin inda ta san sunan can kuma ta tuno da zancen airport.
“Jirgi zamu shiga kenan?”
“Eh”
Ta dafa zuciyarta tana dariya wani shauki na ziyarta ta.
“Tsoro kike ji?”
“Aa dadi dai? Jirgi fa zan hau, dan ma bana gani, wayyo Allah”
Yayi murmushi ya riko hannunta suka fito, sai da ya saka ta cikin motar sannan yaje ya rufe kofar falon ya dawo ya shiga motar ya saka key din ya murda motar ta ki motsawa ko wuta taki dauka, ya murda ya murda ta ki tashi fita tai daga motar ya bude gaban motar ya duba be ga komai ba, ya dawo ya sake tadawa ta ki tashi. Fita yai ya koma cikin gidan, ya dauko key wata mota ya nufeta ya kunna sai ta tashi, dawowa yai ya cire Fadime a motar farko, ya saka a wanda ya kunna Fadime na shiga motar ta mutu.
“Oh Wow....”
Shattima ya furta yana cike da mamaki.
ZAINAB POV.
Tana shiga cikin dakin ya fada kan gado ta rushe da kuka, bakincikin abubuwan da Fadime ta fadawa Shattima ya saka taji kamar ta kashe kanta, da wane ido zata kalle gashi ta hada karya da gaskiya ta fada masa, har abun da Iya ba tai ba. Bata dauka Shattima zai dauki Fadime su tafi ba har sai da ta ji tashin motarsa ta sauko saman gadon da zimmar zuwa tai ma Fadime dukan mutuwa sai ta samu falon babu kowa, tsaye tana tana karewa falon kallo kamin ta nufi dakin da fadime take kwana ta duba ganta ba, ta shiga dakin Iya ko zata same ta a ciki nan ma bata ciki, fitowa tai harabar gidan ta tambayi mai gadinta ya tabbatar mata da tare ya fita da yarinyar, sai ta dawo cikin falon tana mamakin abun da Shattima yai wanda be taba ba, me ma zai saka ya tsaya kulata? Or Maybe saboda tana makauniya ya ke ganin tausayinta. Ina zai kaita? Gashi bata isa ta kira ta tambaye shi ba, indai har masarauta ya nufa da ita ta san Fadime sai ta fadawa kowa cewa Iya mayya ce. Fashewa tai da kuka tana jin ina ma ba a kawo Fadime gidan ba. Tana cikin kukan Iya ta shigo rike da leda tana ta sauke gajiya da alama wani gurin ta fito. Jin Zainab tana kuka yasa ta kalli inda take xaune cike da faduwar gaba.
“Kai Subhanallahi lafiya dai?”
Zainab kamar mai jira ta dago tana duban iya hawaye sharaf a fuskarta.
“Ina lafiya Iya? Kin ja mana abun kunya, kun yi komai a gaban yarinyar nan yanzu ta kwashe ta fadawa Shattima, ba ke kadai ba har ni sai da tasa, tace ni da ke duka mayu ne, yanzu ya dauke ta ya tafi da ita Allah kadai ya san wanda zata fadawa a masarautar nan, gashi ta kiri karya tace kin ce rayuwar