Showing 225001 words to 228000 words out of 286946 words

Chapter 76 - Fulani Book 1 Hausa Novel Complete

20 Dec 2024

921

ta fara jin tsoron zuwan, zuciyarta ta soma raya mata cewar wata kila an rike Zainab ne saboda ana son ta zo waya sani ko wani abun aka shirya mata, take ta tuna da kalaman da Zainab tai mata cewar idan ba ta daina abun da take ba zata bata mamaki wata kila ta fadawa Ammy ko Shattima wani abun ne, wani bangare na zuciyarta kuma yana raya mata ba haka ba, domin jikinta na bata yarta na cikin matsala. Kamin su isa masarautar ta tsayar da mai achaban ta sauka ta dauko kudinsa ta mika masa, ya karba ya bata canji sannan ta karasa masarautar da kafa.

Tana daf da shiga gate din masarautar sai kuma ta ja ta tsaya tana tunanin idan ta shiga zata iya jefa kanta a matsala. Daga nesa ta kira wani police dake gadin masarautar daman tana mutunci da shi sosai, domin yana girmamata. Shi kanshi yayi mamaki da bata karaso a inda suke ba kamar yadda ta saba sai ta tsaya can nesa da su sai dai ba sosai ba ta kira shi.

“Hajiya Iya lafiya dai?”

“Lafiya kalau Jekadiya na ke son gani”

“Hajiya Iya ganin Jekadiya ai baya miki wahala ke da kika fi mu gata cikin gidan na, ko dai akwai matsala ne”

Ta yi dariyar karfin hali.

“Aa babu komai Wallahi, sauri na ke ne ina son na tafi wani guri kuma ka san gidan sarauta idan ka shiga dole ne sai ka shiga ka gaishe da kowa idan ba haka ba kai laifi, shiyasa bana son asan na zo”

“To a kira miki ita?”

Ta dan yi shiru tana tunanin idan wani abun aka shirya mata, idan Jekadiya ta zo ta ganta a nan ba tsira tai ba.

“Aa kira min ita a waya ma”

“To”

Ya ciro wayarsa yana fadin.

“Ai ni ranar na ke samun labarin wai kun bar masarautar nan”

“Eh Hajiya Karama ce ta matsa ta matsa, dole na bita tun da ba a kyale mace ta zauna ita kadai a gida ba”

“Haka kam ai kara da kika koma kam”

Ya shiga neman number Jekadiya tare da aika mata kira, wayar bata dade tama ringing ba ta daga sallama, sai yai saurin mikawa Iya.

“Gashi ta dauka, sai dai bata san ni ne ba domin ni kadai na ke da number ta bata da tawa”

“Too”

Iya ta karba ta matsa can nesa da shi inda ba zai ji maganar ta ba tana sallama.

“Jekadiya..Iya ce, na ce Hajiya Karama har yanzu bata dawo ba”

“Oh daman yanzu nan Shattima ya shigo yace a fada miki ba zata dawo yanzu ba”

A take gaban Iya ya fadi.

“Saboda me? Me ya faru?”

“To be fada min ba gaskiya ya dai ce a fada miki an kaita gidan hoto”

“Hoto? Ita Zainab din?”

“Eh sai anjima”

Jekadiya ta kashe wayar tun kamin Iya ta sake fadar wani abu, domin har ga Allah tsoronta take kuma tana gudun tai wata maganar da zata sabawa abun da Shattima ya fada mata. Iya ta gyada kai yana jinjina lamarin.

“An kaita gidan horo? Saboda batan yarinyar nan? Ko kuma saboda wani abun na dabam? Amman ko minene ai be dace Ammy tai mata haka ba!”

Tana tafe tana wannan maganar har ta iso inda Police din yake tsaye ta mika masa wayarsa.

“Amiru na gode sosai”

“Ai ba komai, kin fi karfin nan Iya”

Ita dai bata sake ce masa komai ba, domin tashin hankalin da take ciki ya dauke mata hankali.

“Ko kuma saboda ni za su hukunta ta? Shattima ne da wannan aikin ko Ammy? Ba mamaki Ammy ce domin ita ta saka aka min turaren nan kuma ta fi kowa bakin hali a gidan ai”

Tana tafe tana magana da kanta har ta isa babban titi ta tari napep ta hau.

“Malam million quarters za ka kai ni”

“To kudinki dari uku”

“Mu tafi”

Ta fada tana ta tunani, yana tafe tana kallon ababen hawaye zuciyarta kuma cike fal da tunani kala kala. Har bakin gate ya sauketa ta ciro dari hudu ta ba shi ya bata naira dari sannan ta juya dama da hadu ta ga idan babu wanda ya biyo ta, sai da ta tabbatar ita kadai ce sannan ta kwankwasa gate din. Mai gadin ya leko yana tambayar waye, ganin ita ce yasa ya bude mata ta shiga, ko sannu da zuwa da yake mata bata amsa ba tsabar hankalinta baya jikinta. Sai da ta shigo cikin falon ta zauna sannan ta samu yar natsuwa ita ma kadan, gaba daya hankalinta ya tattara ya koma kan Masarautar, sai neman dalilin kama Zainab din take ta rasa tudun dafawa idan ta kulla wannan ta kwance wacan. Mikewa tai tsaye ta isa gurin kofar falon ta rufe da makulli sannan ta dawo ta bude dakinta ta shiga ta maida kofar ta rufe. Hijabinta ne farkon abun da ya fara cirewa sannan ta aje jakarta ta nufi gurin da take aje tukunyarta ta bude ta dauko tukunyar tai magana a cikin sai kuma ta maida tukunyar ta aje, ta nufi karkashin gadonta ya janyo kwayar nan da take ajiyar kurwa a ciki, ta bude ta dauko kurwar Maijidda ta warware zaren jiki taka bakin mayafin dake saman gadonta ta lullube kurwar da shi. Tana cirewa sai ga kurciya a hannunta fuska a hade ta kama wuyan kurciyar ta murde iya kar karfinta har sai da jini ya fito ta tabbatar da ta kashe ta sannan ta saka a wani karamin kwanon, ta dauko dayar kurwar ta warware ta saka bakin zanen ta lullubeta, tana budewa sai wani tsohon zakara marar lafiya ya fara motsawa.

“Yanzu idan masarautar ta girgiza sai mu ga waye kuma za a dorawa laifi? Sai na ga yadda za ki yi ke da yayanki”

Iya ta fada tana zaro manyan idanuwanta masu mugun ja da mummunar fuskarta da bata da kyau gani.







WASIM POV.

Ya mike tsaye yana kallon Kakansa.

“Har tsawon wane lokaci za ka dauka kamin ya bar yarinyar can ta samu lafiya?”

“A kullum fata na ke mata na samun lafiya, ku dai zan tambaya sai yaushe za ku kyaleta ta samu lafiya?”

“Sai ranar da k yardar ka bi umarnin mahaifinka, kuma ina mai tabbatar maka tana daf da rasa idonta gaba daya, domin mutumen da aka hannatawa ita daf yake da taba idonta, kuma ka san makomar hakan matukar ya taba idon ba za su taba dawowa ba, hakan kuma ba zaka mu bar ka ka aureta ba, domin ba zaka taba auren wanda ba jininmu ba”

Wasim ya koma ya zauna hankalinsa a tashe, domin ya san dukan abun da Kakansa ya fada masa abubuwan da ya riga ya gani ne.

“Kana wahalar da ita ne kawai, domin tuni ta taba hannun wacan dan Sarautar da yake haukan nemanta kuma ta ji sanyi”

Wasim ya dafe kansa da mugun karfi kamar zai cire kan daga jikinsa, zuciyarsa ta shiga bugawa da karfi, daman abun da yake gudu kenan shiya saka shi kasa taba hannunta tun a wacan lokacin, tsoronsa daya kar ya taba bata ji sanyi ba. Ya daga kansa ya kalli kakansa hawaye masu zafi na sauko masa.

“Kaka ka sani ina son ta”

“Kana sonta kake bari tana cutuwa? Ka nisanta da iyayenta? Ka kaita inda aka gusar da hankalinta? Kuma ka saka take kokarin rasa idonta? Wanda kake so za kai masa fatan samun farinciki ko kuwa farincikinsa na nufin bakincikinka ne”

Ya lumshe ido yana jin wani irin kalar yanayi da be taba jin irinsa ba, yana tuna kalaman Zainab.

“Wani lokacin dole ne mu sadaukar da farincikin mu saboda wadanda mu ke so su samu farinciki...”

Kansa ya daga sama sai ga hawaye sun sauko masa ta gefen idon, wani irin zafi da radadi yake ji idan yai yunkurin tunanin rabuwa da Fadime.

“Rabuwa da Fadime ba shi yake nufin na auri Liya ba, kuma ba zan taba barinta ta samu farinciki ba”

“Kana da damar auren wanda kake so matukar jininmu ce, amman wacan yarinyar idan za ka kashe maza dubu ka zata yi mu'amala da su, ba za ta taba aurenka ba”

Hannunsa ya daga sama ya daki tsakiyar kansa da dukan karfinsa ya rufe ido yana girgiza kai. Mikewa yai tsaye yana wani irin huci kirjinsa har wani sama yake kamar sai yi tsalle.

“Zan rabu da ita, amman sai na taba mutanen da suka taba ta, sai sun shiga kunci fiye da ita”

“Wannan kuma aikin duna ne, zan zan nemo shi... Na ka aikin ka tafi gurin shugaba ka fada masa ka yarda da dokinsa, ni kuma zan bude idanunta”

Kakansa ya fada da yarensu, sai Wasim ya kalli inda Fadime ta ke yawan zauna a lokacin da ta zauna dakin kakansa. Matse hannayensa yai yana jin rabuwa da ita kamar fitar rai ne daga jikinsa, kai ya girgiza ya koma ya zauna.

“Ba zan iya ba, wata kila ka fada min haka ne saboda ku cin ma burinku a kaina”

Kakan yayi murmushi.

“Lallai kana sonta sosai tun da har ka iya karyata ni, amman bari mu gani daga nan zuwa jibi idanuwanta za su bude ne ko kuwa za su tabbata har a bada a rufe? Amman ka sani daga lokacin ni da kai babu abun da zamu iya yi domin dawowa da idanuwanta....”





HAJIYA BABBA POV.

“Amin wa'alaikissalam”

Ta amsa sallamar da Hajiya Zariya tai mata a yayinda ta kara kunnen a wayarta.

“Hajiya ina yini ya gida ya Mai Martaba da jikin”

“Alhamdulillahi”

Ta amsa cike da kasaita kamar ba yar'uwarta ba.

“Hajiya na ce ko Sirleem yayi aure ne ba a fada mana ba”

“Wane Sirleem kuma?”

“Sirleem dai na ki, na wuce ne jiya ta gaban gidansa da yake nan kusa da mu na ga mutane na fitowa na tambaya aka ce min walima ake wai Amarya aka kawo, shi ne abun ya ba ni mamaki na ce to ko anyi bikin ne ba a sanar mana ba”

Hajiya Babba ta aje farantin dankalin jos dake hannunta.

“Aa ai ke ma kin san ba zai yiyu ba, Sirleem yai aure ba ki sani ba, ko da ba a fada miki ba ai duk garin nan sai ya dauka, shi kadai ya rage min fa namiji, kuma aurensa da yar sarautar ai dole ne ma duniya ta sani”

“Ni kaina na yi mamaki, tun jiya abun ya tsaya min a rai ina ta son na kira dai ban samu dama ba, mutanen ma da na ga suna fitowa daga gidan ba wasu na azo a gani ba ne, ko dai haya ya bada gidan ne?”

“No gidansa da ke kusa da unguwarku ai yafi ko wane gida nasa kyau da tsaruwa, ba zai bada hayarsa ba, kuma bana jin zai arawa wani, Amman kin shiga cikin gidan kuwa?”

“Aa wannan dabarar bata zo min ba, ban yi wannan tunanin ba”

Shiru Hajiya Babba tai tana nazari.

“Zan bincike shi idan ya shigo”

“To Hajiya sai an jima a gaishe da su Kausar”

“Za su ji”

Hajiya ta sauke wayar cikin tsananin mamaki, anya ma kuwa gidan ne? Ta tambayi kanta sai dai bata jin Hajiyar Zariya za tai kuren fahimta domin ta san gidan ba ita kadai ba ma yawancin mutanen unguwar sun shaida gidan saboda tsaruwarsa gashi farin gida mai bakin gate sai daukar hankali, sai dai ba kowa ya san cewa na Sirleem ba ne sai daidaikun mutane yan'uwa da kuma wadanda suke kusa da shi sosai.
Tunawa da tai da zancen da yai mata shekaranjiya na cewar zai kwana a can saboda baya jin dadi da kuma jiya da yace mata yana son komawa can so that ya samu damar maida hankali kan harkokinsa yasa gabanta mugun faduwa. Har ta dauko wayarta ta kira shi sai kuma wata zuciyar ta hana ta, da sauri ta mike tsaye ta nufi inda mayafanta suke ta dauko farin gyale ta saka ta nufo gurin da aka jekara takalminta ta saka ta dauki jakarta tare da wayarta ta fito falo.

“Juwairiyya”

“Jurry bata nan”

Karima ta amsa.

“Ke tashi ki kai ni gidan Sirleem da ke 300 houses yanzu nan”

“Okay, amman Hajiya lafiya?"

“Ita na ke son na tabbatar”

Ganin yadda hankalin mahaifiyarta yake a tashe yasa tai saurin dauko mayafinta ta fito rike da makullin motarta, har suka saukon ta shiga motar mamakin abun da ya faru take, ko dai minene ta san abu ne da yake son sirri shiyasa ta zabi ta kaita a maimakon direbobinsu da suke gidan.
Suna isa unguwar Hajiya ta saka tai bakin nesa da gidan sannan suka fito suka taka da kafa har gaban gidan, Karima ta kwankwasa gate din sai mai gadin ya leko. Karima za tai magana Hajiya ta tari numfashinta

“Amarya na nan?”

“Eh suna nan Hajiya Bismillah ku”

Ya bude musu gate din, suka shiga ciki hango motar Sirleem da Hajiya tai ya fi komai kayar mata da gaba, Rima kam tana gefenta da mamakin jin abun da Hajiya ta fada, suka nufi hanyar shiga falon zuciyar Hajiya sai bugawa take kamar zata fasa kirjinta ta fito, sai da ta fara tura kofar ta ji ta a rufe bata ko tsaya duba inda door bell din yake ba ta kwankwasa. Jin shiru ba a bude ba yasa ta sake kwankwasawa. Sirleem ne ya bude kofar yana sanye da jallabiya milk color.

“Hajiya....”

Ya fada kamar wanda ya rude. Tura kofar falon tai ta wuce ciki falon, sai tai arba da abun da bata yi zato ba, wato Falmata tana sanye da doguwar rigar atamfa hannunta rike da dankwali, daga bakin Hajiya har hancinta da idonta kallon Falmata yake with shock, can kuma ta juyo ta kalli Sirleem baki sake ta nuna shi da yatsa, sai kuma ta kasa magana, ta sake juyowa ta kalli Falmata ta daka mata tsawa idonta na cika da kwalla.

“Me kike yi a nan?”

Falmata ta kasa cewa komai jikinta sai rawa yake, Sirleem yayi saurin nufar inda take yana kallon Hajiya.

“Sirleemmmmmm.....”

Hajiya ta kira sunansa daker sannan ta ce

“Dadiro kuke yi?”

“No Hajiya Subhanallahi, she's my wife”

Wife wife wife wife wife wife wife wife wife.... Haka kalmar tai ta maimaita kanta a kunnen Hajiya, nuna shi tai ta nuna Falmata sai kuma ta nuna kanta kamin ta fadi kasa zaune saman tile din. Sirleem na ganin haka yai saurin kama hannun Falmata suka fice daga falon cikin sauri, motarsa ya nufa da ita Rima ta bi su da kallon mamaki ido bude. Sai da ya taba motar ya ji a rufe, sai ya rasa yadda zai yi baya son komawa ciki saboda zuciyarsa na raya masa Hajiya zata iya cewa sai ya sak Falmata a take. Hannunta ya kama be ko kula da dankwalinta dake hannunta ba suka fice daga gidan gaba daya, Falmata kuka kawai take jikinta na rawa kamar mazari. Suna fita su kai sa'a da Napep, cikin sauri Sirleem ya tare Napep din dake tare da wata mata suka shiga, yana fada masa inda zai kaisu.

Sai da suka bar unguwar sannan Falmata ta lulluba dankwalin da ke kanta, mai Napep kam sai mamakin wanda ya dauko yake a zahiri dai fuskar Sirleem yake gani fitaccen mawaki sai dai ba shi da tabbacin shi din ne ko waninsa. A gaban gidan Momy ya sauke su Sirleem ya fito yana fadin.

“Jira ni ina fitowa”

Ya buga gate din gidan mai gadin na budewa yaja hannun Falmata suka shiga ciki, yana isa bakin kofar falon Momy ya buga kofar da mugun karfi, hakan yasa Momy tai saurin budewa hankali tashe. Ganin Sirleem da Falmata ya bata mugun mamaki.

“Sirleem”

“Momy dan Allah ki boye min yarinyar”

“Lafiya?”

“Dan Allah ki boye min ita yanzu yanzu, zan dawo ki saka a daki ki kulle dan Allah kowa ya zo karki fito da ita”

Momy ta nuna Falmata da mamaki.

“Wannan ba Falmata ba ce?”

“Ita ce Momy please ki boye min ita”

Ya fada cikin tashin hankali, saurin kama hannun Falmata tai ta shiga da ita ciki shi kuma ya juya ya koma, upstairs Momy ta nufa da Falmata da ke kuka ta bude dakin Ameer ta saka ta ciki ta rufe ta makulli ta sauko kasa da mamaki kala kala.
Bakin kofar dakin Falmata ta zauna ta fashe da wani irin kuka marar misaltuwa, sai ta ji kamar bata taba fuskantar tashin hankali irin wannan ba, kuka take sosai tun tana yi ba sauti har sautinta ya fara fitowa, kuka tai bana wasa ba har sai da idanuwanta suka fara kumbura, hawayen suka daina zubo mata. Mikewa tai tsaye tana goge idonta da dankwalinta, kamar ance mata juyo ki kalli gefe, tana juyowa sai tai arba da wani tsohon hoton mahaifiyarta, an fadadashi har ya kusan tsawonta, an ajeshi a tsaye yana fuskantarsa, mutuwar tsaye tai tana kallon hoton with shock.



_________
Ina mata matan kwalisa Matan da suka ansa sunansu na Mata? Ina wadanda ke cewa mun yi mun yi bamu ga amfaninshiba? Hmmm to ku zo ga Yar gidan Maifata ta zo maku da Al ajabu, dan tsugunno, gumba da tsimi da Zuma daban daban, maganin sanyi na maza da Mata. Ga kuma garurruka irinsu mallakau sabuzu kuwa, sa bahaushe saibi, Dan hubbare kafi malam aiki, ke kadai ke da miji, dahuwar kaza, tattabara, ciccibi da dai sauransu. Ba anan kayanmu suka tsaya ba, muna hadin amare na musamman turaren sutura turaren tsugunno turaren wanka da na daki da na jiki duka 4amare nasu na musamman ne, amma ga tsuhuwar da ke son komawa yarinya itama zata iya zuwa ahadata kai abundai sai wanda ya gani, dan haka karkubari abaku labari, domin neman karin bayani zaku iua nemana ta wannan number  09029891757 ko 08169311410, muna aikawa ko'ina a fadin kasar nan har waje kasar nan muna aika kaya.
Address: Nasarawa Samaru Area gurin masallacin mai sola Gusau Zamfara state Nigeria.
55


*Littafin nan na kudi ne biya ki karanta cikin aminci. Pay 300 to 2451879008 Hadiza Abubakar Zenith bank, then send the evidence via 08036126660*


Sai da ya koma cikin gidan sannan ya shiga cikin gidan da tunanin Hajiya Babba tana nan har lokacin amman be tararda ita a falon da aka bari a bude, dakinsa ya shiga ya dauko kudi ya sallami mai Napep din sannan ya sake kowa ya dauko makullinsa motarsa ya fito ya shiga motar, sai da yai mata key sannan ya fara tunanin da wani ido zai kalli Hajiya? Me zai fada mata? Taya zai fara mata bayani? Anya ma zata fahimce shi? What if ta cilasta masa sakin Falmata? Haka ya bar motar kunne ya rasa abun yi tafiya ko zama, can dai ya ja


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login