Showing 246001 words to 249000 words out of 286946 words
ba zan iya rayuwa cikin farinciki ba bayan ke kinaa cikin wata damuwar”
Ta kama hannunsa ta sake tabawa, ta sake a karo na uku, sai sake karawa sau ba dadin tana ta kuka.
“Wayyo Allah na”
Tana ta yakar kukanta tana sakawa a zuciya domin bata son ya fito, sam bata ma son ta yarda cewar Wasim zai tafi.
“Ko wani abun na yi maka?”
Ya girgiza mata kai.
“Ba ki yi komai ba”
“Ko saboda na ce Zainab Mayya ce?”
“Zainab ba mayya ba ce, Iya ce mayya, kuma ba saboda haka ba ne, na fada miki idan ban rabu da ke ba, idonki ba zai dawo ba, kuma asirin da Hajiya Babba ta yi miki da Hajiya Talatu ba zai barki ba, asiri suka miki aljani ya dauke ki daga can ya dawo da kenan kuma ya mantar da ke komai, kaka ya ki aminta ya yi magana da aljanin har sai idan na yarda ya rabu da ke, kuma dole na aminta saboda ba ni ne mijinki ba”
“Wasim aa dan Allah... Ka bashi hakuri ka ce na ce dan Allah yayi hakuri”
Yayi murmushin tare da hawaye a lokaci daya.
“Babu wani abu da zamu iya yi, je ki yi ibadarki”
Ya sake ta sai tsaye guri daya tana jin cewar idan ta matsa tafiya zai yi.
“Zan yi marmarin murmushinki, kiriniyarki da ma komai na ki, ina son ki sosai”
“Sake zuba min maganin”
Ta tara mishi hannunta tana kuka sosai marar sauti, sai ya share hawayen idonsa yana kallon fuskarta.
“Ba ki yarda da ni ba ne Fateme?”
Ta daga masa kai alamar eh bata yarda din ba, sai yai murmushi idonsa suka sake cika da kwalla.
“To rufe idonki na miki na ido”
“Idan na rufe sai ka tafi?”
“Aa zan tsaya har sai kin yarda”
Sai ta rufe ido daya ta bude daya, nan ma Murmushi yai yana jin kamar ya kurma ihu saboda zai bar Fadime, dabi'unta na daga cikin abubuwan da ke burgeshi.
“Dole sai kin rufe duka....”
Ya fada cikin kuka irin na masa, domin ya san tafiya zai yi ya barta, ba kamar yadda take zato ba. Sai ta rufe idon tana ta saurare ko zata ji wani abu ko ta gani amman shiru, hakan yasa ta bude idon sai ta ga babu kowa a dakin. Ta fi karfin minti talatin a tsaye tana hawaye sai sauraren abun da ke mata yawo a zuciya yake, can kuma ya kai hannu ta dauki sarewar tana dubawa hawaye har basa bari ta ga komai daidai. Dukawa tai ta aje sarewar ta nufi inda take ganin Hijab ta dauka bata ko tsaya neman prayer mat ba ta yi sallah a kan tile, tana sallah tana hawaye har ta sallame, a lokacin da ta daga hannunta tai addu'a sai ta rasa abun da zata roka, sai kawai ta fashe da wani irin kuka sosai.
***
Muhseen na daf da shiga mota wayarsa dake aljihu tai ringing ciro wayar yai yana duba sunan mai kiran Shattima ne rubuce akan wayar, picking yai.
“Hello Shattima”
“Muhseen ya gida?”
“Alhamdulillah ya hakuri? Gobe zamu shigo Inshallah”
“Allah ya kai mu kana kusa da Fateema?”
“Eh ka yi sa'a yanzu zan bar gidan Mama Fulani”
“Ai kullum cikin sa'a na ke”
“Eh kan tun da ka samu wannan talkative din”
Muhseen ya fada da dariya sannan ya juya ya shiga cikin yana labartarwa Shattima yadda Aliyu ya fada masa sun tsinci Ataa. Kai tsaye ya nufi upstairs ya kwankwansa kofar dakin da Fadime take ciki sannan ya bude ya shiga, sai ya same ta zaune hawaye na sauko mata kamar wanda akai wa mutuwa. Mamaki ne ya rufe Muhseen sai ya sauke wayar daga kunnensa yana kallonta.
“Lafiya?”
Hade kukan kawai take bata iya cewa komai, hakan yasa shi tunanin ko ta sake losing memory ta ne?
“Yasmin?”
Nan ma bata amsa ba, domin jin take idan ta bude bakinta kuka ne zai fito.
“Lafiya?”
Shattima ya tambaya daga cikin wayar, sai Muhseen ya maida wayar kunnensa.
“Kuka take?”
“Kuka? Bata wayar”
Muhseen ya karasa inda take zaune ya mika mata wayar.
“Shattima zai yi magana da ke”
Kin karba tai sai hawaye take tana fisgar numfashi da karfi.
“Ba ta karba ba”
“Me akai mata?”
“I don't know”
“Kara mata a kunne”
Muhseen yayi yadda Shattima ya fada ya kai wayar saitin kunnenta ya kara mata.
“Fateema...”
Shattima ya kira sunanta a hankali tare da fatar ta amsa mishi sai ya ji shiru.
“Fateema talk to me, fada min matsalarki”
“Ai duk kai ne ka taba hannuna har sanyin ya cire gashi nan ya taba ban ji sanyi ba”
Bayan ta amayar masa da haka sai ta samu damar fashewa da irin kuka mai karfi wanda ya saka Mama Fulani da Aliyu da ke downstairs jin muryarta. Runtse ido Shattima yai kamar tana gabansa.
“Na shiga uku....”
Ya fada sannan ya yanke wayar ya sake kira sai Muhseen ya dauka wanda hakan yai daidai da shigowar Mama Fulani da kuma Aliyu har ma da Ataa saboda kukanta da suka ji.
“Ka hau online pls zan kira ta video call”
“Okay”
Ya sauke wayar yana kallon Mama Fulani dake tambayar ba'asi.
“Wallahi ban sani ba, ni ma dai na same ta tana kuka ne”
Mama Fulani ta shiga tanbayarta abun da akai mata amman Fadime ban da kuka babu abun da take, Aliyu dai na tsaye jikin kofa yana kallonta, Ataa ta matsa kusa da ita ta taba ta.
“Lafiya me ya faru? Ko wani ya mutu?”
Nan ma bata iya samawa ba sai kuka take sosai. Muhseen ya yi murmushi domin shi a shirita ya dauki kukanta ganin ta ki cewa komai sai kuka take.
“Kuna ganin wannan yarinyar kun san shagwababbiya ce, mai iya mata sai Allah sai Shattima, dan yanzu ta gama masa masifa a waya”
“To shi Shattima da kansa?”
Cewar Mama Fulani da dan mamaki, domin ta san waye Shattima.
“Kar dai ayi na Ataa da Aliyu”
Ataa ta yi dariya Aliyu kuma ya juya ya fice yana dan murmushi kadan. Mama Fulani ma ficewa tai tana murmushi ita da Ataa.Muhseem na kunna datansa kiran Shattima na shigowa ta Whatsapp video, picking yai sannan ya mikawa Fadime, sai ta ki karba.
“Bata karba ba”
“Aje mata”
“Kar ta fasa min IPhone fa”
“Za a siya maka wata, kai dai aje mata”
Murmushi yai ya aje mata wayar a saman hijabin da take sanye da shi, sannan ya juya ya fita, kamar fitarsa ake jira sai sakon sms ya shigo wayarsa ta line Shattima.
_Kawo mata ruwa pls_
Ya wara ido kamar Shattima ne a gabansa.
“To duk dai”
Ya fada sannan ya sauka kasa ya nufi kitchen, ruwa ya dauko mata tare da cup ya dawo dakin ya aje mata, har lokacin bata taba wayar ba, sai hawaye take ta yi. Shi dai be ce mata komai ba ya fice abunsa yana dariyarta.
“Fateema”
Shattima ya kirata, bata amsa ba kuma bata kallin wayarba, hakan yasa be samu damar ganin Fuskarta da kyau ba.
“Haba Fatee na, ki amsa min mana, ba kin san nima ina cikin damuwa ba? Amman na damu da taki damuwar fiye da tawa”
Nan ma shiru.
“Ba ki gode Allah da ya dawo miki da idonki ba? Ki ce Alhamdulillah wani na can yana neman idon be samu ba”
Maganar yai sai ta ji kamar ya kara takalo mata Wasim sai ta rushe da kuka.
“Wasim fa ya tafi wai ba zai dawo ba, wayyo zuciyata”
Ta fada daker tana kai hannu ta dafe zuciyar. At first he surprised ima ta ga Wasim din? Ina ya tafi?
“Ina kika ganshi?”
“Ya zo yanzu yayi min bankwana ya ce ba zan sake ganinsa ba”
“Better, kara ki rabu da mai kama da wannan aljanin ki huta ai”
Ya fada a ransa a fili kuma sai ya ce.
“Shi yace miki ba zai dawo ba?”
“Eh... ”
Ta labarta masa abun da ya faru daker sai wani sabon kukan ya taso mata. A yanzu kan sai ya ji kukanta ya fara damunsa, ba damuwa ta gundira ko gajiya da kukan ba, no damuwa na hawayen da take zubarwa kuma ta ba shi tausayi sosai domin ya san yadda abun yake, da ace mutun ya bar ka kara ya ace mutuwa yai hankali zai fi kwanciya kuma zuciya zata fi samun salama.
“Ba ni da sa'a, daman babu wanda ya tana cewa yana so na sai shi kuma shi ma ya tafi”
Sosai ya ji ransa ya bace saboda damuwar da take ciki, ta dayan bangaren kuma sai ya ji Wasim din ya bashi tausayi domin rabuwa da abun da kake so abu ne mai wahala balle Fadime duk wanda ya shaku da ita ba zai so rabuwa da ita ba. Ba dan yana so ba yai ta sauraren kukanta har ta iya wanda take jin ya samar mata da sallama.
“Fateema ki saurare ni kin ji”
Ta kalli wayar da idanuwanta da suka rine suka yi ja sosai saboda kuka, farar fatar idonta har ta soma ja kumatunta ma kamar an mareta.
“Share hawayenki ki sha ruwa zan fada miki wata magana”
Sai yai sa'a ta saka hijabin ta share hawayen ta goge hancinta sannan ta cire Hijabin gaba daya ta aje, ta hada uban gumi kamar ba dakin da ke da ac. Jingine wayar tai ta yadda zata iya kallonsa shi ma kuma zai iya ganinta, sannan ta bude ruwan ta zuba a kofi ta sha, ta aje tana wani irin mumfashi kamar ba ita ba, ita kanta bata san ranar da tai kuka irin wannan ba.
“Kin san cewa Babanki yana raye?”
Ta daga mishi kai.
“Mamanki ma haka”
Ta sake daga masa kai.
“Su kadai sun isa ki tuna da su ki ji farinciki domin na tabbatar a yanzu suna can suna jiran dawowarki, bayan su duk wani abun farinciki da zaki samu a duniyar nan a bayansu yake, lokuta da dama muna gina rayuwarta tare da mutanen da be zama lallai mu rayu da su har karshen rayuwarmu ba, wasu su kam shigo rayuwarmu saboda su bar mana tarihi, su tafi ko kuma mu tafi mu bar su, sai dai abun da yake da muhimmanci idan mum tuna, shi ne yadda mu ka yi rayuwa da su, na san yadda kike ji saboda na taba jin fiye da abun da kike ji a yanzu, ke daya kawai kika rasa, kuma ba mutuwa yai ba, ni kuma fa? Na rasa mata da yawa ciki har da Maijidda da ta rasu a yau, na rasa yayana, na kai matsayin da bana kallon mace na ji ina sonta saboda halin da na ke ciki, ta dayan bangaren kuma ga mahaifiya ba shi da lafiya, kullum fargabata kar na rasa shi, a haka na koyawa kaiwa yin murmushi a inda ya zama dole, na ko yi hakuri kuma ya yarda cewar wannan kaddarata ce, wani be isa ya canja min ba...”
Kalamansa ne suka soma tasiri a zuciyarta har ta saka hannunta ta soma share hawayenta.
“Wani lokacin rayuwa tana zuwa ga mutum kamar ya zabi kasancewa a haka, wani lokacin kuma sai ta zowa bawa kamar shi ka fi tsana a duniyar nan, fada min bayan rabuwa da Wasim a yanzu kin taba shiga wata damuwa babba kamar haka?”
Ta yi shiru tana tunani sai kuma ta girgiza masa kai alamar aa.
“To ki gode Allah jarrabawarki kadan ce, idan kin yi hakuri sai Allah ya baki wanda ya fi Wasim komai, kin ji?”
Ta daga masa kai kamar gaske, sai yai murmushi har cikin ransa yake jindadin yadda hankalinta ya fara kwantawa.
“Smile for me, na aje miki wani abu babba”
A maimakon tai dariya kamar yadda ya bukata sai ta fashe masa da kuka mai karfi.
“Wayyo Allah Wasim”
Shattima ya dafe kansa yana jin haushin Wasim for no reason, sai dai har ga Allah baya son hawayen da Fadime ke zubar da hawaye saboda shi, jin ta yake a wani matsayi da bangare na zuciyarsa.
ZAINAB POV.
Kuka tai har na fitar hankali sai a yanzu ta gane ashe bakinciki da kukan da tai a baya duk wasa ne yanzu na gaske ya zo. Sai da tai kukan da take jin ta cancanci salama sannan ta saurarawa kanta ta mike tsaye tana kallon inda Iya take kwance galala tana ta fadin sunayen mutanen da ta ci, tsaye Zainab tai tana ta kallonta ta rasa abun da za ta yi, idan ma ta dauke ta bata san inda zata kaita ba, ta kasa yarda mutanen da su kai mata inuwa su ka bata masauki a zuciyarsu da muhallinsu a yau su suke mata wa'adin barin garin Yola gaba dayansa.
“Miyasa zan zabtu da laifin da ba san lokacin da aka aikata shi ba? Why? Miyasa rayuwa zata min haka?”
Ta tambayi kanta tana karewa dakin kallo kamar bakonta, duk abun da take Wasim na tsaye bakin kofar dakin yana kallonta, sake faduwa kasa tana shafa jikinta.
“Miyasa abubuwan da ban aikata ba za su shafe ni?”
“Saboda ba ki zabi uwa ba, kuma ba ki za bi uba ba, haka ma ba ki zabi halin da kike ciki a yanzu ba, shin hakan be isa ya karantar ke cewar ba mu isa mu zabi yadda rayuwarmu zata kasance ba? Balle mutanen cikinta?”
A firgice ta juyo ta kalleshi.
“Banbanci rayuwata da taki kadan ne, dukan mu muna ciki wani hali”
Yana maganar hawaye na sauko masa kamar ita.
“Ba zaka taba gane yadda na ke ji ba, na rasa komai na farinciki, rayuwar kunci ta bude min kofa, ina son na mutu a yanzu mutuwa kawai na ke so...”
Ta karasa cikin kuka tana kallon hannayenta, sai ya karaso cikin dakin kusa da ita yana kallon Iya.
“Har yanzu kina da sauran farinciki, na tabbatar kina da wasu dangin da za su ba ki farinciki a rayuwarki, wata kila nan kusa ki manta da komai”
Ya saka hannunsa ya tare hawayen idonsa.
“Zan tafi da ita, amman hakan ba zai hana ta mutuwa ba domin an mata aike ne, ke kuma a duk lokacin da kika shirya muna maraba da ke...”
“Kenan mutuwa za ta yi? Shikenan na rasa kowa? Ba zan iya rayuwa ni kadai ba”
Hannayensa ya saka ya dafa kafadunta.
“Ba zan barki ki yi rayuwa ke kadai ba, zan kasance tare da ke, kuma na miki alkawarin farinciki”
Ya fada cike da kwarin guiwa saboda yana jin ta fishi shiga mawuyacin hali. Fashewa tai da kuka tana kallon Iya.
“Komai ta lalace ina sonta, dan Allah karku kasheta, ita kadai ta rage min a yanzu, komai halin da ta shiga ina son ganinta bana son na rasa na rasa komai a yanzu”
Masauki yai mata a faffadan kirjinsa, wanda hakan ya bata damar tausayawa kanta ta fashe da sabon kuka tana jin kamar ta hade zuciya ta mutu ta hutu. Shi kuma ya lumshe ido yana sauraren kukanta dake shiga har cikin ransa yana jin kukanta kamar Fadime da ya baro tana nata kukan!
***
A lokacin da Ammy ta dawo gida da tunani kala kala da kuma mamakin da bakinciki a lokaci daya na abun da ya faru da Iya, sai ta tararda Masarautar da wani sabon labari na rashin lafiyar Jurry da kuma Hajiya Babba. Tufafin jikinta kawai ta canja ta shiga bangaren Mai Martaba ta sanar masa halin da ake ciki, sannan ta fito ta nufi asibitin. Ko da ta isa ta samu Kausar da Karima a dakin Hajiya Babba kuma tana kwana sakamakon allurar bachin da akai mata, saboda yawan maganganun da take na abubuwan da ta aikata, Ammy bata san komai ba akan ciwon kuma wani be labarta mata abubuwan da Hajiya Babba take ta fadaa gadon asibitin ba, sai dai a ta yi mamakin ganin babu family ko daga daga bangaren Hajiya Babba haka ma daga bangaren Mai Martaba sai yayanta kawai, su ma suna ta soke kai kamar ba son kallonta.
“Jekadiya tace Juwairiyya ma ba Lafiya, ita a ina aka kaita?”
“Kanta ne yake ciwo, ban san inda aka kaita ba”
Kausar ta amsa cike da damuwa, Ammy dai bata sake cewa komai ba sai kallon Hajiya Talatu take da baki ya juye gefe daya.
“Anya babu hawan jini na ga shi ke saka haka?”
Kamin su amsa mata Hajiya Babba ta fara motsawa ta juyo saitin Ammy dake zaune akan kujera, ta dade tana murza idon sannan ta bude ta sauke su akan Ammy dake ta mata sannu, Kausar da Karima kam hankalinsu ya mugun tashin, da sauri Karima ya nufi kofa tana fadin.
“Bari na kira likita”
Cikin hanzari ta fice zuwa kiran likitan, so take ya sake mata allurra tai bachi har sai Ammy ta fita.
_________
Ina mata matan kwalisa Matan da suka ansa sunansu na Mata? Ina wadanda ke cewa mun yi mun yi bamu ga amfaninshiba? Hmmm to ku zo ga Yar gidan Maifata ta zo maku da Al ajabu, dan tsugunno, gumba da tsimi da Zuma daban daban, maganin sanyi na maza da Mata. Ga kuma garurruka irinsu mallakau sabuzu kuwa, sa bahaushe saibi, Dan hubbare kafi malam aiki, ke kadai ke da miji, dahuwar kaza, tattabara, ciccibi da dai sauransu. Ba anan kayanmu suka tsaya ba, muna hadin amare na musamman turaren sutura turaren tsugunno turaren wanka da na daki da na jiki duka 4amare nasu na musamman ne, amma ga tsuhuwar da ke son komawa yarinya itama zata iya zuwa ahadata kai abundai sai wanda ya gani, dan haka karkubari abaku labari, domin neman karin bayani zaku iua nemana ta wannan number 09029891757 ko 08169311410, muna aikawa ko'ina a fadin kasar nan har waje kasar nan muna aika kaya.
Address: Nasarawa Samaru Area gurin masallacin mai sola Gusau Zamfara state Nigeria.
60
*Khadeeja Candy*
Littafin nan na kudi ne biya ki karanta cikin aminci. Pay 300 to 2451879008 Hadiza Abubakar Zenith bank, then send the evidence via 08036126660*
Ammy ta dawo gida cike da tunani kala kala, domin babu abun da Hajiya Babba bata labarta mata ba na abun da ta aika, a lokacin ne Ammy ta kara gasgata abun da Fadime ta fada, Shattima kadai ta labarwa abun da ya faru, sai Jekadiya ba ta sanarwa kowa ba saboda bata son ta sanarwa Baba Waziri a yanzu da yake cikin alhinin mutuwar yarsa. Sai dai ta kwana da tunanin abun a ranta tunanin sai ya zame mata kala biyu, ga na Iya ga na Hajiya Babba, sai ta ji tausayin Mai Martaba ya kara kamata da kuma yaranta da ake son ganin bayansu saboda abun duniya da za a mutu a bari. Haka