Showing 195001 words to 198000 words out of 286946 words

Chapter 66 - Fulani Book 1 Hausa Novel Complete

20 Dec 2024

938

zamu koya maka hankali”

“Gafarce ni dan Allah ayi min afuwa”

“Shiga mota muje”

“Okay bari na fadawa Yayata”

Ya juya da sauri ya koma cikin gidan, ko da ya shiga ya samu Anti Rabi a tsaye dafe da kirji tana sauraren abun da zai fada mata domin hankalinta be bata sallamar Allah da Annabi ake  musu ba.

“Su waye?”

“Daga masarauta suke”

Ta dafe kirji tana zaro ido.

“Masarauta kuma? Me kai? Ko ka sake zuwa ne bayan abubuwan nan da suka faru?”

“Wallahi ban sake ba, ni ko hanyar masarautar ban sake bi ba, amman da yanzu zan je na ji dalilin kiran”

“Aa karka je, baka sani ba ko wani abun ne aka shirya maka”

“Idan ban je ba ai wulakanci za su min, kara naje na ji ko minene dai”

“Allah ya tsare, muna ta zancensu aje suna kan hanya da wani kiran, Allah yasa wannan kiran alheri ne, ya tsare”

“Ameen”

Ya amsa sannan ya shiga dakinsa ya canja tufafin jikinsa daga karamin wando da vest zuwa dogon wando ta jallabiya. Ya fito zuwa waje, har bakin kofar waje Anti ta bishi tana kallo tana jifarsa da addu'a kariya. Daidaikun mutanen da suke waje ne suka rika binsa da kallon ganin dogarawan sanye da tufafi har su uku kuma ga sy da mota mai kyau sun saka Sardauna a gaba. Sai da yai addu'a sannan ya shiga motar suma suka shiga mai tukin yai ribas suka juya. Ba su faka a ko'ina ba sai cikin masarautar, sai dai hankalin Sardauna ya dan kwanta ganin a bangaren Ammy suka faka ba bangaren Hajiya ba. A cikin motar suka bar shi har sai da dayan ya fita ya shiga ciki ya fito sannan ya bude masa motar.

“Fito”

Sardauna ya fito da tunani kala kala, sai dai zuciyarsa ta fi raya masa cewar Ammy zata masa tambayoyi ne akan abubuwan da suka faru, ko kuma Nana ce ta saka a dauko shi saboda tana son ganinsa wata kila ita ma ta yi missing dinsa kamar yadda yai nata. A dakin aje baki na musamman aka kaishi na bangaren Ammy, har ya zauna saman kujera sai kuma wata zuciyar ta raya masa ya zauna kasa kamar ko wane talaka. Cikin mintunan da ba su fi talatin ba hadimai suka jera masa kayan marmari ta soyayen namam kaza da na rago ga farfesun kayan ciki, ga jalof ta ji kayan lambu da kayan ciki sai kamshi take, a gafe daya kuma ga kayan sanyi da plates an aje masa.

“Ammy ta ci ka ci abinci kamin ta fito”

Dayat hadimar ta fada sannan suka fice tare da sauran, at first ji yai kamar mafarki yake, tun a kawo shi falon dake cike da kayan alatu da akai kadai ya isa ya sanar masa cewar kiran alheri ne ake masa, balle kuma yanzu da aka kawata zuciyarsa da abubuwan da take so, baki yai arba da abubuwan da suka dade ba su ga juna ba.

“Ammy suke nufi ko Nana dai?”

Ta tambaya kansa cike da kwankwanto, har ga Allah yana son duka abubuwan da aka jera masa sai dai a karon farko ya samu kansa da kasa taba komai, a tunaninsa a zuwa yanzu ya kamata ya rika kawar da kai akan wasu abubuwan musamman wadanda za su zubar masa da kima. Gorar ruwan kawai ya bude ya sha, shi ma saboda ya samu ya jika makoshinsa ne. Ya kusan awa daya a dakin sannan aka turo kofar dakin wata hadima ce a gaba wanda ta rikewa Ammy kofar ta shigo ta zauna a kujerar dake fuskantar Sardauna. Cikin natsuwa Ammy ta zauna tana kallon Sardauna, wanda ya sadda kai kasa ya kasa dagowa ya kalleta, sai kokarin risinawa yai yana mika mata gaisuwa irin gaisuwar da be taba yi ma wani ba.

“Lafiya Kalau”

Ammy ta amsa masa da kanta tana dagawa Hadimar dake kokarin amsawa a madadinta.

“Je ki kira min Nana”

“An gama ranki ya dade”

Hadimar ta juya da sauri ta fice, Ammy ta kalli Sardauna da duba irin na tsanaki ta ce

“Ya sunanka ma?”

“Ahmad Abubakar, amman anfi sanina da Sardauna Hajiya”

Ya amsa mata da sauri yana jin faduwar gaban da ba ta tsoro ko shakka ba face kwarjini da jin kunyar Ammy.

“Yayi kyau, Nana na fada mana abun da kai, kuma na jidadi sosai na yaba”

Ammy ta fada sai kuma yai shiru tana kara sanar da shi isa da izza irin ta matan sarakuna.

“Akwai aikin da kake a yanzu?”

Kamin ya bata amsa Nana ta turo kofar dakin ta shigo, wani irin jan numfashi tai tana zaro da sauri taje kusa da Ammy ta zauna can kuma ta ji zaman be mata ba ta rumgume Ammy tana jin kamar ta je ta rumgume Sardauna, bata tabbatar ta yi missing dinsa sosa ba sai a yau da tai arba da fuskarsa.

“Aa bana aikin komai a yanzu gaskiya”

Ammy ta yi shiru tana karantar natsuwarsa.

“Ka yi karatu?”

“Eh na yi diploma”

“Kana son ka cigaba?”

“Ina so ranki ya dade, burina kenan”

After some sec Ammy ta ce.

“Wace makaranta kake so? Ko kuma aiki kake so?”

“Idan zan samu karatun na fi son sa gaskiya, kuma ba ni da zabi duk inda na samu damar cigaba da karatu zan yi farinciki”

“Zaka iya karatu a waje?”

Sardauna be san lokacin da ya dago ya kalli Ammy ba, sai kuma ya kalli Nana wanda ita ma kallon Ammy take da mamaki.

“Zazzzazzz.....zan iya”

“To zamu bincika maka best universities da suke waje, inshallah zam dauki nauyin karatunka sai ka kawo takardunka da wuri”

Da sauri Nana ta rumgume Ammy tana murna, Sardauna kam mantawa yai ya mike tsaye sai kuma ya fadi zaune kamar ta rude, i cant believe ba mafarki yake ba. Take a gurin yai ma Allah sujada godiya ya dago da hawaye a fuskarsa yana kallon Ammy.

“Na gode na gode na gode, Wallahi ban san abun da zan fada ba zan san iya addu'ar da zan miki ba, na gode Allah ya biyaki da aljanna”

“Ni ma na gode, ka cancanci komai daga garemu, bayan shi akwai abun da kake so?”

“Kin gama min komai Hajiya”

Sardauna na fada har lokacin idonsa na cike da hawaye. Nana ta yi karaf tace.

“Aa Ammy, ba ki gama ba, a gidan Yayarsa yake zaune kuma gidan duk ya lalace, aAmmy dan Allah ki yi wani abu”

“Wannan kuma za a sanarwa Mai Martaba, na san zai yi wani abu akai inshallah”

Nana ta sake rumgume ta tana murna.

“Thank You so much Ammy na gode”

Ammy ta yi murmushi, Sardauna ma murmushi yake yana kallon Ammy yana jin kamar ace yana da damar da zai rumgume ta saboda murna da jindadin abun da tai masa.


***

Kamar yadda suka tsara washe garin ranar Bappa da Kawu Dan iroro suka shirya suka tafi Katsina, bayan mota ta sauke su suka tari napep suka fada mata inda zata kaisu, wato unguwar su Shattima har ba kin gate din gidan Mai Napep din ya sauke su, sai da suka kira Shattima ya sanar musu yana cikin gidan sannan suka sallami mai napep, suna waje tsaye mai gadin ya bude gate din ya shiga da su, shi yai musu iso har cikin falon Shattima, kallon kallo Bappa da kawu suka rika da ma juna kamin su koma kallon tsarin falon da uban dukiyar da aka zuba.
Shattima ya sauko sanye da manyan kaya shadda da hula sai kamshi yake zubawa kamar wani sabon ango, da kansa ya dauko musu lemu sannan yai musu izinin zaman kan kujerar tsabanin kasa da suke zaune. Kalamai na natsuwa da mutuntawa yake musu duk tambayar da suka masa sai ya basu amsa, daga karshe ya kira Ammy video call ya ce ta saka akaiwa Fadime saboda kawai su yarda da shi kuma su samu natsuwa. Ganin Fadime a video call din ya tabbatarwa su Bappa gaskiyarsa, tana jin muryar Bappa ta hau murna tana jindadin jin muryar mahaifinta duk da kasancewar bata ganinsa hakuri ta hau bashi tana ta kuka da hawaye sai fadin take ya zo ya dauke ta.
Bayan sun gama Shattima ya karba yana ta kallon fuskarta ba tare da yace mata komai ba, sannan ya kashe wayar. Da kansa ya tabbatar musu cewar zai siye musu tickets na jirgi na zuwa can Yola din tare da shi, har waje ya rakosu ya saka direbansa ta kaisu har garin Bandalo bayan yayi musu kyauta 100k.

Cikin far'a da jindadi suka isa gida suna da godiya ta sakawa Shattima albarka da yaba halinsa. Tun a daren ranar Shattima ya siya musu tickets kuma ya kira Bappa ya fada masa cewar ya shirya da safe zai aiko direbansa ya dauke su, washe gari tun 6am direban Shattima ya kama hanyar zuwa garin Bandalo dan dauko su Bappa ko da ya isa har sun shirya, suka shiga motar ya juyo da su zuwa Katsina, maimakon a wuce da su airport sai da aka fara biyawa da su gidan Shattima suka karya da lafiyayen abincin da yai musu order sannan suka shiga wata motar ta alfarma tare da shi zuwa airport.
Ba su wuce 30 min da isa airport din ba jirginsu ya tashi zuwa Yola...



FALMATA POV.

Bata yarda da gaske auren za a mata ba sai da aka saka ta lalle gidansu ya cika da mutanen na bangaren Baba da Mamanta, sai dai duk wanda ya ganta ya kuma san yanayinta ya san bata maraba da auren ganin irin damuwar da ta shiga wanda ta haddasa mata rashin iya cin abinci, sai yawan kuka da tagumi, idan aka tambaye ta tace babu komai bata, babu yadda kanen mahaifiyarta ba su yi ba, akan ta fada musu idan bata son aure amman ta ki tace komai, Tumba kam sai karew take har da fadin wai ita ta kawo shi da kanta tace tana sonsa. Kudin da ya bata yace a siya mata kaya sai ta siyo mta atamfar roba 5 sai talkama da yan tarkace kamar budurwar kauye.
Tana jin yadda yan uwan suke labarin gyara gidan da suke je suka gani wanda za a kaita sai yabawa suke suna fadar ya gyara mata abunta ba laifi, suna ta saka masa albarka saboda yace baya son komai, gashi yayi duk wani kokari da ake na al'ada daidai gwargwado, sai dai abun da ya bawa kowa mamaki cewar da yai baya son tai walima a nan sai washe garin ranar da ta tare, wani abun da ya kara bawa Falmata haushi da bakinciki ko ganinsa sau daya tai be sake zuwa ba, sai dai yace yana gaisheta. Sai wasu mutanen da suke zuwa da sunan danginsa kana ganinsu ka san su ma ya ku bayi ne, masu neman a gurin Allah.

Ranar yau ta kama friday ranar da ake daurin aurenta, irin ranar da wasu mata sa'o'in suke jira suke dakon zuwanta, sai dai ita a gareta ta zama kamar ranar mutuwa ce, tana jinta kamar ranar da ta fi ko wace rana bakinciki ce a gurinta, tana jin cewar zata bar wata wahalar ne ta fuskanci wata, taya zata yi rayuwa da tsoho? Samun kanta tai da kuka tun safe ta kasa karyawa da komai har sai da Tumba ta jata gefe tana mata masifa.

“Wai Falmata so kike ace auren dole aka miki ne? So kike a fara zaginmu ni da mahaifinki? Me ke damunki wai? Kina ta kuka kamar wance aka cewa ga mutuwa? Aure ai abun so ne, kamata tai ki yi murna ki yi farinciki Allah ya kaiki gaba, kuma wata kila ma b dadewa zaki ba ya mutu tun da ya tsufa, idan kika tonawa babanki asiri ke da shi ne ni ba ruwana”

Jin haka yasa Falmata ta dago ta kalli Tumba.

“Umma da gaske auren min zaku min?”

“Gashi kina gani anjima za a daura aure? Ko so kike a fasa? Tsab Malam zai iya tsine miki Wallahi”

Falmata ta share hawayenta wasu na sauko mata ta bar Tumba a gurin tsaye ta nufi dakinsu, guri ta samu can karshen shimfidarsu ta kwanta tana ta hawayen da bata san ta ina suke zo mata ba, miyasa ranar yau zata zame mata haka? Why rayuwa ta zabi jefata a irin wannan halin? Me ta aikata duniya ta mata juyin masa? Hannayenta ta saka ta rumgume kirjinta tana jin wani irin ciwon kirji da ba zata iya misaltawa ba.
Ana saukowa daga sallah jumma'a aka daura aurenta, yan daurin aure na dawowa gida ya cika da guda sai ta rufe ido ta dukule cikin hijabi tana amsa sallamar da hawaye ke mata, Daman abun da take tsoron jin kenan gudar aurenta gudar da take jin sautin mutuwa zai fi sosuwa a kunnenta fiye da ita. A dolen dole aka cilas mata yin wanka ta saka sabon tufafinta, da mayafi aka kira wata local mai makeup tai mata makeup aka bata 500.
Misalim 5 na yamma tana zaune a dakin ta saka abinci a gaba ta kasa ci, kawarta Khadija ta shigo, tun daga bakin kofar Khadija ta fashe da kuka, Falmata ta fara nata kukan tun tana yi a hankali har ya ci karfinta, Khadija ta zo ta rumgume ta, tana jin kamar ace akwai abun da zata iya yi ta hana auren domin Falmata ta labarta mata komai, gashi bata son rabuwa da kawarta.

“Ki yi hakuri kin ji wata rana sai labari”

Khadija ta fada tana rike da hannayen Falmata, suna ta kuka aka rasa mai rarrashin wani, sosai Falmata ta ji sanyi har ta samu sha zobon da aka aje mata, sai ta kwanta jikin Khadija tana jin kamar ace mahaifiyarta na raye.
Abun da Falmata bata sani ba, shi ne kuka be shirya raga mata ba a wannan ranar da ya kamata ace ta zame mata ta farinciki amman ta zo mata a haka, cikin kuka da bakinciki.
A lokacin da motoci su kai layi bakin titin unguwar ne mutane suka fara tambayar diyar waye za a dauka, Falmata kam tana cikin dakin Baba da Tumba sai nasiha suke mata tana kuka, tun tana kukan na hankali har ta fara bawa mutane tausayi, ana kokarin fitar da ita daga gidan tana riko mutane tana kuka, har sai da Tumba ta saka hijabinta ta kama hannunta suka fita tare, dayan hannunta na rike da kawarta Khadija. Tafiya kawai take tana jefa kafarta a duk inda ta samu tana kukan da babu sauti har suka isa bakin titin yaran unguwar suna biye da su da sauran yan biki suna ta guda, abun ka da Amarya mai farin jini.
A lokacin da suka isa bakin titi sai kallo ya koma sama, Tumba ta saki ido tana kallon mayan motocin da aka jera na alfarma har kusan guda goma sha biyu.

“Jama'a ina motar mu?”

Ta tambaya gabanta na faduwa, Sai yan bikon su ka ce

“Su ne nan ai, amman ga motar da Amarya zata shiga can”

Sun nuna wata kafirar mota mai kyau fara sol kana ganinta ka ga sabuwar mota, a take kallo ya koma sama, daga Tumba har yan biki suka koma mamaki, ba ma kamar ita ta take ganin kamar mafarki take. Fitilar hannunta ta haska fuskar matar da ita dan kara tabbatarwa.

“To”

Ta fada cikin kunya, da tsoro, wata zuciyar na raya mata cewar wata kila arosu yai ko kuma abokansa ne manyan mutane suka yi masa kara. Kamar hawainiya haka ta nufi motar da aka bude musu ta shiga sannan aka shigar da Falmata da kawarta Khadija wanda ita ma mamaki ya kusa kashe ta.

“Shiyasa Tumba ta dage sai an yi, ashe saboda ta san mai kudi ne ta ci duniya”

Khadija ta raya a ranta, haka aka cika motocin har wadanda ba da su ba a bikin sun samu gurin shiga, unguwa ta dauka cewar Falmata ta auri wani hamshakin mai kudi, wasu na fadar wai ai hakurin da tai ne wasu kuma su ce Allah ya sa na kwarai ne. Tumba kam ciki ya duri ruwa ta rasa wane tunani zata fara yi. Ita dai tana ciki motar ana tafiya har suka shiga wata sabuwar unguwa ta manyan mutane, a zatonta wucewa za ayi, ba ta ankaro ba ta ga an kunna kai cikin wani katon gida. Mai bala'in kyau da daukar hankali, fentin gidan fari sol ga haske kamar rana, idan sama ne mai hawa daya an kawata ko'ina da fulawoyi.

“Kai malam gidan Malam Mu'azu za ku kai mu fa? Ya muka ga nan kuma?”

Tumba ta sauko daga motar tana fadar haka, gabanta sai faduwa yake.

“Nan ne gidan ai Inna”

Daga daga cikin matan da suka zo biko ta amsa ta.

“Ke Ta dela wannan ne gidan da kuka he kuka gani?”

Wacce aka kira da Dela ta girgiza kai.

“Aa ba wannan ba ne”

“Inna an canja wacan ne shiyasa, daman saboda ga a yi ma wannan fenti ba ne yasa aka ce a akaita can, sai gashi kuma an gama kamin lokacin”

Numfashim Tumba ne ya fara rawa ta ja kafa kamar wata marar lakka suka doshi cikin gidan dake ta kamshin turare. Bata raina kamta ba sai da suka nas kafarsu cikin falon da za a iya kira da aljannar duniya. Sanyi ac da katon tv ga manyan kujeru farare masu kawata ido da rudarda makiya suna musu marhabun...
48

*Littafin nan na kudi ne biya ki karanta cikin aminci. Pay 300 to 2451879008 Hadiza Abubakar Zenith bank, then send the evidence via 08036126660*


Tumba ta ja da baya da sauri tana rike da hannun Falmata.

“Aa indai Malam Mu'azu ne da aka daurawa aure dazun tare da Falmata ba wannan ne gidan ba”

“Inna nan ne gidan fa”

“Aa”

Tumba ta jata ta tsaya a waje ita ala dole ba gidan ba ne, domin a iya ganinta tsohon da aka aurawa Falmata be da tarin wannan arzikin, mutumen da yake kamar maroki ma taya ya samu wannan uban arzikin kato gida haka komai a tsare falon ma a kawatashi kamar na yar minister, sai da ta gama kallon ko'ina harabar gidan. Sannan ta ciro wayarta ta kira line Baba, wayar bata dade tana ringing ba ya dauka yana sallama. Ko amsawa ba taba tsaya yi ba ta ce.

“Malam ka kira mutumen ka tambaye shi ina za a kai Falmata, motocin da ya aiko sun dauko mu sun kawo mu wani katon gida da ni

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login