Showing 255001 words to 258000 words out of 286946 words
sai ya bude mata ido ya watsa mata ruwan hannunsa.
“Yarinya yarinya... Mai Martaba yayi mata kyau”
Kyalkyalewa tai da dariya kamar ba ita ba, shi kansa be san lokacin da murmushi ya bayyana a kumatunsa, murmushin da ya bayyana fararen hakoransa saboda farincikin da ya gani a fuskarta.
“Ko ba haka ba ne?”
“Haka ne”
Ta fada tana dariya, sai ya mika hannunsa baya ya dauko sabuwar waya cikin kwali ya mika mata.
“Ga waya na siya miki, kin ga ba zan yi kewarki sosai ba, sai na rika kiranki da ita”
Hannu biyu tana ta karba tana kara fito da ido waje tsabar mamaki.
“Ni ni Fadime? Waya? Wanda ake shafe shafe touching ko?”
“Yeah Pretty”
Sai ta zauna gabansa cikin wani irin farinciki marar misaltuwa ta fara kokawar bude kwalin wayar.
“Handsome man, amman Wallahi ka biyani ni ma na shigo gari, amman boye ta zan yi ba zan bari Bappa ya gani ba”
“Ba za ki daina halinki ba ko?”
Sai tai masa gwalo kadan.
“Wasa na ke zan nuna masa, sai na ce amman kar ya karbe min ko? Zaka kira ni kuma?”
“Me zai hana ba dole na ji muryar Fatee na ba”
Ta yi dariya sannan ta mika masa.
“Kunna min ka nuna min yadda zan yi tabe tabe”
Yayi murmushi.
“Tabe tabe dai”
“To shafe shafe”
Ya sake yin murmushi.
“To touching touching”
Ta fada da dariya, karba yai ya kunna wayar ya ciro line mtn ya saka mata a wayar sannan ya soma nuna mata inda zata taba, be ko gama ba ta ce.
“Na ma gane komai har wanda baka nuna min ba, ba ni wayar”
A garin karba wayar ta fashi ta tsaga daga kasa, wani irin turo baki gaba Fadime tai.
“Ka gani ko? Daman ba da zuciya daya ka ba ni ba”
Wannan karon dariya yai, daman ana bada abu fiye da zuciya daya.
“Da zuciya nawa na baki?”
“Biyu mana, dayar tana cewa a bawa ni dayar na hanawa”
Camera ta shiga daman ta fi kwarewa can a lokacin da yake nuna mata, daukarsa ta rika yi hoto, shi dai be ce mata komai ba har tai mai isarta ta gama ta shiga daukar falon da hotunan Ammy da suke lake falo, duk abun da take idonsa na kanta wani irin abu yake ji kamar ya kamata ya rumgume.
“Ki je ki shirya karfe daya za ku tafi”
“Ba da kai ba?”
Ya daga mata kai alamar eh. Sai ta bata fuska
“Miyasa?”
Kafadunsa ya daga mata alamar shi ma be sani ba, domin ya so ya rakata sai dai yana jin kamar indan suka tafi tare ya baro ta zai fi shiga damuwa fiye da yai mata sallama a nan, duk da yana da tabbacin bayan tafiyarsa zata sake dawowa rayuwarsa. Dawowa tai kusa da shi ta zauna tana ta kallonsa, sai kuma ta ji kewarsa ta kama ta.
“Ni daman ba ni da sa'a sai na sabu da mutum sai ya tafi ya bar ni”
“Amman ai ke zaki tafi ki bar ni, ni da kuka ba ke ba”
Ya fada da fuskar zolaya.
“Dan Allah ka rika kirana kullum ka ji”
“Dolena ai Pretty”
Bata yarda ba da shi za a je ba har sai da lokacin tafiyar yai, ta ga Shattima ya kirata daman ya bata agogon da ya taba bata lokacin da za su yi wacan lafiyar da su Bappa, a nan ta saka masa kuka tana jin kewarsa.
“No no ki daina damuwa zan kawo miki ziyara ai?”
“Da gaske?”
“I promise”
Da kasa ya kama saka hannunsa ya share mata hawayena.
“Dan Allah ka zo ka ji?”
“Kin fara missing dina kenan”
“Kuma kullun ka kira ni karka gaji”
Ya daga mata kai tana jin kamar ya hana ta zuwa, da farko be yi niyar rakata airport ba sai dai ganin yadda take kuka yasa ya rakata airport din, da katuwar jakar kayan da ya saka ka siya mata masu tsada. Motarsa dabam ya shiga ita kuma ta shiga motar su Baba Waziri da mutanen biyu da suke tare da shi, suna isa airport ko minti talatin ba su ba jirginsu ya daga zuwa Katsina. Kusan duk wanda be saba shiga Jirgi ba zaka tarar yana jin tsoro a shigarsa ta farko da ta biyu har zuwa lokacin da zai saba, amman ban da Fadime ko wa can zuwan da su kai da Mama Fulani bata wani tsorata ba, kawai saboda tana cikin damuwa ne yasa bata maida hankali sosai a kai tafiyar ba, yanzu kan har dadi take ji a zaunar da ita kusa da window jirgin tana hangen waje, ta soma daukar hoto da wayarta har mutanen da ke cikin jirgin dauka take. Suna sauka Katsina zuciyarta ta fara kewar Shattima ta dayan bangaren kuma tana mata zillon na son ganin Bappa da Innarta. Ko da suka sauka airport din Motocin Mai Martaba na harabar da ake aje mota suna jiransu, a Front seat ta zauna mutumen da ke tare da Baba Waziri ya shiga gidan baya, cikin motar ma tana ta daukar reban da kanta. Masarautar Katsina suka sauka akai musu tarba ta ta musamman, sai da suka ci suka sha wannan aka hada su da wata tawagar da zata yi musu rakiya har garin Bandalo. Kamin a isa garin Fadime har ta ayyana yadda zata rika kallon kowa, domin tana jin kamar ta fi kowa dace saboda ta je Masarautar Garuk, da ta Yola haka ma Katsina. Tun daga shigowar manyan motocin guda hudu mutanen garin suka fara kallo suna mamaki wane babban mutum ne ya shigo garin, ita tai ta kwantance hanyar da za abi a isa gidansu a lokacin da ta suka shigo garin Bandalo. Kamar taron kasuwa haka kaiwa kofar gidan Bappa da fifi ana kallon manyan mutane da mamakin su waye a ciki, wasu dai sai fadin suke Fadime ta janyo musu da mata rigimar wasu kuma na fadi daga Katsina aka aiko a tafi da Bappa kowa dai da abunda yake fada, dogaran dake tare da Baba Waziri ne suka fita suka isa bakin kofar gidan Bappa suna masa sallama irin wanda dogarai suke yi a kofar gidan talaka. Inna ce ta fito jiki na rawa tana amsawa domin Bappa yana gurin sana'arsa a lokacin, daman abu ne mai wahala ka tararda shi a gida irin wannan lokacin. Fadime na ganin Inna ta yi saurin bude motar ta fito, Inna ma tsaye tai tana kallonta sai hankalinta ya bar gurin dogarawan da take musu bayanin cewar Bappa ba ya gida.
“Inna”
Fadime ta fada tana fashewa da kuka, sai Inna ta rufe baki jikinta na rawa kamar zata fadi a gurin, da gudu Fadime ta je ta rumgume ta, jamar'ar gari suka hau leke kowa na mamaki, kuka sosai Inna da Fadime suka yi, sannan ta rika hannu Fadime suka shiga gida, makota da yan uwa kusa ne suka fara shigowa suna mata barka, wani makocinsu ne ya hau babur dinsa ya isa har inda Bappa yake ya sanar masa dawowar Fadime da kuma motacin da aka shigo garin da su tare da ita, take Bappa ya rufe shagonsa ya hau Babur din mutanen suka kamo hanyar dawowa gida da tunani kala kala a ransa, shi dai tsoro ya fi kama shi sama a lokacin da yai arba da manyan motocin, fargabarsa daya kar ace wata jamgwal din ce Fadime ta sake janyo musu. Sai a lokacin ne Baba Waziri ya fito daga motar bayan an gabatar masa da Bappa a matsayin mahaifin Fadime, Bappa faduwa yai kasa yana kwasar gaisuwa jikinsa sai rawa yake, ko mutumen birni ya yaji a gaban sarki balle na kauye, da sauri fadawan da suke tare da Waziri suka zo suna gyara masa rigarsa suna masa kirari, gaisawa yai da Bappa sannan ya gabatar masa da kansa sannan ya isar masa da sakon Mai Martaba na kudi da kuma gaisuwa, daga bisani kuma ya gabatar masa da albishir din Shattima na gidanda ya siya masa a Kt, daya daga cikin mutanen da suke tare da Wazari ne suka kira Shattima yai magana da Bappa a waya sannan ya kara tabbatarsa masa da abun da Baba Waziri ya fada, kuma ya fada masa cewar idan ya kimtsa yai masa magana a waya zai turo Ra'ees ya dauke shi ya kai shi har inda gidan ya ke kuma ya hannanta masa komai, Bappa sai ya rasa bakin magana ko godiya sai kuka, yana ganin komai kamar a mafarki.
_________
Ina mata matan kwalisa Matan da suka ansa sunansu na Mata? Ina wadanda ke cewa mun yi mun yi bamu ga amfaninshiba? Hmmm to ku zo ga Yar gidan Maifata ta zo maku da Al ajabu, dan tsugunno, gumba da tsimi da Zuma daban daban, maganin sanyi na maza da Mata. Ga kuma garurruka irinsu mallakau sabuzu kuwa, sa bahaushe saibi, Dan hubbare kafi malam aiki, ke kadai ke da miji, dahuwar kaza, tattabara, ciccibi da dai sauransu. Ba anan kayanmu suka tsaya ba, muna hadin amare na musamman turaren sutura turaren tsugunno turaren wanka da na daki da na jiki duka 4amare nasu na musamman ne, amma ga tsuhuwar da ke son komawa yarinya itama zata iya zuwa ahadata kai abundai sai wanda ya gani, dan haka karkubari abaku labari, domin neman karin bayani zaku iua nemana ta wannan number 09029891757 ko 08169311410, muna aikawa ko'ina a fadin kasar nan har waje kasar nan muna aika kaya.
Address: Nasarawa Samaru Area gurin masallacin mai sola Gusau Zamfara state Nigeria.
62
*Khadeeja Candy*
*Littafin nan na kudi ne biya ki karanta cikin aminci. Pay 300 to 2451879008 Hadiza Abubakar Zenith bank, then send the evidence via 08036126660*
Kusan duk wanda yake shakiki a masarautar kuma yake da alaka da Hajiya Babba ko Ammy da Mai Martaba ya jin abun da Hajiya Babba ta aikata, an fi jin nata sama da na Iya, domin ita take labarwa mutane abun da ta aikata da kanta, ga bakinta a juye gefe daya abun har ya fara tana kafarta da hannunta domin bata iya amfani da bangarenta na dama hagun ma sai ta dade tana tunani kamin ta iya mika hannu ta karbi abu ko ta rike, and when ever tana cin wani abu a bakinta ko da abinci ne sai ya zuba ta gafen bakinta ta zama kamar wata musaka, duk kalar juyin duniyar nan da akai mata bata gane Kausar ba, yar autarta ta manta da shafin rayuwar Kausar a cikin tata rayuwar, sai dai tai ta kallonta amman bata san wacece ita ba, gashi idan yanzu za ka fada mata abu anjima kadan ta manta sai an sake fada mata, amman bata mantawa da fadawa kowa labarin abun da ta aikata. Kusan asibiti uku Sirleem na canja mata yana ganin kamar za ta samu lafiya amman shiru. Hakan yasa danginta suka dauke ta aka maida cikin familynsu da niyar za a rika yi mata na hausa, hakan kuma be saka Sirleem ya saduda ba sai ya fara planing din fitar da ita waje. Hakan ya saka aka daga ranar da za a bikin mika masa ragamar kamfaninsa da kuma kananan kamfanonan da suke karkashinsa har zuwa karshen sabon watan saboda halin da yake ciki na tashin hankalin mahaifiyarsa da kuma kanwarsa Jurry, ciwon kai ya sakata gaba duk ta bi ta rame ko abu ta tauna a bakinta sai ta ji kan kamar zai rabe biyu, ruwa ne kawai zata sha ta samu salama amman bayansu duk abun da ta ci sai ta ji kamar zata mutu tsabar ciwon kai, duk asibitin da aka kaita cewa suke ba su ga komai ba, wasu kuma su ce tana shaye shaye ne ko ta taba yi shine abun ya dawo mata yana son taba mata kwakwalwa, alhalin bata taba shaye shaye ba, sai dai mutanen da suka ji abunda Hajiya Babba take fada ya san tare suka shirya sherin suna gane cewar hakkin mahaifinta ne da kuma abubuwan da suka kulla ne ya dawo kansu, daman can idan kai sheri abun ya dawo maka zai maka illa fiye da wanda akai wa sherin, musamman abun da ya shafi aljanu.
Two days after an maida Hajiya Babba gurin Familynta da suke nan Yola Karima da Kausar suka koma can domin kula da mahaifiyarsu yadda ya dace kasancewar bata da wanda ya fisu a yanzu domin mostly wadanda suke uwa daya uba daya duk sun rasu, sai dangin yaya da kane ko kuma yayansu, and when ever abu ya same mutun mai nauyi irin wannan ba kowa zai Iya jinyarka ba sai na ka, su kansu zama gidan ba zai musu dadi ba saboda abun da Hajiya Babba ta aikata duk da kasancewar babu mai tsangwamarsu sai dai su suna tsarguwa a cikin gidan sun saka sakewa, musamman Kausar da take ganin gidan ya mata empty saboda babu Hajiya Babba a ciki.
Sati daya da maida Hajiya Babba Family house aka sallamo Jurry daga asibiti ba dan ta ji sauki ba domin babu abun da ya hausa, daman can babu jikin balle yanzu da ciwo yake ta mata dariya, sai ta koma kamar wata ce mai cutar kanjamau, daga asibitin kai tsaye aka wuce da ita family house na su, a ranar ne Sirleem ya shigo masarautar domin rabonsa da masarautar tun a lokacin da aka kai Hajiya Babba asibiti, bamgaren Ammy yai parking motarsa ya fito a matse ya nufi kofar da zata sada shi da cikin falonta, kamar wani bako haka ya shiga bangarenta, a da idan ya shiga kai tsaye yake wucewa dakinta saboda yana daukar kansa kamar dan gidan saboda Ammy bata tana nuna masa banbanci ba ko kadan, sai dai a yau sai ya samu kansa da kunyar shiga dakin nata, ba dan komai ba sai dan abun da mahaifiyarsu ta aikata, kusan Kausar da Karima da suke cikin hankalinsu ma duk suna cikin damuwa balle kuma da yake yayansu, a falo ya zauna har sai da Jekadiya tai masa sannan ya shiga dakin da sallama. Ammy dake zaune rike da cup ta amsa mata tare da aje cup din kasa.
“Sirleem ya ka zo mana da bakon abu haka? Daman can ka saba idan zaka shigo inda na ke sai an maka iso ne?”
Ammy ta fada da muryar da ke karantarda mai saurarenta wato Sirleem cewar ranta a bace da abun da yai. Kasa dago kai ya kalleta kana kallonsa kasan yana cikin matsala da damuwa kala kala.
“Agafarce ni Ammy”
“Na maka uzuri na yau kadai amman karka sake min haka, akwai abinci a dinning”
Ammy ta fadi hakan ba da dan ta san yana jin yunwa ba ko akasin haka sai dan sanin cewa Hajiya bata masarautar a yanzu, bayan kuma ta san most zamansa a masarautar ne tare da mahaifiyarsa kusan cikin masarautar yake gudanar da rayuwarsa gaba daya.
“No na gode Ammy, daman magana na zo mu yi, kuma na roki wata alfarma a gurinki”
Sirleem ya fada murya can kasan makoshi, har lokacin yana jin kunyar ya dago idonsa ya kalli Ammy. Ammy kuma sai ta gyara zamanta tana fuskantarsa domin alamunsa sun nuna mata maganar da yake son mata mai muhimmanci ce.
“Ina saurarenka”
Ajiyar zuciya ya sauke a hankali sannan ya dan dago kadan yana matsar hannunsa na hagu a cikin na dama tare da hade yawun bakinsa.
“Ammy... Na san kin ji komai kuma kij san komai a yanzu, kuma na san abun da Hajiya da Jurry su ka aikata ba abu ne mai kyau ba, kuma na san irin zafin da kike ji, amman hakan ba zai hana ni roka musu gafararki ba, dan Allah Ammy ki yafewa Hajiya abun da tai miki, kuma ina rokon ki ki roki Mai Martaba shi ma ya yafe mata, ita da juri, ba dan komai ba sai dan su samu sassauci a nan duniya kuma su tashi kiyama ba tare da hakkinku ba, Wallahi har ga Allah Hajiya ko wani be taba labarta mana wani abu ba ni da Kausar da Karima, na mu san komai ba kuma ina fatar laifin Hajiya ba zai yafe su ba...”
Yana cikin maganar idon Ammy ya cika da hawaye.
“Madallah da da kamar kai Sirleem, hakika Allah yayi yana fitar da mai kyau daga marar kyau, kuma yana fitar da rayeyye daga matacce, hakika Hajiya ta yi sa'ar samun da kamar kai, Allah ya maka albarka”
Ta yi shiru tare da sauke ajiyar zuciya sannan ta cigaba.
“Ko kadan ban taba rikon Hajiya da wani abu a raina ba, duk da an san kishi gaskiya ne, amman a tunanina yadda muka girma a haka muna gina rayuwa da yaya komai ya wuce, sai dai ka san zuciyar dan'adam kowa da irin tasa kuma, hakika abun ya ba ni mamaki kuma ya tsorata ni, kuma zan yafewa Hajiya saboda saboda kai kadai Sirleem, ina son ka shaida Allah ma ya shaida na yafewa Hajiya abun da tai min na boye da na bayyane, ina kuma fatar saboda wannan abun da na yi Allah ma ya yafe min, kuma ina tabbatar maka cewar inshallahu Mai Martaba ma zai yafe musu, daman shi sarki ai baban kowa ne, koda baka da alaka da shi ka samu matsala a wani gurin ya sakan kira yayi sasanci balle kuma abun a gidansa? Na tabbatar zai yafe masu”
Sirleem ya saka hannunsa ya taba idonsa dake cike da kwalla.
“Na gode sosai Ammy Allah ya saka da alheri, kuma ina son ki roka min izininsa ina son na fitar da ita waje saboda nema mata lafiya”
“Aa wannan kam hakkin Mai Martaba ne, nema mata lafiya cin ta da shan ta duk abubuwa da suka rataya a wuyansa saboda shi yake aurenta, hakki ne da Allah ya dora masa, kuma na san zai fitar da ita Inshallahu, duk abun da Mai Martaba zai yi a yanzu, yana cikin fushi ne da bacin rai dole mu masa uzuri, amman ina tabbatar maka idan ya sauko komai zai wuce”
Sirleem ya kalleta da duba na girmamawa da ganin kima.
“Na gode sosai Ammy, hakika da ko wace kishiyar uwa za ta zama kamar ke, da yayan kishiya da yawa ba su yi maraici ba”
Ammy ya yi murmushi irin na su na manya.
“Sirleem kenan, kai ma ai da ce yayan kishiya za su zama kamar kai da ko wace kishiyar uwa ba