Showing 138001 words to 141000 words out of 286946 words

Chapter 47 - Fulani Book 1 Hausa Novel Complete

20 Dec 2024

935

tsoro gata da sakewa can you imagine farkon haduwar mu n kadeta amman ce min tai n siya mata kaza da yoghurt? And she's proud ita mai ilmi ce babu kamarta a kauyensu, She's funny, i like her, zan so samu mace mai saka ni nishadi if possible, ko da friend ne”

Ya karasa da murmushin annuri a fuskarsa.

“Kai yanzu yarinyar nan batai maka kama da aljanu ba? Wai ka ji muryarta da kyau kuwa?”

Shattima be ce komai ba bayan murmushin da yai mai sauti ya mike tsaye tare da saka hannunsa na dama aljihu.



FADIME POV.

Bata farka sai da safe babu komai cikin mafarkinta sai abubuwan da suka faru. Tun da asubar fari ta farka a lokacin da duhun dare be gama wayewa ba, sai dai ba zata iya shaidar asuba bace saboda garin basa sallah, da gurin da duhu balle ta iya cewa ta ga agogo, besides bata ma san inda take ba, lalabe ta fara yi a hankali kamin ta sako kafarta kasa.

“Ina zaki je cikin dare?”

Boka kakan Wasim ya tambaya da yarensu duk kuwa da ya san be zama lallai ta ji abun da ya fada ba, kamar maciji haka tai saurin dale kafarta saman gadon, tsabar tsoro da rudewa sai ta ji kamar da larabci kakan yai mata magana, take ta fashe da kuka.

“Na shiga uku na lalace ni Fadime, hadde in bone, Wallahi na rantse da Allah daya halicce ni ni Fadime ba zan sake kin jin maganar Inna ba, a zan sake kin bin umarninta ba, idan tace Fulani zauna zan zauna idan tace dawo zan dawo”

“Shiiiiiii”

Wasim ya fada yana kai hannu ya dafa ta, ba karamin razana tai ba, sai ta kama bakinta ta rike hakan kuma be hanata kiran sunansa ba.

“Wasim...?”

“Na'am”

Ya amsa mata murya kasakasa.

“A ina nake? A duniya ko a ina?”

Saurare take tana son jin amsar da zata fito bakinsa, domin bata yarda a duniya take ba. Duk da kasancewar cikin hudu ne kuma asuba ce hakan be hana Wasim murmushi ba.

“A cikin me nake dan Allah?”

Ya gintse dariyarsa tare da matsawa kusa da ita.

“Dakin Kakana”

Ta dafa zuciyar ta sauke ajiyar zuciya taja numfashi ta sake saukewa.

“Wallahi Allah mai rahama ne, ko bana ji maganar Inna yana tsare ni, dan Allah ka kai ni gida, yau Bappa sai ya dafa nama a tukunya ya gasa shi, na shiga uku ni Fadime”

Ta fashe da kuka tana tunanin irin hukuncin da Bappa zai mata idan ya san ta kai bayan isha'i, domin a zatonta ba safiya bace farkon dare ne. Tashi Wasim yai ya kunna wutar iccen take haske ya baibaye dakin, a lokacin ne ta daga kanta sama tana kallon dakin kamin ta kalli Wasim.

“Yanzu an gama isha'i garinmu ko?”

“Safiya ce zata waye yanzu”

Take ta fashe da kuka.

“Na shiga na lalace ni Fadime, wanda be jin magana be ji dadi ba, I'm very very stupid girl...”

Kakan ya daka mata tsawa saboda ta dame shi da hayaniya, a maimakon tai shiru sai ta sauko saman gadon gaba daya ta nufi inda take hango kofa @360 tana ihu.

“Wayyo ni Allah na boni ni Fadime aljani...”

A iyakar gaskiyarta aljani ta gani, domin sai da yai magana ta lura da inda yake kwance macizai sun zagaye shi suna bachi.




_________
Ina mata matan kwalisa Matan da suka ansa sunansu na Mata? Ina wadanda ke cewa mun yi mun yi bamu ga amfaninshiba? Hmmm to ku zo ga Yar gidan Maifata ta zo maku da Al ajabu, dan tsugunno, gumba da tsimi da Zuma daban daban, maganin sanyi na maza da Mata. Ga kuma garurruka irinsu mallakau sabuzu kuwa, sa bahaushe saibi, Dan hubbare kafi malam aiki, ke kadai ke da miji, dahuwar kaza, tattabara, ciccibi da dai sauransu. Ba anan kayanmu suka tsaya ba, muna hadin amare na musamman turaren sutura turaren tsugunno turaren wanka da na daki da na jiki duka 4amare nasu na musamman ne, amma ga tsuhuwar da ke son komawa yarinya itama zata iya zuwa ahadata kai abundai sai wanda ya gani, dan haka karkubari abaku labari, domin neman karin bayani zaku iua nemana ta wannan number  09029891757 ko 08169311410, muna aikawa ko'ina a fadin kasar nan har waje kasar nan muna aika kaya.
Address: Nasarawa Samaru Area gurin masallacin mai sola Gusau Zamfara state Nigeria.
35

*Littafin nan na kudi ne biya ki karanta cikin aminci. Pay 300 to 0314795884 Abubakar Hadiza Gt bank, then send the evidence via 08036126660*


Da kanta ta shirya ya fito falo sanye da uniform, kamar kullum hadimai na falon kowa na aikinsa, masu mika mata gaisuwa na yi ita dai bata amsa ba har ta isa dakin Ammy, kamar wata bakuwa haka ta tura kofar dakin ta shiga, sai kuma ta tsaya daga jikin kofar ta sanda kanta kasa kamar mai kunyar Ammy.

“Ammy good morning”

Ammy bata ko dago ta kalleta ba balle ta amsa ta.

“Zan tafi makaranta yanzu, akwai abun da zan miki kamin na tafi?”

Sai a lokacin Ammy ta juyo ta kalleta.

“A tunaninki yin hakan zai saka na manta da abunda kika aikata Nana? Zubar da kimarki kimar ta kimar gidan nan gaba daya? Kin san zafin da nake ji idan na tuna abunda kika aikata?”

“Zan zama yarinyar kirki Ammy, alkawari ne ba zan tsaba ba, ba zan sake ba”

Ammy ya dauke kai ba tare da tace mata komai ba. Hakan yasa Nana ta juya ta fice daga dakin, ita kanta ta san ta yi abun da be dace ba, sai dai alkawarin da ta daukarwa Sardauna ba zai saka ta sake aikatawa ba. Ita da kanta ta fito harabar gidan neman direban da zai kaita school, bata son zuwa sai dai alkawarin data daukarwa Sardauna ya tsaya mata a rai, hakan yasa zata daure ta cigaba da zuwan duk kuwa da kasancewar zuwan baya mata dadi. Sai da ta shiga cikin motar sannan ta bude jakarta ta dauko wayar Sardauna ta kunna tana kallon hotonsa dake gaban wayar. Take idonta ya cika da kwalla, ta fara raya yadda zata tunkari Mai Martaba da maganar matukar Hajiya bata saka an sake shi ba.

“Mu fara biyawa cid office inda ka kai ni jiya”

“Tau Hajiya”

Direban ya canja akalar motarsa daga zuwa police station din, sai da suka isa sannan ta share hawayenta ta dauko mask dinta ta saka, ta bude motar ta fita ta bar jakar a ciki, kowa sai kallonta yake ganinta sanye da uniform ta nufi cikin police station din, kamar jiya tana isa ta fada musu wanda take son gani.

“Baya nan an sallame shi”

“An sallame shi ko kuma na canja masa guri?”

Ta tambaya with confused tana kallon police din dake mata maganar.

“An sallame shi tun jiya”

Wani irin dadi ne ya lullubeta, da sauri ta juya ta bar gurin kamin ta isa motar har da hadawa da gudu, tana shiga ta fadawa direban inda zai kaita wato unguwarsu Sardauna, kamin ya isa har ta tsawwala. Har kofar gidan ya faka motar ta bude ta fita da sauri bata ko tsaya rufe motar ba. Kamar wata mahaukaciya haka ta fada gidan da sallama, she got lucky a lokacin Sardauna na zaune waje yana digawa idonsa magani, yana ganinta ya gane ta duk da kasancewar tana sanye da mask, bata san lokacin data cire mask din ba ta washe masa hakora zuciyarta sai bugawa take da mugun karfi irin na zumudin nan, idanuwa sun yi arba da abun da suke son gani. Shi ma murmushin ya samu kansa da sakar mata, sai kuma ya juya gefensa ya kalli Anti Rabi dake watsa masa wani mugun kallo da shi kadai ta san abun da take nufi, take murmushin ya gushe a fuskarsa, Nana na ganin haka sai ta nemi guri ta adana nata murmushin ta ari wasu kalmomin ta yaba abakinta.

“Daman na zo kawo maka wayarka ne, tana mota”

Ta fada tana kallon Anti Rabi, Sardauna dai be ce komai ba, kuma ya kasa motsawa daga inda yake, baya son yai aikata wani abu daya tsaba umarnin Anti Rabi bayan duk gargadin da tai masa a jiya cewar ko hanyar da Nana ta bi kar ya sake bi.

“Bari na dauko maka wayar”

Ta fada tare da juyawa ta fice ganin yadda Anti Rabi ke kallonta, komawa tai cikin motar ta dauko wayar ta sake shigowa cikin gidan ta isa har inda Sardauna yake ta mika masa wayar tana kallon fuskarsa.

“Yau zan cigaba da zuwa makarantar, kuma ba zan fasa ba har sai na gama, ko bana jindadi zan cigaba da yi a haka”

Juyawa yai a hankali ya kalli Anti sai ga idonta na kansu.

“Na gode”

Ya furta sannan ya karbi wayar, Nana ta juya a hankali ta fara tafiya tana jin kamar Sardauna ya kirata ya fada mata wata maganar. Har ta kai kofar fita sai kuma ta juyo ta kalli Anti Rabi ta kalleshi.

“Sardauna zaka dawo aiki idan ka ji sauki?”

“Aa ko hanyar da kika bi Sardauna ba zai sake bi ba Inshallah, dan Allah ki fita daga rayuwarsa ina son ki fahimci akwai tazara da banbanci a tsakanin ke da shi, kin gan ni nan? Sardauna B shi da kowa sai ni, ke kuma kina da komai, dan Allah karki sake jefashi a matsala”

Idon Nana ya cika da kwalla, sai ta ji kamar ta budewa Anti Rabi zuciyarta ta san bata da niyar cutar da Sardauna. Sai da ta sake kallonsa sannan ta juya ta fice daga cikin gidan, cikin motar ta koma tana jin kamar Anti Rabi tace mata Sardauna ya mutu, domin rashin daduwarsa a gidansu tamkar an sanar mata ya mutu ne, sai a lokacin ne ta kara jin nadama da bakinciki abun da ta aikata wata kila da bata aikata ba ta yanzu duk wannan be faru ba.

“I will keep his promise”

Ta furta tana share hawayenta, sai ta ji wani courage din zuwa school din fiye da ko yaushe.



ZAINAB POV.

Hawayen dake makkale a idonta ya sauko mata da cikin katon madubin idon dake fuskarta, duk yadda take tausayin kanta tana jin kewar Auwal ya tafi ya barta sai ta manta da nata ganin yadda matarsa take ta kuka, yaranta na zaune kusa da ita. Duk wanda ya Zainab tana hawaye sai ya dauka ko tausayin kawarta ne ya sakata kuka, tabbas akwai tausayin kawarta sai dai be kai kewar da kaunar Auwal da take ji a ranta ba.

“Daman wai bashi da lafiya ne?”

Zainab ta tambaya tana cire gilashin idonta tare da saka tissue t share hawayenta.

“Mai rai dai da mutuwa, ciwon be dade ba, ya fada min yana jin ciwo kai da ciwon awazu sama sama har yaje asibiti sun bashi magani, sai abu ya kwanta ya taso, shekaranjiya dai da yake na ajali ne sai ya fara fitar da jini hanci da baki, kamin a kai shi asibiti yace ga garinku, ko da muka isa asibitin rai yai halinsa”

Ta kara fashewa da kuka, wanda hakan yasa wasu sabin hawaye suka saukowa Zainab. A gidan suka wuni sai da aka yi addu'ar uku da nema masa rahama da afuwar Allah sannan Zainab tai musu sallama suka fito tare da kawarta. Sai da ta fara biyawa ta sauke kawarta sannan ta dauko hanyar masarautar tana kuka.

“Kaico Rayuwa”

Ta furta tana jin kamar ace akwai abun da zata iya yi ta dawo da Auwal. A harabar gidan tai farkin ta bude motarta ta fito, har ta dauki hanyar da zata sadata da dakinta, sai kuma wata zuciyar ta raya mata why not taje ta sanarwa Ammy rasuwar Auwal kuma tai magana da ita akan abun da Iya tai maybe zata fahimta, haka ta dauki hanyar shiga falon Ammy duk da wata zuciyar na raya this is not the right time da za ta yi haka. Door bell din kofar ta danna, babu bata lokaci Jekadiya ta bude mata kofar.

“Maraba da Hajiya Karama an dawo?”

“Eh”

Ta amsa tana kallon yadda Jekadiya ta tsare mata kofa.

“Kina son magana da Ammy ne? Idan wani abun ne ki fada min sai na sanar mata domin tace bata bukatar ganinku a falonta ke da Iya indai ba wani babban abun ya taso ba”

Wani irin abu Zainab ta ji kamar an caka mata mashi a kahon zuciya, sai duk ta ji ta muzanta, ba a taba wulakanta kamar haka ba.

“Oh No daman zan duba Labib ne ki gaishe shi”

Bata ko tsaya jiran abun da Jekadiya zata ce ba ta juyo ta fara saukowa stairs din tana jin cewar ba zata iya kwana a gidan ba, domin bata dauka cin mutuncin da wulakancin ya kai haka ba. Silently ta shiga dakinta ta bude drawer ta, ta dauko keys din gidanta dake million quarters ta fito waje, sai da ta iso harabar gidan sannan ta kalli agogon hannunta, biyar saura kwata ya nuna mata, dan tsayawa tai tunani sai kuma ta nufi bangaren da Hadiman gidan suke zama, uku ta kira suka biyota har gurin motarta, sai da ta bude motar tana kokarin shiga sannan ta fada musu abun da take bukata.

“Wani gida zan kai ku ku gyara min dan Allah”

“To ranki ya dade ba matsala”

Sai da tai ma motar key sannan ta basu izinin shiga cikin motar jiki na rawa suka bude suka shiga, ya fisgi motar kamar ba a cikin masarauta take ba.
Sun yi yar tafiya mai nisa kamin su isa million quarters, domin irin sabuwar unguwar nan ce da ake yi a bayan gari. Gaban wani madaidacin gida ta faka motar ta fito tai knocking, a zatonta mai gadin zai bude mata gidan ne daga ciki, sai ta hangosa tafe da gudunsa ya baro wata runfar da suke hutawa.

“Sannu da zuwa Hajiya”

Ya fada yana daga mata hannu, wata uwar harara ta watsa masa mutumen da ya ci ace ta kira shi da Baba ko Malam sai ta kira shi da ainahin sunansa.

“Ali... Gadi na dauke ka ko kuma dan kaje wata rumfar kana shan inuwa?”

“Gadi kika dauke ni Hajiya”

“To ya zaka bar min gida ka koma can wata inuwar kana hutawa?”

“Na ga gidan ba kowa ne Hajiya, kuma duk wanda ya zo daga inda nake zaune ina hangoshi”

“Ai na san gidan ba kowa na dauke ka aiki, idan ka sake bar min gida ka koma gurin wata inuwar ka zauna a bakin aikinka”

Tana fadan kai ta kai makulli a jikin gate din ta murda ta bude da kanta.

“Allah ya baki hakuri Hajiya, Allah ya baki hakuri Allah ya wadata kowa”

Bata kula shi ba ta shiga cikin gidan hadiman na biye da ita, madaidacin gidane mai wadace da shuke shuken fulawa sai kuma tiles a ko wane lungu da sako na gidan idan ka cire tsakar gidan da akai masa ado da interlock. Kofar gaba da bude ta wuce cikin matsakaicin falon su kuma suna biye da ita kamar bawa da ubangidansa.
Kallo daya zaka yi wa falon ka san sabon gida ne da ba a taba zauna shi, sai dai komai akwai na more rayuwa kama daga cushion har plasma, daman ta dade da gyara gidan da zimmar dawowa sai Iya ta hana tun a wacan lokacin tana nuna mata be dace dan ta yi arziki ta yi gidan kanta ta bar masarautar ba, hakan kamar butulci ne wa Hajiya.

“Ta mun dawo tun a wacan lokacin a yanzu duk haka bata faru ba”

Ta furta cike da jin zafin abun da akai mata, Hadiman dai sai kallonta suke domin babu wanda ya san wani abu a cikinsu.

“Akwai mopper da tsintsiya a side din can, wata tai shara wata tai mopping, ruwa yana ta can baya bohore ne kunnawa kai zaku yi ku debi ruwa, idan kuna neman wani sai ku tambayi mai gadin nan, zan koma gida yanzu after isha zan dawo na dauke ku, har two bedroom din nan a gyara ga kitchen can shi ma a gyara komai ayi matsa tsab”

Duk suka hada baki gurin amsawa da

“To Hajiya an gama”

Ta juya rai ajagule ta bar falon, tsakanin abun da Ammy tai mata da kuma mutuwar Auwal sai ta rasa wanne ya fi yi mata zafi. Cikin Masarautar ta koma ta sake saka wasu Hadimai su hada mata kayanta a guri daya, wato tufafi da kuma kayan aiknta sai yan abubuwan da take amfani da su na yau da kullum. Sai da suka gama hada mata komai sannan ta saka suka kwaso kayan suka kai gurin katuwar motar bus dake gidan, da kanta tai ma direban magana cewar tana son ya saka kayan aciki da ma sauran da za a kawo, sannn ta nufi dakin Iya da Hadiman.

“Ku hada komai ba guri daya kamar yadda kuka min”

“To Hajiya”

Tana fada suna fara aikin, da kanta nufi wardrobe din Iya ta bude ta fara fiddo kayan ciki, tana kai hannunta saman wani wata atamfa sai ta ji abu a ciki kamar kololon wani abu, dayan hannun ta kai ta dauko atamfar da aka nade tukunya a ciki ta bude. Wani irin faduwa gabanta yai a lokacin da Idanuwanta su kai arba da karamar tukunyar kasa an rufe bakinta da jan kyalle, juyawa tai ta kalli Hadiman dake ta aikin hada kayan Iya, ganin hankalinsu ba a kanta yake ba yasa ta maida tukunyar a cikin zanen ta aje a inda take ta maida wardrobe din ta rufe, juyowa tai zuciyarta cike da tambayoyi kalakala, sai kuma ta ji tana bukatar ganin abun da ke cikin tukunyar, tana kokarin juyawa Iya ta shigo dakin hankali tashe.

“Waye da wannan aikin? Ina can gurin dawakai jikina ya fada min an taba kayana”

“Hajiya ce ta saka mu hada kayanki”

Sun nuna mata Zainab, sai a lokacin ne ma ta san da Zainab na cikin dakin domin hankalinta gaba daya yana kan kayan tsafinta.

“Zainabu lafiya?”

“Iya ba mun gama magana ba? Ina son a hada komai ne a akwashe, ba dan yamma ta yi ba ma da yau zamu koma, amman gobe inshallah zaman mu ya kare a gidan nan”

“Hana Abule, ai ba a fushi da matan sarki da Sarauta... Nan da dan lokaci zata fuce komai ya koma daidai, ni kam zamana a gidan nan yana min dadi”

“Wallahi na rantse da Allah ba zamu zauna a gidan nan ba, kin ji


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login