Showing 177001 words to 180000 words out of 286946 words

Chapter 60 - Fulani Book 1 Hausa Novel Complete

20 Dec 2024

952

wani kike bibiya wai kin cinye matansa kina cin yayansa wane irin abu ne wannan?”

Ba shiri Iya ta saki ledar hannunta.

“Ita yarinyar ni zatai wa lazafin maita?”

“Ba gaske bane? A gabana Wasim ya fada miyasa baki karyata shi? Bakinciki abun da na ji ne ya saka na kyale ban miki magana har yanzu, amman yanzu ina bukatar sanin komai asalina wacece ni, ina mahaifina i need to know, Wasim ya fada min saboda Maita aka koreki daga garinsu kuma na san ba zai min karya ba, miye dalilinki na daukar maitar nan Iya? Why?”

Gumi ne ya fara kemowa Iya ta ko'ina, jikinta na rawa ba abubuwan da Zainab take tambayar ne ne ya daga mata hankali ba, zancen Fadime ne ya tsaya mata a rai. Sai dai hakan be hana zuciyarta dakewa bakinta ya amsawa Zainab tambayarta ta ba ta sigar da kwararun mayu suke yi.

“Karya ne fa, ke kin taba ganin maita? Babu maita ko a kur'ane, idan ana son bata maka sunane ake maka wannan abun, karki sakawa zuciyarki shakku akan mahaifiyarki”

Zainab kallonta take tana tunanin karyar da take zargin Fadime ta yi wanda tai daidai da abunda yake faruwa a zahiri wato mutuwar matan Shattima da kuma yayansa.

“Taya akai yarinyar nan ta san haka har tai karya a kai?”

“Me kenan?”

Zainab ta yi shiru bata ce komai ba, sai ma juyawa da tai ta nufi dakinta. Iya ta kara bata mummunar fuskarta tana jin bakincikin abun da Fadime tai duk da masancewar ba a gabanta tai ba.

“In ban da sakarci irin na ki taya zaki bar shi ya tafi da ita?”

Ta tambaya kamar Zainab din tana kusa ta amsa mata.

“Wallahi bana son irin mutanen nan sam, miyasa Wasim zai kawo min ajiyar?”

Ta furta mayu basa son mutun marar jin magana da mafadaci kurwarsa na da wuyar ci.

“Dole ne na bi bayanta dole ne sai na taba ba, idan ba haka ba zata bata min suna a gidan nan kuma ta tona min asiri, ni ko da nai kunya biyu kara na yi guda”

Ya duka ta dauki ledar ta nufi dakinta ta aje sannan ta fito ta saka makulli ta rufe dakin sannan ta fice da sauri gabanta sai faduwa yake tana tunanin kalar surutun da Fadime zata zuba a gidan gashi ta ji komai.



***

Tun ranar da suka kai rahoton abun da ya faru, suka dukufa da addu'a ba dare ba rana, musamman ma Inna da tafi jara'a akan cewar aljanune suka sace ta, washe gari kuma Bappa kuma ya koma asibitin domin jin ko an samu wani abu a can din. Wannan karon shugaban asibitin da kansa ya kira shi yana masa bayani cewar ya dage da addu'a kuma yai har hakuri tun da an saka cigiya a ko'ina a gashi kuma likitan da abun ya shafa an masa rasuwa sai ya nemo ya daga masa kafa har nan da kwana hudu zuwa biyar ko sati. Su kansu za su taya su nema, har ya bukaci idan akwai hotonta a kawo masa sai saka a media ko Allah zai saka a dace, da wannan Bappa ya baro asibitin ya nufi gurin police duk da kasancewar ya bada number wayars cewa idan aka same ta ko aka ji wani abu a sanar da shi. A can din ma da ya tafi babu labari har ya taka yaje har gidan redio da aka kai ciya duka dai maganar daya ce ba a ganta ba.
Kamar wani marar lafiya haka ya dawo gida gaba daya wunin ranar be tafi kasuwa ba, ko ya iso ya samu Inna ba lafiya, har wani yayansa ya dauko mai allura yayi mata guda biyu.
A gefen tabarma da take kwance ya zauna yana mata sannu, shi kanshi ji yake kamar lafiyar bata ishe shi ba. Be wuce minti ashirin zuwa ashirin da biyar da zama ba, wata matashiyar budurwa ta shigo gidan tana sallama, makociyar Inna ce dake gyara gida ta amsa mata.

“Hauwa ce?”

“Inna Ramla ina wuni?”

“Lafiya kalau”

Budurwar da ba zata wuce sa'ar Fadime ba ta juya gurin Bappa tana mika masa gaisuwa da yaren fulatanci, bayan ya amsa ta fada masa ana masa sallama a waje.

“Bappa wani ne a waje yace a sallamo ka, yace ace Wasim na maka sallama”

Ta fada da yaren fulatanci.

“Wasim?”

Bappa ya maimaita jin sunan wani iri da be tana ji ba, sai kuma ya yunkura cike da gajiya ta mike tsaye yana hamdalla ya nufi kofar gida.



_________
Ina mata matan kwalisa Matan da suka ansa sunansu na Mata? Ina wadanda ke cewa mun yi mun yi bamu ga amfaninshiba? Hmmm to ku zo ga Yar gidan Maifata ta zo maku da Al ajabu, dan tsugunno, gumba da tsimi da Zuma daban daban, maganin sanyi na maza da Mata. Ga kuma garurruka irinsu mallakau sabuzu kuwa, sa bahaushe saibi, Dan hubbare kafi malam aiki, ke kadai ke da miji, dahuwar kaza, tattabara, ciccibi da dai sauransu. Ba anan kayanmu suka tsaya ba, muna hadin amare na musamman turaren sutura turaren tsugunno turaren wanka da na daki da na jiki duka 4amare nasu na musamman ne, amma ga tsuhuwar da ke son komawa yarinya itama zata iya zuwa ahadata kai abundai sai wanda ya gani, dan haka karkubari abaku labari, domin neman karin bayani zaku iua nemana ta wannan number  09029891757 ko 08169311410, muna aikawa ko'ina a fadin kasar nan har waje kasar nan muna aika kaya.
Address: Nasarawa Samaru Area gurin masallacin mai sola Gusau Zamfara state Nigeria.
44

*Littafin nan na kudi ne biya ki karanta cikin aminci. Pay 300 to 2451879008 Hadiza Abubakar Zenith bank, then send the evidence via 08036126660*


Da tunani kala kala Iya ta isa masarautar, domin ta san ita Fadime zata fara fallasawa kamin ta fadi kowa, tabbas indan ta fadi abun da Zainab ta fada mata kowa zai gane kuma za a yarda da Fadime, sai da ta kusa isa gate din Ammy sannan ta tuna gargadin da Ammy tai mata cewar kar ta sake shigar mata falo, idan wani abun take so ta fada a sanar da ita. To idan ma ta shiga me zata yi? Ai dai ba zata iya cewa Shattima ya bata Fadime ba, idan ma ta bukaci hakan wani tonon asirinta ne domin Fadime ihu zata saka ta fara mata ihu tana kiranta da Mayya, anya ma zata iya shiga ciki ta hada ido da Shattima? Idan tace masa Fadime ta zo dauka ai wani karin abun tonon asirinta ne. Zaune tai gindin gate din tai tagumi hantar cikinta sai kadawa take, tana ta tuke tana tauna abun duniya ya mata yawa.

“In da na san haka yarinyar nan take, Wallahi kame kurwarta zan yi na matse ta kwanta ciwo sai na ga bakin maganar”

Taja tsaki.

“Dai dai nai kunyar duniya kara ta kiyama gaskiya ba zan yi kunga biyu ba”

Ta mike tsaye ta nufi hanyar bangaren Ammy, da tsoro ta doshi gurin tana kawar dai kai, sai dai jin yadda kowa yake mika mata gaisuwa kamar yadda suka saba yasa ta ji sanyi, ko da yake ko ta fada ai be isa ace har sauran mutanen gidan sun ji ba, sai idan ta yi kauri. Ta isa bakin kofar ta kwankwasa tana ayyana yadda zata fadawa Ammy cewar daga wani gurin ta fito ta biyo ta nan ta gaishe ta, ba dole sai ta nemi tafiya da Fadime ba ko kurwarta ta samu sa'ar kamawa ta san ya wadatar da ita.
Ta dade tana kwankwasar kofar kamin ta samu a bude mata, daya daga cikin manyan hadiman gidan nan, a take ta washewa Hadimar hakora.

“Ramatu ana nan”

“Ina nan Iya ya gidan?”

“Lafiya kalau, Allah yasa Ammy na ciki, ita dai Hajiya na gaisota tana nan ita”

“Eh Ammy tana nan amman ta shiga dakinta kuma tace kar a dame ta”

“Oh bachi take ina jin, to Babban Mutum fa?”

“Aa Shattima baya nan”

“Baya nan? Kin tabbata kuwa”

“Ba shi nan ai ba zan kiki karya ba Iya”

“Haka ne, kuma ba ku yi bakuwa ba ko? Wata yarinya haka fara yar makauniya”

“An yi ta baki gaskiya masu shigowa gaisuwa, amman babu makauniya, duk ba ba lallai na san komai domin ba kullum nake zama ba”

“Aa ita fa da yamma nan ne ko awa daya ina jin ba ayi ba”

“Gaskiya makauniya bata shigo ba, yawancin yan matan da suke zuwa wasu duk kawayen Nana ne”

“Haka ne, to a gaishe da Hajiya ni zan koma”

“Inshallah zata ji”

Iya ta juya ba dan ta yarda ba, wata kila ma Shattima ko Ammy ne suka ce mata yarinyar bata nan, waya sani ko tana can tana zuba musu surutun nata. Iya ta ji kamar ya daka tsalle ta ganta a gaban Fadime, tsabar bakinciki bata san lokacin data fara kudar hakora ba tana tsatsagarsu.

“Wallahi sai na nunawa yarinyar nan iyakar ta, ai daman na fada duk wanda ya shigo gonata nake kawarwa, ba a taba min abun da tai min ba, babu wanda ya san sirrina sai da ta zo, babu wanda ya damu da rayuwata sai da aka ka kawo min fitina, gashi har Zainab tana kokarin ballo min wani balli, lallai wannan makauniyar sai ta san ta taba maye...”

Ta yi kwafa tana jin wani irin bakinciki a ranta. Ji tai ba zata iya tafiya ba tare da ta tabbarta Fadime tana cikin gidan ba, juyawa tai ta koma ciki sai da wannan karon ta gurin dawakai ta nufa, domin tana da tabbacin a can ne kadai zata yi abun da take so ta gama ba tare da an ganta, domin ta saba shiga gurin. Sai da ta gaisa da mai kula da dawakan sannan ta shiga ciki tana fadin.

“Wai dokin Babban mutum zan duba, na san yayi kewata kwana biyu”

Shiga tai can kurya har ta wuce dokin Shattima ta karasa can ciki sannan ya duke kasa gurin dawakan, ta fara karanta wasu abubuwan tana tsutsar halshe, jikinta na tsama sai kafafuwanta suka fara nadewa guri daya suna yin shatin jikin kadangare irin ogan nan (Kiski a hausar ta Sokoto da Gusau) idanuwanta suka fara rikidewa ko'ina a jikinta ya dauki dumi tana ta fisga a hankali, sai da kafafuwanta suka fara zama siffar kiskin sannan jikinta ya soma dauka idanuwanta suka fara rikidewa suna kara ja daman can jajaye ne irin na mayu, har ta fara kankancewa sai kuma ta koma daidai.

“Oh Oh”

Ta furta tana aje numfashi da karfi kamar wanda tai gudun fanfalaki. Tana ganin hakan ta san ba zata iya rikada a yanzu ba, domin rabon da ta rikida ta zama wani abu tun kamin cikin Zainab, idan har tana son ta koma tana rikida kamar da sai ta sha garin maganinsu da suke amfani da shi suna sha duk shekara wasu kuma duk sati wasu duk wata wasu kuma kullum ne, ya danganta da kalar maitar da ka dauka da kuma irin karfinta, domin wata maitar tafi wata karfi, akwai wadanda basa gashi idan sun kama kurwa a take suke cinyeta danya ba tare da sun soya ba, irin su ne suka fi kowa hadari a cikin mayu domin su kap daya suke yi wa mutum, bayan su sai masu saidawa su ma idan sun siyar basa karbowa sai wani ikon Allah, akwai kuma masu siyarwa basa ci, wasu kuma su ci kuma su siyar, irin su ne suka fi arziki a cikin mayu.

Mikewa tai tsaye ta kabe jikinta ta fito a gurin ba dan ranta ya so ba, sai dan ta san idan har ta sake yunkurin zata wahalar da kanta ne kawai, idan har tana son tai saurin riki dole ne sai ta sha maganin wanda zai suma jikinta ta taimakawa aljanin maitar da take yawo da shi. Mai kula da dawakan na mata magana bata ko kula shi ba tsabar haushi da takaici ta wuce shi kamar ana turata ta nufi gate.



WASIM POV.


Bappa ya mika wakawa Wasim hannu suka gaisa, sannan Wasim ya cire hular kansa ya kalli Bappa.

“Sunana Wasim, na san baka san ni ba, duk da bani da tabbacin ko Fadime ta taba labarta maka wani abu akaina”

“Aa bata taba fada min komai ba, lafiya dai”

Wasim ya gyara tsayuwarsa tare ta saka hannayensa duka biyu aljihun wandonsa na jean.

“Na dade da sanin yarka sai dai bata tana sani na sai daga baya, ina yawan ganinta idan taje kiwo ko diban ruwa, amman ban taba mata magana ko nuna na santa sai daga baya, cikin kankanen lokaci muka shaku da ita, ni ne mutumen da ta bukaci na yi mata dabon maciji na yi mata ta dawo gida da maciji a tulu an yi haka?”

“Tabbas la shakka an yi haka”

Bappa ya fada yana kara kallon Wasim da kyau a take ya nemi gajiyar da yake ji ya rasa sawun giwa ya take na rakumi.

“Na yi mata, bayan haka ni ne mutumen daya sauya mata murya a ranar da wani zai zo ganinta daga birni sai dai ba tare da ita din ta so haka ba, ka tuna”

Bappa ya daga kai cike da gamsuwa.

“Na san da wannan”

“Ni ne mutumen daya fada mata akwai wuta maita da take bibiyarta, kuma ni ne mutumen da na kama mayyar na daki cikinta a lokacin tana cikin siffar mage, ban san iya abun da tai ba, amman ba dukan wasa nai mata ba, doka ne wanda ke taba hankali duk wata halitta mai jini da hanta, wanda n tabbatar har yanzu bata samu lafiya ba”

“An yi haka, hakikanta amri”

“Ban yi zato ba yarka ta zo tare da wata mata ta fada min cewar tana son na shiga da matar garinmu ta dauki hoto, na kaisu ba saboda matar ba sai dan saboda Fadime duk da na san garin mu gari ne da basa karbar bako, a lokacin ne muka samu akasi har mahaifina ya ganta, yasa aka kira mu ya bata naman kura yace ta ci, ta ci naman da ke saka duk wanda ba dan garin ba kaiyi a makoshi da baki, a kokarin mahaifina na horani sai yace be yarda a fitar da yarinyar daga garin ba, wanda na san yayi haka ne saboda ya san zata matsu ni ma kuma zan ji ba dadi na takurar da mahaifina yai mata, sai a nan ma na kasa bin umarninsa saboda ta matsa min da kuka cewar tana son na dawo da ita a nan, na fito da ita ba tare da izinin sarkin garinmu ba, mahaifina kenan wanda haka ne ya haddasa mata makanta, shi ma daga mahaifina ne a kokarinsa na sake min horo ni da ita, wanda ko gobe aka ce ta zo garin ko kuma ni na kaita ba zan kara ba, Kaka ne ya fada min cewar an tura mata makanta kuma kun dauketa zuwa asibiti har a inda zan same ta shi ne ya fada min kasancewarsa matsafi ne, ni na na shiga asibitin na dauke na fitar da ita daga garin da sunan zan kawo ta gurinku sai na kaita wani gurin ajiya, a inda na kaita kuma na kafeta irin kafin da ko mutuwa tai ba za a iya dawowa da gawarta har sai idan ni naje na dawo da ita...”

Bappa jin yai kafafuwansa ba za su iya daukarsa, sai ya nemi guri a kusa da kofar gidan ya rage tsayunsa, wanda hakan yasa Wasim din shi ma da kansa ya rage nasa tsawo. Ban da kallon Wasim babu abun da Bappa yake, a yadda yake ganin kamala da natsuwa a fuskar Wasim da kuma ladani alamansa sam ba zaka ce zai iya yin wani tsafi ba.

“Kenan kai dan garin can ne da ake kira da Garuk?, amman miyasa ka dauke ta?”

“Saboda za a iya taba idonta a nan, idan baku kaita asibiti wata kila zaku iya gwada yi mata na hausa, wanda ko wane a cikinsu yana da illar da zai iya saka ta rasa ganinta gaba daya, bayan wannan a nan za ku yi mata fada ba zaku saurareta ba, musamman kai da kake mahaifinta, domin a kullum maganarta Bappa zai karyata ko sai ya kusa asheta, na zabi zuwa na fada muku gaskiya domin na san ba lallai ne Fadime ta fadi gaskiya ba saboda tana tsoron ku, kuma saboda na kwantar muku da hankali ku samu natsuwa kuma ku sn cewa yar ku tana nan cikin koshin lafiya, kuma da zarar idonta ya bude zan dawo da ita dawowa ta har abada”

Bappa yayi shiru out of words be san abun da zai sake cewa ba for now. Abun da Fadime ta fada masa cewar aljanu ne kenan ba gaskiya ba ne? Ashe duk abun da take fada masa karya take shirya ba, sai a yanzu Bappa ya tabbatar Fadime ta wuce tunaninsa da iya tsara abu kamar ya faru da gaske. Dagowa Bappa yai yana fadin.

“To amman da ka....”

Da sauri Bappa ya mike tsaye yana waige waige ganin babu kowa a gurin sai shi kadai.

“Subhanallahi”

Ya furta cike da tsoro marar misaltuwa.

“Ya bace bat...!”

Da sauri Bappa ya juya ya koma cikin gidan, a gaban makociyar su Inna ya labartawa Inna komai, a take Inna ta tashi zaune tana jin kamar ta samu lafiya.

“Amman da ya taimaka ya kawo mana ita, in ya so sai mu kiyaye duk abun da ya fada”

“Ni ma abun da na tashi fada masa kenan ina dubawa sai na ga babu mutum”

“Kasan tsafi ne da su, wata kila yana da layar bata, layar zana”

“Ba mamaki, amman Fulani akwai karfin hali yanzu har ta taka taje garin nan? Anya kuwa Fulani bata da aljanu gaske? Kwata kwata babu tsoro ko fargaba komai a idonta”

Inna ta rausayar da kai.

“Fulani kam Allah dai ya shirya, gaba daya rayuwarta ban san wace iri bace, kuma babu yadda ban yi mata gargadi ba akan kar taje garin nan amman bata ji, to yanzu ya zamu yi kenan?”

“Hakuri zamu yi kawai, kuma gobe idan Allah ya kai mu sai na tafi na fada musu na na jany karar”

“Bappa Fadime ai ba kara ka kai ba, kai cijiya ka kai musu, dan haka ka kyalesu kawai domin idan ka koma wata kila ma za a ce ka kawo wani abu ne, ka kyale su kawai idan ma sun ji wani abu


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login