Showing 270001 words to 273000 words out of 286946 words

Chapter 91 - Fulani Book 1 Hausa Novel Complete

20 Dec 2024

891

weeks ya bar kasar ya samu Anty Rabi da wata shawarar.

“Anty akwai maganar da nake son mu yi wata magana, ban san yadda zaki kalli abun ba, amman ina ganin ya dace na tunatar da ke idan kin manta, domin zai amfane mu ne gaba daya”

Anty Rabi ta dauke hankalinta daga gurin karamin plasma ta kalleshi.

“To ina jinka”

“Anty daman akan maganar aure ne, ni sai na ga kamar aure baya gabanki, kuma ya kamata ace kin yi aure domin kina da kurciyar da maza za su so ki, ko dan saboda ki kara tsare mutuncinki da kuma na yayanki, misali ni yanzu zan tafi karatu wata kasar, zan yi nesa dake ya kamata ace akwai Namiji a gidan wanda zai rika kula da gidan da kuma ke kanki,ko ba komai hakan zai kara miki kima a idon mutane kuma za ki samu wanda zai rika tsawatawa yaranki”

Anty ta yi murmushi.

“Sardauna kenan, ba auren ne bana so ba, zaman ne sun zama sai hamdala, an mutu an barka da yara kana neman mai tallafa maka wasu kuma abun da suke dubi ya za ayi su ci daga gareka, kuma ba ko wane namiji ne yake son yayan wani ba, ba auren ne bana son ba, rayuwarce nake duba yadda tai tsanani kowa ta kansa yake, yayana kuma a yanzu ba su da kamar ni a rayuwarsu, idan ba su jidadi a hannun mahaifiyaba a hannun wa za su ji?”

“Kina da gaskiya amman ai kin ga ke kina da gidanki kuma kina sana'arki, duk wanda zai aureki zai same ki a gidanki ne, idan yaji ba zai iya ba kuma sai ya kama gabansa, ina jin tsoron yadda zan tafi na barku ku kadai ne a gidan nan”

“Allah shi zai kare mu, kai dai kai mana fatan tsarin Allah kawai”

“Allah ya tsare”

Ta amsa da Amin tana kallonsa, tun a lokacin ta fara kewar dan'uwanta, ba dan neman ilmin zai je ba ta ba zata yarda yai nisa da ita ba. Ya fara shirye shiryensa da bankwana da mutane a cikin satin, ranar da ya sauka a uk sai ya ga komai sabo a gunsa turawan da yake gani a film yau gasu yana gani a fili, duk da kasancewar cikin dare suka isa kasar.


FADIME POV.

Suna sauka airport matoci har biyu suka zo daukarsu, a iya tunaninta masarautar za a sauke su sai ta ga an nufi wata unguwar da bata sani ba da su, ba dan hoton Baba Waziri da ta gani a falon Hajiya Maryam ba wato uwargidan da tace ba a yola take ba, domin bata san kowa ba a cikin iyalan gidan, daga Hajiya Maryam har yaransa da kuma yaran Hajiya Talatu da kulawarsu ta dawo karkashin Hajiya Maryam, sakamakon haukacewar da mahaifiyarsu tai wato Hajiya Talatu.
Sun samu tarba ta musamman daga gurin Hajiya Mairo, sannan ta kaisu masaukinsu, a nan su ka yi karo ta kalolin  abinci da aka jera musu, ga lafiyayyen gurin bachi da bandaki mai kyau, plasma da ac suna kunne suna aikinsu, ba laifi Fadime ta natsu saboda kunyar da take ji, sai dai ta taji muryar Namiji sai tai ta saurare tana son taji ko yana tare da Shattima ne. Washe garin ranar da suka iso da safe Baba Waziri ya shigo ya gaisa da su, kuma ya isar musu da sakon gaisuwar Ammy da Mai Martaba. Two days after aka canjawa Fadime daki, aka kaita wani dakin na dabam, baka jin komai sai kamshi, gadonta da take bachi kamar an yi ambaliyar turare, kullum da safe mai aikin Hajiya Mairo zata shigo mata ta turare tai n jiki da na tsuguno da kuma na wanka, order Hajiya Mairo tai mata tun daga Zamfara har yola, Yar gidan Mai Fata tai mata gadin kayanyaki kala kala tun daga na gyara jiki har na turaruka da kuma kayan mata, hadi tai mata na musamman na Amaren, kullum mai dilka zata zo tana gyara mata jiki, Fadime bata fara kuka ba sai da aka fara mata shafa mata halawa, ta soma jin zafi tana ganin yadda ake fitar mata da gashin jiki kamar ba a sonta. Ba dan tana jin kunyar Hajiya Mairo ba da babu yadda za ayi ta kyale ana zaluntarta da sunan gyara, yanayin turaren da ake saka mata ana ana turara mata a jki da tufafi da kuma dakinta sai kamshi ya soma bin jikinta ta zarar ta wuce zaka ji kamshi yana tashi, farinta ya kara fitowa ga dogon hancinta gwanin sha'awa sai dai ta yi rama saboda fargabar gyaran jikin da ake mata kullum da shi take kwana take tashi a ranta, domin har ga Allah abun ya isheta sai dai babu yadda ta iya.
A zatonta haka gyara jikin ne kawai a iya jikinta abun zai tsaya, sai gashi ta ga ta Hajiya Mairo da kanta take saka ta gaba tana bata hade haden da aka karbo mata daga Zamfara, duk wanda Fadime ta sha ta ji a shi da dadi sai ta aje mai zakin sai ta shanye duka.

“Wannan naman duka za ki cinye”

“To”

Ta karba ta dan ci kadan sai ta ji shi kamar ba naman kaza ba, saboda hadin maganin da ya sha.

“Inna tace na daina shan abu mai daci yana da illa ga lafiya”

Hajiya Mairo ta yi murmushi.

“Wannan ba wata illa da zai miki sai dai ya kara miki lafiya, ki yi kokari ki cinye”

“To”

Ta saka bowl din a gabanta kamar ci zatai da gaske, ganin hakan yasa Hajiya Mairo ta fice daga dakin, Fadime na ganin ta fita ta tashi ta shiga bandakin ta kunna fanfon ta wanke kazar ta dawo da ita ta ci ta a haka ba tare da magani ba.

“Haka kawai sai a rika bawa mutum abubuwa cikin mutum ma sai ya lalace”

Ta fada tana turo baki, duk yadda ta zo ta cinye kazar sai ta kasa saboda babbar kaza ce kuma Hajiya Mairo ta riga ta cika mata ciki da garin magani masu kyau.
Kwantawa tai saman gadon tana ta nishi kamar mai nakuda saboda cikar da cikinta yai.

“Ni gaskiya na gaji, kullum sai an bani wannan bakin abun, su nan garin haka suke aure ni Wallahi garin mu ba haka ake ba”

Ta wani turo baki gaba tana jun cikin ya kame mata ta ko'ina, daker bachi yai gaba da ita, la'asar na yi aka tashe tai sallah sannan aka bata na yamma, wannan karon da hawayenta da komai ta sha tana ta tsirewa Hajiya Mairo albarta a ranta. Ranta be washe ba sai ta aka fara gabatar da events, ta fara ganin fata da rawar jiki kamar za a cinyenta. Ranar da akai bukar kai wasu yan'uwan Bappa da Inna suka u
Iso, the following day akai sa lalle na al'adar mutanen Yola sannan akai Walima, aka daura aure on Saturday. A babban masallacin jumma na Katsina aka daura auren Shattima da Fadime, akan sadaki 800k.
  Fadar irin farinciki da Bappa yake a wannan lokaci ba zai yiyu ba, baki bude sai gaisawa yake da mutane yana sanye cikin Blue Shadda mai dan karen tsada sai wani haske take, a babbar Hotel aka yi liyafar cin abinci, sai abun da ranka yake so kake ci, kusan duk wanda yake jigo a masarautar ya hallarci daurin auren ban da Jarma, da aka nema aka rasa tun lokacin da asirin su Hajiya Babba ya tonu, sai ya tattara komai nasa da iyalansa ya bar garin. Misalin 4 jirgin da sukai booking ya tashi zuwa Yola, karka ku so ganin Fuskar Shattima, murmushinsa ya kasa boyuwa, zuciyarsa kal kamar be taba shiga wata damuwa ko bacin rai ba.
  A daren ranar da aka daura auren Ammy tai bikinta tare da kawayenta, sai kuma Amarya da aka jira mai walima ta zo tun daga sokoto birnin Shehu tana gabatar da karatunta, babu wanda zai yi ma Fadime kallo daya ya dauke ido, saboda kyau da tai, maroon lace ne jikinta da farar alkibba sun haskata sosai ta yi kyau kamar ba ita ba, ba laifi ta kama kanta sosai domin tun da aka fara bikin Hajiya Mairo da wata yar'uwar Mai Martaba suka saka ta gaba suna koya mata tafiya da kuma yadda zata rika amsawa mutane idan sun gaisheta, sannan suka gargade ta ba kowa za tai wa murmushi ba, ba kowa zata sakarwa fuska ba. Hakan yasa bata wani sake ba har sai da ta hango Inna ta shigo gurin tare da tagwarta, kana ganin tufafin da suka saka kasan hadimar ta Ammy ce, Ammy da kanta ya mike ta tarbi Inna dake sanye da atamfa yar ubansu da Hijab ta zaunar da ita kusa da ita, sai Inna ta ji wani girma da kwarjini ya kamata, tana kallon yarta a guri na musamman da aka kawata ita kuma gata a kusa da matar sarki.
 
  Sai kusan 11pm aka yi addu'ar rufewa bayan mutane da yawa sun gabatar da jawabai ciki har da Ammy, a gaban teburin kowa rika aje takeaway mai cikin da kayan dadi da kuma abubuwan tsinuwa irin su agogon hannu wasu tsarka kowa da abun da yake samu a ciki sai dai duk abun da aka saka a cikin sarka ko agogo worth 50k.
  On that day Fadime ta kwana a gidan Sarauta kuma ta wuni da mahaifiyarta tana ta mata nasiha kala kala, da yamma aka shiga da ita bangaren Mai Martaba yai mata maraba da shigowa cikin familynshi sannan ya dora mata da nashi nasihan, karku so ganin yadda wayoyi suke daukar Fadime da camera, daman tun da aka fara events din ake daukarta a video da hotuna, sai haskawa take ga ta ta sha jan lallen kamar dan ita kawai akai shi. Ita kanta a yanzu ta san ta taka wani matsayi a rayuwa, matsayin zama surukar sarki da kuma matsayin zama matar aure, wadannan abubuwa guda biyu sun zo mata a lokaci daya. Kwance tai a cinyar Inna tana ta hawaye sai a lokacin ta fara missing din abubuwa da ta saba da su, ba ma kamar Inna da kawayenta da kuma Bappa, domin mafi yawan nasihar da Inna take mata na ta yi uwa mijinta biyayya ne, a cewarta su yanzu sun sauke nauyi hakkinta da kulawarta yana karkashin mijinta ne, daga karshe Inna ta rufe mata da bankwana tana hawayen ita ma.
  Misalin 8pm aka shiga da amarya gidanta gaba da baya manyan motoci ne na alfarma, daidai kofar shiga falon aka faka motar Amarya aka shimfida mata wani jan carpet wanda zata taka ta shiga ciki, Gwaggonta da wata Gwaggon Shattima ne suka riko hannunta suka fito da ita motar hadimai na zuba kirari, masu guda suka karade gidan da guda, daga bisani aka soma busar sarakuna.

“Ki ce bismillahi”

Gwaggon Shattima ta fada tana sanye da black lifaya tana rike da hannun Fadime, Jekadiya kuma na daga baya tana fesa mata turare. Daker Fadime tai bismillah saboda kukan da take domin a yanzu ta yarda rayuwarta ta canja kuma ta yarda ya rabu da su Inna da Bappa zata koma rayuwa da Shattima da yan'uwansa, ga wani jazabar aure da take jin tana sauko mata, a katon falon na biyu aka daunar da ita baka jin komai sai guda da kamshin turare ta ko'ina, daga waje kuma masu busa suna ta aikinsu.

ZAINAB POV.

Bata gamsu Iya ta mutu ba har sai da Wasim ya kaita gurin kabarinta ta saka hannunta ta taba kasar gurin sai ga ta tana hawaye da murmushi a lokacin daya, ko za a kasheta a yanzu ba zata iya fadar yadda take ji ba, ba ta san yadda zata misalta ba.

“Finally...”

Ta furta tana mikewa tsaye sannan ta sannan ta juyo ta kalli Wasim da ke tsaye bayanta, takawa ta fara yi har ta isa inda yake tsaye yana kallonta cike da tausayi.

“Ban taba mafarki ko tunanin wata rayuwa za ta zo min a haka ba”

“Haka ne abubuwa da yawa ba mu saka su a tsarin rayuwarmu ba kuma su kasance mana”

“Yeah haka Allah ya tsara, yana tsarawa bawa abun da yake so ba abun da bawa yake so ba”

Ta karasa tana danne kukanta, ya fara takawa tare da ita suna tafiya. Tana tafiya hawaye na wanke mata fuska, a ranar mutuwa ne kawai Zainab ba tai ba akan kuka, duk yadda take jin rashin kyautar Iya da yadda take jin kamar zata iya tafiya ta barta mutuwarta ya kawar mata da komai, sai ta ji kamar ace bata mutu ba, no matter how bad she is ta ji tana bukatarta a kusa da ita. Da kukan tai bachi da shi ta farka da asuba ma haka tai ta kuka sannan tai alwala bayan ta gama sallah asuba sai ta daga hannunta da zimmar yi ma mahaifiyarta addu'a sai kuma ta fashe da kuka, idan ta yi mata addu'ar za a amsa mata ko kuma aa?
Within a month Zainab ta koma abar tausayi bata iya cin komai sai yayan itatace da ruwa, jikinta ya koma very weak bata da wani kuzari, duk yadda Wasim yake son ta sake sai ta kasa bata komai sai yawan kallon mutane ko saurare abu mai wahala ta bude baki tai magana, abubuwa da yawa sun taru sun yi mata yawa, gashi a nan bata chat balle ta rage wasu abubuwan.

After some months...!!!
   
       **     **     **
As usual suna zaune akan wani dutse yana ta mata fira amman kwata kwata hankalinta ba ya gurin, ko saurarensa bata yi.

“Wasim... Idan na bar garin nan zaka rika kawo min ziyara ne?”

Kallonta yai jin yadda ta dauko wani zance na dabam, ba akan firar da suke ba.

“Zan biki dai mu tafi tare, ta ya zan kyale ki rayu inda baki da kowa kuma ke kadai?”

“Bana ka aikata wani laifi da zai saka yan'uwanka su ga laifinka, kai kana jindadin zama a garin nan, kuma kowa na ka yana nan be kamata ka bi son ranka ba ka aikata kuskure, bana fatar wani ya sake aikata wani kurkuren saboda ni”

“Idan har babu ke a garin nan, ai garin ba zai min dadi ba, ban ga amfanin zamana a nan ba matukar ba ki tare da ni”

Ta kalleshi

“Saboda me?”

Sai shi ma ya kalleta ido cikin ido

“Saboda ina son ki...”

Saurin mikewa tai tsaye tana maida numfashi tare da hade yawu da karfi, zuciyarta ta shiga bugawa tana rabawa sassan jikinta jini. Daman da dade da fahimtar hakan a kalamansa da yanayin yadda yake mu'amalantarta sai dai bata tsammaci haka daga bakinsa ba a yanzu, kuma a irin wannan lokacin. Shi ma mikewa yai tsaye yana kallonta.

“Kin ji abun wani iri ko? Ni ma haka na ji a lokacin da abun ya fara kamani...”

Ta yi shiru bata ce komai ba, shi maWaziri shirun yai can kuma yana kallon yadda hawaye ke sauko mata.

“Cancanta ba ko? Ko kuma na yi sauri ne? Ko kina duba alakar addininki da nawa ne?”

Hannu ta kai ta share hawayen ta da ta tafiya ba tare da kalleshi ba.

“Zan shiga ciki na huta”

Da kallo ya bita har ya daina hangota sannan ya sauke ajiyar zuciya, ya saka hannayensa biyu ya shafa kansa zuwa fuskarta, he can't lie to himself shi kansa ya san yana son Zainab kuma yana tausayinta fiye da yadda yake tausayin kansa, but still yana jin son Fadime har yanzu a ransa, maybe sooner or later zata fice mishi daga rayuwa da tunaninsa but for now idan ya tuna yana jin wani iri.

FALMATA POV.

Tana jingine jikin gadon shi kuma ya dora kansa saman karamin cikin nata yana sauraren hausar da take karanta masa.

“Ko wane jaririya ko jaririya su kan yi kuka a lokacin haihuwarsu da kuma kurciyarsu, sai dai kuka bayan girma kowa yana da dalilin yinsa
Da ace na wa kukan na mutuwa ne, da nafi kowa farinciki, ashe ba sai rai ya bar gangar jiki ake mutuwa ba, na tabbatar da mutuwa kala biyu ce, kaico ni Aminatu!
A yanzu kan na gasgata cewar na dade da mutuwa gangar jikin ce kawai a aje, kuma na yarda mace bata da gata, gurin yan'uwa da al'ummarta...”

Ta rufe babin tana juya bayan littafin tare da karanta sunansa tare da sunan marubuciyar.

“BAKAR WASIKA Na Khadeeja Candy, gaskiya daga ganin littafin nan zai yi abun tausayi”

Dan dagowa yai kadan ta kai hannunsa ya taba bakinta.

“Ko?”

Sai tai murmushi ta kalli agogo.

“Ka ce 9:30 zaka tafi gashi har 10 ya wuce fa”

Lumshe ido yai ya saka dayan hannunsa yana shafa wani bangare na cikinta

“Ban gaji da ganawa da dana ba ne shiyasa, let him meet his dad”

Ya karasa tare da kissing din cikin nata na 5 months.

“Kai ne oga kuma kai kake karya dokar kamfani”

“Zan fada musu madam ce ta hana ni fitowa tana ta ba ni.... ”

Be karasa ba ta buge masa baki domin ta san abun da zai fada, ba kunyarta yake ba dirty talk any how yake mata, shi da fada ita da jin kunya. Sai ya tashi yana dariya tare da gyara suit dinsa.

“Me zan dawo miki da shi?”

“Bana son komai”

“Really....”

Ya kanne mata ido zai fara barin zance ta dauki fillo ta jefa masa, sai ya fice dakin da gudu yana kyalkyalar dariya, ita ma dariyar tai ta sauko da kafafuwanta kasa.

“I love you babyn Baby”

Ya fada da murya da zata iya jinsa, murmushi tai ta mike tsaye ta isa gurin window tana kallonsa yana daga mata hannu har ya shiga motar yana jefo mata kiss, ita kuma ta karba ta manna a kumatunta duka biyu.




_________
Ina mata matan kwalisa Matan da suka ansa sunansu na Mata? Ina wadanda ke cewa mun yi mun yi bamu ga amfaninshiba? Hmmm to ku zo ga Yar gidan Maifata ta zo maku da Al ajabu, dan tsugunno, gumba da tsimi da Zuma daban daban, maganin sanyi na maza da Mata. Ga kuma garurruka irinsu mallakau sabuzu kuwa, sa bahaushe saibi, Dan hubbare kafi malam aiki, ke kadai ke da miji, dahuwar kaza, tattabara, ciccibi da dai sauransu. Ba anan kayanmu suka tsaya ba, muna hadin amare na musamman turaren sutura turaren tsugunno turaren


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login