Showing 198001 words to 201000 words out of 286946 words

Chapter 67 - Fulani Book 1 Hausa Novel Complete

20 Dec 2024

971

na san ba na shi ba ne”

“Wani gida kuma?”

“Eh ba gidan da muka je muka gani ba, wani gidan ne na dabam, ka kira shi ka tambaye shi inda za a kai yarinyar”

“To shikenan”

Ya kashe wayar, Tumba ta saka wayar a cikin zanenta tana kallon yan'uwan Baba da sukai cirko cirko.

“Ni sam ban yarda gidansa ba ne, domin be da irin wannan arzikin da zai samu wannna katon gida, idan ma yana shi to boye mana yai kuma ba na halal ba ne, wannan irin abu haka”

Ana nan dai wasu suka saka na su baki, suka taya ta wasu kuma su ka kama bakinsu su kai shiru, Inna laure dai na tsaye da tunani biyu a ranta, domin a yanzu ta gane dalilin kukan da Falmata take yi, bata son auren ne, ita kuma Tumba ta tsaya mata akan auren ne saboda ta sha wahala sai gashi ta ga abun da ba tai zato ba hakan yasa ta rudewa tana fadin wani ba gidan ba ne. Suna nan tsaye Baba ya kira Tumba jiki na rawa tai picking.

“Tumba yace nan ne za a kaita indai Unguwar 300 House's ne”

“Unguwar ne Wallahi, amman Malam ba wacan gidan da muka je muka gani ba ne”

“Babu komai tun da har yace nan ai sai ku kaita kawai”

“To Amman Malam baka ga gidan ba, abun tsoro ne kar sai mun bada baya ya yanke mata kai”

Inna laure na jin haka ta kada baki ta ce.

“Wane irin magana ne wannan Tumba? A maimakon ki jidadi ki yi mata fatan alheri sai ki fara wani magana marar dadi”

Ta fisge hannun Falmata ta jata zuwa ciki.

“Zo mu je, mu da zuciya daya muka aurar da ke, kuma muna miki fatan alheri fatan na gari, yi bismillah ki shiga da kafar dama”

Falmata ta yi bismillah sannan ta shiga da kafarta ta dama kamar yadda Inna Laure ta umarta, Inna Laure ta shiga da sallama mata biyun da ke ciki suka amsa mata.

“Mashallahu”

Ta fada sannan ta kai Falmata saman doguwar kujera ta zauna. Sauran yan'uwa da yan unguwa suka shiga sauran dakunan da kitchen suna dubawa, dakuna uku ne a upstairs din na farko ya bi na biyun kyau na biyun kuma ya fi na ukun kyau, sai dai kowane daki fararen kaya ne, kicin din ma an cika shi da kaya ga abinci kala kala a store din. Khadija ce ta zo ta zauna kusa da Falmata ta kama hannunta ta rike, tana ta murmushi kamar ba ita ce ta gama kuka ba a dazun, ganin gidan da irin kayan dakin da aka zuba a gidan ga gidan ya hadu iya haduwa. Nasiha sosai Inna Laure tai mata ciki har da ta addu'a.

“Karki kuskura wasa da addu'a kuma kar wani ya kawo miki wani abu yace ki baw mijinki ko ki amfani da shi da sunan kayan mata ki karba, kin ga Tumba nan ki yi hankali da ita, ki san abun da zaki fada ko ta baki ki karba, sannan ki yi ta hakuri zaman aure sai da hakuri, idan kin samu ki taimaki babanki mamanki kuma ki bita da addu'a da sadaka Allah ya ba ku zama lafiya”

Khadija ce ta amsa da Ameen, sannan Inna Laure ta saki hannunta ta hau sama ta duba dakunan ta sauko tana ta sanya albarka. Tumba dai na tsaye bakin kofar dakin ta kasa shigowa, gaba daya kanra ya dau zafi ga zuciyarta kamar zata fashe take sai tukiki take mata, gaba daya ta rasa ma kalar tunanin da za ta yi, cikinta har murdawa yake.
Tana a bakin kofar har su Inna Laure da matan da suka musu rakiya suka fito sannan ta juya ta bi bayansu ta kasa cewa komai har suka shiga motar aka juya da su, sai gidan ya rage daga Falmata sai Khadija sai kuma sauran kawayenta da yan'uwa da suke sa'aninta. Khadija ta bude mata mayafi.

“Bude fuska ki ga gidanki, duba ki ga inda Allah ya kawo ki Falmata”

Falmata ta dago kadan tana kallon falon, sai ta ji kamar ba gaske ba daman ranar yau ta zame mata kamar a mafarki. Jan mayafinta tai ta rufe kanta, a yanzu bata sna me zata yi ba kuka ko murna? Idan murna ne anya ya dace tai murna da auren tsoho ko da ace ya tara mata wannan uban dukiyar. Sai da aka maida su Inna Laure da Tumba sannan motocin suka je dauko ango.
Kawayen Falmata na jin tsayawar motoci suka fara gyare gyaren jiki, Falmata kuma ta kara maida kanta kasa.
Abun da ya bawa mutane mamaki ganin abokan ango yara amman angon tsoho da har da hurhura, yana sanye da mayan kaya har da babbar riga shaddaraa sai shinning take. Kusa da Falmata ya zauna yana ta kamshin turare kan ganinsa ka ga sabon ango. Duk wani abun da ake fada be ce komai ba iyakarsa murmushi, abokansa ne suka bawa yan matan da suke tare da Falmata kudin siyen baki har 200k, ba karamin mamaki ne ya cika su ba, har tsoron karbar kudin suka yi, sai Khadija ce ta karba har tana fadar wai a karo amaryar mai tsada ce, ita ce ta fara yin addu'a tana bada shawarwarin zaman lafiya, wani abokin ango ma yai nasa sannan suka Fita tare da kawayen amaryar domin aje su gidansu, sai da suka fice sannan ya mike tsaye ya isa bakin kofar falon ya rufe ya shiga kicin ya dauko cup da plate ya dawo kusa da ita ya aje a kasa.

“Amarya...”

Ya furta ta ainahim muryarsa, dan dagowa Falmata tai jin kamar irin muryar Sirleem, sai dai bata dago ba.

“Dago ki kalli angonki mana”

Ya sake fada yana murmushi, hannu ta saka ta dafa zuciyarta ta lumshe ido tana kara jin kamar mafarki take. Zaunawa yai kusa da ita ya kai hannunsa ya dage mayafinta yana kallon fuskartaz fuskarsa dauke da murmushi, janye mayafinta yai baya ya sauke shi kasa, ya kai hannunsa ya dago fuskarta, har lokacin idonta a rufe ya ke. Matsawa yai kusa da fuskarta ya hura mata iska a idon.

“Bude idonki Teema”

Jin irin sunan da ya kirata da shi yasa tai saurin bude idon zuciyarta na bugawa da mugun karfi. A zatonta za ta arba sa Sirleem ne sai tai arba da tsohon nan, sai dai a yau yana da haske sosai ga shaddar jikinsa sai kyalli take, tsabanin ganin da tai masa na farko da yake sanye da tufafi masu datti kuma da dauda a jikinsa.

“Teema...”

T kasa amsawa kuma ta kasa ce masa komai kana ta kasa dauke ido a akan fuskarta, wadansu siraran hawaye ne suka sauko mata, ta hade yawu ta sake hadewa.

“Teema... ”

A nan ma ta kasa amsawa. Mikewa yai tsaye yana murmushi ya cire babbar rigar jikinsa ya aje gafe, sannan ya kai hannu a fuskarsa ya fara cire furfurar dake fuskarsa. Mikewa tai tsaye da sauri ta zaro ido tana girgiza masa kai.

“Aa”

Ya sakar mata murmushi yana kokarin kai hannunsa ya rikata sai tai saurin ja da baya hawaye na sauko mata sosai.

“Aa”

Ta sake furtawa tana kara yin baya. Can kuma ta kai hannu ta fara murza idonta, domin gani take kamar mafarki take, matsawa yai kusa da ita zai taba ta sai ta fashe da kuka ta kara ja da baya tana kuka mai karfi.

“Ohhh.....”

Ya furta yana kallon yadda hawaye ke sauko mata. Ta saka hannayenta ta rufe fuskarta tana kuka mai karfi.

“Teema...”

Ya sake kiranta a karo na hudu yana matsawa kusa da ita. Bata amsa ba sai kuka take, hannayensa ya saka janye hannun da ta rufe fuskarta da shi yana kallon fuskarta.

“Falmata kukan ya isa haka”

Ta bude idon tana kuka.

Sai ya jata jikinsa zai rumgume tai saurin juya masa baya tana kuka gaba daya ta kasa gane komai duniyar ma gaba daya juya mata take. Rumgume ta yai ta baya.

“Kina mamaki ne?”

“Ni ba kai aka aura min ba”

Ta fada daker saboda kukan da ya ci karfinta, sai yai murmushi ya juyo da ita ta rumgume ta.

“Ni aka aura miki, ta sigar da babu wanda ya san ni din ne”

Falmata ta dago kai ta kalli fuskarta sai ta ga shi din ne dai ba wani ba. Take ta girgiza kai.

“Ta ya? Ya ya? Ko dai mafarki na ke?”

Dogowa yai ya hade hancinsa da nata ta saita bakinsa saitin nata ya kama lip dinta na kasa ya fara sotsa a hankali sai ta lumshe ido tana kokarin baya amman yaki bata dama, sai ma hannunsa daya da ya saka ya tallafo kunkurunta tai sama.

“Wow...”

Ya furta bayan ya cire bakinsa daga nata yana kallon fuskarta, ita kam ta rufe ido sai sauke numfashi take a hankali har lokacin zuciyarta bugawa take da karfi, ga jikinta sai wani yanayi yake bata na dabam.

“Yanzu kin yarda ni aka aura miki?”

Ta girgiza kai alamar no, sai yai murmushi mai sauti ya ja zuwa kan kujera suka zauna, ya rumgumeta jikinsa tsantsan.

“Daman na san ba lallai ne ki yi aurin yarda ba, domin ba ki zato ni ne wannan tsohon ba right?”

Ta yi shiru bata ce masa komai ba, sai y sake yin murmushi ya rumgume ta da kyau yana jinta har cikin ransa.

“Ban taba haduwa da wata halitta da nake tausayi ba, kamar ke kin shiga taskun rayuwa kala kala, abun da nake miki fata shine ki samun jindadi”

Yayi shiru yana shafa bayanta a hankali.

“Na san idan na je neman aurenki a matsayin da kike ba za a bani ke ba saboda ba a son ki huta, hakan yasa na samu mai kwalliya ya lalata min jiki, na saka furfura kuma na je har kofar gidanku na yi sallama da step mother dinki, na fada mata na ganki a hanya kuma na bincika ance nan ne gidanku”

Yayi murmushi yana kokarin dago Falmata ya kalleta.

“And i got lucky ina rokonta da neman ta shige min gaba sai ta amince tana ta jindadi, na bata number wayata akan ta kirani idan mahaifinku ya dawo sai ta karba tana ta murna, daga lokaci ne ma kara gane cewar baki da gata, sai tausayinki ya kara kamani”

Ya karasa yana jan hancinta.

“Babanki ya tambayi waye ni sana'a sai na fada masa, ina cin kasuwar kauye ne, ina siyo dabboni na siyar a kauye, kuma matana da yayana suna can, amman ke idan na aureki a nan zan aje ki, sai ya fada min na nemi so a gurinki, bayan mun yi haka sai na kirata a waya na fada mata, sai tace kar na damu an bani yarinyar, haka ya kara tabbatar min cewar baki da gata, i tot ko wasa take sai gashi mahaifinku ya kira yace ya bani ke, kin san irin dadin da na ji a irin wannan lokacin?”

Ya saka hannunsa ya cire dankwalin da ke kanta ya sumbanci kitson dake kanta.

“Na yi murna sosai, irin murnar da ban yi zato ba, kuma idan aka tambaye ni a wannan lokacin ba zan iya fadar dalili ba, maybe saboda ina jin zan taimaki wata ne, ko kuma saboda ban tana neman aure da kaina an ba ni ba ne i can't tell”

Ta sake dagowa ta kalleshi har lokacin ji take kamar mafarki ne. Bakinsa ya kai ya sumbanci hancinta.

“I cant believe halalina nake tabawa, ashe abun yake da farinciki, so haka angwaye suke ji, ina jindadi sosai, tun da aka daura aurena na samu kaina cike da farinciki, duk da yake Hajiya ta bata san na yi auren nan ba”

Falmata ta tashi zaune tana raba jikinta da nashi.

“Ban gane ba? To mutanen da ka tura fa?”

Ido ya kura mata yana ta kallon kyakkyawar fuskarta.

“Biyansu nai, da mutanen da na gabatar a matsayin iyayena da yan uwana duka siyensu na yi, just saboda na tsirarta dake dga halin da kike ciki, da kuma halin da Momy take kokarin jefaki”

“Ni...?”

Ta nuna kanta, sai da ya sumbanci goshinta sannan ya ce.

“Ke fa, ke ba zaki sani ba ne, amman na ji abubuwan da Momy take fada a lokacin da kuke kicin, zuciyata ta raya min cewar Momy zata iya miki dashe, saboda haihuwa ne abun da kadai take nema a yanzu, idan ba shi ba miyasa zata ce wai tana fatar idan ta bukaci wani abu daga gareki ba zaki hanata ba, and zargina ya kara tabbata ne a lokacin da na ji tana kokarin inganta rayuwarki.

I know Momy tana da kirki da karamci, amman miyasa zata miki duk wannan cikin kankannen lokacin da bata gama shakuwa da ke ba, and na ga irin tashin hankalin da ya same ta a lokacin da na sanar mata aure za a miki, har take so hadaki da Ameer? Why? Maybe saboda ta samu cin ma burinta, a iyakar tunanina ya bani cewar idan ban aureki ba, rayuwarki zata shiga matsala, wa zaki aura? Me zai faru kamin aure duk babu wanda ya sani, domin a lokacin da naje neman aurenki da ace wani ne ba ni ba haka za a aura masa ke, a jefa rayuwarki cikin matsala, kowa burinsa yayi amfani da ke, ke kuma abun da kike bukata a yanzu shi ne kulawa karatu da kuma ingantacciyar rayuwa, na daukarwa kaina alkawarin aurenki, sai dai bana da tabbacin kina so na ko akasin haka, iyakar abun da na sani shi ne auren zai fitar da ke daga kangi kuma zan tallafawa rayuwarki, sai dai na miki wani alkwari guda daya”

Sai yai shiru har sai da ta tambaya.

“Minene?”

“Na miki alkawarin ba zan taba cilastaki ba, ba zan taba miki abun da rai ki baya so ba, idan har baki so na, ko baki bukatar zama tare da ni, ba zan taba cilastaki ba, zan baki damar duk da kike so, daman dai na yi hakan ne saboda na tsiratar da rayuwarki”

Ya karasa yana kallonta har lokacin tausayinta yake ji. Ita ma kallonsa irin kallo na ban yarda a farke nake ba. Can kuma ta kalli jikinta.

“Na kasa yarda komai gaskiya ne, na kasa yarda cewa kai na aura, na kasa yarda cewar nan din gidan aurena na ne, har yanzu ina jin kamar mafarki na ke, na yi zaton tsohon zan aura da gaske, na yi zaton rayuwa zata zo mi a wahale ne”

Ta lumshe ido hawaye a sauko mata.

“Ban cancanci zama matar babban mutum kamar kai ba, duk da na san ka yi ne saboda ka taimake ni...”

“Kin cancanci auren wanda ya fini ma Teema, kina tarbiya ga hakuri kowa wane namiji mai mutunci zai so yayi dace da ke a matsayin mata”

Ya kai hannu ya kama hannunta ya rike yana murza yatsunta a hankali.

“Kina da kananan shekaru amman kina da tunani da hakuri kamar babba, rayuwarki na burge ni, a yanzu ma kin yi zaton ni din tsoho ne amman a haka kika zabi zama da ni ki rumgumi kaddararki, hakan yasa na kara jin kin kwanta min a rai fiye da da”

Ya saka dayan hannunsa yana share mata hawaye.

“Kuka ya kare, bana son kina saka kanki a damuwa yanzu”

Ta bude idon still tana hawaye, shi da kanshi ya tayar da ita tsaye sannan ya suka ya dauke ta cak.

“Ashe ma amarya ta bata da nauyi”

Fashewa tai da kuka, har lokacin bata jin ta koma daidai ba. Sama ya haye da ita ta zaunar da ita akan katon gadonta ya sumbanci goshinta.

“Kina da alwala?”

“Aa”

Zai sake wata maganar wayarsa tai ringing, sai ya saka hannunsa aljihu ya ciro wayar ganin number Hajiya yasa gabansa faduwa.

“Hello Hajiya?”

“Sirleem kana ina?”

Ya dan yi jimm yana tunanin ko an labartawa mata wani abun ne, duk da ya san be fadawa abokansa ba balle wani ya fada har Hajiya ta ji, sai amininsa shi ma dan yana da tabbacin ba zai fada ba ne.

“Ina gidana, kaina ne yake dan ciwo a nan zan kwana”

Yana jin lokacin data sauke ajiyar zuciya sannan ta amsa masa da.

“Allah ya kara sauki, for now on bana son kana kwana a waje, kasan na saba fada maka wannan ba sau daya ba”

“Na sani Hajiya, amman ba abun da kike zargi ba ne”

Ya fada yana kashewa Falmata ido daya, Hajiya bata son yana kwana wajen masarautar ne saboda Mansura, a tunaninta idan ba ya kusa da ita to yana kusa da Mansura ne, duk kuwa da sanin cewar ba a Yola take ba, sai dai ta san wani lokacin tana zuwa Yola gurinsa, saboda Hajiya ta hana shi yin komai a Kaduna yanzu ba dan komai ba sai dan ya daina haduwa da Mansura.

“Shiga ki yi alwala bari na dauko mana kazar mu”

Ya fada yana jefar da wayar kan gado.

“Sirleem”

Ta kira shi sai ya juyo ya kalleta fuskarsa na ta annuri.

“Hajiya Nana take son ka aura, kuma Mansura ma tana sonka, kuma yanzu ka aure ni”

“Yeah...”

Ya furta sai kuma yai shiru ya dawo kusa da ita ya zauna.

“Maganar gaskiya, haduwar da nai da ke yasa na ji ba zan iya auren Mansura ba, saboda tana da bad habit, na yi iya abun da zan iya na raba da samari na kasa, na san tana so, amman tana mu'alama da wasu mazan, a iya tunanina idan na aureta ba zata daina ba ni kuma ba zan samu aminci da ita ba, and every good man yana son ya samu mata mai tarbiya kuma yar gidan mutunci kamar ke...”

Ta yi masa da kanta.

“Nana fa?”

Ya tabe baki tare da daga kafadunsa.

“Na taba fada miki cewar hadin Hajiya ne?”

Ta dago tare da daga masa kai.

“I don't think ina son Nana a raina, ina mata dai so ne irin na kanwa da yaya, amman bana soyayya ba, kawai dai na bi umarnin Hajiya ne, ita kanta Nana a yanzu idan aka tambaye ta za ta ce bata so na”

“Amman idan Hajiya ta ji, Ammy da Shattima da Mansura da Nana zan shiga uku...”

Ya dora yatsansa a kan bakinta.

“Shiiii you talk to much, ki manta da kowa a yanzu, duk wata matsala da rigima ni ne zan shiga ba ke ba”

Ya mike tsaye.

“Bari na dauko abu downstairs”

Yana juyawa sai Falmata ta mike tsaye ta rumgume shi da baya.

“Wata kila idan na rumgume ka zan yardar kai ne, kuma zan yarda ba mafarki na ke ba”

Ta fada tana lumshe wasu hawayen da bata san na minene ba su ka


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login