Showing 204001 words to 207000 words out of 286946 words
zabura da sauri ya ya shiga gaba suna binsa a baya har suka isa gurin da ya sauke su Bappa, shi da kansa ya shiga karamin falon da sallama suka amsa masa, suna bata cikin hakkinsa. Fadime na jin muryar Bappa ta fara kokarin sakin Jekadiya tana kiransa.
“Bappa...”
Kamin ya fito har Jekadiya ta kama hannunta ta shiga da ita cikin falon, ganin Fadime yasa idon Bappa cika da kwalla ita kam tu ni nata hawayen suka fara zuba sai hannu take mikawa ta taba shi.
“Bappa... Kai ne”
Ta fada cikin kuka da shauki, sai ya amsa mata da yaren fulantanci yana kama hannunta.
“Fulani...! Har nan kika kawo mu? Fulani baki jin magana dubi yadda kika koma?”
Sai ta fashe da kuka tana taba fuskarsa.
“Dan Allah Bappa ka yafe min, na yi dana sani kuma ba zan sake ba, Bappa idona na ya rufe bana ganin komai tun ranar idon be bude ba har yanzu, Bappa ba dadi bana ganin kowa, sai dubu kullum komai zan yi sai dai na yi lalabe”
Ta kara fashewa da kuka sosai, sai lalaben fuskar Bappa take, Jekadiya na ganin haka ta juya ta fice tare da Sarkin gida.
“Ai rashin jinki ne ya ja miki, daman wanda be ji bari ba zai ji hoho... Ko ina ke ce Fadime ke ko tsoro baki ji”
Cewar Kawu dan iroro cikin fada yana tsude hannu, Fadime na jin haka ta kama Bappa ta rike tana kokarin rumgume shi.
“Bappa dan Allah karka min fada, ka ga bana gani yanzu, dan Allah kar ka ga laifina, zan fada maka gaskiyar komai da komai Wallahi na rantse”
A gurin da take tsaye ta zauna ta fara labarta musu abubuwan da suka faru na gaskiyar inda ta san ta yi karya sai ta fashe da kuka tace Bappa ya yafe mata ita ma ba da son ranta tai ba, duk abun da ta fada kwatankwacin abun da Wasim ya fada musu ne, sai karin wasu abubuwan da Wasim be fada ba domin ita zai ta fede daga biri har wutsiya, sai da ta kai karshe sannan ta tsaya tambayar Bappa tambaya mai nauyi.
“Bappa zaka bar ni na auri Wasim?”
Kamin Bappa yace komai Kawu ya kwatseta ta hanyar daka mata tsawa yana zaginta da hannu kamar tana ganinsa.
“Ke arrrr Fadime, kina abu kamar ba ki sha nonon Fulani ba, duk wannan abun da ya faru da ke be isa ya saka ki natsu ba, ki yi hankali? Ke wace irin yace? Rashin kunya kiri kiri har kina tambayar aure? To shi Wasim din musulmi ne aka ce miki? Kuma mutumen da danginsa suka miki haka kina tunanin za su yarda ki aureshi ne? Tsafe ki za su yi ko ma su kashe ki gaba daya”
Ta dafa zuciyarta da karfi tana zare ido.
“Na shiga uku... Bappa ai zai iya musulunta kuma dan sarauta ne baka ga yadda ke masa ba”
Ta fada da iyakar gaskiyarta, domin ta gani da idonta irin yadda ake bawa Wasim girma a garinsu saboda yana dan sarki abun da ya kara mata son sa kenan a ranta, tana jin ita idan ta aure shi haka za ayi mata. Bappa ya sauke ajiyar zuciya yana kallon yarsa, gaba daya ya rasa a wane muhalli zai saka Fadime, tunaninta har yanzu be bata ta fara jin tsoron ta nisanta kanta da Wasim ba sai neman aurensa take, kuma kai tsaye take fada masa haka abun da ya tabawa al'adarsu ta fulani.
“Fulani natsu ki saurareni, kin girma ya kamata ace kina da hankali da tunani kamar sa'o'inki, ke yanzu mutumen da zuwa garinsu kadai ya maida ke haka har zuciyarki take miki shaa'war aurensa? Ki fara bari ki ga idon idan ya bude tukuna kika sani ko a haka zaki zauna har abada? Sanadinayar abun da kika aikata Allah kadai ya san halin da kika jefamu, Shatu har da ciwo tai ke kuma kin zama a haka ni da Kawu da ba mu taba mafarkin zuwa yola ba gamu a gidan babba sarki a yola saboda ke, to ya isa haka nan idan kina yin hankali da tunani ki fara tun yanzu idan kuma ba zaki yi ba, ni na san maganinki?”
“Menene maganina Bappa? Ai shi Wasim din ba zama zai yi a garinsu ba, zan fada masa ya dawo garin mu ya zauna tare da mu, Bappa dan Allah”
Bappa ta ji kamar ya dauke ta da mari sai kuma wata zuciyar ta hana shi ganin halin makantar da take ciki.
SHATTIMA POV.
Yana tura kofar dakin Ammy suka yi ido biyu da Baba Waziri, wani irin abu Shattima ya ji kamar ya fasa ihu ko kuma ya juya ya koma amman ba hali, yanayin yadda ya ga Ammy na murmushi ya san ba zai wuce zancen aurensu da Maijidda ba.
“Waziri samun dan'uwa irinka abu ne mai wahala a wannan zamani, kwata kwata kai ta kanka kake ji ba ta dan'uwanka”
Cewar Ammy tana kallonsa da murmushin irin yadda yake nunawa mai martaba da yayansa kulawa abun har mamaki yake bawa Ammy. Baba Waziri yayi murmushi.
“Ammy kenan, irin mu suna nan da yawa, ai ko'ina akwai mutanen kwarai, kuma rayuwar duniyar nan idan ba ka yi dan Allah da zumunta ba dan me zaka yi? Mu na yi saboda yaranmu su ma su gani su koya daga garemu, a can ba mu san kanmu ko yayan mu sai yayan yan'uwa su ne namu na mu kuma su ne na su”
“Allah ya saka da alheri ya kara hada kanku kuma ya hada kan zuri'ar gaba daya”
Sai da Baba Waziri ya gama magana da Ammy sannan Shattima ya mika masa gaisuwa yana kallon Ammy domin ta hanyarta yake gane labari mai dadi ko akasin haka, tsoronsa daya kar ace zancen aurensa ne Baba Waziri ke yi, tun da ya sanar masa tun a waya cewar ya fara shiri, Baba Waziri ya duba Shattima duba bana wasa ba, irin duban nan na babba da yaro ya soma magana cikin dattijantaka.
“Shattima ka yi hakuri, ban nemi shawararka ko izininka ba na tsayarda rana karshen watan nan, na san idan na tsaya neman shawararka zaka fara kawo wasu kabli da ba'adi ne, kuma ina jin na isa da kai shiyasa nai haka”
Shattima yayi shiru be ce komai ba, sai dai har ga Allah be son wannan hadin da Baba Waziri yai tsakaninsa da Maijidda, ya san tana tsoron ta aureshi ta mutu kamar sauran matan, kuma ko da babu mutuwa ba lallai ne a samu kwanaciyar hankali a tsakaninsu ba, domin shi be taba kawo ta a ransa ba, ita ma kuma bata taba kawo shi a ranta ba, ko da ma ace sun taba irin yadda Hajiya Talatu taka kin Ammy abu ne mai wahala ta bar su su yi zaman lafiya balle kuma ga wannan jarabawar da take tare da shi.
“Ba ka ce komai ba”
Baba Waziri ya fada jin yayi shiru ya kasa furta komai, ga fuskarsa bata nuna jindadi ko akasin haka ba. Shattima ya dago ya kalli Ammy sannan ya kalli Baba Waziri ya ce.
“Baba ita Maijidda ta amince? Idan har bata amince ba dan Allah kar ayi mata dole, ni akwai wanda zan iya nema a hadamu...”
Ammy ta watsa masa wani kallo mai kama da harara, Baba Waziri ma kallonsa yake.
ZAINAB POV.
Cikin abun da be fi kwana biyu ba, ta rame ta koma kamar marar lafiya, ko da yake za a iya kiranta da marar lafiyar amman ta zuci ba na jiki ba, damuwar da take ciki ya mata yawa, idan ta fara tunani sai ta rasa ta ina zata tonke. Ta ya zata tuna cewar mahaifiyarta ce ta kashe mijin da zata aura ta ji sanyi? Ta ya tunaninta zai tsaya akan abun da mahaifiyarta ta aikata na kashe mutanen da basu mata komai ba face kyautawa hankalinta ya kwanta? Ta ya zata tuna yadda rayuwa ta zo mata a birkice a haife ta bata hanyar sunna ba kuma ta jidadi? Anya farinciki zai sake kusantarta? Sai a yanzu ta gane darin dukiya da kyau ko isa ba shine farinciki ba, kuma a yanzu ta yarda ba komai kudi suke iya siya ba, domin da ace kudi suna siyen komai da ta siye wata uwar ta canja iya, da ta siye wani uban ta canja wacan da yai cikinta a tasha wanda ko sunansa ba ta sani ba.
Barin jikin window tai ta saka hannunta ta share hawayen da suka zubo mata, sannan ta nufi kofar dakinta ta bude ta fita, a falo ta samu Iya tsaye tana gyaran zane da alama fita zata yi domin har ta sanya hijabi.
“Ina zaki je?”
Zainab ta tambaya daga jikin kofar dakinta da take tsaye, sai Iya ta dago ta kalleta.
“Unguwa”
“Unguwa gurin me? Shekaranjiya kin fita jiya ma kin fita kullum sai kin fita, amman wannan fitar da alama mai muhimmanci ce shiyasa kika saka sabon kaya”
Iya ta daura zanenta tana kallon Zainab da mamaki.
“A da can baki min irin wannan sa'idon, ke da na haifa kike da damar fita ki yi yadda kike so balle kuma na haife ki? Ni ce uwarki fa karki manta”
“Na san ke ce uwata ai, na san ke kika haife ni haihuwar da bata min rana ba, enough is enough Iya! Ki bar Ammy da iyalanta su huta, ki bar Shattima yayi rayuwa kamar kowa, mutanen nan ba su miki komai ba sai karamci da kyautatawa, idan ma tsoron kike asirinki ya tonu miyasa kika aikata tun farko? Wallahi idan baki kyale su ba Iya sai na aikata abun da baki taba tunani ba”
Ta karasa cikin kuka mai karfi hawaye na sauko kamar dan ta kadai akai yi su, juyawa tai da sauri ta koma dakinta tana kukan da ita kanta ba zata iya fadar na wanene a cikin danuwarta ba, kamin ta karaso gurin gadonta ta hango Wasim tafe sanye da kananan kaya kamar wacan karon, banbancin wacan dress din da wannan wacan black ne wannan kuma red T-shirt da blue jean sai hular sanyi da ya rufe fuskarsa da ita ma red ce.
_________
Ina mata matan kwalisa Matan da suka ansa sunansu na Mata? Ina wadanda ke cewa mun yi mun yi bamu ga amfaninshiba? Hmmm to ku zo ga Yar gidan Maifata ta zo maku da Al ajabu, dan tsugunno, gumba da tsimi da Zuma daban daban, maganin sanyi na maza da Mata. Ga kuma garurruka irinsu mallakau sabuzu kuwa, sa bahaushe saibi, Dan hubbare kafi malam aiki, ke kadai ke da miji, dahuwar kaza, tattabara, ciccibi da dai sauransu. Ba anan kayanmu suka tsaya ba, muna hadin amare na musamman turaren sutura turaren tsugunno turaren wanka da na daki da na jiki duka 4amare nasu na musamman ne, amma ga tsuhuwar da ke son komawa yarinya itama zata iya zuwa ahadata kai abundai sai wanda ya gani, dan haka karkubari abaku labari, domin neman karin bayani zaku iua nemana ta wannan number 09029891757 ko 08169311410, muna aikawa ko'ina a fadin kasar nan har waje kasar nan muna aika kaya.
Address: Nasarawa Samaru Area gurin masallacin mai sola Gusau Zamfara state Nigeria.
50
*Littafin nan na kudi ne biya ki karanta cikin aminci. Pay 300 to 2451879008 Hadiza Abubakar Zenith bank, then send the evidence via 08036126660*
SHATTIMA POV.
“Wannan wane irin zance Shattima? Waziri na iyakar kokarinsa kana son gujewa abun da yake shirya maka? Dan Allah ka kwantar da hankalinka babu abun da zai sake faruwa Inshallah”
Ammy ta fada sannan ta kalli Baba Waziri ta ce.
“Waziri a cigaba da shirye shirye, karka biye masa, domin na gane manufarsa ya cigaba da zama a haka”
Baba Waziri yayi murmushi irin na su na manya.
“Ammy kenan, ai Shattima ko be auri Maijidda ba, dole zai auri wata, na zaba masa Maijidda ne saboda na san a halin da ake yanzu yana wahala ace ga wanda yake so, kuma Inshallah babu fashi duk wani shirye shirye da ya kamata na fara shi, kuma yau zan yi magana da mahaifiyarta Inshallah”
Shattima yayi shiru yana saurari kamin ya dago kai da zimmar yin magana sai Ammy ta hana shi da ido, hakan yasa shi yin shiru har sai da Baba Waziri yai ma Ammy sallama ya fita, sannna Ammy ta kalli Shattima cikin damuwa ta ce.
“Abun da kake be kamata ba, na san ba lallai ne ace kana son Maijidda ba, amman ko dan darajar Waziri da irin yadda yake maka tsaye a komai ya kamata ace ka amince, idan tsoro a ranka ka cireshi, indai har da gaske iya ce take cinye maka mata, zan tabbatar kuma zan yi magana da Hajiya Talatu da kaina”
“Ki yi magana da ita kuma? To ai za ki jefa rayuwar Fadime ne a hadari, aa gaskiya kar a cutar da ita, tana fama da makanta a kara mata wani”
“Sai na fada maka zuwa zan yi na fada mata cewar wata ce ta zo ta fada min? Kamar baka san wacece ni ba? Kowa ya ji haka a ba zai dauki abun da gaske ba”
“No Ammy bana son yarinyar ta shiga matsala, karki yi magana da Hajiya Talatu, ni nasan abun da zan yi”
Yana fadar hakan ya tashi cikin rashin jindadi, ya fice daga daki. Ammy da bishi da kallo har ya fice sannan ta dauki wayarta ta kira jekadiya.
“Ki shigo ina nemanki”
Ta aje wayar ba tare da ta jira abun da Jekadiyar zata fada ba. Cikin yan dakiku Jekadiya ta shigo dakin da saurin ta bayan ta yi knocking Ammy ta mata izinin shiga.
“Ranki ya dade gani”
“Jekadiya ina son ki samo min hantiti, da tsakin kuka, sai bushenshen kashi, ki hade su guri daya, idan an samu ki fada min, sai na aika kiran Iya, idan zata shigo nake son ki turara shi a falo”
“To ranki ya dade za a nemo da yarda Allah”
Ammy ta dauko 3k ta mika mata, duk da ta san hantitin ne kawai abun da zta nemo domin tsakin kuka bushesshe da ƙashi ba abu ne mai wahalar samu ba.
SIRLEEM POV.
Shi ya fara shiga yai alwala ya fito sannan ya rika hannunta ya shiga ta ita bandakin, kusan rabin alwalar duk shi yai mata sannan ya sakota gaba suka fito da kansa ya shimfida katuwar carpet ya shiga gaba ita kuma ta tsaya daga baya tana yafe da mayafin da aka kawo ta da shi ta kabbarta tana binsa a baya, raka'a biyu yai ya sallame sannnan ya dora da addu'a kana ya juyo ya kama kanta ya karanta addu'a, sai ya ji wani irin natsuwa da nishadi yana sauko masa, duk da kasancewar yana a halin da shi kansa ya san ba son Falmata yake ba, sai dai yana tausayinta kuma kuma yana jin idan har ya aurenta yayi dacen mace mai hakuri da tarbiya kuma zai taimaki rayuwarta.
Sai ya ji wani girma da dattijanta ta kama shi, look at him wai shi ne mai aure a yanzu kuma matarsa ce a gabansa abu kamar a mafarki. Naman da ya siyo ya dauko ya aje gabanta ya fara cira yana kai mata a karamin bakinta, sai ta kasa karba saboda kunya da nauyinsa da ya kamata, tashi yai ya koma kusa da ita ya zauna ya jata kusa da shi sosai ya kwantar da kanta a kirjinsa, sannan ya kai mata naman a baki, a hankali take taunawa tana jin wani irin kunyarsa ya cika mata ido, bata wani ci da yawa ba tace masa ta koshi, sai ya zuba lemun ya bata ta sha shi ma kadan, sannan ya hada komai ya maida gefe.
“Teema...”
“Na'am”
Ta amsa ba tare da ta kalleshi ba, hannunsa ya kai ya kama hannunta ya soma mata magana a natse.
“Na san kin saba da kalubalen rayuwa, kin saba shiga abubuwa kala kala, ina son ki san rayuwar yanzu da kika shiga da ta baya ba daya ba ne, ada can ke budurwa ce yanzu kuma matar aure, matar auren ma matar Sirleem, mutumen da ya aureki a boye, na fada miki wannan ne saboda kin san cewa akwai kalubale a gareki nan gaba, ban ce zaki shiga wani tasku na rayuwa ba, amman na san kamin ki sha da dadi a gurin Hajiya zai kin fara karbar azaba, so ina son ki daure saboda mahaifiyata ce, ni kaina a yanzu ta hana yin waka, ba abu ne mai sauki a gareni ba, amman a haka na tattara komai na aje, saboda na bi umarninta, na san idan ta sani ranta zai bace sosai, shiya saka ko dangin mahaifina ban labartawa ko wa ba, domin na san maganar zata koma a kunnenta, saboda akwai shakuwa da fahimtar juna a tsakaninsu dole za a samu wanda zai labarta mata, ba daga Hajiya kadai ba har dangin mahaifina na san ba lallai ne su karbe ki da wuri ba, kuma ba lallai ne su nuna miki so kamar sauran matan yan'uwa ba, saboda banbanci matsayi da kuma yanayin yadda na auro ki, ina son ki saka a zuciyarki cewar kina da kima da daraja mai yawa a gurin mijinki, kuma duk wani abu da zai bata miki rai zan yi kokarin kiyayewa domin a yanzu farinciki kike bukata, ina son na fada miki wani abu wanda be zama lallai yai miki dadi ba, idan har Hajiya ta cilasta cewar sai na auri Nana ko wata, ba zan bijirewa umarninta ba, sai dai hakan ba yana nufin na wulakanta ki ba...”
Yana soma fadar hakan sai jikin Falmata yai sanyi, tabbas ta baro wata wahalar zata fuskanci wata, ta san a yadda take ba kowa ba idan Hajiya ta ji ya aureta sai ta sha wahala da wulakancin a duk familynsa, bayan ta laka mata sata a lokacin da babu hadin komai a tsakaninsu balle yanzu da danta ya aureta, a take ta nemi farincikin auren Sirleem din ta rasa, zuciyarta na raya mata kara wacan da wahalar da wannan da zata fuskanta.
“Ba ina fada miki wannan ba ne saboda hankalinki ya tashi, ina tunatar da ke ne abun da ke gaba wanda be zama lallai ya zo kusa ba, wata kila sai nan da shekaru”
Ya fada yana murza tsiraran yatsun hannunta a hankali yana kallon fuskarta.
“Karki min kuka fa come here”
Ya kara janta jikinsa ya kwantar yana shafa kanta zuwa wuyanta.
“Ko da wasa wata