Showing 81001 words to 84000 words out of 286946 words
dauki tray tana fadin.
“Idan kin isa ki tsaya na je na kai wannan tray a gida ki ga yadda ake hauka, Wallahi fadan kaza zan miki”
“Tsoro kike ji yarinya shiyasa kike son ki gudu, kin san ba zan taba raga miki a balle ki sha da dadi”
“Ke dalla can gafara jahila da bata iya turanci ba, nonsense stupid girl, if you dare touch my body i will regret it”
Dan turanci da Fadime tai yasa hankalin samarin dake wajen ya dawo kanta har ma da matan, suna ta kallonta cike da burgewa, Bintalo kuma tai cikinta ta ci kwalarta zata fara dukanta sai Fadime ta saki tray ta fara bamkarewa tana aljanun karya.
“Mu zaki taba mu aljanu?”
Ba shiri Bintalo ta saketa ta auna da gudu yan matan dake kusa ma ko wacce ta ari kafar kare, Fadime dadi ya kume ta ta fadi a gurin tana ta kuka kamar gaske, duk abun da take ana bata hakuri da masu tofa mata addu'a kudinta na mallake a hannunta, sai dariya take cikin Hijabin daya rufe mata fuska. Da taimakon samarin gurin aka rikata aka kaita gidansu. Inna na ganinta kamar a sume hankalinta ya tashi Amo ma bakin kofa ta fito ta tsaya tana kallon ikon Allah. Fadime kamar ficewar mutanen da suka kawota take jira ta fara wani sabon kuka wanda yai daidai da shigowar Bappa, sai ta fara karkace kai.
“Dole ne a barta taje birni gobe, dole ne sai an nemo wannan saurayin, dole ne ace ya dawo ayi auren kun gane....?”
“Eh to to”
Inna ta amsa da sauri jikinta na rawa, jin Bapppa be ce komai ba yasa ta fara tunanin ko dai ya gano ta.
“Mun san cewa ka fadawa Baban abule cewar ya kara aure ko ba haka ba Bapppa?”
Bapppa ya gyada kai dan ya san daga shi sai abokin nasa su kai wannan maganar, kuma abokinsa ba sa'an Fadime ba ne balle yace shi ya fada mata, yanzu kan ya fara yarda aljanun ne sai dai ba zai yarda su cutar masa da ya ba.
“Kwarai kuwa an yi haka, wai me kuke nema a jikinta ne?”
Fadime ta yi shiru tana tunanin abun da zata fada, can ta tuno da som bada magani da take da kuma maganar wutar da Wasim ya fada mata ko ma karya ne yai mata shi yake saka mata wutar yau zata mata rana.
“Magani zamu fada, saboda akwai mayu a ko'ina masu bin mutane da wuta, kuma akwai mugayen bil'adama”
Fadime na rufe baki, Amo tai fuu ta shige bukkarta tana jin mararta na cika da fitsari, ga wani uban rawa da jikinta yake kamar mazari. Bappa ya girgiza kai.
“A a ni ƴata ba zata yi bokanci ba, haramun ne sam ba zan bari ba, ko dai ku fita daga jikinta ko nasa bulala yanzu na zaneku kuma na muku karatu na kone ku”
Fadime na jin zancen bulala ta kwanta a gurin.
“Mun tafi sai anjimanku bye bye bye”
Ko minti biyu bata yi ba ta mike tsaye wai aljanun sun tafi. Inna dai sai kallon tsoro take mata. A daren Amo kasa fita rawa tai duk kuwa da irin yadda jikinta take tsuma na son fita rawar da take, gashi gobe Bapppa zai juyo da girkinta ba damar fita tun da kwana biyu biyu suke. Haka nan dai ta daure ta fito tsakar gidan, sai ta zagaya can bandakin dan wuta har ta fara fita jikinta, tana shiga ta fara ɗaye fatar jikinta ta cireta tsaf sannan ta aje a gefen wani dutse da ba za a gani ba ta fara karanta wasu abubuwa tana rawa da halshe tana birke ido, sai ta fara kankancewa tana yin kasa ta dora hannayenta a kasa irin yadda dabbobi suke yi, a take jikinta ya fara gashi hallitarta ta canja daga mutum zuwa bakar mage, tsale daya tai ta tsallake zanar da aka zagaye bandakin da ita sai gata a filin dake harabar wajen zanar, a nan ma cigaba da karanta abun da take karantawa gashin ya fara barin jikinta ta dawo a mutum sai ta mike tsaye ta fara rawa wuta na fita a jikinta idonta ta sauya kala kamar ba nata ba, halshenta sai rawa yake kamar zai zazzago kasa, sai dai kafafuwanta suna nan a na mage tana ta rawa da su tana barin sawu, can kuma ta sake zama magen ta tuma ta dafa kan bukkar Fadime tana wani iri kuka na tayardar hankali, Fadime na fara ihu ta sauka ta nufi makotansu. Sai dai bata yardar ta bar sawu a na makonta ba saboda ta san, idan maye yai rawa da dare, da safe idan aka duba inda yai rawar zaka tararda sawun irin dabbar daya zama yai rawa, idan doki ne ko zaki ko mage ko kare ko akuya ko kura ko saniya duk za a gani matukar sun yi rawar a kasa.
(Allah ka mana tsari da mayu da duk wani abu mai cutarwa, suna cikin al'umma ba iya gane su sai Addu'a)
*Littafin nan na kudi ne biya ki karanta cikin aminci. Pay 300 to 0314795884 Abubakar Hadiza Gt bank, then send the evidence via 08036126660*
22
*Littafin nan na kudi ne biya ki karanta cikin aminci. Pay 300 to 0314795884 Abubakar Hadiza Gt bank, then send the evidence to 08036126660*
Tun a jiya da Ammy ta fada mata cewar zata rika zuwa aiki 7am sai ta aje daukan ruwa, tana tashi da safe ta share ko'ina ta yi wanke wanke sannan ta shiga tai wanka, ta shirya ta saka Hijabinta ta fito garin ma be gana wayewa ba, ta fito ta saka talkaminta ta isa kofar Tumba wacce ke dunkule tana bachi.
“Umma Umma”
Sai da ta jera mata kira ya kai goma sannan ta amsa.
“Ya akai?”
Tumba ta amsa da karfi.
“Zan tafi aiki”
“To ki tafi mana ina bachi zaki wani tashe haba mana”
Falmata ta juya ta kama hanya, sai da tai addu'ar fita daga gida sanna ta fita tana tafe tana kallon unguwar ta so da mutane ba su gama fitowa ba. Idan Tsohuwa mai koko ta biya, ta shiga gidan da sallama, tsohuwa dake zaune tana kunna wuta ta amsa mata.
“Falmata ce”
Sam bata ji abun da tsohuwar tace ba sai kawai ta dora mata da gaisuwa da kuma bukatar abun da ya kawo ta.
“An tashi lafiya, Tsohuwa dan Allah kina da goro ki sammanin?”
Tsohuwa ta gyada kai tana murmushi.
“Eh ina da goro kuwa yau goro za a ci”
A nan kam ta ji abunda tsohuwa tace domin tsohuwa ta fada da karfi tana unkurin tashi.
“Eh dan kunne zan like”
Daki tsohuwa ta shiga ta dauko goro daya ta raba rabi ta mikawa Falmata.
“Gashi yar albarka”
Falmata ta saka hannu biyu ta karba.
“Na gode Allah ya saka da alheri”
Ta juya cike da jindadi ta fice daga gidan, a yau ba ta titi ta bi ba saboda tana son diban furen tunfafiya da yake a tsakankanin gidanjen da ba a gama ba na unguwar. Ta cikin unguwa take tafiya har isa gaban wani katon gida da aka fara gine ba a karasa ba, gefen gidan ciyawa ce sai tunfafiyar da ta fito da yawa wata babba wata karama, sai dai ba ko wacce ce ke da fure ba, haka ta rika bi tana dubasu har ta samu wacce ke da fure ta tsinka ta jimke tare da goron sannan ta kama hanya.
Sai kusan 7:40am ta isa, kamar kowa kowa hada hadarsa kawai yake ita kuma tana tafe tana rabon ido ko zatai yi arba da Iya, so take ta kara tabbatarwa idan har da gaske mayya ce, jiya dai kam bata ganta ba har ta bar gidan. Cikin sa'a kuwa Falmata ta hangota tana magana da suwa hadimai da alama nuna musu take inda za su gyara. Da sauri Falmata ta balla goron ta saka furen tufafiyar a baki tana taunawa, sai mulgunar baki take kamar wata tsohuwa, tana isowa gurin Gate din ta mikawa Iya gaisuwa sai kallonta take.
“Barka da safiya”
Suna hada ido Iya tai saurin kawardar kanta tana yamutsa fuska kamar wacce tai arba da kashi, ta daga mata hannu alamar ta wuce ta wuce kawai.
“Almu dauko min karen can”
Ta nuna karen iccen mangoro daya fado tana ta kokarin juyawa dan kar ta sake ganin Falmata, da sauri Falmata ta nufi karen ta dauko ta miko mata da yatsu biyu dan kara tantancewa, domin a iya saninta ba a nuna maye da yatsu biyu yatsan manuni da mai binsa ba a mika musu abu da shi ko a nune su da maye da mai sirihi donin manuni yana karya lagon mutun, Mama ta taba fada mata haka tun bata girma sosai ba. Falmata na mika mata karen Iya taja baya ta bude baki tana kallon yatsun Falmata.
“Ya haka haka? Miye haka kuma? Miyasa zaki yi haka? Amman dai baki kyauta ba, ke wai wace irin yarinya ce”
Maganar kawai take kamar wacce ta rude sai kallon karen da Falmata mika mata take ta kasa hada ido da Falmata dake ta aikin taunar goron tana kallon cikin idon Iya da mugun mamaki. Jefar da karen tai ta nufi cikin gidan tana waige Iya, a yanzu kam ta tabbatar Iya mayyace dan ga zahiri ta gani, abubuwan nan biyu da tai bayan na shekaranjiya da ta fara mata addu'a ta kawar da kai.
‘Ke nan ita din mayyace, amman su ba su sani ba’
Ta fada a ranta, tana cigaba da tafiyar tsoro na kara shigarta domin bata taba arba da maye ido da ido kamar yanzu ba. Har da isa bakin kofar tai knocking aka bude mata bata daina tunani ba. Har kasa ta kai ta gashe da Jekadiya sannan ta mike tsaye ta nufi dakin yan uku, samunsu tai a kwance suna bachi, kamar yadda aka fada mata ba a shara idan suna cikin daki dan haka ta dauki Labib a hankali ta fito da shi daga dakin ta nufi dayan dakin da aka nuna mata jiya, tana shiga ta samu babban gado da kayan wasan yara kala kala a dakin kamar wani karamin kamfani, ga fentin dakin pink, washe baki tai tana kallon yadda aka tsara dakin kamar ba a mutuwa, wai kuma nan dakin yara ne, ko da yake ko a tsarin gidan ta duba ai ta san sun isa.
Sai da ta gama bawa idonta abinci sannan ta aje Labib akan gadon dake shimfide da zanen gado dan ubansu mai taushi da laushi ga shi sai sheki yake kamar an zuba masa kyalkyali. Juyawa tai ta fita ta dauko Luma ita ta dawo da ita dakin ta kwantar kamshin dakin sai dukan hancinta yake.
Komawa tai dayan dakin ta gyara shi tsab sannan ta dawo inda suke ta tararda da sun farka har sun fara kuka, da sauri ta dauki Labib ta rarrashinsa sannan ta fita dashi daga dakin ta koma dayan dakin ta dorashi akan gadonshi ta bude wardrobe ta dauko madararsa ta dama masa da ruwan zafin dake cikin flask aka dora a dorowar, ta zuba a cikin fidarsu ta fara bashi. Sai da ta tabbatar ya koshi sannan ta dauko Luma ita ta shayar da ita, bandakinsu ta shiga ta hada musu ruwan zafi sannan ta fito ta fara cire musu tufafinsu ta saka su a cikin ruwan dumin data hada ta wanke musu kashi, ta nade su cikin wani farin tawul. Cikin kuzari Labib ta hau wasa Luma kuma tana da kuka sama sama. Kanta Falmata ta dafa ta karanta masu addu'ar tsari wacce Annabi S. A. W yake karantawa jikokinsa, sannan ta dora mata da ayatul kursiyu, sai da ta gama da Luma sannan tai wa Labib, ganin taki daina kuka yasa ta goyata da tawul tana jijjigata, tana yi ma Labib wasa daga tsayen da take.
Wata hidimar ce ta shigo dauke da babba tray ta aje wa Falmata a gabanta.
“Ance ki aje yaran ki fita waje ki karya”
Falmata ta sauke Luma dake bayanta ta mikawa matar sannan ta duka ta dauki tray ta fita waje, kamin ta isa har wani hadiyar yawu take, biredi ne yaka biyar sai kwai ga dankali da plantain da tea mai kauri ga kuma ferfesun kayan ciki a gefe har wani tiriri suke, Falmata fitowa tai daga bangaren gaba daya dan kar ma ta zauna a inda za a ga lomarta ta zagoyo ta gaban ita cen lemu dake kusa da babban garden ta zauna, kayan cikin ta fara kaiwa aiki tana yi tana ashe hannu kamar sabuwar mayya.
AA POV.
Daga bakin kofar dakinsa Anti Rabi ta aje masa dumamem tuwon shimkafa da miyar taushe da tai jiya, sai ya wani yatsine fuska.
“Kai ni ba zan ci dumame ba daga yanzu na daina cin dumamae”
Anti Rabi ta kalleshi da mamaki.
“To yau kuma?”
“Eh daga yau gurin aiki zan rika karyawa, na san abincin kala kala zaka yi asuwaki kaji ka kuskure baki da lemu, Malam harka irin da mutunci”
“Eh nan kuma ta rashin mutuncin ce ba, ka ma samu sa'a mun tashi da dumemen da koko zaka gani, gurin aikin da basa iya baka komai sai ka siye”
Anti Rabi ta fada tana harar shi.
“Amman dai tsakani da Allah kina ganin zubina kin san ni ba jini talaka ba ne, kawao dai Allah ya kawo ni cikinku ne, ni yanzu na fara jin kamshi arziki kusa kusa, kin san ance arziki kashi ko? To na fara takawa”
“Wato dai baka rabo da yarinyar nan ba AA? Sai ka jawa kanka wata matsalar?”
“Aa fa ni ko sunanta ma na manta, ina nan dai ina addu'a kin san mai neman a gurin Allah baya fidda rai”
“Allah dai ya kyauta kuma tsare dan ni wannan neman kudi naka har tsoro yake ba ni”
Yar dariya yai ya shafa kansa.
“Wato ba zaki gane ba ne Anti saboda kina cikin geto area, da ace kina zaune a birni ko? Ga babbar mota ga kato gida ba irin wannan ba, ga kajin safe sa da rana namam rago da dare soyayyar hanta, Wallahi wannan baki baki nan jikinki ma duk bacewa zai yi, ai kudi sun yi a rayuwa, Ni wallahi har jin nake kamar masu kudin garin nan duk yan'uwana ne yanzu”
Ganin yadda take kallonsa da kamar tsoro da kamar mamaki yasa shi daukar talkaminsa yasa yana fadin.
“To wai waye baya son kudin nan ne dan Allah? Kudi fa Anti bama neman haram amman halal kam sai inda karfi ya kare”
Ya nufi kofa yana laleben aljihunsa dan tabbatarwa idan makullin motar da aka bashi yana nan ciki.
“Na tafi ni”
Sai ya waigo ya kalleta jin bata masa addu'a sai yai ma kansa.
“Allah ya tsare ya kai ni lafiya ya dawo da ni lafiya, Anti ayi ta addu'a kudi fa suna tafe mun fara taka matakin nasara”
Ita dai bata ce komai ba har ya fice, tsoro take kar ya saka kansa a wata mummunar hanyar, wannan son kudin nasa yayi yawa. Mai achaba ya tara ya hau ya fada masa inda zai kai shi, kamin su isa gidan ya sauka ya biyashi sannan ya doshi gurin masu gadin gate din ya gaisa da su, tana kallon cctv camera dake leke a gurin, a nan ma sai da suka tare shi suna tambayar inda zai je.
“Ni ne sabon direban Hajiya Nana kun gane ko?”
Ya fada yana jin wata isa sai kace wani sarki ko wani mai babban mukami. Ba su yarda ba har sai da aka ce ya kirata yai magana da ita, sai ya kira number Hajiya bata dade tana ringing ba aka daga.
“Hello Hajiya Nana”
“Wake magana?”
Jin babbar murya yasa shi duba wayar ya gani idan number ce ya kira, sai ya sake maida wayar a kunne sa.
“AA ne sabon direban Nana, da wannan wayar muke magana da ita shiyasa na kira na fada mata gani na zo zan kaita makaranta masu gadin sun tare ni sun hanani shiga”
“Ba su wayar”
Hajiya ta fada daga dayan bangaren, sai AA ya mika musu suka karba su kai magana da ita sannan suka bar shi ya wuce, kai tsaye ya nufi gurin da motar take, tun kan ya karasa ya matsa key din, sannan ya bude ya shiga yai warming dinta yai reverse ya fito daga daga parking space din ya zo bakin kofar fadar Ammy ya faka. A iya tunaninsa kamin Nana ta fito za a fara bashi abun karyawa ne, hakan yasa ya fito ya tare wani bawa dake aikin mopping din gurin yace.
“Dan Allah Malam dan shiga ka ce musu sabon direban Hajiya Nana ya iso yana waje”
“Ba ni da hurumin shiga ciki Malam, sai dai kai ma wadancan hadiman magana”
Kai tsaye AA ya nufi matan ya fadawa daya ya dawo cikin motar ya zauna. Ba a dade ba sai ga ya hango Nana ta fito sanye da uniform yai saurin fitowa daga motar ya bude mata kofar, ita kuma sai kallonsa take tana murmushi wani irin dadi take ji zai fara tukata, sai da ta shiga ya maida motar ya rufe, ya shiga mazaunin direba ya ja motar suka fita.
“Hajiya ina zamu je?”
“Wani guri mu huta sai lokacin dawowa daga makarantar yayi sannan mu dawo”
Kallonta yai ta madubin gaba sai ya ga ta kara kyau kamar ba ita ba.
“Ina kenan? Hajiya”
Ta kara kwantawa tana kallon titi.
“Wani guri dai”
“To amman biya zaki yi ko?”
Ta kalli madubin ta watsa masa harara.
“Eh lallai mai wannan yaron, ban ce na saka an dauke ka aikin”
“Aikin da aka daukani daban, kin kaiki makaranta daban, har inda zan boye ki sai kin biya shine deal din”
“Aiko zaka ja na koreka daga aiki”
“Ai ba kika dauke ni ba, ita wannan Hajiyar ai ta sani shiyasa ta amince ni ina jin ma kamar yar'uwarmu ce, kuma duk kika fada sai na fadi cewar ba ki zuwa makaranta guduwa kike”
“Ni kuma na ce ke kai kake kai ni wani guri ka boye, shiyasa ka ce na dauke ka aiki”
“Na ce karya kike”
“Ai ba a karyata dan Sarauta kana cewa karya nake za a maka bulala ko a saka ka aikin wahala ko a rufe a gidan yari”
Ya dan yi shiru yana tunani sai kuma ya marairaice murya
“Nana yanzu haka zamu