Showing 210001 words to 213000 words out of 286946 words

Chapter 71 - Fulani Book 1 Hausa Novel Complete

20 Dec 2024

898

alheri ne gashi kin fara gani”

“Amman da farko ai wuya ka sha”

Yayi dariya yana kade takardunsa.

“To ai dadi baya zuwa cikin sauki, kuma wani lokacin sai anjarrabeka kamin a baka abun da kake bukata”

“Haka ne, kuma in da hakuri sai ka ga komai ya zo ya wuce kamar ba yi ba, na jidadi sosai da ta saka maka da wannan, amman tafiyarka ba zata min dadi ba domin zaka yi nisa da ni”

Ya karasa da muryar da ke nuna har a ranta abun ya taba ta, dan murmushi yai irin murmushin nan na rashin jidadi.

“Ni kaina ba zan jidadin tafiya na barki ba, amman Anti wannan ce kadai damar da ke da ita, idan nai karatu na samu result mai kyau, sai na samu aiki da zan iya daukar nauyin kaina da kuma na ki ”

“Allah ya baka iko kuma a taimake ka, ita kuma Allah ya saka mata da alheri ya nisanta da dukan shari”

“Amin ya rabb, bari na tafi na kai mata takardun, wata kila ma idan ta gan ni ta tuna da zancen gidan da tace zata baki”

“Allah ya sa mu samu, aiko da mun gode, wannan sai a saka shi haya ana ajewa yara kudin saboda gaba”

“Zamu ma samu Anti tun da Nana ce tai maganar kuma ita da kanta Ammy sai da tace zata fadawa Mai Martaba, kin ga ko ta manta Nana zata iya tuna mata, ni Wallahi jin nake kamar yar'uwar mu ce, matar nan akwai kirki sosai, ni Wallahi har kunyar ta nake ji”

Anti Rabi ta yi dariya tana cigaba da tankaden garin dan wakenta, sai ya rufe jakar takardun ya maida daki ya dauki na sannunsa ya saka a wata jakar sannan ya kara fesa turare ya fito.

“Ban ce ka labartawa kowa ba, ka bar abun sai ya tabbata sai kawai mutane su ji zaka je”

“Anti ban da abun ki wa zan fadawa, ni kaina ai sai komai ya tabbata sannan jindadi zai kara tabbatuwa a gareni, Allah yai ya bude mana kofafin alheri”

Anti ta amsa da Ameen. Yana ma ta sallama ya fice cikin jindadi da zumudi.

_________
Ina mata matan kwalisa Matan da suka ansa sunansu na Mata? Ina wadanda ke cewa mun yi mun yi bamu ga amfaninshiba? Hmmm to ku zo ga Yar gidan Maifata ta zo maku da Al ajabu, dan tsugunno, gumba da tsimi da Zuma daban daban, maganin sanyi na maza da Mata. Ga kuma garurruka irinsu mallakau sabuzu kuwa, sa bahaushe saibi, Dan hubbare kafi malam aiki, ke kadai ke da miji, dahuwar kaza, tattabara, ciccibi da dai sauransu. Ba anan kayanmu suka tsaya ba, muna hadin amare na musamman turaren sutura turaren tsugunno turaren wanka da na daki da na jiki duka 4amare nasu na musamman ne, amma ga tsuhuwar da ke son komawa yarinya itama zata iya zuwa ahadata kai abundai sai wanda ya gani, dan haka karkubari abaku labari, domin neman karin bayani zaku iua nemana ta wannan number  09029891757 ko 08169311410, muna aikawa ko'ina a fadin kasar nan har waje kasar nan muna aika kaya.
Address: Nasarawa Samaru Area gurin masallacin mai sola Gusau Zamfara state Nigeria.
51

*Littafin nan na kudi ne biya ki karanta cikin aminci. Pay 300 to 2451879008 Hadiza Abubakar Zenith bank, then send the evidence via 08036126660*


Juyowa tai ta fito daga dakin tana share hawayenta, da sauri ta nufi kofar fita daga falon ta bude sai ta gashi tsaye jinkin kofar yana kallonta. Wani irin faduwa gabanta yai a lokacin da idonta ya sauka cikin na shi.

“Ina Fadime?”

Ya tambaya yana cire hular kansa wanda hakan ya bawa gashin kansa fitowa ya sarara.

“Bana son jin sunan yarinyar, ita ce silar wagaza farincikina, zuwanta ta zo min da bakaken abubuwa i hate her”

Ta fashe da kuka tana sakin kofar da zimmar faduwa kasa sai ta ji saukar hannayen Wasim a kafadarta. Mikar da ita yai tsaye ya ya girgiza mata kai, sannan ya matsa da shoulder sa ta dora kanta.

“Ba laifinta ba ne, laifinki ne ke da kika nemi kulla alaka da ita tun farko, da baki je garin ba da duk haka be faru ba, har halin da take kokarin shiga a yanzu da bata shiga ba”

Ta dago kanta hawaye na mata zuba.

“Kasan iya abubuwan da ta sanadiyarta na ji?”

“Na sani...”

Ya amsa mata calmy.

“Ba ni da komai a yanzu, ta bata min komai na rasa farincikina, ba ni da kowa sai uwar da bata da tausayi”

“Kina da ni...mu yan uwa ne kin tuna?”

Ta fada yana kallon cikin idonta holding her hand tight, fashewa tai da wani irin kuka wanda hakan ya bashi damar yi mata masauki a kirjinsa. Ya dora kansa saman nata nasa idon na cika da kwalla.

“Na san yadda kike ji, ina jin makamancin abun da kike ji, Baba ya fada min ba zai bar Fadime ta samu idonta ba har sai na yanke alakar da ke tsakamina da ita alaka ta har abada”

Dagowa tai ta kalleshi sai ta ga hawaye a idonsa.

“Hakan na nufin sai ka rabu da ita sannan zata samu lafiya”

Ya daga mata kai.

“Miyasa ba zaka iya rabuwa da ita ba then?”

Ya lumshe ido, can kuma ya bude ya kalleta.

“Miyasa kika bari aka kaita inda zata kara cutuwa?”

“Ban gane ba”

“Waya dauke ta? An kaita inda za a cutar da ita, miyasa kika bari aka tafi da ita? Miyasa kika musguna mata? Bayan duk kyautatawar da tai miki? Ko kin manta saboda ke take cikin wannan hali? Zan miki uzuri ne kawai saboda kina cikin wani kunci...!”

“Ina da tabbacin ba za ta cutu a can ba, ina jin ba za a mata koma a inda ta tafi ba, kuma ba da izini na ta tafi ba, ta bi shi ne saboda ta yi tabargaza”

“Zata cutu, kakana ya fada min akwai wanda zata cutar da ita a gidan, na yi iya kokarin na ganin ya hana faruwar hakan, shi ma ya ki amince min har sai na bi umarnin mahaifina”

“Ba zaka iya rabuwa da ita ba na sani, rabuwa da abun da kake so akwai ciwo sosai”

Zainab ta fada tunawa da yadda ta rasa Auwal, kamin ta zare hannunsa daga nata ta juyo ta shigo cikin falon, binta yai da kallo kamin shi ma ya taka kafarsa zuwa cikin falon. Bayan duk wannan bakincikin hango mata yake wanda zata shiga a gaba.

“Sako na zo na baki...”

Ta juyo har lokacin tana kuka.

“Duk abun da zai sake ta, ki fada musu kar a mata maganin asibiti, musamman idonta kar a taba su, kuma ki bata wannan”

Ya ciro sarewar da yake busawa ya mika mata, sai da ta kalli sarewar ta kalleshi sannan ta tako zuwa inda yake ta mika hannu ta karba.

“Indai har kana sonta da gske, wata rana kai da kanka zaka bukaci rabuwa da ita saboda samun lafiyarta da kuma farincikinta, wani lokacin dole ne mu sadaukar da farincikinmu saboda wanda muke so ya samu farinciki, ba dan haka ba da yanzu na nisanta kaina da Iya, da ni da kaina zan kasheta saboda ta kashe masoyina”

Ta fadi durkushe a gurin tana kuka, gaba daya sai Wasim ya manta da tashi damuwar, tausayin Zainab ya nemi guri a zuciyarsa ya shiga yai lamo. Zuwa yai gabanta ya tsaya yana kallonta.

“Wani lokacin ba ma iya zabe daga kaddarar mu, sai dai kaddara ta zaba daga garemu, da ace zabin kaina ne da Fadime bata kasance a halin da take ba a yanzu, da ace ina da iko da karfin yin wani abu da na canja mahaifiyarki, na dawo da masoyinki kuma na siya miki wani abun, hakan kadai ya ishe ki ishara, ina da tabbaci wata rana zaki samu wanda ya fi saurayin da kika rasa, wata rana zaki nemi labarin Iya ki rasa, wata rana komai zai wuce, yaushe zai wuce? Yaushe komai zai zama tarihi shi ne ba mu sani ba”

Dagowa tai ta kalleshi da hawaye shabe shabe a fuskarta, kamar ta yi magana sai kuma ta gagara ce masa komai, har ya mike tsaye.

“Iya na san kina jina, na san kudirinki akan Fadime, kina da damar ki yi mata yadda kike so, amman tabbas ba zan kyale kowa ba, ina nufin kowa, zan tafi ban sani ba dawowata kusa ne ko nesa, amman tabbas ba zan dawo ba sai idon Fadime sun bude...!”

Ya juya rike da hularsa a hannu ya fice daga falon. Zainab ta mike tsaye da sauri ta isa bakin kofar falon ta tsaya tana kallonsa har ya fice daga gate din Mai Gadi na rike da gate din yana mamakin fitarsa bayan be ga shigowarsa ba.
Lumshe ido tai wasu hawayen suka sauko mata, tausayin rayuwarta take, samun wanda zata so ko ya so ta a yanzu abu ne mai wahala, ba dan komai ba sai dan saboda asalinta. Ta dade a tsaye bakin kofar falon sannan ta juya ta koma dakinta cikin rashin kuzari da walwala.

Iya na cikin dakinta dafe da zuciya, bata samu natsuwa ba har sai da Wasim ya bar gidan, wani irin tsoron Wasim take ba dan komai sai dan tsoron aiken da Babanta yace zai mata, sannan ta san yadda tsafin gidansu yake ba ya haduwa da maye ko kadan. Duk da kasancewar ya fita bata fito cikin dakin ba sai hudu, shi ma saboda Mai gadin ya turo kofar dakin ne yana sallama, sai ta fito ta tsaya daga bakin kofa.

“Waye ne?”

“Hajiya, wai wasu ne suka zo, dogarawa a mota, wai sun ce na sallamo ki”

“Ni”

Ta nuna kanta gabanta na mugun faduwa, ko ba a fada mata ba ta san daga inda suke, sai dai ba kiran ba ne abun tsoro, dalilin kiran ne abun firgitarwa, what if Fadime ta fada musu wani abu ne suka nemi a kirata? Ko dai minene bata isa ta hana kanta zuwa ba, hakan yasa ta share gumin daya karyo mata ta koma ta dauko mayafinta ta fito tana tafiyar kamar bata son fita yadda gabanta yake faduwa sai ka rantse da Allah zuciyarta zata fasa kirjinta ne ta fito, sai da ta kai bakin kofar fita sai kuma ta ji kamar fitsari ya cika mata mara ta juyo ta dawo dakinta da sauri ta shiga bandakin tai fitsari, sannan ta fito cike da tunani kala kala ta fita. Bata raina kanta ba sai da tai arba da dogaran tsaye jikin wata 406 su biyu suna jiranta, abun ka da an saba sai ta sakar musu murmushin karfin hali tana sama gaisuwar da suke mata.

“Lafiya dai?”

“Inshallahu lafiya kalau ne, Jekadiya ta ce mu dauko ki Ammy na son ganinki”

“Ikon Allah Ammy da kanta? Ya akai kuka gane gidan?”

“Jekadiya tai mana kwatanci, duk da haka ma sai da mu ka yi tambaya sannan muka gane”

Dayan ya bude mata kofa sai ta nufi motar ta shiga kamar ba komai, sai dai zuciyarta na ta zillo gumi sai karyo mata yake, babu abun da take hararowa sai Fadime, gashi gidan Sarauta ne asirinta na tonuwa kowa zai ji. Take ta nemi natsuwarta da dakiyar zuciya ta rasa, suna isa cikin masarauta ta sake jin mararta ta cika da fitsari, sai dai bata iya cewa komai ba ta nufi bangaren Ammy tana tafiya kafafuwanta na mata nauyi ga wani uban naso ta da saka fuskarta a gaba. Ta dade a tsaye bakin kofar kamin tai jihadin kai hannunta ta kwankwasa kuma, kamin a bude mata ta share gumi ya kai sau hudu, da ace tana da hawan jinin da tun a lokacin yayi azalinta. Jekadiya da kanta ta bude mata kofar falon, tana ganin Iya ta washe mata hakora tana dariya kamar ba komai.

“Aa Iya har an iso, shigo Ammy ke son magana da ke”

Ta wangale mata kofar dakin, Iya ta yi mata murmushin yake tana cira kafarta ta nasa cikin falon, babu kowa a falon sai tv taku daya biyu Iya ta ji wanin abun da ke hana mayu da macizar da aljanu zama lafiya, wato hantiti da tsakin kuka da kuma ƙashi, a rikice ta juya da wani irin sauri ta fice daga falon tana toshe hanci.

“Kai kai yau dakin Ammy ne yake wannan warin haka?”

“Me kika ji?”

Jekadiya ta tambaya tana mata kallon mamaki domin Ammy ta fada mata komai. Tambayar da Jekadiya tai mata yasa ta dawo hayyacinta har ta tuna abun da ta furta, gaba daya sai ta ratsa natsuwarta, ta rika jin warin yana biyota har waje, daman maye baya zama idan irin wannan hayakin yake.

“Jekadiya ki fada Ammy zan je na dawo”

Kamin Jekadiya tace komai Iya ta juya da sauri ta fara sauko kasa sai wani abu take kamar mahaukaciya gaba daya notin kanta ya kwance, duk yadda Jekadiya ta so tsayar da ita sai ta ki saurarenta, gaba daya jin tai bata bukatar zama a cikin gidan ma, sai da ta fita waje ta tari napep ta hau sannan hankalinta ya so ma kwanciya jin ta fara shakar iskar unguwarsu, sai a lokacin ne wani tunani ya zo mata, wata kila Ammy ta yi haka ne saboda ta gasgata zancen Fadime, saboda ta gano idan da gaske ita din mayyace ko kuma a a, kuma yanzu ta san dole ne zata yarda tun da har ta kasa shiga cikin falon balle har ta isa dakin Ammy.
Wani irin bakinciki da bacin rai ne ya kusanceta, bakincikin da ko mutuwa bata kai shi ɗaci ba a gurinta.

“Ammy ta yi haka ne saboda ta gane ko?”

Ta furta a fili tana jin wani tukikin bakinciki na ta so mata. Mai Napep din ya juyo ya kalleta a zatonsa ko magana take masa ne, sai kuma ya ga wani gurin take kallo rai a bace. Kunya ta zame mata biyu, ga ta abubuwan da ta aikata wanda ta san izuwa yanzu Fadime ta fada musu komai ga kuma wata karin kunyar kasa shiga falon Ammy da tai.

“Ba ki tabbatar ba, yanzu zan tabbatae miki, kin yi wauta na kokarin kama ni ta wannan hanyar, dole ne na yi abun da zai dauke mu ku hankali kuma kamin a kara wani abun ya kamata wannan kam na zanja salo”

Wannan karon a cikin fai furucinta tana sauke kafarta kasa daga kam Napep din.

“Hajiya kudinki 500 ne”

“To jira ni ina zuwa”

Ta juya ta shiga cikin gidan domin bata fita da komai ba, kana ganin tafiyarta kasan ba lafiya ba kamar an korota haka ta shiga cikin falon ta, ko ta can Zainab dake kwance kan doguwar kujera tana waya bata bi ba, ta wuce dakinta ta dauko jakar kudinta ta ciro 1k ta fita sai sauri take kamar zata tashi sama.
Bata ma isa gate din ba ta kira mai gadi ta mika masa kudin.

“Ka bawa mai Napep yana nan waje, ka karbo min canjina”

Yana karbar kudin ta juyo da sauri ta dawo cikin gidan. Fuuuu ta wuce dakinta Zainab dai sai binta take da kallo, da ada ne zata iya tambayarta mi yake faruwa amman a yanzu iyakarta da ita ido, duk da tana ganinta cikin rashin natsuwa.

Iya na shiga dakinta ta maida kofar dakin ta rufe, ta zauna bakin gadonta tana mamakin abun da Ammy ta shirya mata.

“Tun farko ita ya kamata ace na fara kamawa, da yanzu bata samu damar yin wannan abun ba, na yanzu tana can kwance tana jinya kamar mijinta, amman saboda na kyale ta har ta samu damar yi min haka? Ta tona min asiri a cikin Masarautar nan?”

Ta mike tsaye tana jin kamar ana sukanta a zaunen da take.

“Ko da yake ba laifin Ammy ne kadai ba, har da laifin yarinyar nan Fadime? Amman na san maganin abun”

Ta fada zuciyarta na raya mata ta yanke kurwar Maijidda tun a yanzu ba sai biki ya matso ba ko kuma an yi aure kamar yadda take yi ma sauran, domin idan tai tun a yanzu babu wanda zai zargeta kuma hankalin Ammy zai koma a can, sannan bata san abun da aka shirya mata ba a nan gaba.




FADIME POV.

Wata hadimar ce ta shigo falon da su Bappa suke tana sinne kai kasa ta ce.

“Shattima ya turo na tafi da Fadime idan kun kallama”

“Ki tafi da ita ina zaki kaita?”

Bappa ya tambaya, kamin hadimar ta amsa Fadime ta mike tsaye tana fadin.

“Cikin gida can gurin matar sarkin, ai a can nake zaune”

“To yayi kyau, kuma idan kin je ki yi musu shirme da kika saba, Wallahi ki kwantar da hankali ki san irin abubuwan da zaki fada ko ki yi, kina yin wasa Wallahi za su daure ki, kuma Wallahi kin dauro har abada, dan sarki babu ruwansa da makantarki”

“Bappa wai sarki ne babba?”

Fadime ta tambaya jin yadda Bappa yake tsoratata.

“Sarki ne babba, garin Yola fa gaba daya, kamar ace sarkin Katsina”

Ta zaro ido tana jin wani irin kimar Shattima da kwarjininsa suna kankwaro mata, sai a yanzu ta gane ya sarautarsu ta ci uban ta su Wasim da take gani da girma, sai a yanzu ta gane dalilin da ya saka baya son yawan magana kuma yake dadewa kamin ya bata amsa wani lokaci.
Ta mika hannunta ta inda take zaton hadimar na gefen.

“Mu tafi”

Hadimar ta kama hannunta suka fice daga falon Bappa sai nanata mata yake ta bi a hankali da yaren fulatanci. Suna tafiya Fadime na tuna abubuwan da suka faru tsakaninta da Shattima, ita ma ai ya kamata ta gane babbar Sarauta ce tun daga jin gidan sama da suke da kuma yadda suke da yawan hadimai, kuma ga sanyi ac da kayan dadi a ko'ina.
Har cikin fadar Ammy Hadimar ta shiga ta ita sannan ta saki hannunta.

“Ina za ki je?”

Bata samu damar amsa mata ba sakamakon hannun da Shattima ya daga mata sai tai saurin ficewa ta tare da tace da Fadime komai ba.

“Ke ina kika kawo ni”

“Wani guri”

Ta ji muryar Shattima daf da ita, shiru tai kamar ba ita ba tana jin girmasan da kwarjininsa na kamata, sai ta ji ta kamar yar wata kudan zuma a wata duniyar babbar duniya, gabanta ya shiga bugawa da karfi abun da bata saba ba.

“Kin ga Babanki?”

“Eh Ranka ya dade”

Ya wara yana murmushi.

“Ni ne ranka ya dade a yau kuma?”

“Dan Allah ka yi hakuri da duk abubuwan da na yi maka”

Ya juyo da ita tana fuskantarsa duk da kasancewar bata ganinsa.

“Me kika min?”

“Abubuwa da yawa ba za su


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login