Showing 213001 words to 216000 words out of 286946 words

Chapter 72 - Fulani Book 1 Hausa Novel Complete

20 Dec 2024

945

kirgu ba”

“Baki min komai ba, na san ai ba ki san komai ba, kuma ko kin sani rayuwarki ki simple ba lallai ne komai ya burge ki ba”

Shiru tai ta natsu sosai tana saurarensa kamar ba ita ba.

“Ina son nai miki sallama ne, na siya muku ticket jirginku zai tashi 7am ba lallai ne na shigo gida kamin lokacin ba, so i wanted to say goodbye”

Ta yi shiru tana wani abu na rashin jindadi yana ziyartarta duk da kasancewar tana son gida kuma tana son kasancewa tare da Bappa da Inna da kauyenta, sai dai a yanzu da Shattima yai mata wannan maganar sai ta ji kewarsa da dan sabon da tai tare da Nana ga dadin da take ci kullum.

“Ranka ya dade, yanzu shikenan ba zan sake ganinka ba?”

Ya lakace hancinta yana murmushi.

“Daman kin gan ni ne?”

“Ina nufi ba zan sake jin muryarka ba?”

“Yes ni ma ba zan sake ganinki ba, zai je ki cigaba da rayuwarki kamar yadda kika saba, kuma i hope idonki zai bude soon i mean very soon”

Ta kasa cewa komai sai saurarensa take tana jin kamar ta fashe da kuka. Ya cire agogon hannunsa ya kama hannunta ya saka mata.

“Ga wannan ki rika tunawa da ni, ban taba haduwar da macen da na ji bana son rabuwa da ita ba irinki, tun a ganin farko da na yi miki a Katsina kika kwanta min a rai, to be frank komai na ki yana burgeni i like you”

Ya fada yana kallon cikin idonta dake cike da kwalla. Ya dade yana kallonta kamin ya kai bakinsa saitin kunnenta ya rada mata.

“Bye Allah ya tsare hanya”

Lumshe ido tai hawayen idonta suka sauko, kashe kunne tai tana sauraren sawun kafarsa har ya fice daga falon, sai ta rage tsawonta ta zauna a gurin ta share hawayen da bata san dalilin zubarsu ba. After like 5 min ta ji sallamar Jekadiya ta shigo gurin sannan ta kama hannunta.

“Ta so mu je yace za ki yi ma Ammy sallama, sai na maida ke daki”

Fadime ta mike tsaye tana jin kamar a barta tai ta zama a gidan duk bata iya shaidar fuskar kowa a gidan saboda bata gani. Babu abunda take sai saurare har suka isa dakin Ammy, tana Jekadiya ta rage tsawo ita ma ta rage ta zauna kasa.

“Ammy Shattima ne ya ce na kawo ta ta yi muku sallama”

Ammy dake kishimgide ta dago tana dubanta tare da cire gilashin idonta tana murmushi.

“Yarinyar mai abun al'ajabi, ki zo mana da abubuwa zuwanki ya zama mana alheri, yaushe za ku tafi?”

“Gobe ya ce, da karfe bakwai za mu hau jirgin sama”

“Yayi kyau Allah ya tsare hanya, kamin ku tafi Jekadiya zata ba ki tsabarki”

“Na gode ranki ya dade Allah ya saka da alheri”

“Godiya take, godiya take Ammy Allah kara miki lafiya”

Jekadiya ta fada da dariya sannan ta sake rikon hannun Fadime suka fito daga dakin. Dakin Nana ta sake maida ita, dakin da take komai a ciki wanka abinci canja tufafi duk a dakin take, Nana ta bata kusan kala biyar duka sabon kaya da zata rika canjawa idan ta yi wanka.
A dakin ta wuni, abincin ta na dare ma a dakin aka kawo mata, sai dai bata wani ci da yawa ba, kadan ta ci ta bar sauran, ta tashi da kanta ta shiga bandaki ba tare da ta yi addu'a ba, daman can addu'a bata dame ta ba, tana tura kofar bandakin ta shiga sai ta ji wani irin iska da yanayi kamar ba a bandaki ba, juyowa tai ta zimmar fitowa sai ta ji ta taka abu kamar titi juyowa ta sake yi ta taka gaba sai ta sake jin abun, ta kara yin baya sai ta sake jin abun. Can kuma ta ji wani irin kara ya cika mata kunne gashi bata ganin komai sai duhu, tsaye tai a gurin kamar an dasata. tana ta sauraren karar da bata san ko na minene ba, sai dai tana jin sautin kamar ya mata yawa a kunne, can ta soma jin sautin bugun wani abu kamin ta fara jin sautin muryar mace.

“Lalalala...lafiya ...kika tsaya a tsakiyar titi?”

“Titi”

Fadime ta maimaita tana juyo ta inda take jin sautin muryar matar, kamin matar ta sake magana mijinta ya karaso ya jata ya maida bayansa da dayan hannunsa yayinda dayan yake rike da jariri.

“A ina nake?”

Ta tambaya tana jin kamar ta taba jin abun da ake kira da titi. Matar ta kalli mijinta mijin ma ya kalleta.

“Bana ganin komai sai duhu dan Allah a ina nake?”

Fadime ta sake tambaya, sai matar ta waiga tana karewa unguwar dake cike da haske a ko'ina kamar ba dare ba.

“Daga ina kika zo nan? Waya kawo ki nan?”

“Ni ma ban sani ba, ban sani ba”

Ta fada hawaye na sauko mata.

“Ya sunanki?”

“Ban sani ba, ya sunana to?”

Ta dafe kai.

“Miyasa na ake jin kaina kamar ba komai ciki? Miyasa bana ganin komai sai duhu a ina nake?”

Ta fashe da kuka ta durshe a gurin. Matar ta kalli mijinta cike da tausayi.

“We need to help her”

Wani kallo yai mata na mamaki, kana ganinsa kasan irin miskilan mazan nan ne da magana ke musu wahala.

“Aliyu bana son na ga mutum a cikin damuwa ban taimaka masa ba, na san yadda ake ji, ni ma babu irin wahalar da ban sha ba kamin rayuwa ta kawo ni a nan, har bara na yi, ko ka manta? Babu irin wahalar da ban yi ba babu irin wulakancin da ban gani ba, bana son na ga wani a cikin damuwa na kasa taimaka masa”

Dauke kai Aliyu yai ko kadan baya son tunawa da halin da matarsa ta shiga a baya, domin har yanzu yana ganin shi ne silar komai saboda dashen kodar mahaifiyarta da akai ma matarsa uwargidansa, his late wife Rahma.

“Fine idan kuma ba mutum ba ce ba? Ataa think please”

Ya fada kamar ana matso maganar daga bakinsa.

“Daga gani mutum ce, aljana ta yi wuri ta fito mana haka, ko isha'i fa ba a gama ba wani gurin, idan mu ka tafi muka bar ta nan zata sha wahala kamin ta samu taimako, ka san unguwar nan fa kowa na cikin gidansa, kamin ka ga wulgawar mota ma aiki ne, ko ma dai wacece mu da zuciya daya zamu yi mata taimako, Allah ba zai bata ikon cutar da mu ba”

Kallonta kawai yake yana gyara takwaransa dake kafadarsa. Sai ta saka hannayenta biyu ta rike kunnenta.

“Please Hamma na....”

Uffan be ce mata ba, daman can kowa ya san Aliyu ya san magana ma wahala take masa, juyawa yai ya koma gurin motar ya bude mata back seat alamar ya aminta kenan.

“Yauwa dan wajen Mama Fulani i love you”

Cewar Ataa tana dariya, shi kuma sai yai murmushi ya zagaya side dinsa. Ataa ta leki fuskar Fadime.

“Ta so mu je”

Fadime ta dago tana kallon Ataa kamar tana ganinta.

“Su waye ku?”

“Ni sunana Aisha amman ana kirana Ataa, mijina kuma sunansa Aliyu, cutar ki zamu yi ba taimakonki zamu yi”

Yunkurawa tai ta mike tsaye sai Ataa ta kama hannunta suka nufi gurin motar, sai da tai addu'a sannan ta saka ta a motar ta rufe, ta bude front seat ta shiga ta zauna.

“Ka wo Haidar din”

“Kyale shi bachi yake”

Ya fara tuki da hannu daya yana fadin.

“Za mu fara zuwa police station”

“Why? Ni fa ka san na tsani police, saboda Doc Asim mutanen nan suka rufe ni a cell kwana na biyu a ciki, bayan kuma ni ke da gaskiya, sanadin haka na rasa Lukman the one and only brother da nake da shi”

“Miyasa kike ta kokarin sai kin tuna min da abubuwan da suka faru a baya ne Ataa? Kin san zafin da nake ji? Yanzu ai komai ya wuce ya kamata ki manta”

Ta furta cikin muryar da ke nuna ransa ya bace, kallonta ta kwantar da kanta jikinsa.

“Im sorry”

He kiss her front head sannan ya cigaba da tukin. Lokaci zuwa lokaci take juyawa ta kalli Fadime da ke bayan motar duk da bata ganinta sosai saboda duhun motar sai dai ta gane kuka take saboda yadda take ja majina.
Fadime dai sai hawaye take tana ta sauraren tafiyar motar da take jin kamar ta taba jin irinsa amman ta kasa tunawa idan tai kokarin zurfafa tunaninta sai ta ji kamar an mata yaki a cikin kai.



___________

Ba mu da nepa jiya shiyasa ban samu na yi typing ba. Sai yau da safe aka kawo I'm sorry.


_________
Ina mata matan kwalisa Matan da suka ansa sunansu na Mata? Ina wadanda ke cewa mun yi mun yi bamu ga amfaninshiba? Hmmm to ku zo ga Yar gidan Maifata ta zo maku da Al ajabu, dan tsugunno, gumba da tsimi da Zuma daban daban, maganin sanyi na maza da Mata. Ga kuma garurruka irinsu mallakau sabuzu kuwa, sa bahaushe saibi, Dan hubbare kafi malam aiki, ke kadai ke da miji, dahuwar kaza, tattabara, ciccibi da dai sauransu. Ba anan kayanmu suka tsaya ba, muna hadin amare na musamman turaren sutura turaren tsugunno turaren wanka da na daki da na jiki duka 4amare nasu na musamman ne, amma ga tsuhuwar da ke son komawa yarinya itama zata iya zuwa ahadata kai abundai sai wanda ya gani, dan haka karkubari abaku labari, domin neman karin bayani zaku iua nemana ta wannan number  09029891757 ko 08169311410, muna aikawa ko'ina a fadin kasar nan har waje kasar nan muna aika kaya.
Address: Nasarawa Samaru Area gurin masallacin mai sola Gusau Zamfara state Nigeria.
52


*Littafin nan na kudi ne biya ki karanta cikin aminci. Pay 300 to 2451879008 Hadiza Abubakar Zenith bank, then send the evidence via 08036126660*


Har suka isa police station din suka yi abun da za su yi suka gama police su kai wa Fadime tambayoyi bata iya ganin komai sai duhu, ta kasa amsa ko wace tambaya komai jin sa take ya zame mata sabo, sai dai ta kan ji wani kamar ta taba jinsa. Bayan sun kama Ataa ta sake kama hannunta ta sakaa baya Aliyu kuma ya shiga gaba ita ta shiga front seat su ka ja motar zuwa gida.
A nan ma saurare kawai take har suka isa, tana jin karar bude gate din sai ta ji kamar ta taba jin irin karar sai dai a ina? Shi ne abun da ta kasa tunawa. A harabar gidan suka faka motar Ataa ta fita ta bude mata motar ta riko hannunta.

“Fito a hankali”

Ta fito tana jin kamar wani ya taba rika hannunta ta fito daga mota amman ta kasa tuna a ina ne kuma wanene. Tana biye da su har suka shiga cikin katon falon mai cike da kayan alatu, ga sanyin ac da plasma dake ta aikinta. Tana ji muryar yaran da suka yo kan Ataa da gudu.

“Momy ba ku siyo komai ba?”

“Ba mu je ba ne”

Ataa ta fada sannan ta zaunar da Fadime saman kujera, zata zare hannunta daga na Fadime, sai Fadime ta jimke hannun.

“Miyasa na ke ganin hudu? Bana komai sai hudu, haka ke ma kike gani? Duniyar ce a haka? Ko kuma ni ce ba daidai ba?”

Ta tambaya hawaye na sauko mata, sai Ataa ta juya ta kalli Aliyu da fuskar tausayi, kamin ta sake kallon Fadime.

“Ina jin ko dai idonki ya samu matsala ne, amman mu na ganin komai”

Ta saki hannun Ataa a hankali tana jinta a wani yanayi marar misaltuwa, hayaniyar tv da take jin sai ta yi kamar zata tuna wani abu sai kuma ta kasa. Hannayenta ta saka ta dafe kanta ta fashe da kuka.

“Miyasa na ke jin abu marar dadi yana ratsa ni? Me yasa bana ganin komai kamar ku? Ina jin kaina kamar babu komai a ciki”

Ta fara taba jikinta domin tantan ita din wace irin hallittace.? Ta mike tsaye sai kuma ta koma ta zauna, kamar an tsikareta sai ta sauka kan kujerar ta zauna kasa, sai kuma ta ji zaman babu dadi gaba day sai ta rasa abun da ke mata dadi a duniya, kwamtawa tai a gurin kasa ta takure kanta jikinta sai rawa yake kamar mazari. Ataa da yayanta dai sai kallon ikon Allah take, Aliyu kam har ya haye sama ya bar su a falon. Ataa ta duka kusa da ita ta kai hannu ta taba jikinta sai ta ji shi da zafi sosai hawaye sai zuba suke mata kamar ruwa.
Wani irin tausayin Fadime ne ya kama Ataa sai ta tuna ta tata rayuwar shekarun baya, wata kila ita ma wahala da azabar rayuwa ne ya saka ta a wannan halin. Mikewa tai tsaye ta nufi upstairs tana share hawayenta, kofar dakin Aliyu ta tura ta shiga, sai ta tsaya daga bakin kofar shi kuma ya dago kansa daga wayar dake hannunsa ya kalleta, be ce mata komai ba ya mika mata hannunsa alamar ta zo, sai ta karasa kusa da shi ta zauna idonta na sake cika da hawaye.

“Hamma zaka duba ta? Jikinta yayi zafi sosai kuma kuka take yi, and i think idonta ya samu matsala”

Rumgume tai sosai ya sumbanci saman kanta.

“Da ace na tsaya dubata cewa za ki yi ina kula ta”

“Ai ita wannan bata gani bata san yadda kake ba balle ta ce tana sonka”

Yayi murmushi.

“Idan kuma idon ya bude fa?”

Ta kai masa dudu a baya, har sai da yai yar kara kamar ya ji zafi da gaske.

“Ni fa ba likita ba ne balle na dubata”

“Yeah na sani, wai ka ga halin da take ciki mana”

Sannan ya sake ta ya mike tsaye, sai ta biyo shi a baya suka fito tare. Ko da suka sauko Fadime ta matse jikin kujerar sosai tana jin kamar ta shige ciki har lokacin jikinta rawa yake hannayenta kuma dafe a kanta tana ta irin kukan kamar na fita hayyaci. Dukawa yai gabanta yana kallonta yanayin da take ciki abun tausayi ma matuka, abunda ya fahimta kamar ta yi losing memory ta ne, and gashi bata gani. Hannunsa ya kai ya taba jikinta ya ji shi da zafi, sai ya mike tsaye.

“Ba mu da magani a gida, and i think Muhseen ya kamata mu kira ya duba ta”

“Okay ka je ka siyo ko kuma ka tafi da ita asibitin ya dubata”

Ataa ta fada tana jin kamar ta fashe da kuka.

“No tafiya da ita asibiti zai dauki lokaci yanzu, bari da a siyo mata wanda zata samu bachi kamin gobe sai mu ga abun da za'ayi”

“Okay bari na kai ta daki”

Ya nufi sama be dade ba ya sauko rike da keys dinsa ya fice Ataa kuma ta kama hannunta.

“Ta zo mu je ciki ki na kawo miki abinci”

Ba musu ta mike tsaye ta bi Ataa ake rike da hannunta.

“Taka a hankali stairs”

Ataa ta fada mata, the way da tai pronouncing stairs sai ta ji kamar ta taba jin wani abu makamancin haka, but she cant remember when and where, sai da ta fara takawa ta sake jin abu na kokarin tuna mata baya, sai da su kai rabi sai ta soma tuna kamar an taba rike hannunta a guri irin wannan and namiji ne ba mace ba, a kokarinta na zufafa tunaninta sai ta jiyo dariya a cikin kanta kamar ta jarirai ga wani uban kara kamar ana rushe gini, da sauri ta fisge hannunta ta dafe kanta ta saka ihu da kuka a lokaci daya.

“Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un
Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un
Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un”

Ataa ta fada har sau uku cikin dakiya tana kallon Fadime da ke yin gaba ta yi baya kamar zata fadi.

SHATTIMA POV.

After sallah isha'i ya shigo bangaren Ammy, ko kadan baya jin dadin tafiyar da Fadime zata yi, ji yake kamar sun dade a tare, tuna idan ta tafi ba za su sake haduwa ba ya fi komai taba shi. A karamin falo Ammy ya zauna, doing nothing kuma still yana jin wani irin yanayi babu dadi, and he cant tell why. Yana jin wayarsa na ringing ya ki ya daga har sai da ta kusa yankewa.

“Ra'ees”

“Ranka ya dade, transfer ka ya fito an tura maka copy a email”

“Ina suka kai ni?”

“General hospital Yola”

“I think ya kamata na bude nawa asibitin na huta fa”

“Gaskiya ya kama, amman ko ka bude ai ba zakin wannan zaka yi ba, sai ka hada biyu idan ka samu hutu kana asibitinka, ko kuma idan baka da duty”

“No ina bukatar tawa ta kaina, na shiga a lokacin da na ga dama, na fita a time din da na dama”

“Shattima kenan a gurin aikin sai an nuna musu Sarauta, kana da right tun da kana da halin budewa”

“Zan kira ka aje wayar”

“Lafiya dai?”

“Ba komai”

Ra'ees ya yanke wayar kamar yadda ya bukata, Shattima ya mike tsaye yana tuna alkawarin da yai ma Fadime na siya mata kaza da yogurt, murmushi yai ya mike tsaye yana jin ya kamata ya cika mata alkwarinta, a kokarinsa na faranta masa rai zuciyarsa ta raya masa ya tafi tare da ita daga can ya siya mata wasu abubuwan na tsaraba. Fitowa yai daga falon yana wani irin takun kasaita kamar wanda baya son taka kasa fuskar nan a hade kamar be taba dariya ba. A hankali ya kai hannunsa ya tura kofar dakin Nana ya shiga, sai ya hango abinci a kasa kusa da gadon Nana yanayin yadda aka abinci aka raga kadai ya isa ya sanar masa cewar Fadime ce ta ci shi, ga kuma agogonsa da ya bata a kasa kusa da plate din shimkafar, karasa yai gurin ya duka ya kai hannunsa ya dauki agogon yana taba kamin ya dago idonsa kadan ya kalli kofar bathroom din dake bude, maida dubansa yai kan agogon yana shafa shi, ganin an dauki lokaci bata fito ba yasa shi mikewa tsaye ya nufi bandakin, hannunsa ya kai ya kara tura kofar, sai ya ga wayam babu kowa a ciki, dan mamaki yai ya juyo yana karewa dakin kallo. Yana kokarin juyawa Nana ta shigo rike da wata sabuwar jaka sai murna take.

“Ya Shattima yaushe ka shigo?”

“Yanzu ina Fateema”

Ya amsa mata da murmushi. Sai ta nuna inda abincin da Fadime ta ci yake.

“Nan na barta ta na cin abinci ko ta shiga bandaki ne?”

“No bata ciki”

“Ko ta fita? Lemmi ask”

Ta aje jakar a saman gadonta sannan ta fita da sauri zuwa falo. Jekadiya da Inna wuro da wasu hadimai dake gurin ta fara tambaya duk suka ce ba su ga fitowarta ba. Sai ta


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login