Showing 156001 words to 159000 words out of 286946 words
zaune rike da redio ta nufa, yana ganin ta nufo shi ya mike tsaye da sauri ya aje radio.
“Hajiya?”
“Ali kai ka tsiyowa Iya tantabaru?”
“Aa Wallahi ba ni ba ne”
“Ka ga lokacin da aka shiga da su?”
“Aa ban gani ba Hajiya, ai bayan kawarki da ta zo jiya babu wanda ya sake zuwa babu wand ya shigo”
“Okay”
Ta amsa cike da mamaki, kamin ta maida hankalinta gurin Gate din da ake bugawa, mai gadin ya tashi da sauri ya nufi gate din ya bude karamar kofar ya leka.
“Malam Sannu dai”
Ya fada kamin yace.
“Eh tana nan wa za a ce mata?”
Ya saki gate din ya juyo gurin Zanab.
“Hajiya ana sallama da ke a waje”
“Waye?”
“Be fadi sunanshi ba, yace dai ace miki bako ne?”
“Bako? Ka san shi ne?”
“Aa yana tare da wata dai”
“Da mota yake?”
“Aa a kafa yake”
“Ce ya shigo”
Ta fada a zatonta irin mutanen nan masu neman taimako ko wani abu, Mai gadin ya nufi gate dan cika aikinsa.
“Bismillah Malam”
Mai gadin yaja baya yana bude musu karamar kofar gate din. Sai da Wasim ya fara shigowa sannan ya janyo hannun Fadime ta shigo. Daga kasa Zainab ta fara kallonsa kananan kaya ne a jikinsa wando da riga sai facing cap, tufafin sun karbe shi sidai ga shi fari sol cikin bakin tufafi, ba dan Fadime dake tare da shi ba da ba zata iya gane shi ba. Zaro ido tai cike da tsoro tai baya baya tana wani irin numfashi da karfi, ta da fa kirjinta.
SHATTIMA POV
Wani gurin ya nufa wayar na makkale a kunnensa.
“Ammy...”
“Na'am”
Ta amsa masa tana maida numfashi.
“Shattima na san kai mai yarda da kaddara ne, na san kai mutum ne mai karba duk abun da ya zo masa ”
A take yaji gabansa yayi mummunar faduwa.
“Lafiya Ammy?”
“Kasan rayuwa aro ce Allah yake ba mu, ni kaina wata rana zaka wayi gari babu ni, ina son kai imani da wannan kaddarar”
“Wa na rasa Ammy?”
Ya fada yana rika karfen dake gabansa.
“Labib da Luma, aron da Allah ya baka ya karbi abunsa...”
Matsa hannunsa yai jikin karfen sosai kansa na mugun tsarawa, take idonsa y cika da kwalla.
“Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un. Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un. Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un”
Shi ne abun da yai ta furtawa ta jingina da gurin ya dafe zuviyarsa, sai dai hakan be hana idonta cika da hawaye ba, wayar dake hannunsa ta subuce da fadi kasa sakamakon nauyin da yaji ta masa, gaba daya sai yaji jikinsa kamar ba nasa ba, muryar Ammy nata maimaita kanta a kunnensa.
“Doc Lafiya?”
Wani friend dinsa ya fada ya dauko wayar ya mika masa, sai Allah ya ba shi ikon bude ido ya sauke ajiyar zuciya tare da kai hannu ya karbi wayar ba tare da yace masa komai ba. Ya juya ya koma office dinsa, zaunawa yai saman kujerarsa sam ya manta da wani zancen Fadime, ya jingina da kujerar ya sake rufe ido yana kansa na mugun sarawa. Shigowar Inna da Bappa da kuma Sule ne yasa shi bude idonsa da su kai masa ja.
“Mun dawo an musu komai ranka ya dade”
Kai kawai Shattima ya iya daga masa, ya kalli Inna yana tunanin inda ya bar Fadime, a kujera right.
“Ba ku fita da yarinyar ba?”
“Aa nan na barta, ba kai kace mu barta ba muje mu dawo”
“Ni ma na barta nan na je amsa waya ko maybe ta fita, Dan Allah Sule a dubata waje”
Ya fada yana saka duka hannayensa ya murza each and every side of his head.
“Zata iya shi indai Fulani ce ai, bata jin magana”
Cewar Bappa yana bin bayan Sule, Inna kuma ta bi bayansu hankali tashe. Suna fita Shattima ya dauki wayarsa ya kira Ra'ees.
“A sama min ticket gobe zan je Yola, idan kuma za a samu yau lemme know pls, i lost my kids”
“Oh....... Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un”
Ra'ees ya amsa daga dayan bangaren, Shattima be tsaya saurarensa ba ya aje wayar ya sauke idonsa kan littafin Fadime dake saman teburin.
HAJIYA BABBA POV.
Kamar yadda ta fada kai tsaye ta wuce Kaduna su kuma suka sauka a Yola, yadda ta tararda yayarsa sai abun ya tayar mata da hankali, wata kila da bata yi ma mai martaba karya da ita ba da yanzu tana lafiya, domin bata sanin shigowar kowa balle fita hankalinta gaba daya ya face, kana ganin yayanta ka san hankalinsu a tashe yake. Ita ma kanta Hajiya hankalinta a tashe yake domin Hajiya Hansai ce kadai ta rage mata a cikin yan'uwa na kusa kuma wadanda suke jini daya, sai dai ganin hankalin yayan ya tashi musamman mata sai yasa dole ta danne nata tashin hankali ta rika basu magana tana nuna musu cewar zata tashi, duk kuwa da kasancewar ita ma kanta ta tsinke da rashin lafiyar, domin Alamu na nuna kamar bankwana take da duniya.
Kwananta biyu a asbitin ita take mata komai na jinya duk da kasancewar yayanta na kusa, domin Hajiya uwa ce a gurinta, kuma daman can tana kaunar jininta indai jininta ne wanda bata so bare ne.
Bayan ta gama sallah azahar tana zaune a harabar asibitin rike da carbe tana ja tana dan taba wayarta, kiran yarta Rima ya shigo wayarta.
“Hello”
“Hajiya”
“Na'am Karima ya gidan?”
“Ba lafiya, yanzu na ji ana cewa wai Luma da Labib sun rasu”
Hajiya ta dan tabe baki kamar abun be taba ta, kuma be bata mamaki ba.
“Da gaske kuma”
“Hajiya an karyar mutuwa ne? Wallahi da gaske ne”
“To Allah ya jikansu, sun lashe abun su kenan, mugun abu da bi su, daman ai ba albarka za su yi ba tun da suka saka mugun abu a gaba”
“Hajiya mutuwa ce? Haba ai kowa be wuce lokacin fa, ni Wallahi jikina duk yayi sanyi”
Wannan furucin da Rima tai yasa Hajiya ta tuna da Karima take waya ba Juwairiyya ba.
“Haka ne kuma Allah ya sa mu cika da imani”
“Ameen Hajiya yaushe zaki dawo?”
“To gani dai sai Hajiya ta ji sauki tukuna, Talba din ya dawo?”
“Aa ba ki yi waya da shi ba?”
“Taya ni zan kira shi shi be kira ni ba? Ina matsayin uwarsa daga tafiya n dawo ya taka jirgi ya bar gari zuwa wani birthday abokinsa a Abuja? Ai ko rikonsa nake na cancanta ya fada min, amman sai ya rika min abu kamar ni ce kasa da shi? Ya duba yayansa Shattima mana, shi haka yake? Haka ya ga yana yi ma Ammy, kullum ina fafuta akansa amman hankalinsa yana can wani guri”
“Hajiya yanzu fa duniya ta waye no need ace dan zaka je wanu guri sai ka fada, it's free world”
“Okay tau yayi kyau, ku cigaba”
Hajiya ta tsinke wayarta cike da bacin rai. Ta aje wayar tana kallon wani bangare na asibitin, cike da jindadin labarin mutuwar yayan Shattima, daman can tana bakin ciki da ba ta kanta Mai Martaba ya fara samun jikoki ba.
“Ai kadan kuke gani Wallahi, sannu sannu dai, duk wani mugun abun da kika shuka sai kin girbeshi, gashi nan kina komawa babu komai, ance bar ganin ka tara kiyayya mai nema”
Ta furta da murmushi a fuskarta, kamar wanda akaiwa albishir, sai ka rantse da Allah ba sakon mutuwa aka fada mata ba. Ya mika hannu ta dauko wayarta ta kira layin Hajiya Talatu.
“Hajiya yanzu nake shirin kiranki, sai gashi kin kira”
“Ince ke ma kin ji mutuwar?”
“Mutuwar wa kuma?”
“Yan jikokinmu, yau duk su buyin suka tafi”
“Ikon Allah? Kuma dai? Tau wannan abu wai ya yake ne?”
“Waya sani? Gamu dai gani ai da sannu sai mun cin ma nasara gashi Allah yana taimakonmu, shiyasa na ce miki ni maganar wannan bokan ba zata kayar min da gaba ba, bari dai Hajiya ta samu lafiya babu abun da za a fasa”
“Yo daman ai ba fasa zamu yi ba, ita dai wannan na dafa mata abun a nama na bata ta ci, ban san ni ko zai yi aiki oho, kuma an fada min akwai wata mai aljanu tana nan kusa da garin mola”
“Irinta ai sai dai a dauko mana ita, domin shiga irin wannan garin ai zaka ga wadanda suka sanka sosai”
“Eh nima ai haka na ce sai kin dawo zan saka a daukota, dan ce ita da madubi take aiki kuma zata fada maka komai, ko mutum kake so zata saka a dauko maka shi”
“Yauwa irinta na ke so, Allah dai ya ba Hajiyata lafiya na dawo Yola”
“Ameen, ya jikin nata yau duk ban kira ba”
“To jiki gashi nan sai hamdala, ba a cewa komai, ance ciwo ba mutuwa ba”
“Oh Allah ya bata lafiya”
“Ameen sai kin ji ni”
“To Hajiya Allah kara girma”
“Ameen”
Tana sauke wayar wani kiran na tsinkewa daga line Jurry, nan da nan ta kara kira. Hajiya ta yi picking tana murmushi a zatonta zata labarta mata ancen mutuwar yayan Shattima ne.
“Hajiya jirgin da Talba ya biyo ya fadi”
Kamar an cira Hajiya sama haka ta mike tsaye, dafe da kirji.
“Wane Talban?”
“Yaya Talba dai na mu, jigin ya kone gaba daya...”
“La'ilaha illallah, La'ilaha Illallah, La'ilaha Illallah”
Ta saki wayar ta dora hannayenta duka biyu a kai, gaba daya hankalin mutanen dake gurin sai ya dawo gurinta sai kallonta ake.
“Na shiga uku na lalace jama'a, dana Talba! Ta tabbata tafiyar da ba dawowa La'ilaha illallahu”
Yayan Hajiya Hansai sun nufo inda take da kukansu a zatonsu mutuwar mahaifiyarsu take yi ma kuka.
“Mun shiga uku Hajiya Mama ta tafi Mama ta tafi ta bar mu”
Macen ta fada tana kuka, Hajiya Babba ta juyo tana kallonta hawaye shabe shabe a fuskarta.
“Kuma dai...”
Ta furta kamin ta fadi rigigif a kasa....
_________
Ina mata matan kwalisa Matan da suka ansa sunansu na Mata? Ina wadanda ke cewa mun yi mun yi bamu ga amfaninshiba? Hmmm to ku zo ga Yar gidan Maifata ta zo maku da Al ajabu, dan tsugunno, gumba da tsimi da Zuma daban daban, maganin sanyi na maza da Mata. Ga kuma garurruka irinsu mallakau sabuzu kuwa, sa bahaushe saibi, Dan hubbare kafi malam aiki, ke kadai ke da miji, dahuwar kaza, tattabara, ciccibi da dai sauransu. Ba anan kayanmu suka tsaya ba, muna hadin amare na musamman turaren sutura turaren tsugunno turaren wanka da na daki da na jiki duka 4amare nasu na musamman ne, amma ga tsuhuwar da ke son komawa yarinya itama zata iya zuwa ahadata kai abundai sai wanda ya gani, dan haka karkubari abaku labari, domin neman karin bayani zaku iua nemana ta wannan number 09029891757 ko 08169311410, muna aikawa ko'ina a fadin kasar nan har waje kasar nan muna aika kaya.
Address: Nasarawa Samaru Area gurin masallacin mai sola Gusau Zamfara state Nigeria.
39
*Littafin nan na kudi ne biya ki karanta cikin aminci. Pay 300 to 2451879008 Hadiza Abubakar Zenith bank, then send the evidence via 08036126660*
Inna da Bappa suka fara bin asibitin suna bincikawa, Malam Sule kuma ya dauki wani bangaren, tun suna dubawa da tunanin za a ganta har abun ya fara bawa Inna tsoro, a tare suka dawo office din Shattima sai su same shi tsaye jikin window office din ya bawa kofar shigowa baya.
“Wallahi mun duba ko'ina ba mu ganta ba, nan dai kusa, kuma ai ba zata iya zuwa nesa ba”
Juyowa yai ya kalli Bappa kansa na mugun sarawa.
“Kun tambayi mutane kuma? Ni dai a nan na bar naje na amsa waya ko da na dawo ban ganta ba, so n dauka ko ta fita ne ko kuma kun zo kun dauke ta ne”
Ya karasa daker numfashinsa na dannewa, yana nuna musu kujerar da su kar barta. Inna ta kalli Bappa idonta na cika da kwalla.
“To ko sun sake dauke ta ne?”
“Su wa?”
“Aljanun mana”
“Aa kar ma ki kawo wannan maganar, haba dai”
Cewar Bappa yana kallon Malam Sule daya shigo yana tambayar Bappa.
“An ga yarinyar?”
“Ina fa”
“Na tambayi mutane sun ce an ga wani namiji fari ya fita rike da hannunta”
“Wani kuma?”
Bappa ya tambaya? Kamin ya juyo ya kalli Shattima.
“Ka san shi ne?”
“No, ban san shi ba, na fada muku a nan na barta”
Ya dauki labcoat dinsa da wayarsa da keys dinsa ya nufi kofa sai suka biyoshi, fitowa yai ward din yana tambayar Nurse din da suke nan, sai sun suka bashi amsa daya.
“Ba mu ga shigarsa ba gaskiya, amman mun ga fitowarsa tare da ita, yana rike da hannunta har tana fadin gurin na da nisa ne? To ni n dauka kana ciki ma Wallahi”
“Ina yabi da ita?”
“Fita sukai ta kofar can, yana ssnye da kananan kaya bakake da facing cap ja, fari ne sosai ina ganin fulani ne dan'uwanta”
“Aa bata da wani dan'uwan ba mu zo da kowa ba, sai dai idan aljani kika gani”
“Aljani kuma?”
Nurses din suka hada baki gurin fadar hakan suna kallon Inna da tai maganar tana kuka. Bappa ya daka mata tsawa da halshen fulantanci.
“Wai wane irin maganar banza kike haka ne? Idan ma shi ya sace ta ai kin bashi damar kubuta,bana son shashanci Wallahi”
Fulatancin Katsina da na Yola akwai bambanci amman hakan be hana Shattima fahimtar abunda Bappa ya fada ba.
“Me zai saka na sace ta? Me zan yi da ita idan na sace ta? Ina zan kaita? Wata kila akwai abun da kuke boyewa, wanda ni ban sani ba”
Bappa yayi shiru yana kallosa kamar mai tunani, shi dai kam be yarda wani ne ya shigo ya dauke ta, idan ma aljani zai dauke ta ai sai dai ace ta bata ba wai ace anga wani ya fito tare da ita ba, waya sani ko siyar da ita yai duk da be yi kama da mai yin hakan ba, amman sanin mutum ai sai Allah.
“Zan sanar da hukumar asibiti, za a ganta inshallah, ni ma hankali ba kwance yake ba yanzu aka kirani yaya biyu sun rasu, so duk abunda ya kamata asibiti zata yi”
A nan Nurses din suka masa gaisuwa, shi kuma ya wuce da su Inna gurin hukumar asibitin ya sanar musu abunda yake faruwa, sannan ya sanar musu rasuwar yayansa saboda yana son ya wuce gida ya shirya komai tun yanzu, alam baram Bappa yace babu inda Shattima zai je sai an ga Fadime, Inna kam bata aikin komai sai kuka, kamin kace kwabo labari ya karade asibitin, a lokacin da bincike ya kai har gurin masu gadin asibiti sai su bada shaidar cewar tabbas sun ga shigowar shi da kuma fitarsa tareda yarinya, a gurin da ake faka napep din haya ya nufa da ita ta shiga Napep din nan. A lokacin ne Bappa ya kara yarda cewar ba aljani ne ya dauke ta ba, likitan ne ya siyar da ita. Shattima ya rasa da wanne zai ji mutuwar yayansa ko kuma wannan abun daya same shi? A dole ya koma office dinsa ya zauna after ya yi sallah la'asar. Yana nan zaune kiran Baba Waziri ya shigo wayarsa, ya dauka ko Baba Waziri zai masa gaisuwa ne ko kuma ya bashi hakuri, ashe wata mutuwar zai sanar masa.
“Ka yi kokari ka zo gobe da Safe, bayan yaya da ka rasa ka sake rasa dan'uwan, Talba ma Allah ya karbi abinsa”
Kamar an jefo masa aradu haka yaji maganar Baba waziri ta sauka kunnensa, ya mike tsaye da sauri ya cire wayar a kunnensa ya duba sunan mai kiran ya ga Baba Waziri ne, ba zai masa wasa ba, ko ma zai masa ba zai masa ta mutuwa ba.
“Talba fa kace Baba”
“Talba Shattima, wai yaje Abuja, jirgin daya biyo ya fadi”
“Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un”
Ya furta yana sauke wayar daga kunnesa, Talba ne kadai dan'uwa namiji da yake da shi, how could he bear the lost of him kids and his only brother at the same time? The pain was almost more than he could bear. Yadda hawaye suka fara saukowa daga idonsa sai ka rantse da Allah saboda irin wannan ranar kawai aka halitto masa su, he couldn't bear the thought of losing them, be bude baki yayi kuka da haniniya yadda mata suke ba amman be iya tana hawayensa zuba ba, zuciyarsa kuma bata iya daukar nauyin ita kadai ba, har sai da ta rabawa wani bangare na jikinsa wanda hakan ya haifar masa da zazzabi da nauyin kirji ga gumi, da wani sabon ciwon da suka sallamo masa.
Babu wanda ta fado masa a rai a wannan lokacin sai Hajiya Babba, saboda yasan yadda take son Talba fiye da duka yayanta, kuma Talba is the only male son da ta haifa da Mai Martaba, after ita ya tuna halin da Mai Martaba zai shiga idan ya ji wannan labarin. Ta sauri ya dauki tissue ya goge hawayensa ya kira number Baba Waziri ringing tai har ta katse be dauka ba hakan yasa ya kira number Ammy, a maimakon ya ji muryarta sai ya ji muryar Nana ta amsa cikin kuka.
“Ina Ammy?”
“Ta tafi bangaren Hajiya Babba, Ya Luma da Labib sun rasu, Ya Talba ma haka”
Ta fada cikin kukan dake nuna da gaske kukan take irin kukan nan wanda baya jin rarrashi.
“Nana...”
Ya kira sunanta sai ta amsa masa da muryar kuka.
“Na'am”
Sai kuma ya rasa abun da zai fada mata ba, shi kan shi yana bukatar wanda zai fada masa wasu kalamai da za su sanyaya masa zuciya, duk wani karfi hali da dakiyar zuciya a yau ya neme su ya rasa.
“Nana ki fadawa Ammy kar ta fadawa Mai Martaba”
“Ya gaba daya gidan kuka ake, i don't want to lost someone again, I'm scared”
Kasa ce mata komai yai ya aje wayar wayar saman teburinsa ya lumshe ido, duk wanda zai ce yana jin tsoron rasa wani a gidan a bayansa yake, tun yana rasa mata yana jin tsoro har abun ya soma zame masa jiki yanzu kuma yaya ya rasa da kuma dan'uwan.
Sai biyar har da yan mintuna ya bar office din ya nufi gurin da ya san ya bar Bappa da Inna da kuma sauran ma'aikatan asibitin. Ko da yake ya tarar an tafi da su zuwa police station domin bada cigiya bisa ga shawarar da hukumar asibitin ta bayar, sun fada masa sai idan anyi bincike ba a gano inda take ba sannan yake da damar shigar da kara ko kuma daukar matakin daya dace akan yarsa amman for now ya fara zuwa ya sanarwa hukuma ayi bincike har gidanje redio za a saka cigiyar.
Shattima be bar asbitin ba har sai da ya rubuta takardarsa ta neman transfer,