Showing 153001 words to 156000 words out of 286946 words

Chapter 52 - Fulani Book 1 Hausa Novel Complete

20 Dec 2024

925

shigo sanye da uniform da alama shi ma ma'aikacin asibitin ne.

“File za a bude musu guide them pls ka yi musu komai”

“Tau ranka ya dade, ku ta zo muje”

Mutumen ya fada sannan ya nufi kofar fita, a tare Inna da Bappa suka mike tsaye Inna na kokarin kama hannun Fadime Shattima ya dakatar da ita.

“No Mama ki bar a nan, kuje ku dawo, zai zama mata wahala ne tun da ba gani take ba”

“To mun gode Allah ya rufa asiri”

Inna ta fada sannan ta bi bayansu Bappa da Sulen da suka rigata fita. Sai da suka fice sannan Shattima ya kalli Fadime dake zaune gabansa.

“Fada min gaskiya, miya samu idonki”

“Wallahi gaskiya na fada”

“Na fa san halinki ba ki jin magana”

“Ka san ni ne?”

“Eh”

“A ina? Wanene kai?”

Ta tambaya tana ta kyabce kyabce da ido, mikewa yai tsaye ya zagaya inda take ya kai hannunsa ya kama hannunta da nufin kaiwa a fuskarsa ta lalaba sai tai wani irin jan numfashi kamar ta ga abun tsoro, sakamakon sanyin da ta ji a hannunsa ya gauraya da nata hannun, wanda hakan yai daidai da shigowa kira a wayarsa.
Saurin sakin hannunta yai yana kallon kyakkyawar fuskarta da makantar bata rage ta da komai ba a kyau da haske, what if bata saba rika hannun maza ba? What if tsoron mutane take ji a yanzu tun da bata gani? Ya ma kamata ya rikata ne? Shi ne abun da yake tambayar kansa kamin ya nufi gurin wayarsa dake ringing ya dauka ya fice daga office din gaba daya.
Hawayene ya sauko a blind eyes dinta, zuciyarta ta hau bugawa da mugun karfi, jikinta ya hau bari, sai ta jimke hannun sosai kamar wanda aka cewa idan ta bude hannun zai fadi.

“Wanene wannan? Wanene kai?”

Ta mike tsaye ta fara lalaben teburin kamin ta juyo ta ta fara tafiya da lalabe tana nufar inda take zaton kofa take, tafiya kadan ta ji ta ji ta taka mutum, sai ta dauke kafarta ta yi baya, ya mika hannunta sai ta ji mutum, matsawa tai tana lalabe riga ce a jikinsa mai kamar ta sanyi, sai da ta lalabe kirjinsa tsab sannan ta kai hannunta gurin fuskarsa, hancinsa ta taba ta sauko gurin bakinsa sai kuma tai sama gurin idanuwansa, can kuma ta saka hannu biyu tana lalabar fuskar gaba daya, dage tai ta lalabo kansa sai ta ji hulla a kan facing cap, dawowa tai gurin fuskarsa tana lalaben sai ta ji hawaye ya sauko a idon mamallakin fuskar, numfashinsa kuma na kara kusantota.

“Zo muje na kai ki gurin su Inna”

Ya rada mata a kunne har lips dinsa na laba hijabinta lumshe ido tai hawaye ya sauko mata.

“Wasim...”

Ta furta domin ta gane muryarsa, wuyan hannunta ya kama ya fita da ita daga cikin office din.


FALMATA POV.

Tana cikin gyara dankalin ta ji kara door bell, sai dai bata tai wani yunkuri ba har sai da ta ji an sake danna kuma an kwankwasa irin yadda tai, sai ta aje wukar da sauri ta fito falon, ganin babu kowa yasa ta nufi kofar ta bude cike da zumudi, domin ko ba a fada mata ba ta san Sirleem ne.

“Wow”

Ya furta yana fito da idonsa waje. Sai ta sakar masa murmushinta mai kama da dariya.

“Ina kwana?”

“Lafiya Kalau, ya kike har kin iso?”

“Eh”

Ya kara fito da idon waje, ganin be daga murya sosai gurin magana ba amman ta ji.

“Kin ji abun da na fada?”

“Eh”

“Taya aka yi kika ji?”

“Na ji dai”

Ta furta cike da far'a, sai ya sako kafarsa cikin falon yana kallonta mamaki.

“Jinki ya dawo kenan?”

“Eh amman ba kamar da ba, ina jin maganar kamar daga wani daki ne?”

“Wow..... ”

Ya furta yana jin kamar ya dagata sama ya juya.

“Soon zaki dawo normal inda kina amfani da maganin daman mai karfi ne sosai, I'm happy”

Ita ma ta yi dariyar jindadi, sai ya sakar mata ido hakan nan kawai take burgeshi, if you ask him miya kawo shi a gidan yau he can't explain kawai dai ya ji yana son ganinta ne.

“Miya samu idonki?”

Ya tambaya ganin idon ya kumbura, sai tai kasa da idon ta kasa cewa komai.

“Ko an dokeki ne?”

“Aa”

“Then miya samu idonki? Karki min karya na san ba halinki ba ne”

Dagowa tai ta kalleshi sai idonta ya cika da kwalla.

“Babana...”

Sai kuma tai shiru, a hankali tana wasa da yatsun hannunta. Yatsun ya kalla yadda aka jera mata su gwanin sha'awa, sirara ga akaifar fara fes.

“Ina Momy?”

“A nan na barta da bakuwa kila tana dakinta”

Ta fada tana nuna upstairs. Sai da kalli inda yake nuna masa sannan ya kalleta.

“Me kike yi?”

“Dan kalin turawa nake gyarawa”

“Je ki cigaba bari na gaishe da Momy”

“Tau”

Ta buya sai ya fita da kallo har sai da ta shige kitchen din sannan ya nufi upstairs. Sai da ya fara knocking kofar sannan ya tura ya shiga, be samu Momy a dakin ba sai motsin ruwa da yaji a bandakin hakan ne ya tabbatar masa da tana bathroom din,jikin kofar y tsaya har sai da ta fito.

“Momy ina kwana?”

“Lafiya Kalau, yau gidan nan tun da safe”

Ta amsa shi tana kawardar fuska,  bata son ya kalli fuskarsa saboda kukan da tai. Sai yai murmushi.

“Yeah kawai na biyo ne, i thought ko iyayenta sun hana ta zuwa”

“No ta zo tana kitchen ma”

“Eh ita ta bude min kofar ma”

“Okay”

Ya saki kofar yana kallonta kamar ya tambayi damuwarta sai kuma wata zuciyar ta hana shi, wata kalma bata sake shiga tsakaninsu ba ya juya ya fita daga dakin, har ya sauko kasa be daia kwankwanto da tunanin damuwar Momy ba, duk da ya san a duniyar nan bata da damuwar da ta wuce ta neman haihuwa. Bakin kofar kitchen din ya tsaya yana kallon Falmata da yanka dankalin sala sala.

“Cutie..”

Ta dago ta kalleshi ba dan ta san abun da kalmar ke nufi ba, sai ta samu kanta da sakar masa murmushi.

“Fada min Baba ne ya taba ki?”

Ta maida kanta gurin abun da take kamin ta sake dago kan ta kalleshi.

“Ya.. Ya..”

Haka kalmar ta makale a bakinta ka kasa fitarwa, karasa yai kusa da ita ta duka yana kallonta, kamshin turarensa ya cika mata hanci.

“Ya me? Feel free ki fada min damuwarki, ba ki son ni ma na rika fada miki damuwata ina neman shawararki?”

Ta kalleshi.

“Ni”

“Eh, fada min me Baba yai?”

“Aure zai min...”

Ba numfashinsa kadai ba har bugun zuciyarsa sai da ya tsaya cak na yan dakiko, can kuma ya sake tambayarta kamar wanda be ji da kyau ba.

“Aure?”

Ta daga masa kai.

“Saboda me?”

“Ni ma ban sani ba”

Daga haka ta kwashe abun da ya faru ta fada masa.

“Wai mi yake damun iyayenki ne? Wannan step mom dinki bata da imani? Taya zata goyi bayan babanki ya aura miki tsoho? A shekarunki? Mutumen da baki ma sani ba?”

Ita dai bata ce komai sai hawaye take.

“Kuma ke yanzu aurenshi zaki yi?”

“Na riga na roki Allah, idan auren alheri Allah ya ba ni ikon yi ma mahaifina biyayya idan kuma ba alheri ba ne Allah ya musanya min”

Duk sai ya ji tausayinta ya kara kamashi.

“Ban baki shawarar aurensa ba? Zaki ruguza rayuwarki ne kawai”

Ta kalleshi hawaye na mata zuba.

“Ina kallonka a mutum mai kima da daraja, da za a bani da da duniya zan bi ina rubuta sunanka a ko'ina, saboda kwarjinka ya cika idona, amman ba zaka ba ni shawarar bijirewa umarnin mahaifina ba, kamar yadda baka bani shawarar na gudu na bar gida ba”

“Ko da hakan zai cutar da ke? Rayuwarki nake magana ba tawa ba, ban ce ki bijirewa umarninsa ba, kuma ban baki shawarar auren tsoho kakanki ba, rayuwar aure is the last life da mutum yake da, idan ka dace ka dace, idan kuma ka samu jarabawa to rabin rayuwar duniyar ba zata maka dadi ba”

“To guduwa zan yi?”

“Ban ce ki gudu ba”

“Ce masa zan yi ban amince ba?”

“Ban ce ki ce haka ba?”

“To me zan yi?”

Ido ya kura mata.

“Kina da wanda kike so?”

Ita ma idon ta sakar masa, kamar mai tunani can kuma ta sunkuyar da kai.

“Aa ba ni da kowa”

Mikewa yai tsaye yana juyowa sai yai arba da Momy dake kokarin shigowa kitchen din, at that time wayarsa dake aljihu tai ringing. Ciro wayar yai sannan ya fice daga kitchen ya kara wayar a kunnensa.

“Hello”

“Hello kawai kamar ba ka gane mai magana ba?”

“As how”

“Ya ka saba kirana?”

“Hey listen...”

“I'm not listening, ko dai ka zo Kaduna ko kuma na zo Yola, saboda magana ce mai muhimmanci I'm pregnant”

“As how you're pregnant wani abu ya taba shiga tsakaninmu ne?”

“I don't care, ko ka aureni ko na bata maka suna, ba zai yiyu na gina ka ba, wata karamar yarinya ta karbe min kai, you always telling Maman ka ce bata son aurenmu amman yanzu na gane ba ita bace kai, saboda kana soyayya da karamar yarinyar kuma har a cikin gidanku, and ba zai yiyu ace mamanka bata sani ba”

Mansura ta fada daga dayan bangare.

“Wow... Awesome... Haka zuciyarki ta raya miki? Kin manta waye Sirleem a gurinki? Yarinyar da kike dorawa laifi babanta auren dole zai mata so what's your problem?”

“You're my problem, idan ba ka rabu da yarinyar ba, i swear to God zaka ja mata matsala, ka san ni Sirleem”

“Yeah and you know me too”

Ya katse wayarsa yana mamakin yadda Mansura ta kasa masa uzuri.


After Sirleem ya fita daga kitchen din Momy ta dauki dankalin ta saka a fanfo ta wanke, sannan ta kalli Falmata.

“Matsa kusa ki ga yadda ake kunna gas din”

Falmata ta matsa kusa da ita sosai tana kallo har ta kunna, ta kashe sannan ta sake kunnawa.

“Kin ga yadda ake yi?”

“Eh”

“Good dauko kwai a firjin din can ki fasa min ki saka magi da yaji da albasa sai ki kunna wannn bangaren ki soya, ai kin iya soyar kwai ko?”

“Eh”

Momy ta bita da kallo, gaba daya rasa na zaba tsakanin burinta maganar Hajiya Umaima da kuma bijewa zuciyarta. Tabbas gaskiya Hajiya Umaima ta fada this is last chance da take da shi, this is the only hope da za tai fatan cika burinta? Amman a sirinsa ba tare da sanin Falmata ba ko kuwa da saninta? Idan ta sani zata aminta ne? Idan kuma tai mata a boya zata sake yarda da ita? Anya ya dace ya jefa rayuwarta cikin matsala bayan wacce take ciki? Ya zata kalli Sirleem nme zata fada masa? Wane hali zata kara jefa Falmata? Anya lokaci yayi da zata aikata haka? Yaushe ma yarinyar ta zo? Amman idan ba tai a yanzu ba sai zuwa yaushe za tai?

Haka ta jerowa kanta tambayoyi man da ta dora saman wuta yana ta soyuwa bata sani, ba, can kuma wata zuciyar ta bata amsa.

‘Duk abun da zai faru indai har na samu biyan bukata! Komai zai zo da sauki, zan dauki dawainiyarta zan tallafi rayuwarta, na yi mata duk abun da take so’

Ta sauke ajiyar zuciya tana kallon Falmata dake numa mata man yana konewa.

“Oh Sorry hankalina yana can wani guri”

Ta fada da murmushi a fuskarta, sannan ta fara zuba dankalin tana kallon yadda Falmata take soya kwan kamar daman can shi ne aikinta.

“Fulani baki yi karatu ba ko?”

“Eh ban yi ba”

“Kina son ki yi?”

“Eh amman yanzu ai a yi girma sosai”

“No ba a girma da karatu, zaki iya shiga a haka kuma idan kika maida hankali har jami'a sai ki je?”

“Jami'a? Karatun da ake zama likita?”

Maganar likita da tai yasa Momy ta tuna cewar ai bata ji sosai.

“Yes, Fulani yanzu kina ji da kyau ne?”

“Eh”

Ta amsa tana murmushi. Momy ma ta yi murmushi.

“Mashallah haka ake so, daman ina sa ran haka saboda maganin mai tsada ne kuma yana aiki sosai, Allah kara lafiya, sauran makaranta na nema miki ko?”

Falmata ta kalleta da sauri.

“Makaranta?”

“Eh ko baki so?”

“Ina so sosai ina son idan na ga abu na karanta ko na rubuta, ina so sosai”

“To zan nema miki inshallah, har jami'a idan kina so zan sama miki, ni ma kuma ina fata idan na nemi abu wajen ki ba zaki min ba”

“Me kike so Momy?”

“No ba yanzu ba, wata rana dai”

“Inshallah zan miki ko minene, ba zaki same ni mai butulci, ko dan Sirleem kin cancanci komai a gareni”

Momy ta mata wani kallo. Kamar tai magana sai kuma ya fasa ganin Sirleem ya dawo kitchen din.

“Baka wuce ba?”

“Eh yanzu dai zan wuce”

“Ba zaka tsaya ka karya ba?”

“No thanks”

Be tsaya jiran abun da zata fada ba ya juya da sauri ya fice daga kitchen din with so much confused. A tare Momy da Falmata suka hada breakfast din, sannan Momy ta saka Falmata ta jera masu a dinning, what Falmata thought Momy zata zuba mata nata dabam ne ta ce taje ta ci, but to her surprise sai Momy ta bukaci ta zuba da kanta wanda zai isheta kuma ta zauna a dinning din ta ci.
Duk wani abu da suka hadawa na breakf Falmata kadan take zubawa gudun kar Momy tace ta cika, beside ba a tana aje mata komai ace ta deba ba, ba a taba mata wannan gatan ba.

“Ki zuba mai isarki, idan sun kare kara siyowa za a yi, feel free ki ji kamar a gidanku kike, ni kuma ki dauke ni a matsayin mahaifiyarki”

Dagowa Falmata tai ta kalli Momy sai hawaye ya cika idonta, lallai bayan rasa uwa a yau ta samu wata uwar, Tumba na matsa mata tana musguna mata wata dabam bare tana son taimakonta. Momy ta shiga hada nata tea tana jin rauni a kudurinta, bata yi ma Falmata wannan gatan kadai dan tana tausayinta ba sai dan daman can halinta ne kawaici da girmama dan adam, gashi tausayin Falmata ya shiga zuciyarta yayi kwance.

‘Ina bukatar nai tunani, kuma ina bukatar shawara, kar na aikata abun da zai zame mana na nadama, kar na cutar da wata kuma na cutar da kaina, i need to think’

A ranta take wannna tunanin tana jin ya kamata ta nemi shawarar mijinta, domin har ga Allah bata jin natsuwa a abun da take tunanin aikatawa.


ZAINAB POV.

Zaune take bakin kofar shiga falon, tana sanye da kananan kaya, kanta sanye da wular sanyi, iska na kado mata a hankali.
A hankali murmushi ya cika fuskarta, kana kallonta kasan tana cikin nishadi da walwala abun da yai kaura a gare kwana biyu da suka wuce. Ta tattara hankalinta gaba daya ta maida akan system din dake gabanta, hotunan da ta dauka a garin su Wasim take kallo, al'adarsu na da kyau a gurinta, yadda suke rayuwarsu abun ya burgeta.

“Oh... ”

Ta yi murmushi mai sauti tunawa da tai da abubuwan da suka faru, jinginawa tai jikin kujerar, ta kalli zaren da Wasim ya daura mata har yanzu yana a hannunta ta samu kanta da kasa cire shi, murzashi take a hankali tana tunanin abubuwan da suka faru a lokaci. Kamar an cikare ta sai ta tashi ta shiga cikin falon, kai tsaye ta nufi kitchen tana shiga ta dauko cup ta bude firji ta dauko ruwa, a kokarinta na rufewa ta hango Iya jikin icen abaya da be gama girma ba ta juya mata baya ta sirina a gurin. Mamaki ne ya kamata, me zai kai iya gurin? Ko maybe tana son shuka wani abu ne? Shine abun da zuciyarta ta raya mata, sai ta zuba ruwan a kofi ta aje gorar ta fito rike da kofin waje. A saman teburin data dora laptop dinta ta aje ruwan ba tare da ta sha ba ta zagaya ta inda Iya take. Kamin ta karasa Iya ta mike tsaye ta juyo rike da wuka, dayan hannunta kuma rike da tantabara har biyu. Tsaya tai cak kamar yadda Zainab ma ta tsaya cak tana mata kallon mamaki. Sai da tai da gaske sannan ta iya tattaro karfin hali da dakakkiyar zuciya irin ta maye ta cigaba da takawa tana furta.

“Ni har kin tsorata ni, tafiya ba sawu kamar mai sata”

Zainab bata ce komai ba har Iya ta zo ta wuce ta, sai ta juyo ta bita da kallo, abun da bata taba gani ba yau take gani a gurin Iya, ta yanka tantabara har biyu da kanta, me za ta yi da tantabara? Idan kwadayi take ji why not ta ce a siyo mata kaza? And when ma aka shigo da tantabaru gidan? Takawa tai ta bi bayan Iya tana tafe tana tunani har ta shigo cikin falon, sai ta ji motsinta a kitchen tana kokarin kunna risho, wani abun da ya bata tsoro bata bata saka ruwan zafi ba ta fige tantabaron a haka ta saka su a cikin wata roba, gasu yan kanana kamar wani karamin tsuntsu.

“Iya? Me zaki yi da tantabara?”

Iya ta kalleta.

“Me zan yi? Me ake da tantabara ba ci ba? Na yi kwadayinta ne”

“Amman kuma kanana haka? Kuma ki yanke da kanki”

“Ke bana son tambayoyin ki yau mace ta fara yanka? Wadannan yan tayin zan kira wani ya yanka min? Yaya ne fa! Ni dai ki saka a canja min abubuwan bandakin can bana jindadin amfani da su, kuma ki samo mai rika mana aikin gida”

Zainab bata sake cewa komai ba ta juya ta fita, Iya ta mike tsaye da sauri ta leketa, a zatonta dakinta zata shiga sai ta ga ta nufi hanyar waje, komawa tai ciki ta cigaba da gyara tantabarun.
  Zainab fitowa tai waje ta zauna, tana ta tunani domin bata gamsu da abun da Iya ta fada mata ba, me zai saka tai haka? Why zata siye kanana? Tunawa tai da tukunyar da ta gani a dakinta, sai kuma tai saurin girgiza kai domin bata son tai wani tunani marar kyau akan mahaifiyarta. Ajiyar zuciya ta sauke ta cigaba da duba hotunan wannan karon kan na Fadime data dauke ta a idansu idonta ya sauka, sai a lokacin ta tuna da ita.

“Ko tana ina ma?”

Ta tambayi kanta tana tabe baki, hakan nan take jin yarinyar bata mata ba, ta cika rawar kan tsiya. Ta mitsa sosai gurin duba hotunan tana gyara su amman hankalinta ya kasa kwanciya, ta kasa samu natsuwa da abun da Iya tai. Mikewa tai tsaye ta nufi gurin gate din. Mai gadinta dake

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login