Showing 78001 words to 81000 words out of 286946 words

Chapter 27 - Fulani Book 1 Hausa Novel Complete

20 Dec 2024

941

da gudu kamar an korota.


SHATTIMA POV.

8pm yana zaune dakin karatunsa yana operating system dinsa Ra'ess ya shigo gidan. Mikewa yai tsaye ya kashe wutar dakin ya fito ya hanyo kofar, silently ya shiga kitchen ta hada ma kansa coffee yana fitowa Ra'ess na kawowa kofar kitchen din.

“Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un”

Ra'ess ya fada da karfi yana kallon Shattima dan be san da akwai mutun a cikin kitchen din ba, tun abun da ya faru a kauyensu Fadime ya kasa dawowa daidai ga shi ya kasa daina jin muryar a kunnensa.

“Are you okay?”

Shattima ya fada yana kallonsa, sai ya shafa fuskarsa yana jin kamar gumi na sauko masa.

“I'm not, Wallahi i'm not....... kai......!”

Ya fada sannan ya karasa cikin kitchen din ya bude fridge ya dauko ruwa mai sanyi ya sha sannan ya firo falon ya zauna, Shattima dai a tsaye jikin kofar yana kallonshi. Can ya dago ya kalli Shattima.

“Neman aure na je wani kauye, amman na rasa ganewa, amman garin ai akwaishi, sai dai idan su wadanda muka je gurinsu ne aljanu, malam kaji wata murya?”

Ra'ees be karasa ba Shattima ya tintsire da dariya kamar ba shi ba, daman can ya san Ra'ees da tsoro, amman a yanayinsa na yau ya tabbatar da abun da ya gani babba ne ba karami ba, but the funniest part is neman aure fa suka je kamar yadda ya fada, be fada masa komai ba a matsayinsa na babban abokinshi gashi yanzu sun dawo da wahala.

“It's not funny Man ba abun dariya ba ne”

Shattima ya gintse dariyar da murmushi.

“Then kuka kake son nai? Imagine ka je neman aure ba tare da sanin best friend dinka ba?”

Sai da Shattima yai maganar sannan Ra'ess ya tuna cewar Ammy tace kar ya bari ya san komai sai magana ta yi karfi.

“Kai ba fa aure zan kara ba, wani na raka”

Ya fada yana kokarin kawarda tunanin Shattima daya kasa daina murmushi ganin yadda gumi yake ta karyoma abokin nasa.

ZAINAB POV.

Sai da suka gaisa sannan ta shigo da shi falon baki a inda ta saba shigowa da shi idan za su fira, sannan ta tashi ta shigo cikin gida ta saka mai aikin gidan ta jera masa abinci da lemu.
Be ci komai ba, dan babu abun da yake bako a cikin abun da aka shirya masa, ruwa kawai ya sha ya cigana da danna wayarsa.
Ba a dauki dogon lokaci ba ta dawo fuskarta dauke da murmushi zuciyarta kuma cike da kaunarsa ta zauna a kujerar dake kusa da tashi.

“Zata fito yanzu ku gaisa, idan ka gaisa da ita sai na kira Ammy ku gaisa”

Ya gyada mata kai yana kara kallon kyakkyawar fuskarta wacce ke dauke kamar masa hankali a ko yaushe, ba ma shi kadai ba most mazan da suke sonta kyauta ne yake daukar hankalinsu.

“Allah yasa dai kar sai magana ta yi karfi matarka tace na ci amanarta”

Gyara zama yana cigaba da kallonta fuskarsa dauke da murmushi.

“Ai ba haram mu kai ba, kuma ko da baki nemi ni ba, ni zan kawo kaina da kaina gurinki, idan na fada miki cewar na dade da kaunarki cikin raina ba za ki yarda ba”

Ta yi murmushi.

“Zan yarda ma ganin yadda kai saurin amincewa da ni”

Lokaci daya suka daga kai suna kallon Iya wacce ta shigo falon cikin shiga ta alfarma kamar ba ita ba. Ba laifi ta sake masa fuska kamar da gaske tana na'am da shi din, har kasa ya kai ya gasheta Zainab kuma tana ta kallon Iya cikim jindadi, a iya tunaninta irin wannan ranar Iya take jira na ganin surukunta. Halshe Iya ta fitar kadan ta laso kurwarsa dake yawo a bayan kansa tasa hannu ta jimke ba tare da ita Zainab din ta kura ba balle kuma shi da ya ki yarda su hada ido.
Cikin mutunci da girmamawa suka gaisa sannan ta mike tsaye tana Allah shi masa albarka ta fice. Sai ya ciro bandir din yan dubu ya mikawa Zainab.

“Baby gashi ki bata ta siye goro”

Zainab ta karba tana murmushi ta bi bayan Iya ciki farincikin yau uwarta da mijin da zata aura sun gaisa da juna.

*Littafin nan na kudi ne biya ki karanta cikin aminci. Pay 300 to 0314795884 Abubakar Hadiza Gt bank, then send the evidence via 08036126660*




21

*Littafin nan na kudi ne biya ki karanta cikin aminci. Pay 300 to 0314795884 Abubakar Hadiza Gt bank, then send the evidence via 08036126660*

ZAINAB POV.

Sai da ta kira masa Ammy suka gaisa sannan ta raka shi har gurin mota, sannan su kai sallama. Part din Ammy ta nufo rike da kudin da ya bata yace ta bawa Ammy 100k, dayan hannunta kuma rike da wayarta sai juyawa take har ta isa cikim falon. Kusa da Ammy ta zauna amman a kasa yayinda Ammy take zaune a saman cushion ta aje mata 100k din.

“Ammy gashi yace a baki ki siye goro”

Ko kallon inda kudi suke Ammy ba tai ba, tana ta aikin jar carbin da take ta ce

“Ina fatar kin kira masa Hajiya ya gaishe ta”

Zainab ta dan yamutsa fuska.

“Miye hadina da Hajiya Ammy”

“Hadin da kike da shi da ni”

Ammy ta amsa mata tana kallon cikin tsakiyar idonta. Sinne kai kasa Zainab tai sannan ta mike tsaye.

“Ammy tafiya gobe ce In-Sha-Allah”

“Ki kirashi ya zo ya gaishe ta idan kin dawo”

“To”

Ammy ta dauke kai ta maida gurin plasma, ko kadan Zainab bata jidadin abun da Ammy tai ba na cewar ita da Hajiya daya suke a gurinta bayan kuma har a bada ita ta san ba za su tana zama daya ba. Tana fitowa bangaren Ammy ta nufi dakin mahaifiyarta, sai ta same ta zaune bakin gado ta dora kafa daya saman daya tana kallon kofar kamar tana jiran shigowarta.

“Ya tafi, yace idan ya fadawa iyayensa zai sanar da ni sai a sanar da dangi na”

Iya ta kalleta a yayinda take kokarin zama kusa da ita.

“Na ga har yanzu ba ki gane hanya ba, to bari na kai miki gidan, ke a yanzu duk soyayyar da kike yi ma Shattima ta me ce?”

Zainab ta yi mata wani kallon rashin fahimta da mamakin furucinta.

“Ban gane ba?”

“Baki taba sha'awar ya zama mijikin ba? Me Shattima ya rasa wanda wannan yaron yake da shi?”

“Shattima yana da komai Iya, tabbas ya kai a so shi amman mi kallon dan'uwa nake masa”

“Babu alakar jini a tsakaninki da shi balle ta tsoka, ni da ke da duk wanda ya san waye mu a gidan nan kallon bayi yake mana, har yanzu baki fara tunanin samun yanci ba? Baki fara tunanin yadda zaki zama matar sarki kamar Ammy ba? Baki fara tunanin wata rana Shattima zai zama sarki ba?”

Iya ta karasa tana bude mata ido tana ji kamar ta hau ta duka. Zainab ta girgiza kai.

“Aa ban taba yi ma Shattima kallon miji ba, ban taba jin sonsa a raina ba, ina masa kallon dan'uwa ne, saboda ya dauke ni kamar kanwarsa, yana kula da matsalolina yana nuna damuwarsa akaina, mahaifiyarsa kuma ta dauke ni ya, kanwarsa ta zama kanwata wannan kawai ya isheni, idan tunaninki na hada aurena da Shattima ma ne to ki daina, ki kina ganin akwai wanda zaki cilasta min sonsa ki aje, Auwal kawai nake so a yanzu kuma shi zan aura”

Tana kaiwa nan ta mike tsaye a fusace ta fice daga dakin, ta rasa gane dalilin Ammy na son cilasta mata son Shattima, tabbas Shattima yana da kyau yana da siffar da mace sata ganshi ta hade yawu amman ita bata taba masa kallon miji ba.
Bayan fitar Zainab Iya ta kada kai ta bude tsokar dake hannunta, ta mike tsaye ta isa gaban madubinta ta bude durowar madubin ta dauko bakin zare ta nade tsokar wacce ke ta motsi kadan kadan alamar akwai rai a tare da ita.

“Kin jawa yayansa zama marayu, matarsa tai takaba ke kuma sai mu gani idan zaki auri gawa”

Ta karasa tana zare ido cikin bacin rai. Zainab na isa dakinta ta bude karamin fridge dinta ta sha ruwa sannan ta kwanta saman gadon tana ta mamakin yadda tunanin iya ya bata wannan, saboda su ta zama abunda ta zama a yau saboda su aka santa a instagram har ta samu aikin photography duk wannan be isa ba? Akan me zata hararo hada aurenta ta Shattima bayan ta san shi ma kansa Shattima be taba mata kallon so ba, kuma sai a yanzu da ta samu wanda take so?
Cikin daren ta shirya duk wani abu da zata shirya na tafiyarta, sanin jirginsu zai tashi 9am yasa tun cikin dare taje tai ma Ammy sallama, sannan ta shiga gurin mahaifiyarta.

“Ina tunanin tun 8:30 zan isa airport, maybe ko da zan wuce ba ki tashi bachi ba”

Iya ta kalleta tana jin haushinta har yanzu.

“Ni ban taba zuwa garin ba, amman sai fada miki kar na waiwayi garin kuma baki tashi fada min ba sai a yanzu da gobe zan wuce? Sometimes Iya bana iya gane”

Uffan Iya bata sake ce mata ba, hakan yasa Zainab ta mike tsaye ta nufi kofa, sai Iya ta zira halshe ta laso kurwar yarta, ta jimke ta a hannu, sai da Zainab ta fita sannan ta mike tsaye ta nufi gaban madubinta ta dauko zare ta nade kurwar ta bude wardrobe dinta ta dauko wata tukunyar kasa ta bude bakin kyallen dake kai ta fadi bukatarta sannan ta maida ta aje ta rufe wardrobe dinta ta mike sokar tsaye wacce tai ma wani tsoro daya da zare ta masa gefen tsoron sai ta sake saka yatsanta ta matsa gefe, ta nufo gefen gadonta ta daga karamin carpet dake gurin ta saka tsokar ta maida carpet din ta rufe tana ta zare ido kamar za su fito.

“Sai ki yi tafiyar na gani”

***   ***    ***
Zainab na kokarin kai hannu ta bude kofar dakinta ta ji kanta ya tsara da karfi ya amsa har gurin bayanta.

“Ouchhhhh”

Ta fada tana dafa kan da dayan hannunta sannan ta karasa cikin dakin ta bude durowar ta ta dauko magani ta balla ta sha, sannan ta kwanta tana jin kamar ciwon na karuwa, cikin karfin hali ta kunna data ta shiga instagram sannan ta leka whatsapp tana kokarin ashe datar ta sauka kiran Auwal ya shigo wayarta, dan murmushim karfin hali tai sannan tai picking call din.

“As usual i just call to say good night baby”

“Thank You i love you”

“I love you more, ki kula min da kanki”

“Sure”

Ta aje wayar tun kan ya kashe saboda bata son yin magana ciwon kan da gefen hakarkashinta ya soma matsa mata da ciwo, ko tufafin jikinta bata iya canjawa ba ta kwanta hakan nan saman gadon. Bata farka ba sai da sanyi asuba ya soma shigowa dakin, kasancewar bata kwanta a natse ba ko window dakinta bata rufe ba.
Bandakinta ta shiga tai wanka tai alwala sannan ta fito daure da tawul tana jin kan har yanzu be daina mata ciwo, ko mai bata shafa ba ta saka abayarta ta saka Hijab tai sallah sannan ta saka alarm a wayarta ta sake kwantawa. 8:30 ta farka ta kashe alarm din ta dauki karamar jakarta ta rataya babbar kuma ta janyo ta ta fito dakin rikw da wayarta da kuma ticket dinta. Sai da ta saka key a kofar sannan ta nufi hanyar da zata sadata da bangaren Ammy duk da tasan ba lallai ne ta same ta a bangarenta ba at this early morning matukar ita ke da girki yau.
Kamar yadda tai tsamma haka ta samu falon cike da hadimai masu gyara gurin kullum safe, kai tsaye ta nufi dinning ta hada ma kanta tea ta riko cup din ta fito dan ba zata iya jira ya huce ba, arba da tai da Jekadiya yasa ta saki murmushi.

“Jekadiya yaushe kika dawo?”

“Da yamman jiya, fatar Hajiya karama tana cikin koshi lafiya”

“Ina kalau yanzu ma tafiya zan yi”

“Ammy tace hadimai su raka ki airport”

Jekadiya ta fada tana kallon Zainab sai ta nuna kanta.

“Ni...?”

Sai jekadiya ta gyada mata kai.

“Kawarai kuwa”

Dan murmushin jindadi Zainab tai a iya saninta, jinin gidan ne kawai ake yi ma rakiya da hadimai idan zasu tafi wani gurin, amman yau Ammy ta karramata.

“Suna waje suna jiranki, Baaba zo ki rika mata jakarta”

Jekadiya na rufe baki Baaba ta zo a guje ta karbi jakarta dake hannun Zainab ta wuce.

“Na gode Jekadiya”

“Aikin Ammy ne”

“A mika godiya ta a gareta, Allah ya kara mata lafiya”

Ta fada da murmushi a fuskarta, sannan ta bi bayan Baaba ko da ta fito hadimai har hudu na tsaye jikin motar da zata shiga da diriban da zai kaita suna jiranta, duk da ciwon da take ji be hanata jindadi da kuma nuna farinciki akan abun da Ammy tai mata ba.

FADIME POV.

Ba karamin mamaki ne ya cika Amo ba ganin yau ma ba wutar ya kai ta fita? Waya sake cire mata ita? Tana wanke kwaryar da take zuba manshanu idonta na kan Fadime dake taya Inna zoya gida. Ganin karan zai kare yasa Inna ya yaba gyalenta ta nufi dajin dan yi yayeyaye. Fadime na ganin ta tashi tai saurin baro gaban wutar ta nufi Amo tana fadin.

“Inna Hajjo idan zaki je birni zaki fada musu cewar muryana ya dawo daidai? Su dawo”

“Aa tare dai za mu je su gani da idonsu saboda su yarda”

Fadime ta yi murmushi cike da jindadi.

“Eh shikenan ma sai su gan ni da idonsu”

Sai da Fadime ta juya sai kuma ta juyo sakamakon kiran da Amo tai mata.

“Idan kin je daji kina haduwa da wani ne?”

Fadime ta yi shiru tana nazari, ta fada mata gaskiyarta ko ta boye?

“Aa ni bana haduwa da kowa, cewa akai ana ganina da wani ne?”

“Aa kawai dai yadda kike dawowa ne wani lokacin yake bani mamaki”

“Bana ganin kowa, sai daji sai duwatsu, sai bishiyoyi”

“Allah ya kyauta”

Ta fada a ranta tana ayyana cewar duk ranar da Fadime zata je daji sai ta zama mage ta bi bayanta dan ganewa idonta.

“Amman Inna Hajjo idan zaki je da ni sai kin yi wayo dan Bappa zai iya cewa ba za aje din ba”

“To Allah yasa su bari, ko na Innarki ta bari ba lalle ne Malam ya bari ba, amman zan masa magana na ji”

Fadime ta juya ta koma gurin zamanta cikin jindadi, tana cigaba da juya gidar dake kan wuta. Sai da Inna tai kara mai yawa sannan ta shigo cikin gidan ta sauke ta cigaba da soyar gidar. Yunin ranar Fadime da tunanin zuwa birni ta wuni a ranta, ta dayan bangare kuma tana ayyana cewar ba zata sake zuwa gurin Wasim ba balle har ya samu nasarar yi mata wani sherin domin har yanzu haushinsa take ji.
A daren ranar saboda farincikin za aje birni yasa Fadime bata ko jira Inna tace mata ta dauki gidar ta tafi da ita dandali ba ta zuba da kanta ta kirga.

“Ta dari takwas ce Inna”

“To idan kin siyar duka ki dauki hansi ki kawo min dari bakwai da hansin”

“To Allah ya bamu sa'a”

Tare da Hajjo suka fita, ita ta dauki gyada Hajjo kuma ta dauki dawon (Fura) da Amo take sarowa gurin Larai, har suka isa dandalin babu wanda da wani uffan daman can Hajjo da Fadime ba wani shiri suke ba, yadda basa son kula junansu abun har mamaki yake bawa mutane ganin suna gida daya ko da kasancewar mahaifin Hajjo daban. A inda ta saba zama ta zauna tana ta rabon ido a dandalin sai kallon yadda samari suke watsawa yan matansu kudi take, abun da yafi burgeta kenan fiye da komai, a take zuciyarta ta tafi wani bangare tana tunanin yadda kowa zai ji idan aka fadi cewar dan birni zata aura, idanuwanta sai gizon fuskar Ra'ees suke mata.
Ba kasafai take siyar da gidar idan ta zo da ita ba, domin mafi akasarin masu siyen abubuwa dandali maza ne ita kuma bata da samarin da za su siya balle su mata juye, sai dai a aiko yaro ya zo ya siye, an siye sosai samari da yan mata da kuma yaran da ake aikowa. Wani ma da ya zo sai yace ta kirga masa ta nawa ce gaba daya.

“Ta dari hudu da 20 ta rage”

“To ki yi sadaka sai na baki kudin”

Ta daga kai tana kallon mai maganar jin kamar ta san muryar, saurayi ma mai kira da siffar samartaka yana sanye da dogon wando sai rigar fulani, ya saka hullar sanyi a kansa irin ta fulani sannan yai rawani ya rufe rabin fuskar yadda ba za a iya ganewa ba. Hannyensa take kallo a lokacin daya kika mata yan dari biyar guda hudu fari ne sol duk da kasancewar wutar karar tana maida mutanen dake gurim jajaye da irin haskenta, sai dai baya haka hasken farin mutum fita balle kuma wannan da yake da haske sosai ga mazantaka dake nunawa a jikinsa, ta karbi kudin ta kirga 2k

“Na dauka duka?”

Ya gyada mata kaina yana ta kallonta kamar wanda be tana ganin irinta ba. Ba shiri Fadime ta jenye tray gabanta ta fara masa godiya, tana jin wani irin dadi marar misaltuwa ita ma yau an mata irin yadda ake ma sauran yan mata, be ce mata komai ba ya duka ya dauki kulli gyaɗa ta juyar sandar dake hannunsa ta korar shanu ya raba gefenta ya bi hanyar shiga gari, da kallon mamaki da jindadi Fadime ta bishi baki har kunne.

“Kiyaye”

Ta fada tana daga masa hannu duk da be waigota ba. Yarinyar dake kusa da ita taja tsaki.

“Mtscheeeessss bakauya kawai sai kace kanta farau”

“Dalla can matsa yarinya kin ji zafi kin yi hassada kin ga na fara samari, kuma ke ce yar kauye jahil da ko turanci bata iya ba, bakinki ma warin zunubi yake, ehhhh yarinya kin ji kunya beeeee ige zalla tumba yake yake”

Fadime ta fada tana mata gwalo tana mata tsowa. A take yarinyar ta mike tsaye ta kwance ganwonta ta daure kugunta.

“Ke Fadime wallahi ki shiga hankalinki dan ni na fi karfinki”

Fadime ta dubi zubin Bintalo ta san ko a kalle bata isa ta kalli Bintalo da harara ba balle tace zata bugeta, sai ta duka ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login