Showing 69001 words to 72000 words out of 286946 words

Chapter 24 - Fulani Book 1 Hausa Novel Complete

20 Dec 2024

932

kiran sallah asuba, kamar yadda tai a jiya haka ta shiga bandakin tai alwala ta fito ta sake shimfida dankwalinta tai sallah. Tana cikin addu'a Sirleem ya turo kofar dakin ya shigo. Tea mai kauri ya aje mata da bread sai sake mikewa tsaye kamar dazun tana kallonsa.

“Dan Allah karka maida ni gida”

Uffan be ce mata ba, daman kuma be da niyar ce mata komai yana aje mata tea ya juya ya nufi kofa.

“Wallahi idan ka maiyar da ni Baba ya ji cewar na gudu sai ya yanka ni, kuma Umma sai ta kusa kashe ni saboda na taba mata kudi”

Daf da zai fice ta fadi haka, sai ya tsaya cak ya juyo ya kalleta, tausayinta ya kama shi how old she is da zata zabi guduwa da bar gidansu? Ko bata fada masa ba ya san ana azabtar da ita tun da har ta zabi barin garinsu da gidansu ta zo inda bata san kowa ba, amman rayuwarta yake ji kar ta aikata irin abun da Mansura ta aikata ya zame mata tabo, a kurciyarta zata iya lalata rayuwarta, amman idan tai hakuri da wahala zata ci riba kuma zata wuce kamar ba ayi ba.
Juyawa yai ya fice daga dakin, ita kuma ta zauna ta fara kuka tana tunanin irin mugun dukan da Baba zai mata, bata tunanin zai barta ta rayu ma idan ko har ta rayu to sai dai ta zama musaka.
Misalin 6:30 ya sake turo kofar dakin, ya tsaya daga jikin kofar yana kallonta,  ya same ta a yadda ya fita ya barta, tana kuka kuma bata taba tea ba.

“Fito muje”

Mikewa tai tsaye ta nufi kofar hawaye na sauko mata kamar dan irin wannan ranar kawai ta tanade su. Bata ce me zata ce masa ba, tun da har ya kasa sauraranta ta san ba zai fahimce ta ba, a yanzu ba ta da wanda zata karantawa damuwata balle ya nade mata kuncinta. Ta yarda a gidansu bata da gata, a nan din ma bata da gata. Da kanshi ya bude mata gidan gaba ta shiga ta zauna ya rufe sannan ya zagaya ya shiga mazauninsa ya ja motar.

Tun da ya fara tafiya wata kalmar bata shiga tsakaninsu ba, daji take kallo tana share hawayenta lokaci zuwa lokaci, ta sadakar kuma ta yardar da kaddarar da ta rabo da gida, ta yarda wata kaddararce take bibiyarta a yanzu na fadawa wata damuwa. Tun yana tukin tana kallon titi har bachi ya sallama mata ita kuma ta amsa masa cikin sauki, daman tun jiya basu hadu ba. Sai da ya tabbatar da bachin nata ya yi nisa sannan ya faka motarsa gefe ya fita ya zaya gefenta ya bude mata a hankali kwantar mata da kujerar ya rufe, kamin ya dawo motar ya ciro wayarsa ya kira Mansura bugu daya ta dauka.

“Sirleem ina yarinyar nan ta kwana?”

“Tun jiya na saka ta a motar Yola”

“Ina ta kiranka baka dauka ba tun jiya, kuma ka san zan samu”

“Shiyasa na kira ki yanzu”

Ya fada yana kallon Falmata ta cikin farin gilashin motarsa, bachinta take hankali kwance kamar wacce bata da damuwa. Ta saka hannu ta share hawayen idonta.

“Kana ina kai”

Ya daga kansa yana kallon katon dajin.

“Somewhere.... Anjima zan kira ki”

Be jira cewarta ba ya yanke wayar ya maida aljihu ya zagaya ya shiga motar ta cigaba da tukinsa. After every deep breath sai ya kalli Falmata wacce ke ta ranko bachi har ya shiga garin Yola.
Kai tsaye ya nufi GRA, a gaban wani katon gate ya faka motarsa sannan ya fita ya doshi gate din yai knocking, babu bata lokaci mai gadin ya leko.

“Ranka ya dade kai da kanka kake buga gate”

Sirleem ya dan yi murmushi.

“Allah yasa Momy dai tana ciki”

“Yanzu yanzu ko ta dawo”

Mai gadin ya fada yana matsa masa daga kofa. Sai da ya danna key mota yai ta shiga lock sannan ya shiga cikin gidan. Kato gida mai yanayi da na turawa domin babu hayani sai kukan tsuntsaye dake saman itatuwan da suka zagaye harabar gidan su kai masa ado, ga wasu manyanna alfamar. Entrance din ya hau ya isa gaban kofar yai knocking.
Wata kyakyawar mata ce ta bude masa kofar fuskarta dauke da murmushi matar zata yi 40 to 42 years tana sanye da farar atamfa, sai farar t labcoat dake saman atamfar.

“Celebrities ganinku sai da ticket, sai kuma idan kun so kawo ziyara”

Dan murmushi Sirleem yai ya naso kafarsa cikin falon mai cike da sanyi ac.

“Ba ma ziyara na kawo ba ni alfarma na zo nema”

“To yau kuma a gurina”

“Na san ke kadai zaki min ai”

Ya fada yana kokarin zaunawa.

“Yanzu yanzu na dawo daga aiki, lemme go and change”

Sai da ta aje masa lemu da ruwa sannan ta nufi upstairs ta shiga dakin farko. After like thirty minutes ta fito sanye da Hijab din dake nuna alamar sallah ta gama, sai da ta sauko kasa ta zauna sannan Sirleem ya kalleta yace.

“Wata yarinya ce na hadu da ita a Kaduna, ban ji labarinta ba amman a yadda na fahimta tana shan wahala ne a gurin rikon nata ko gurin Babanta, saboda tace min mamanta ta rasu, kuma ta gudo ne daga gidansu zuwa Kaduna, bayan kuma bata san kowa a can ba, so idan na kyale ta a can rayuwarta zata iya lalacewa shiyasa na zabi dawo da ita gida saboda yar nan Yola ce”

Iya nan ya tsaya yana sauke numfashi a hankali, tun kamin ya gama labarta mata abubuwan ta soma jin tausayinta.

“Allah mai iko ina yarinyar take?”

“Muna tare a mota, ina son kije gidansu ne tare da ita, ki ce ke kika kadeta kuma hankalinta ya gushe sai yanzu ta farko ta fadi gidansu kika kawo ta, saboda ta nuna min idan ta koma gida Babanta ya ji cewar ta gudu zai yankata, kuma ta taba kudin ko waye i don't know zan tambaye ta kudin sai na bata”

“Allah mai iko, wasu suna neman haihuwa wasu kuma suna wulakantawa”

Momy ta fada cikin rashin dadi rai, Sirleem yayi murmushi yana kallonta cike da tausayinta, kamin ya mike tsaye.

“Bari na shigo da ita”

“Okay”

Fita yai daga falon, ko da ya isa gurin motar ya tararda ta farka tana ta kalle kalle, unlock din motar yai sannan ya bude side dinta.

“Fito”

Ta fito kamar daman can umarnin take jira, be yarda ya shiga cikin gidan ba sai da ya saka ta a gaba, ita dai tafiya kawai take ba dan tasan a ina take ba a Kaduna ko kuma a Yola? Ina zai kaita? Shine abun da take ta tambayar kanta, rage tafiya tai har sai da ya sha gabanta sannan ta bi bayansa suka shiga cikin falon.
Wani irin kallo Momy take mata na tausayi, karamar yarinyar kamar wannan ace zata gudu ta bar gida? Ta jefa rayuwarta a hadari?

“Sannu zauna nan”

A maimakon Falmata ta zauna a kujerar da Momy ta nuna mata sai ta zauna kasa ta sinne kai gabanta na faduwa, bata ji me tace mata ba amman ta san alama take mata da ta zauna.

“Ya sunanki?”

Momy ta tambaya, Falmata kan bata ma san tana yi ba dan kanta a kasa yake kuma ba ji take ba.

“Bata ji sosai sai kin daga muryar”

Sirleem ya amsa mata, sai tausayinta ya kara kama Momy, ta dan daga muryarta ta sake tambayarta.

“Falmata”

Ta amsa ta ba tare da ta kalleta ba.

“Sannu Mamana”

Momy ta fada cike da tausayawa sannan ta mike tsaye ta nufi kitchen, cornflakes ta hada mata da madara sannan ta dauko wani plate da zuba mata fruits ta dawo falon ta aje a gabanta.

“Yanzu na dawo aiki ban dora komai”

A nan ma Falmata bata jira tace mata dauki ki sha ba, dan yunwar da take ji ta musammance, sai ta dauki cup din ta cire cibin ta aje ta kafa kai ta sanye shi dika, wani irin dadi ta ji har cikin kanta domin bata taba shan cornflakes ba. Tausayinta ne ya cika Momy har ta rasa me zata ce sai kallonta take kamin ta kalli Sirleem.

“Ka kaita ciki ta yi wanka ta huta”

“No Momy Hajiya na jirana, na fi son a kaita gidansu sai tai can”

Ya kalli Falmata.

“Nawa ne kudin da kika taba?”

“Dubu biyar ne”

Ta amsa masa muryarta na rawa, sai yasa hannunsa aljihu ya ciro wallet dinsa ya kirga 5k ya mika mata, sannan ya sake kirga 10k ya mika mata.

“Wannan idan kin je ki samu wata sana'a ki rika yi”

Ta yi saurin girgiza kai.

“Aa idan aka gan ni da kudi da yawa za a iya dukana”

Sirleem be ce komai ba ya maida kudin wallet dinsa ya mike tsaye.

“Ka kaita gurin motana zan kira oga na fada mishi”

“Okay”

Tare suka fito da Falmata ya nuna mata motar Momy.

“Ki jirata a can, idan ta zo ki fada mata unguwarku, kuma duk abun da tace ki ce eh haka ne”

Sai da yai maganar ne Falmata ta gane cewar sun iso Yola kenan, kamar kazar da kwai ya fashewa a ciki haka ta nufi gurin motar da Sirleem ya nuna mata ta tsaya tana karewa gidan kallo.

AA POV.

Ganin bakuwar number yasa gabansa faduwa, duk kuwa da Nana ta fada masa cewar bata fada a gida ba, amman ya kasa natsuwa. Haka yai ta kallon wayar har tai ringing ta gama sannan mike tsaye ta fito daga dakin Hindu ya nufi waje, a nan kiran ya sake shigowa sai da yai Bismillah uku sannan ya dauki kiran, jin muryar Nana yasa hankalinsa kwanta ba.

“Saurdauna”

“Na'am”

“Yauwa kai ne, ya kake?”

“Ina lafiya”

“Kana ina?”

“Ina ina? Ina Yola”

Ya amsata yana juyawa ya gani ko wani na binsa, ko kallonsa.

“Ka zo gidanmu na fadawa Hajiya tace na kira driver, ka bashi key din motar”

Wani irin dadi ne ya lullube shi, ya matsa kusa da wata transforma ya fada ta yana jin kamar ya rumgumeta.

“Da gaske Nana?”

“Wallahi da gaske, ka zo yanzu ka ji”

“To ina ne unguwarku?”

“Kasan Turaki area”

“Eh”

“To ka zo nan daga shigo kace ina ne gidan Mai Martaba idan kan zo kace gurin Nana ka zo, sai ka kira line nan”

Wata kalar kabbara yai ya lumshe ido ya bude ya rumgume transforma da hannu daya

“Allahu Akbar yanzu Nana ke yar sarauta ce?”

Dariya Nana tai ta tashe wayar ba tare da tace masa komai ba. Wayar ya kurawa ido yana tuna farkon haduwarsu, sai yaji abun kamar a mafarki, duba yai yaga babu mai kallonsa sai ya fadi yai sujada sannan ya mike tsaye yana gyara rigarsa.

“Shikenan Kakata ta yanke saka, na yi arziki malam”

Da sauri ya koma cikin gidan ya canja tufafin jikinsa ya fito ba tare da ya fadawa kowa ba, ya fito ya tari mai achaba ya hau.
Ba a sauke shi ko ina ba sai Turaki area (Fake area) Unguwar masu arziki da naira unguwar da babu irinta kaf a fadin garin Yola, manyan gidanjen yake bi da kallo kamar be saba bi yana wucewa ta unguwar ba, wani karin dadi yake ji a ransa, yana sauka ya mikawa dan a chaban 500 yace ya yafe nasa canjin, cikin tsoro tsoro ya karasa gate din ya gaisa da masu gadin ya fadu musu gurin Nana ya zo, ba su yarda da shi ba sai da ya kira wayar ta daga tai musu magana sannan aka barshi ya shigo.
Gaba daya rikecewa yai ya rasa ina zai bi ganin masarauta mai kama da wata unguwa, saboda fadi da girma gashi an raba ko'ina part part, kai tsaye ya nufi apartment din Hajiya yana tafe yana jin wani dadi na daukarsa sai raba ido yake yana kallon amsu aikin dake kai da kawo da sauran mutane dake ta sha'aninsu. Bakin gate din ya tsaya ganin mota na fitowa a zatonsa Nana ce sai ya gata wata marar jiki ta tsaya daidai shi da motar.

“Ya kai?”

“Na zo gurin Nana ne”

“Me zata maka?”

“Nine sabon driver da za a dauka”

Jurry ta kare masa kallo from head to toe sannan ta watsa masa wani banzan tsaki.

“Malam fita ka bamu guri ba za a dauke ka ba”

“Amman Nana tace na zo”

“Nana ita take da ikon kanta i say out...”

Ya juya da sauri ya fice aransa yana fadin.

‘Wallahi ba zai yiyu na ga samu na ga rashi ba, dole ne sai an dauke ni’

***
Nana ta kwanta saman gadonta tana dariya, ba karamin dadi ta ji ba na samun number sa da tai, daman kuma ta san ba zata mata wahala ba indai a line Hajiya ne. Duka numbers din da ta duba a call list tashi ce kawai ba suna.
  Wani irin dadi take ji zai zama driver ta domin har ga Allah yana burgeta kuma gashi yana jin maganarta komai tace masa. After some minutes kiransa ya shigo wayar Hajiya dake hannunta ta daga tai magana da mutanen dake gate din sannan ta kashe ta mike tsaye ta fice daga dakin.

SHATTIMA POV.

Relaxing yai akan kujera yana busar da iskar bakinsa, manyan idanuwansa na wani lumshi alamar bachi yake ji da kuma gajiyar tiyatar da ya gama a yanzu. Wayarsa dake gaban teburin ce tai ringing Sunan Hajiya Karama ne rubuce a gaban screen din, sai da ya dan matsa da kujerarsa baya sannan ya amsa.

“Hello Sis”

“Shattima ya aiki?”

“Al-hamdulillah how is kids?”

“Suna nan kalau, on Saturday zan zo Katsina fa gurin aikin da na ce maka”

“Okay this Saturday?”

“Yeah na san dai ba zaka je asibiti ba ranar right”

Ya dan tabe baki kadan kuma yai shiru na wani lokacin kamin ya amsa mata.

“Zan je da Yamma”

“Okay ni da safe zan shigo”

“Allah ya kai mu”

Ya fada bayan yayi shiru kamar ba zai ce komai ba. Aje wayar yai be kashe ba, daman can haka yake ko shi ya kira ka sai dai kai ka kashe, shi nashi aje waya ne kawai. Ya mike tsaye yana murmushi yana kallon screen din wayar dake dauke da hoton yayanshi.

*Littafin nan na kudi ne biya ki karanta cikin aminci. Pay 300 to 0314795884 Abubakar Hadiza Gt bank, then send the evidence via 08036126660*
19

*Littafin nan na kudi ne biya ki karanta cikin aminci. Pay 300 to 0314795884 Abubakar Hadiza Gt bank, then send the evidence via 08036126660*

Hannun rigarsa ya fara budewa sannan ya bude ya fara bude maballan rigarsa yana ta kallon kansa a jikin madubin dake gabansa. Dan murmushi yai kamar wanda ya tuna abu sannan ya juyo ya cire rigar gaba daya ya dora saman gadon ya dauko vest ya saka ya sauko kasa.
Kai tsaye kitchen ya wuce ya dauki cup ya aje sannan ya bude fridge ya dauko lemun tsami ya matsa a cup din ya bude durowar kitchen din ya dauko wata farar roba ya bude ta debi kanwa kadan ya zuba a cup din ya saka karamin spoon ya garwaye sai da lemun ya hade da kanwa sannan ya daga cup din ya shanye yana bata fuska tsamin na kai masa har cikin kai. Ra'ees ne ya shigo kitchen din sai zuba kamshin turare yake.

“Shattima ni zan wuce”

Ra'ees ya fada daga tsayin da yaje bakin kofar kitchen din. Juyowa Shattima yai ya kalleshi, irin kallon nan na ina zaka je? Indai Shattima ne zai bude baki ya tambaye shi ba sai dai kar ya sani, ba dan komai ba sai dan magana taba masa wahala, yana da nauyin baki furta wata kalar tafi komai yi masa nauyi a baki da jiki, abu ne mai wahala ka ganshi a cikin mutane ko da kuwa Ammy ce ko Zainab yana fira, sai dai yai shiru yai ta saurarensu idan sun gama ya tashi wani lokacin kuma sai yi murmushi idan an fadi abun dariya idan kuma tambayarce zai iya ce maka eh ko aa ko ya girgiza kai. Magana ta fi komai yi masa wahala a rayuwa, gashi kuma likita haka nan dai yake ta fama kamar dole.

“Zan je kauyen kaita, akwai wani aiki da nake son yi a can”

Ra'ees ya amsa masa ba tare da ya jira ya tambaye shi ba, daman kuma ya san halin abokin nasa indai sai ya tanbaye shi ne sai a mutu a tsaye.
Shattima na son ya tambayeshi me zai je yi a can kuma yaji ba ya bukatar wahalar da kansa, sai kawai ya tabe baki ya daga masa hannu.

“Safe trip”

“Thanks”

Ya juya ya fice daga kitchen din, kamin ya isa gurin motarsa Yayarsa ta masa kira ya kai uku domin mijinta ya shirya shi kawai ake jira. Da motarsa ya isa gidanta sai ya aje motarshi ya shiga motar mijin suka kama hanyar Kaita daga Katsina.
Suna tafe suna firar kasa da rashin tsoron da ake fama da ahi da yunwa, har suka isa, a cikin garin kaita suka yi sallah sannan suka yi tambaya aka fada musu hanyar da za su bi ta kaisu garin Bandalo. Alhaji Tukur ne yake jan motar Ra'ees yana front seat, yana karewa garin kallon, garin Bandalo gari ne mai cike da burgewa, tun farkon shigowa garin zaka fara arba da manyan gonaki, domin garin ya kasu kashi biyu ne, fulani makiyaya sai kuma hausawa da kusan sune rabin garin, daman fulanin irin masu yada zango nan ne a gari, yamma da garin ne bangaren fulani kana daukar hanyar da tai can zaka fara arba da bukoki da shanu da masu kiwon shanun gwanin burgewa.

“Rabun da na ga bukka da idona ni har na manta”

Ra'ees ya fada yana kara bawa idonsa abinci, sai da su kai nisa sosai sannan Alhaji Tukur ya tsaya kusa da wasu fulani suka zaune gaban wani massalaci na kasa yana tambayarsu Malam Jauro.

“Dan Allah muja cijiyar wani Malam Jauro Sama'ila”

“Kun zo gida, daga ina kuke?”

“Daga birni mun zo, gurin Matarsa ne Amo”

Wani bafullatanin mai tsaga a fuska ya mike tsaye.

“Muje na karasa da ku daman gidan Modibbo zan je”

A kafa yake tafiya su kuma tana binsa a kasa har suka isa kofar gidansu Fadime, gidansa ne mai girma da aka zagaye da zana an share gaban idan tas ga kasar gurin ta kwanta kamar yashi. Malam Bala da kansa ya sallama cikin gidan sai Hajjo ta amsa masa ta fito ta gaishe shi tana karewa mutanen kallo da yaren Fulatanci yake

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login