Showing 1 words to 3000 words out of 286946 words
Jihar Katsina jiha ce daga cikin jihohin Nijeriya guda talatin da shida (36), tana yankin arewa ta yamma na kasar Nijeriya. Ansamar da ita ne daga cikin jihar Kaduna, Mutanen jihar Katsina mafiya yawansu Hausawa ne, sai kuma Fulani kuma sana'o'insu noma ne da kiwo. suna da halsuna Hausa, Fulani, Turanci. Tana da kananan hukumomin 34 sune :-
Bakori
Batagarawa
Batsari
Baure
Bindawa
Charanchi
Dan-Musa
Dandume
Danja
Daura
Dutsi
Dutsin-Ma
Faskari
Funtua
Ingawa
Jibia
Kafur
Kaita
Kankara da sauransu, GARIN BANDALO (garin bandalo da sunan garin duka na kirkira ne) babban gari ne da ke cikin karamar hukumar Kaita, garin bandalo garin Fulani ne da ke da fadi da yalwan arzikin noma da kiwo. Ya wacin mutanen garin da suke kiwon shanu a yammacin gari da kewaye, wa su kan shiga birni yin fatauci, matan su kuma na shiga birane tallar nono da danyen manshanu, yawacin fulanin da suke garin ba asalin yan garin ba ne, irin fulanin nan ne makiyaya, masu yada zango a duk garin da suka tarar yana da albarka da ruwa. Wani abun da zai burge duk wani bakon garin shine yadda fulanin suka kawata garin da bukkaken fulani, a tsakanin wacan bukkar da wata akwai tazara sosai, domin kowa ya yi gidansa ne a cikin gonarsa, masu wadata da arzikin cikinsu ne suke zagaye gidansu da zana su killace kansu kamar masu babban gida.
MALAM JAURO SAMA'ILA Shine Sarkin Fulanin wannan yankin, sarki mai adalci da kamanta gaskiya a tsakanin Fulanin da yake mulka, sarki ne daya kafa tarihin da babu wani bafullatani a yanki da ya kafa irin tahirinsa, ta hanyar bawa yarsa Faɗime ilmin boko da na muhammadiya, shi ne kai da mutumen da yake daukar yarsa ya shiga da ita birni a duk safiya ta Allah idan zai je fatauci ya aje a makarantar bokon da ke garin Kaita shi kuma ya shiga cikin garin gurin harkokinsa.....
FAƊIME
Ya daya tillo a gurin Malam Jaure, kuma ya daya tillo a gurin Tumba, yar da ta kafa tahirin shiga makarantar boko a garin Bandalo. Yar da kowa ke gudu yar da kowa ke kyama yar da kowa ke fargabar arba da ita, yar da Tumba tai mata alkunya da FULANI.
FULANI POV
Hawaye ne ke fitowa daga lussasun idabuwanta da take sharar bachi da su, fuskarta kuma na kawatuwa da murmushin dalilin mafarkinta.
"Fulani Fulani Fulani"
Firgigit ta bude ido ta tashi zaune tana kallon mahaifiyarta wacce ke tsaye a sanye da riga da zane na Atamfa, kwayar nono a hannunta.
"Dun Allah Dun hanyar hillacin ki tashi ki kai shanun ga yamma su sha ruwa su yi kiwo, hay Fulani rana hwa ta na ga yi kuma kin san ba su ci komi da safe ba"
Wacce aka kira da Fulani ta saka hannunta na dama da na hagu ta share hawayen bachinta.
"Amman Inna yau ba Hajjo ce da zuwa daji ba?"
"To Inna Hajjo ta hana ta ta ce ba zata je ba, hadda ta turata bunni gurin talla dawo da nono tun dazun suka tafi tare da Mairo, dan haka ke sai ki tashi ki tahi kamin Malam ya dawo, kin fi kowa sanin cewar baya son a bar mai nagge da yunwa"
"To Inna zan tai yanzu"
"To tashi yar albarka, idan kin hito sai ki sha sabon kindiro yanzu na taso shi"
Inna Ladi na fadar hakan ta juya ta fice rike da kwayar sabon nonon da ta taso yanzu, nonon da ko manshanu ba a cire masa ba.
Mika Fulani tai tana sauraren busar Sarewar da take yawan jin a cikin bachinta, ba kuma dan ana burar a Sahiriba sai dan sabo da tai da ita a kowa wane bachi, ya'alan na safe ne ko na rana ko dare, indai har ta kwanta sai ta yi mafarkin wannan mutumen da ya bata baya yana ta burar sarewa a saman dotse, busar da ke sakata hawaye da murmushi a lokaci daya kuma a cikin duniyar mafarkinta, sai dai murmushin da hawayen har a zahiri ana ganinsu, yayinda busar sarewar kuma ita kadai take jin abarta a cikin bachinta. Mikewa tai tsaye ta nufi gurin jakar kayanta ta dauki littafinta da buro ta zauna a gurin ta soma rubutunta kamar yadda ta saba.
_Yau ma na yi mafarkinsu, dayan a gefena mai busar ya ba ni baya, dayan kuma a bayana_
Bayan ta rubuta ta rike biron tana ta tunanin yadda mafarkin ya zo mata, a kullum mutanen nan uku mafarkinsu take, sai dai ba zata iya siffanta su ba, domin bata iya shadar fuskokinsu balle kuma wani abun da zai saka ta iya cewa aljanuna ko mutane. A zahiri dai sun fi kama da aljannun domin shi mai busar sarewar kullum baya yake bata, tun tana jin busar a nesa har ta fara mafarkin tana tsinkayarsa ya bata baya, to shi kuma wanda ta bashi baya wanene? Wanda kuma yake gefenta wanene? Su ma duka aljanun ne ko kuma wani abun ne na dabam? Miyasa take yawan mafarkinsu? Miye alakarta da su?
"Fulani....."
Kiran mahaifiyarta ne ya katse mata dogon tunanin da ta fara, da sauri ta mike tsaye ba dan tana son zuwa kiwon ba, gudun irin abubuwan da suke faruwa wani lokacin, mawuyacin abu ne ta fita ta dawo ba tare da wata saniya ta samu karaya ko kuma ta mutu ba, ko da yake idan ba tai kiwon ba mi za tai? domin a kullum cikin fargabar fita take a cikin jama'a saboda abubuwan da suke samunta ko kuma suke samun jama'ar da take kusanta, kusan ta zama annoba kowa a garin tsoronta yake gudunta yake idan ka cire iyayenta babu mai iya zama da ita ya wanye lafiya........
Omar Abdallah Jari da na biyu a gurin Sarkin Yola wato Sarki Abdallah Jari da Hajiya Kilishi. Mutum ne mai yawan kyauta da nuna kauna da ga talakawa ga yawan murmushi da haba haba da jama'a.
SHATTIMA OMAR POV
Tsaye yake jikin window falonsa yana kallon yadda ruwan sama ke sauka harabar gidan yadda ya kurawa gurin ido sai ka rantse da Allah kirga ruwan yake, babu komai a zuciyarsa sai kewar triples dinsa, saboda suya baro gurin aikinsa sokoto ya zo garin iyeyensa kuma garin haihuwarsa Yola, amman yana fargabar tunkarar Masarautarsu saboda mahifiyarsa wato Hajiya Kilishi.
Hannu ya saka ya cire wayarsa da ke aljihu ya nemo number Nana ta aika mata kira, ringing biyu ta daga.
"Hello Ya Shattima"
"Babbar Kanwa ya kike? Ke kadai ce?"
"Eh kuma ina nan Lafiya, ya aikin?"
"Ina son ganin Triples i miss them, dan Allah ki sato min su ki kawo min su guest house, zan ba ki goro"
"Oh Sorry Shattima ka dawo kenan, shiyasa dazun Ammy ta aiko jekadiya ta ce a fada min kar na kuskura na fita da triples"
Ya dan wara ido yana fadada murmushinsa.
"Ta san na dawo?"
"Maybe amman tun da ka ji tace haka kam ai ta san ka dawo"
Dariya yai dariyar da ta bayyanar da fararen hakoransa ya sauke wayar. He wonder how mahaifiyarsa take da basira haka har ta tasan da dawowarsa. Baba Adamu ne ya fado masa a rai a take ya bar jikin tagar ya nufi dayan falon da Baba Adamu yake. Baba Adamu na ganinsa yai saurin mikewa tsaye irin na girmamawa, har sai da Omar ya zauna sannan shi ma ya zauna a kasa.
"Tashi kasa zauna saman kujera"
"Aa ka bar ni nan ranka ya dade"
"Kai ne ka labartawa Ammy na shigo gari?"
Shattima ya tambaya yana dora kafa daya saman daya. Baba Adamu ya kara yin kasa da kansa.
"Ita ce ta bukaci sani, wannan dalilin ne yasa ta maido da ni gurinka saboda ta rika sanin halin da na ke ciki"
Murmurshi Shattima yai mai sauti ya shafa kansa.
"Amman Baba Adamu ba ni da ikon yin sirri da kai? Ko ruwa na sha sai ka fadawa Hajiya? Ana rayuwa haka?"
Ya tsosa lips dinsa, yana kallon Baba Adamu, Baba yake kiransa duk kuwa da kasancewar karkashina yake sai dai ganin dattijo ne wanda ya isa ace ya haife shi be zai iya kiran sunansa hakan nan kawai ba.
"Yanzu ga shi ina son ganin yayana amman ba ni da dama saboda ka fadawa Ammy, ni kuma ba son shiga na ke gidan ba daga ita har Mai Martaba ba barin yi min maganar aure suke ba"
Ya fada yana daga kafadunsa. Baba Adamu ya kalleshi cikin Ladabi ya ce.
"Ranka ya dade suna son kai auren ne, kai kanka za ka fi kima da daraja da aure"
"Haba dai Baba Adamu kamar ba kasan ni ba? Aure nawa zan yi Fisabilillahi? Mace shida ina aure suna mutuwa yanzu idan na kara ta bakwai kenan waya sani ko ita ma iyayenta su rasa ta, ni fa tsoro mana ke kar a fara min zargin maita"
Ya fada yana mikewa tsaye. Baba Adamu ya daga kai yana kallonsa.
"Ranka ya dade ba maita ba, kalmar ba da ka furta a bakinka ina ganin kamar be dace ba, waye be san kaddarar Allah ba?"
"To ka bincika min wace uwar ce ta son rasa yarta da zata aurawa Omar a samo min ita"
Yana fadar hakan ya nufi upstairs yana murmushi. Baba Adamu ma Murmushi yai duk da kasancewar duk mace da ta auri Shattima mutuwa take wata tana amarya wata bayan ta yi wata hudu zuwa kasa, Maimuna ce kawai tai shekara da wata biyar har ta haifa masa yan uku, bayan ita ya auri Basira ta rasu da wata daya, sai dai hakan ba shi zai saka yarima Omar auren ko wace mace ba a ganinsa sai wacce iyeyensa suka zaba masa ko kuma shi yake ganin ta dace da shi......
WASIM RAU dan sarkin maharba kuma jikan sarkin matsafa na garin GARUK. Mutum ne mai son busar sarewa da zaman dajin, be fiye son harbin ba, duk kuwa da kasancewar shine gadonsa, ba shi da tsoro sai dai ban tsoro.
WASIM POV
A yau ba saman dotsi yake busar ba kamar yadda ya saba, a saman ice ya hau yana busa sarewarsa, cikin natsuwa da kwanciyar hankali yake busar, ba mutum kadai ba ko aljani idan ya ji busar sai zuciyarsa ta sosu. Lumshe ido yake yana budewa shi kanshi busar dadi take masa domin tana saka shi nishadi da walwala, idan ka cire abinci da ruwa da rai baya iya rayuwa sai da su to busar sarewa ce abu na biyu da yake kauna a rayuwarsa, busa ce mai dadi kuma mai daidai da yanayin garin da ya hada hadari da iska mai dadi....
AHMAD ASHIRU UNCE A A matashin sarauyin da bashi da aikin yi ba dan be yi karatu ba, sai dan aikin a Nigeria ya zama sai wane da wane, sai mai hanya da gata sai kuma wanda Allah ya tsago da rabon abincinsa a gabnatin jiha ko ta tarayyah, a gurin yayarsa yake zaune wacce ta tsaya masa bayan raye uwa da uba, ita ta zame masa tamkar uwa duk wani fadi tashi na karatunsa da hudimar rayuwarsa ita ce take masa duk kuwa da kasancewar ita ma din ba wani abun hannu ne da ita ba, sai dai tana sa'ar siyarda kayan masarufi a cikin gidanta sana'ar ta karbeta sosai a ciki take ci ta ke sha har ma tai ma mijinta wata hidimar kasancewarsa karamin lebara ne wata....
UNCLE A A POV.
Shinkafa da wanke ce da mai da yaji an yanka tumatur a cikin da albasa, sai kuma ganyen salat da aka yanka a sama shi ma kadan. A hankali yake tauna ragowar shinkafar da ke bakinsa, hannunsa rike da waya yana duba duniyar facebook.
"Uncle A A ba zaka ci abincin ba sai ya sha iska? Ba dadi idan ya huce"
Dauke idonsa yai daga kan wayar ya kalli Jamila wacce ke maganar yai dariya.
"Zan ci yanzu Jamila"
"Ai ka saba kullum hankalinka yana kan waya"
Cewar Anti Rabi, dariya yai ya ce.
"Anti abunda ke ban mamaki wai sai ka ji mutum daya ya yi sama da dukiyar talakawa ta miliyoyin nairori, ni har ganin na ke kamar kudin nan karya ne, wai yanzu akwai irin kudin nan muke zaune haka?"
Dariya Anti Rabi tai tana aikin kulla man kulin da take ta ce.
"Gaskiya ne akwai kudin idan kudi, sai dai masu kula da kudin ne macuta kuma mazanbata"
"Hmm Allah dai ya kyauta, mu ko aikin ya gagare mu samu, da ma degree ne wata kila da za ka fi samu amman ba kowa ke ganinta da daraja ba"
"Karka damu Ahmad wani abun a nesa yake, kuma kowa da irin kaddararsa"
"Haka ne Allah yasa mu dace"
Anti Rabi ta amsa da amin.
*** *** ***
Kadan kenan daga cikin abunda littafin FULANI ya kunsa.
Best Regards ❤🌹
Khadeeja Candy.
*🐄🐄 FULANI 🐄🐄*
By Khadeeja Candy
*Free Page -1*
©®Hakkin mallaka nawa ne ni kadai, ban yadda a saffaramin labari ta kowace siga ba balle har a dorashi a YouTube ba tare da izinina ba, yin hakan kuskure ne babba domin zai iya hanyowa mutum matsala a kiyaye ⚠
Ban yarda kowa ya hada document na littafina ba, ni ma na iya idan ina ra'ayi zan iya yi da kaina, ina albishir ga wanda ya hada document din Gobe na da duk wani littafi nawa cewar ban yafe ba ina rokon Allah ya saka min kuma ya mana shari'a da ko waye ne❗️
FICTION.
FREE PAGE.
FALMATA POV.
Yola...
Tun tana surfen da kuzari har ta kai bata iya daga tabaryar da karfi, babu komai a tare da ita sai tarin yunwa da gajiya ga wani uban ciwon kai da ya saka ta gaba.
Cike da juriya ta
karasa surfen sannan ta risina tana kwashewa tana zubawa a kwayar da ke gefen turmen, sai da ta kwashe shi tas sannan ta hade da sauran da ta surfe, mikewa tai tsaye tana rike da surfen ta nufi gurin tukuyar ruwansu.
"To mai kunne kashi ban fada miki idan kika yi surfenki ki rika zuwa bohal kina debo ruwanki ba? Ke wai Fulani sau nawa za ayi miki magana ne?"
A wahale Falmata ta kalli Tumba wacce ke mata maganar, ta amsa mata tana jin kamar ta fadi a tsakar ranar da ke dukan kanta.
"Umma idan na gama zan je na debo wasu sai na cika"
"Ban yarda ba, kije ki fara debowa ki yi abunda za ki yi wannan wanda kike debo mana na aiki ne bana wankewa wasu banza surfe ba"
Uffan bata sake ce mata ba, sai ta nufi gindin bishiyar dogon yaro ta aje surfen, sannan ta sake komawa ta dauko wani katon bokoti ta riko shi a hannu ta nufi kofar fita jiki ba gwari, tafiya take a hankali kanta a kasa bata kallon kowa sai hanya, gaisuwar girmama ce abunda yake fitowa daga bakinta sa'adda duk tai arba da sa'ar iyayenta.
A yayinda ta isa bohal din sai ta nemi guri ta tsaya tana ta kallon yadda fanfon bohal din yake cike da mutane yara da manya. Matsawa ta kara can gefe tana daga zanenta kamar mai kyankyamin ruwan da ke zube a kasa.
Kallo daya za ka yi mata ka karancin irin natsuwa da tarbiyar dake tare da ita, sa'aninta na gaban fonfon suna gogoriyon dibar ruwa ita kuma tana tsaye gefe abunta tana kallonsu kamar ba diban ruwan ta zo yi ba.
"Falmata kawo na baki bokiti daya"
Cewar Khadija kawarta, abun ka da mai nema sai tai saurin cira kafa ta isa gurin da Khadija take tsaye rike da kan fonfon ta mika mata bokitinta.
"Na gode kawata"
"Karki damu, indai akwai mu ba kya rasa komai kawata"
Khadija ta fada tana daga mata gira, murmushi ne ya fadada kansa a fuskar Falmata ya bayyana fararen hakoranta wanda ya karawa bakar fatarta sheki.
"Yau ba za ki je gidan Sarki ba? Kin san fa ke ce mai gyara dakin yan uku da kula da su"
Khadija ta tambaya tana daga muryar wai dan mutane da ke gurin su san kawarta na aiki a gidan Sarki. Wata irin kunya ce ta rufe Falmata abun ka da bakauyen mutum sai duk ta ji ta muzanta.
"Ke Madam ba za ki ba yau?"
"Na tafi, har na dawo sai kuma gobe"
Ta amsa mata kamar ana matso maganar daga bakinta, gaba daya kunya ta gama rufe ta, kamin bokitin ruwan ya cika duk ta tsawwala, bokitin na cika Khadija ta kama mata ta dora a kai sannan ita ma ta dora nata suka kamo hanya tare.
"Mtswwwww Wallahi Falmata ba ki hadu ba, wai ina son ayi kurin nan ke kuma kin wani noke ba ki ma son amsawa"
Abun nan dai da ya zame mata al'ada ta yabawa fuskarta, wato murmushi sannan ta soma magana da muryarta mai taushi da dadin sauraro.
"Khadija kunya na ke ji"
Wani banzan kallo Khadija tai mata.
"Kunyar me? Aikin a gidan sarki? Allah ya kai Khadija Wallahi har tafiya sai na sauya"
Wannan karon dariya marar sauti Falmata tai, tana jinjina lamarin kawarta, daman can indai kaudi ne da iyayi da ba ni na iya ba dai Khadija ba.
"To ai na ga ni ban wani dade da fara aikin ba, da har za a ce na fara kuri wannan zuwan da nai dazun fa shi ne zuwana na uku, kuma ni na ga..... "
Sai kuma tai shiru bata karasa ba, sai dai karara yanayinta ya nuna akwai damuwa a tare da ita kamar yadda fuskarta take nuna akwai tarin maganganu a kasan halshenta.
"Miya faru?"
Tsayawa tai tana kallon Khadija kamar yadda Khadijar ma ta tsaya tana kallonta.
"Sai na ke ganin kamar ba su yarda da ni ba...."
Fuskar Mamaki Khadija tai.
"Ban gane ba?"
"Kin ga tun da aka dauke ni aikin, har yanzu ban ga yaran ba, sai dai na gyara dakinsu, kuma idan zan gyara sai a saka dogari ko wata baiwa sun tsaya dakin har nai na gama"
"Suna da wulakanci ne?"
"Aa har yanzu ba a taba min ba, ban ga alamun hakan a iyalan gidanba, duk da yake dai ban gama ganin kowa da kowa ba tun da zuwana na biyu kenan, sai dai da alama suna da wuyar aminta da mutum"
Hannu daya Khadija ta saka ta dafa kafadarta.
"Karki damu, daman su yan sarauta basa saurin aminta da mutun, amman dai da sannu za su fahimci kawata mutuniyar kirkice su aminta da ita"
Ta karasa tana dariya tare da rika fuskarta.
"To Allah yasa"
"Amin, kuma bari na fada miki ba wai saboda wannan bakar Tumba ta tura ki aiki dan ki samo