Showing 141001 words to 144000 words out of 286946 words
na rantse k Iya? Dan Allah ki bar su su yi aikinsu, idan sun gama za su fitar da kayan gurin mota”
Iya ta dafe goshinta tana jin kamar ta fasa ihu, domin ko kadan bata son barin gidan, da ta san Zainab zata zabi barin gidan ne da bata fada mata abunda ya faru ba, domin ba haka aka so ba kanen miji ya fi miji kyau, sai dai babu yadda ta iya dole ta amince tun da Zainab din har ta yi rantsuwa.
“Su kwashe komai, amman kar su taba min wardrobe, da karkashin gadon can ni zan hada komai nawa”
“Ba tufafinki bane a wardrobe?”
Zainab ta tambaya tana kallon Wardrobe din, irin wardrobe nan ce ta tsofi da ake zuba taikace da kuma tufafi a ciki.
“Eh amman dai bana son kowa ya taba min kaya, ni zan hada abuna”
Kallonta kawai Zainab tai for the time zuciyarta ta raya mata kamar akwai wani abu duk da bata san ko minene ba.
“To ki hada komai na ki, mota tana jira Mibahu zai saka komai a bus ya bi bayana ya sauke mana a can”
“Sai sun gama aikinsu sun fita tukuna, sai na samu natsuwar hada kayana”
Zainab dai bata sake ce mata komai ba ta fice daga dakin ta koma dakinta. A daren ranar babu abun da ya kwana a gidan na Iya ko a Zainab, tas ta saka aka kwashe komai aka saka a bus din sannan ta shiga motar ya bi bayanta, be sauke kayan a ko'ina ba sai gidanta, da taimakon hadiman data bari su gyara mata gidan aka shigar da kayan ciki, sannan ta kira Baba Ali ta bashi kudi nepa tana nanata masa.
“Kaje gobe ka kai kudin nan fa, da yamma zan dawo gidan nan ina son kamin na dawo n tarar sun zo sun maida wutar nan”
“To Hajiya, safe zan tafi ma kai musu kudin in Allah ya yarda”
“Ku kuma idan kun tashi ku zo ku shiga mota na maida ku”
Shine kawai abun da ta fada babu sannu balle na gode, jiki na rawa suka shiga motar gudun laifi, domin sun san halinta ba tun yau ba.
Sai ta maida su Masarautar sannan ya ciro kudi tai musu ihisani daidai gwargwado, suka karba suna godiya da sanya albarka.
A cikin daren babu yadda Iya bata yi ba akan na son ta canja ra'ayin Zainab na barin gidan amman ta tsya kai da fata akan ita a zata iya cigaba da zama a gidan ba, bayan ta labartawa Iya abun da Jekadiya ta fada mata ta kara da.
“Yanzu aka fara haka kenan? Nan gaba me kike tunani? Ba wai alaka zamu yanke gaba daya ba, no tun da bata son muna kusantarta kara mu yi nisa da ita kowa ya huta”
“Ke yanzu ba zaki yi tunanin yin abun da zai janyo hankalin Shattima ba? Sai neman barin Masarautar da tai miki riga da wando? Haba dai?”
“Iya sau nawa zan fada miki babu komai a raina akan Shattima? Dan Allah karki sake min maganarsa? Kuma idan baki son zuwa ni ba zan miki dole ba amman ni kam ba zan zauna ba”
Iya ta rafka uban tagumi tana ta tunani a ranta, sai yamutsa abincin dake gabanta take. Zainab ta kalleta tana murza zaren da Wasim ya daura mata a hannunta na dama.
“Iya akwai tambayar da nake son yi miki”
“Ina jinki?”
“Kin fada min cewar, ku bayi ne da aka kamo daga Masarauta borno bayan an ci taku masarautar da yaki, aka dawo da ku wannan masarautar tun kaka da kakanni har kika kawo yanzu”
“Wannan haka yake tabbas”
Iya ta amsa mata tana tsame hannunta daga abincin da yake gabanta.
“Amman miyasa a lokacin da naje garin matsafan nan Garuk suka bani nama na ci be min komai ba har suke furta cewa ni jininsu ce?”
Take gumi ya karyowa Iya, gabanta ya shiga faduwa.
“Zainab? Kina tunanin ni mahaifiyarki zan miki karya? Wayewa ta saka kin fara min kallo makaryaciya?”
“Ba haka bane Iya, kawai ina mamaki ne,domin yarinyar da muka je tare da ita ta ci kuma abun yayi effecting dinta, a can ma na bar ta”
“To ki daina mamaki, domin tun kina ciki mahaifinki ya bani wani magani n sha, daga ni har ke babu abun da zai iya futar da mu na ci ko na sha, kamar ya san hakan zai faru”
Zainab ya dauke kai daga barin kallon Iya ba dan ta gamsu ba.
“Kuma shi Wasim din a lokacin daya rika hannu sai yace min ke jinin Iya ce, na yi mamakin yadda akai ya san haka, ko da yake ance suna da tsafi wata kila shiyasa ya san haka, har yana fadawa yarinyar cewa a masarauta nake zaune kuma ba tare da na fada masa ba”
“Wasim.... ”
Iya ta ambata da karfi, numfashinta na sarkewa. Kamar wacce ta tuna wani abu sai tai saurin cewa.
“Wane irin sunana ne wannan?”
Zainab ta tabe baki.
“Haka dai ake kiranshi, saurayi ne kyakkyawa, da a nan ne sai kin ga yadda yan mata za su yi rushing dinsa, gashi yana da ji da kai kamar ba dan garin ba”
Ta karasa tana dan murmushi, kamin ta maida dubanta gurin zaren daya daura mata, haka nan ta samu kanta da kasa tsinke zaren ta jefar duk kuwa da kasancewar ta san ba abu ne mai tsada ba, kuma ba kasafai take saka abu a hannunta ba bayan agogo.
HAJIYA BABBA POV.
Tun a daren ranar data kudirta ta fadawa Mai Martaba cewa mun babbar yayarta wanda ita kadai ta rage mata a raye, sai yai mata izinin tafiya tare da tambayar a mota zata tafi ko jirgi, saurin katse masa hanzari tai da cewar jirgi zata bi kuma Jurry ce zata siya mata ticket din domin a tare za su tafi, bata bar bangarensa ba sai ya kira Baba Waziri a waya ya fada masa kudin da zai sakawa Hajiya Bilki a account wanda zata tai hidima da shi, daman ya sama musu a duk lokacin da irin wannan tafiyar ta taso, biki ko suna ko gaida marar lafiya ko kuma ganin gida.
Washe gari suka fara duk wani shirye shirye da za su yi, the following day suka ama hanyar airport, Jarma be san da Hajiya Talatu za ayi tafiyar ba sai da ya ganta a airport din, ta sha uban gilashi ta rufe ido ga mask amman hakan be hana shi gane ta a kasancewar tana da jiki sosai fiye da Hajiya Babba, ga shi kuma tana tare da Hajiya Babba da Jurry, shi akansa yadda ya sha hular sanyi ya saka mask da glass ba lallai ne kowa ya gane shi ba. A waware suka kasu, hakan ya bawa Jarma damar komawa gefe ya kira Hajiya Babba.
“Hajiya ya haka na ga Hajiya Talatu tare da ke?”
“Karka damu, ni da kaina na nemi ta rakani, ai ta hannun damana ce ita ma, zan maka bayani daga baya”
Ya kashe wayar badan ya jidadi ba, daman can zuciyarsa na raya masa Hajiya tana munafuntarsa kamar yadda shi ma yake nasa shirin ba tare da saninta ba.
Daga Hajiya sai Jurry ne suka zauna a kujera kusa da kusa, Hajiya Talatu kam da Jarma suna can baya kowa daban daban kai kace ba su san juna ba, kamin Jirgin ya sauka Katsina Jarma ya cika ya batse da takaicin Hajiya Babba. Suna isa airport Hajiya Babba ta kira Hajiya Amutu ta shaida mata sun iso, ko minti 20 ba ayi ba direba ya zo ya kwashesu zuwa gidan Hajiya Amutun, a can suka huta su kai sallah sannan direban ya kama hanyar kauye da su, tun suna cikin garin Kaita Jarma ya kira mutumen dayai musu jagoracin wacan tafiyar zuwa garin Garuk ya sanar da shi sun kusa isowa inda yake, daman tun a Yola ya sanar masa da tafiyar saboda ya zama cikin shiri, sama sama Hajiya Talatu da Jurry suke zancen hanya da irin dajin da suke wucewa, Jarma dai be ce komai ba balle kuma Hajiya Babba da tunaninta yai nisan kiwo.
FADIME POV.
Gaba daya ta kasa natsuwa ta kasa kwantar da hankali, babu inda take tunani sai gida, babu yadda Wasim be yi ba dan ya kwantar mata da hankali amman ta ki ta natsu, kullum maganar ta Bappa da Inna.
“Yau fa kwanana na uku kenan? Ka ce ba zaka bari wani abu ya same ni ba, amman baka min komai ba, na san yanzu Inna ta yi kuka har ta gaji, kuma Bappa har jininsa ya hau kila ma sun dauka na mutu”
Wasim ya kalleta.
“Da baki a nan ciki da ke kanki baki san iya abun da ya same ki ba, bana son na fitar da ke garin nan ne sai da izinin Baba, idan ba haka ba zaki iya cutuwa, amman ki kwantar da hankali Kaka ya masa magana wata kila ma gobe ki koma gida”
“To ka canja min guri, kullum gurin wannan makahon tsohon nake kwana shi kuma da macirai yake kwana, ina jinsu a jikina suna bi na har a bachina, kuma kullum nan nake wuni”
Ta fashe da kuka, sai ya kai hannu ya shafa kanta.
“Amman ni ma ai a nan nake kwana ko? Kuma saboda ke ne, idan ba a nan kika kwana ba za a iya miki wani, ki kwantar da hankalinki Fateme zan maidaki gida lafiya na miki wannan alkawarin babu abun da zai same ki”
“Ni daga yanzu ma har abada ba zan sake cin nama, ko wane iri ne, kuma ba zan sake kin jin maganar iyayena ba, Allah ka yafe min...”
Ta fara rera masa kuka kamar yadda ta saba masa kullum yana rarrashinta, ko abinci yake son ta ci sai ta masa kuka yana lallabata kamar ba cikinta ba. Mai yi wa mutane iso gurin bokan ne ya shigo yai magana da shi da yarensu sannan ya fita ya shigo tare da wani bahaushe wanda zai fassara musu Hajiya Babba da Hajiya Talatu da Jarma da Jurry suna biye da shi, Fadime na ganinsu ta tashi ta koma bayan Wasim ta boya, haka take a duk lokacin da wasu mutane suka shigo wai dan kar wanda ya santa ya ganta yaje ya fadawa Bappa.
_________
Ina mata matan kwalisa Matan da suka ansa sunansu na Mata? Ina wadanda ke cewa mun yi mun yi bamu ga amfaninshiba? Hmmm to ku zo ga Yar gidan Maifata ta zo maku da Al ajabu, dan tsugunno, gumba da tsimi da Zuma daban daban, maganin sanyi na maza da Mata. Ga kuma garurruka irinsu mallakau sabuzu kuwa, sa bahaushe saibi, Dan hubbare kafi malam aiki, ke kadai ke da miji, dahuwar kaza, tattabara, ciccibi da dai sauransu. Ba anan kayanmu suka tsaya ba, muna hadin amare na musamman turaren sutura turaren tsugunno turaren wanka da na daki da na jiki duka 4amare nasu na musamman ne, amma ga tsuhuwar da ke son komawa yarinya itama zata iya zuwa ahadata kai abundai sai wanda ya gani, dan haka karkubari abaku labari, domin neman karin bayani zaku iua nemana ta wannan number 09029891757 ko 08169311410, muna aikawa ko'ina a fadin kasar nan har waje kasar nan muna aika kaya.
Address: Nasarawa Samaru Area gurin masallacin mai sola Gusau Zamfara state Nigeria.
36
*Littafin nan na kudi ne biya ki karanta cikin aminci. Pay 300 to 0314795884 Abubakar Hadiza Gt bank, then send the evidence via 08036126660*
Ko kallon inda Fadime take ba su yi ba suka zauna a inda mutumen ya nuna musu. Kana ganinsu kasan a tsorace suke, domin fuskarsu ta nuna hakan, ba kamar Jurry da bata saba shiga irin wannan sabgar ba.
Ganin hakan yasa Fadime ta dawo inda take ta zauna tana ta kallonsu, Sai da suka natsu sannan Hajiya Babba ta kalli Jarma ta ce.
“Jarma a dan daga mana kafa za mu yi magana”
Kadan ne ya rage mamaki be kashe shi ba, lallai a yau ya san wacece Hajiya, har akwai abun da zata boye masa? Be isa yai mata musu ba, daman tun a airport yake jin haushinta balle kuma yanzu da abun ya karu, be ce komai ba ya mike tsaye ya fice daga dakin yajin nadamar kawosu a gurin da yai.
“Daman abun da yake tafe da mu...”
Hajiya Babba ta fada sai bokan ya daga mata hannu alamar ta dagata, ya fara karanto musu abun da ya kawo su mai fassarar yana fassara musu.
“Kin zo ne akan maganar mijinki, wanda kike son ya mutu danki ya gaje shi, kina son a kashe babban dansa Shattima, kuma kina son a rufe bakin yar mijinki mai suna Nana, kina son a saka mata kaunar danki Sirleem, kuma kina son ki mallake komai na gidan? Sannan kina son a yiwa Falmata da Sardauna iyaka da masarautar, kuma kina son a fada miki wacece Fadime?”
Mutumen na kai wa nan Fadime ta kalli Wasim tana dariya jin an ambaci mai irin sunanta. Hajiya Babba kan ita da Hajiya Talatu mamaki ne ya kashe su. Bayan ya gama ya koma gurin Hajiya Talatu.
“Ke kuma kina son a saka mijinki ya fasa hada auren yar ki Maijidda da Shattima”
“Haka ne Wallahi tabbas haka ne”
Cewar Hajiya Talatu cikin tsananin mamaki da al'ajab domin bata taba shiga wani guri da aka karanta mata abun da ya kawo ta ba tun kamin ta fada.
Bokan ya mika hannu ya tabo macijin dake bayansa, daga shi sai Fadime da Wasim dake zaune bayansa ne suke iya ganin macijin, kamin ya sake magana Hajiya Babba tace.
“Ina ciki matsala saboda Falmata nan, ban san yadda akai ma dana ya santa ba, gashi wacce ta dauke ta aikin wato abokiyar zamana tana min mullkin mallaka, ta mallake komai sai abun da tace ake yi, ina son ita ma a karya lagonta, ita ma Nana ina son a juye mata kwakwala, kuma a lalata mata rayuwa, Shattima kuma a kawar da shi, ya zama na ni kadai zan rika juya komai a gida, zan yi duk abun da kake so kuma ko nawa zan kashe dan na samu biyan bukatata...”
Fadime ta kurawa Hajiya Babba ido tana kallon rashin imani kiri-kiri, a ashe dan mijinta a juya kwakwalwar yar mijinta ta mallake gida
“Bata da imani ko?”
Fadime ta radawa Wasim a kunne, sai ya saka mata murmushi ba tare daya kalleta ba, sai kakansa yake kallo da yake masa magana da yarensu.
“Idan nai musu aikin nan rayuka da yawa za su lalace ciki har da ta yarinyar nan”
Wasim ya kalli Fadime hankali a tashe kamin ya kalli kakansa ya tambaye shi da yarensu.
“Taya? Tana da alaka da su?”
“Bata da alaka da su amman rayuwarta zata salwanta matukar nai musu aikin nan”
Wasim ya kalli Fadime dake kallonsa kamar zata fasa kuka ya sake tambayar kakansa.
“Taya hakan zai taba ta?”
“Idan na fada maka abu ka yarda kawai”
Wasim ya sake kallon Fadime, iya kar abun da yake sani a mutun kadai ne, duk karfin tsafinsa be kai kakansa ba, kuma be isa ya ga abun da kakansa ya gani a cikin tukunyar tsafinsa ba, ana iya gano asali da ala idan ya taba hannun wanda yake son ganewa, amman be isa ya hararo abun da zai faru ba, kuma shi baya bokanci kamar kakansa, iya tsafin da yake da shi n tsoron kansa ne, sai kuma wanda ya zame masa dole na gadonsu.
“Karka musu aikin, karka musu komai, bana son abun da zai taba ta, da ace ta samu matsala kara ace ni na samu, idan wani abu ya same ta sai na hargitsa komai, bata cutar da kowa ba, babu ruwanta da kowa ba zan bari a cutar da ita ba, ko da ace zata samu wata matsala bata bangarena ba, ba zan yarda wani abu ya taba ta”
Wasim ya fadawa kakansa da yarensu.
Kakan be sake ce masa komai ba ya sake kai hannunsa bayansa ya shafa macijin, kamin ya maida dubansa gurin Hajiya Babba ya fada musu sakamako, mutumen na fassara musu.
“Tun a wacan ya kamata ki dauki mataki, da ace kin kawo aiki tun a lokacin da aka fada miki Falmata da Sardauna zasu lalata miki aiki, da yanzu komai be faru ba, za a iya yiwa mijinki harbin kasko, ya mutu amman dan ki Talba ba hau Sarautar ba, za a iya rufewa Nana baki, kuma a a iya lalata mata rayuwa, amman ba zata auri danki ba, za a iya nisanta da masarautar ammam alakarta da danki ba zata yanke ba, ko da ta yanke na dan lokaci ne, domin yarinyar tana da tsaro, dan ki ma yana da tsaro, Shattima ma yana da tsoro, Ammyn ma tana da tsaro, Nana ce kawai a sake sai Sardauna, kin yi latti da ba ki yi latti ba da komai be faru ba”
Kamar an saka gatari an sare mata jiki haka Hajiya ta ji, a maimakon a mata maganin matsalarta sai kuma a bata wani labarin marar dadi ji a kunnenta.
“A iya tunani babu abun da yake gagararku, na kawo kuka a nn ne dan a share min hawayena, ka fada min ko nawa kake bukata zan biya domin kawai na samu cikar burina, na san na yi sake da ban yi saurin zuwa ba, amman amin afuwa, a taimaka min”
Be cewa Hajiya komai ba, ya shiga magana da Hajiya Talatu.
“Ba sai kin yi wani asiri ba, Shattima ba zai auri yarki ba”
Hajiya Talatu ta ji kamar ta zuba ruwa a kasa ta sha tsabar jindadi.
“To a taimakawa yar'uwata ita ma, mun san mun yi nawa amman a yafe mana”
“Abun da aka fada mata babu wani gyara ko kuskure a ciki, babu wani abun da za a iya miki”
Kakan ya fada mutumen ya fassara musu.
Hajiya Babba ta ji kamar ta saka kuka, gaba daya ranta ya bace.
“Amman wacece Fadime? Sai na tare ta tun da wuri kar ta lalata min aiki, domin ita kadai ce ta rage a yanzu da ban gani ba”
Fadime ta bude baki tana gwalo ido waje kamar ta san da ita ake, ta sake kallon Wasim tana rufe baki.
“Yarinyar da bata kusa da masarautar ku me zaki iya mata?”
“Bata kusa da masarautar kuma zata lalata min shiri? Ina take? Kuma take da