Showing 192001 words to 195000 words out of 286946 words

Chapter 65 - Fulani Book 1 Hausa Novel Complete

20 Dec 2024

965

murmushi, haka nan yake samun kansa cikin nishadi da sakewar zuciya.

“Fateema ko?”

Ta yi dariya tare da saka hannayenta ta rufe idonta.

“To ba na zo birni ba”

Yayi murmushi yana kallon fuskarta sai lumshe ido yake, Falmata ce ta shigo tare da jekadiya suka zube kasa, take Shattima ya hade fuska kamar be taba murmushi ba. da hannu yai ma Jekadiya alama da ta tafi, sai ta mike tsaye ta fice.

“Ya sunanki ma?”

“Falmata”

Ta amsa da sauri tana sanda kai kasa.

“Zan tambaye ki wani abu, kuma gaskiya nake son ki fada min”

“To ranka ya dade”

“Kina ganin wata alama a gurin su Labib?”

“Eh wani a farkon zuwana suna zabura, amman da nake musu addu'a sai suka daina har yawan kukan da suke”

“Okay, idan kin kaisu gurin Iya tai musu wanka kina ganin wani abun?”

Kamin Falmata ta bada amsa Fadime ta zaro ido.

“Oh ashe yayanka ne Iya take bibiya, ashe ita take cinye maka mata kenan? Ke ma wannan Falmata kin shiga uku Hajiya Babb...”

Bata karasa ba Shattima ya saka hannunsa ya rufe mata baki. Falmata kam kanta na kasa bata son kallon Shattima gudun kar tai laifi.

“Ina jinki”

“Gaskiya idan na musu addu'a idan na kaisu bata karba, kuma daga baya sai ya zamana kamar tana tsoron tabasu ma”

“Shine kawai abun da kika sani?”

Falmata ta yi shiru tana tunani,tana son ta fada masa cewar ta hada goro da furen tufafi ta ci ta ga Iya na gudunta, sai dai tana tsoron kar abun ya wuce nan a kirata kotu ko wani gurin ta kasa maimaita haka.

“Shikenan abun da na sani”

Yayi mata alama da ta fice, sai ta tashi da sauri ta fice daga gurin jikinta na rawa sai mamakin tambayar take. Sai da ta fice sannan Shattima ya dauke hannunsa daga bakin Fadime.

“Falon mu kowa na shigowa har da Iya idan ba ki iya bankinki ba zata ji, kuma Hajiya babba ma tana shigowa, kuma kin san idan ta ji zata ja miki wahala ne, dan haka ki kama bakinki ban da yawan magana”

“Da gaske, dan Allah kace a aje ni daki”

“Tau

Ya fada yana murmushi sannan ya kira Jekadiya a waya ta zo ta tafi da ita. Dafe take da hannun Jekadiya har suka isa cikin falon, Jekadiya ta zaunar da ita kasa kusa da ita, Fadime ta zauna ne kawai ba dan tana so ba. Jin Jekafiya ta tashi sakamakon buga kofar falon da akai yasa ita ma ta mike tsaye tana kallon inda take jim sautin takun tafiyar Jekafiya. Jekadiya ta karasa gurin kofar ta bude ganin Kausar tare da wasu mata uku yasa ta bude musu kofar tana musu sannu da zuwa.

“Ammy na nan?”

Kausar ta tambaya sai jekadiya ta amsa mata da sauri.

“Eh tana ciki, ayi mata magana ne?”

“Eh su Hajiyan Zariya ne za su mata gaisuwa”

“To”

Jekadiya ta juya da sauri ya nufi hanyar dakin Ammy ta kwankwasa mata kofa, sai da bayan minti biyar Ammy ta bata izinin shiga. Sai ta tura kofar dakin a hankali ta shiga ta sanar mata. Ammy ta amsa ba tare da ta juyo ba domin bata son Jekadiya ta ga idonta ya yi ja saboda kukan da ta sha.

“Ina zuwa, a kaisu karamin Falo”

“To”

Ta juya ta fita da sauri. Ta karaso inda suke ta sanar musu Ammy na fitowa.

“Bismillah muje karamin falo”

Fadime ta na jin haka ta kira sunan Jekadiya.


“Jekadiya su waye suka zo?”

Sai da Jekadiya ta kalli Kausar sannan ta amsawa Fadime.

“Kausar ce da baki”

“Ni dai ki dora ni akan kujera, ba Shattima yace ki kula da ni ba? Kuma ya ce ki boye ni kar Hajiya Babba ko Iya ta gan ni”

Daga Kausar har Hajiyar Zariyar da Kawayenta biyu sai da suka kalli Fadime.

“Wacece Wannan?”

“Wallahi ban san sunanta ba, ke amsa kina jin ana magana”

Jekadiya ta fada, aiko Fadime ta kama baki ta tsuke taki tai magana.

“Hajiya Bismillah ku...”

Suka bi bayanta suna kallon Fadime cike da mamakin wacece ita.


NANA POV.

Littafai ne ta zube a gabanta hannunta rike da biro, ta dukufa sai karatu take saboda exam din dake tafe, tun daga lokacin da tai wa AA alkawarin zuwa makaranta ba ta taba fashi zuwa ba, and no matter how zata ga kudi Ammy ko na wani tana kokarin ta hana kanta tabawa, duk wani son kudi da take a yanzu tana kokari ta yaki abun a ranta, domin ko kadan bata son tsaba alkawarin Sardauna a iya ganinta ta haka ne zata saka masa da abun da yai mata. Turo kofar dakinta akai a hankali tana dago kai tai arba da Ammy, dan sauke idonta tai kasa tana tunanin laifin da dai, domin ba kasafai Ammy take zuwa dakin dubata ba sai dai yi mata fada ko saka ta wani aikin. Ammy ta zauna kusa da ita tana kallon littafan dake gabanta.

“Karatu kike yi”

“Eh muna da exam Monday”

“Yayi kyau”

Ammy ta fada sai dai wannan yarta take kallo cike da tausayinta.

“Ammy wani abun nai?”

“No kawai na zo na duba ki ne”

Nana ta yi shiru tana dan mamaki, Ammy ta kai hannu ta dauki daya daga cikin littafan tana dubawa.

“Nana ba ki da kamar ni a duniyar, kina da wata damuwa ko kuma akwai abun da kike so, ki fada min kai tsaye na miki alkawari matukar abun nan be fi karfina ba zan miki shi”

“Yaya ya ce miki Wani abu ne?”

“Be fada min komai ba, kawai dai na ga baki da gatan daya wuce ni, na fahimci damuwarki a yanzu, kina bukatar kulawa da soyayyar mahaifiya”

Nana ta dago tana kallonta.

“Wani abu ne ya faru?”

Idon Ammy ya cika da kwalla ta fara kirga yatsun hannunta.

“Ban jidadin rashin saurarenki da nai ba, ya kamata nai hakuri na kai zuciya nesa, amman na kasa, wani lokacin abubuwa suna min yawa a akaina, na kan rasa ta ina zan samu natsuwa, kuma ban taba tunanin ki na yin wasu dabi'u ba ne saboda wasu matsalolin, a tunanina kina yi ne kawai dan ki bakanta min, amman yanzu na gane ki yi hakuri kin ji”

Sai Nana ta ji wani iri ganin hawaye na saukowa a idon mahaifiyarta.

“Ammy ki daina kuka dan Allah, Sardauna yace na daina bata miki rai”

Ammy ta share hawayenta wasu na sauko mata.

“Sardauna yaron da ya cece ki ko?”

“Eh, Ammy...”

Sai kuma tai shiru. Ammy ta kai hannu ta dago fuskarta.

“Fada min matsalarki Nana, ki dauke ni kamar kawa”

“Dan Allah ki taimaka Sardauna ya dawo, yayarsa taceba zata bari ya dawo ba, amman ni ina son ya dawo kuma shi ma yana so”

“So kike ya dawo?”

Ta daga kai.

“Zai dawo Nana na miki wannan alkawarin, kuma zan masa gatan da baki taba zaton mahaifiyarki zata iya ba”

“Ammy da gaske?”

Ammy ta daga mata kai hawaye na sauko mata. Nana ta rumgume ta da sauri.


“Thank you so much Ammy Thank You”

Ammy ya kwantar da kanta kirjinta ta rumgumeta sosai tana hawaye.

“Nana ki min alkawari kullum da safe zaki yi addu'an tsari, akwai husnil muslim a dakina zan kawo miki, ki tsare addu'a safe da yamma, kuma kar Hajiya Babba ta sake baki wani abu ki ci ko ki sha ko shafawa kinji yata?”

“Daman Sardauna yace min na daina zuwa bangarenta ma”

Ammy ta lumshe ido hawaye na sauko mata tana yaba kyautatawar Sardauna a ranta.

47

*Littafin nan na kudi ne biya ki karanta cikin aminci. Pay 300 to 2451879008 Hadiza Abubakar Zenith bank, then send the evidence via 08036126660*

Sau uku tana mika hannunta da zimmar kaiwa ta bude kofar dakinta sai ta saka saboda kukan da ya ci karfina. A bakin kofar dakinta a zauna tana wani irin kuka mai ban tausayi, da tasa irin abubuwan da Iya zata fada mata kenan da bata bukaci sanin komai ba. A yau sai ta ji ta raine kanta sai a yau ta gane ita din ba kowa bace, daukarar da take da ita ya yawan mabiya a instagram be haifar da mata da komai ba, a yau ta tabbatar da kaskantatun mutane da take rainawa wayo ma sun fita a yau, domin wasu da yawa ta hanyar sunna aka haife su, tsabanin ita da aka haifa ta hanyar zina zinar ma a tasha, sannan tai rashin dacen mahaifiya ta kwarai.
Daker ta yunkura ta tashi tsaye ta kai hannunta ta bude kofar dakin ta shiga ta bata da mu ta rufe ba ta taka har gaban gadonta ta zauna tana jin kanta na juyawa idonta na nauyi kamar zasu fito, zuciyarta na bugawa ta karfi.
A yanzu ta gane bata yi sa'ar rayuwa ba ta ko'ina, ta kwanta saman gadon tana jin tausayinta kanta, domin ta san wannan sirrin dole wata rana zai bayyana dole ne wata rana duniya zata sa wacece ita, wacece ita na asali ba na daukakar da aka riga aka santa da ita ba.

“Komai ba shi da amfani a gurina asali mai kyau shine komai”

Ta furta wasu hawayen masu zafi na sauko mata.

“Na rasa komai”

Ta sake fada tana jin wani irin tausayin kanta marar misaltuwa. A cikin kowa ce rayuwa akwai faduwa da tashi akwai samu da rashi, kuma akwai jarrabawa a yanzu kam ta yarda wannan ita ce jarrabarwata kuma jarrabarwa da tafi ko wace muni. Ta kwanta ba dan bachi ba domin har dare ya raba bachi be kusanci idonta ba, babu komai a kwakwalwarta sai tunani kala kala a cikin har na zalincin da Iya tai ma Ammy. Domin a iya ganinta be su cancanci a masu masauki a fadar ba amman aka ba su har aka jasu a jiki amaimakon ta kyautata sai ta cutar da Ammy har take bibiyar yayanta. A yanzu ta kara jin tausayin Shattima a ranta sanin gaskiyar abunda  yake faruwa, a yanzu ta gane dalilin da yasa Iya take cilasta mata son Shattima, a yanzu ne ta gane dalilin da ya saka Iya bata taba mata fada akan yin ibada ba, bata taba ganin ta yi wata shiga ta kusheta ba ko kuma ta nuna mata kar tai, Ammy ce ko Shattima wani lokacin suke mata fada kan yanayin shigarta, sai a yanzu ta gane dalilin da ya saka Ammy tace kar a sake bari su shigar mata falo saboda Iya ta nemi a hada Shattima da ita, Ammy ta yi gaskiya da ta fada ma Iya cewar kalar zaren ba kalar yadin ba ne. Da tunani kala kala ta washe safiya tana yin sallah asuba ta fito harabar gidan ta zauna sai ta rasa abun da ke mata dadi, ita dai ba tace bata da lafiya ba, ba ta ce lafiyarta kalau ba, haka ba zata iya bayyan yadda take ji a zuciyarta ba for now.
Tana zaune a gurim har rana ta fito tana sanye da kayan bachi tana zaune a gurin sai kallon harabar take, a zuwa yanzu bata san abunda ya kamata tai ba kuka ko dariya? Ko murna? Ko bakinciki ko kishiyarsa? Tama kasa yarda cewar wai ita ce Zainab aka samu ta wannan hanyar, duk irin jin da kanta da take sai ta ji kamar ta fi kowa kaskanci tsakanin jiya da yau.

“Kenan Iya ita ta cinye Auwal?”

Ta fadawa kanta tana jin wani sabin hawaye yana cika mata ido, rabon da hawaye ya kusanci idonta tun jiya da abun ya faru domin ta tabbatar wani abun yafi gaban kuka, a tsakar dare neman kuka tai ta rasa. Ta lumshe idonta kana ta saka hannunta ta dafe zuciyarta tana sauke numfashi a hankali.

“Komai zai wuce zai zama tahiri Zainab, zaki samu farinciki wata rana zaki tuna wannan ki ji ba komai ba, ba ki da laifi ba ki ce a same ki ta wannan hanyar ba, ba ki ce a haife ki a haka ba, ba ke kika saka mahaifiyarki ta zama haka ba...”

Ta fadawa kanta a kokarinta na kwantarwa da kanta hankali. Bata taba sanin hawaye na da zafi ba sai a yau, domin hawaye masu dumi ne suke sauko mata, a take ta ji wani zafi ta taso mata ya baibaye jikinta har saman kanta.

“Zainab har zuwa yaushe za ki daina wannan kukan?”

Iya dake tsaye bakin kofar falon ta tambaya, ganinta a gurin zaune bayan ta duba dakinta bata ciki.

“Har zuwa lokacin da zan mutu...”

Ta amsa mata ba tare da ta bude idonta ba.

“Na san zaki samu kanki a damuwa shiyasa ban taba labarta miki wannan ba, shiyasa na boye miki kuma na shimfida miki wata karyar wanda zaki rayu akanta kuma jiki dadin rayuwa”

“Ko ba ki fada min a yanzu ba, wata rana gaskiya zata bayyana kanta, dole ne za a binciko wannan abun, dole ne za a bukaci sanin asalina, domin shi n martaba ya mace”

Iya ta sauke ajiyar tana jin damuwar da yarta take ciki, ba damuwar abun da ta aikata ba.

“Na sani, amman dai yanzu ki manta da komai ki kwantar da hankalinki, bana son damuwarki....”

Zainab ta mike tsaye sannan ta juyo ta kalli Iya hawaye na bin fuskarta.

“Ba ki son damuwata? Amman kina son damuwar wasu? Me Ammy tai miki kike cutar da ita? Ba mu cancanci mu taka bakin kofar falonta ba, amman ta bar mu mun rabi jikinta, sanadim mijinta da yayanta ake min kallo mace mai kima bayan ni ba kowa ba ce, ba ki auna yadda wata uwar zata ji ba idan ta rasa nata yaya? Baki ayyana yadda Ammy take ji saboda halin da Shattima yake ciki? No Iya fada min akwai hannunki a jikin Mai Martaba ko?”

Iya ta daga mai kai, kai tsaye tana kallonta da idanuwanta na maita. Zainab ta yi kasa da kai tana murmushin da ya fi kuka ciwo, can kuma ta dago ta kalleta.

“Ke kika kashe Auwal?”

Nan kam ta daga mata.

“Ina yin komai ne saboda ni da ke...”

Zainab ta girgiza kai tare da kada mata tsawa.

“Ba saboda ni da ke kike ba, saboda son zuciyarki kike, wace irin macece ke? Wace irin zuciya ce a kirjinki? Baki da tausayi Iya? Baki jin be kamata ki yi wani abun ba? Miyasa zaki cutar da bayin Allah? Me suka miki? Why? Why?”

Ta tambaya tana dukewa a kasa ta fashe da kuka.

“Na yi nadamar haihuwata da kika yi a yau, ina ma na zo a mace, ina ma na mutu tun kamin wannna burin ya shiga rayuwarki? Kin cutar da mutane da dama, kin cutar da ni ta hanyar haihuwata ba ta hanyar sunna ba, kin cutar da Ammy da iyalan gidanta bayan ba su miki komai ba sai kyautata, har Auwal da be miki komai ba kim cutar da shi, kin maida yayansa marayu kin maida matarsa bazawara...”

Iya bata ce komai ba ta juya ta koma ciki, ko kadan bata taba jin nadamar abubuwan da tai ba, bata taba jin tausayin kashe rai ba, bata taba jin tausayin cutar da kowa ba, saboda babu tausayi babu imani a zuciyar maye, shiyasa ake cewa su bada wani shakiki na su, kamar uwa ko uba ko da ko wani dan'uwa ta yadda ba za su taba jin tausayi ko fashin cin kurwar wani ba, babu komai a cikin zuciyar mayu sai keta da hassada ga rashin tausayi da rashin imani, domin sai mutum ya siyar da imaninsa sannan yake iya yin maita.

SARDAUNA POV.

Farin bokitin wanki ne a gabansa ya maida hankali sai wanke kayansa yake, yana amsawa Anti Rabi firar da su ke sama ma, da fira tai dadi ne take dauko masa zancen mutuwar da akai a gidan Sarki.

“Ni ma na aji, indai ta bangaren Ammy ne gaskiya ba zan ji mata dadi ba, amman idan bangaren Hajiya Babba ne Allah ya jikan musulmi, ta fi kowa a duniyar nan bakar cuta da zalinci”

Ya fada yan murza wandon dake hannunsa da dukan karfinsa, Anti Rabi ta yi dariya tana saka kananan itace a wuta.

“Kai ba baka a taba ka baka iya yafiya ba”

“Wallahi na zance yafiya tsakanin da baiwar Allah nan, ta cutar da ni ina maraya na ta cutar da ni, bayan Annabi yace wanda ya taimaki maray kafada da kafada za su shiga aljanna tare da shi, amman ita neman cutar da ni take, hakam ya nuna ba karamin cutar mutanen gidan nan take ba”

“Ai kai yanzu ka wuce maraya, ka girma ka isa tallafawa kanka fa”

“Aa ni ban tashi a maraya ba, sai ranar da na gina kai, irin ginuwar da zan iya taimakon wasu”

“Ni na tsorata sosai a lokacin nan, Allah ne dai ya saka abun ya zo da sauki”

“Ni Wallahi na dauka ko akashe ni za su yi, babu imani a fuskar police din nan, dukana suke kamar sun samu kayan wanki a take suka sauya min fuska, ina da dan haskena yanzu na zama baki, jikina be gama dawowa ba”

Anti ta girgiza kai tana murmushi, ashe sara sukai akan gaba, suna tsaka da zancen wani katon bafade ya sallamo musu kofar gidan. Tun daga yanayin sallamar da tsayarwar mota ya isa ya sanar musu masu sallamar na musamman ne. Sardauna ne ya sama sannan ya wanke hannayensa ya nufi kofar gidan, yana ganin mutane dake sanye da jajayen kaya ya ji gabansa ya fadi domin ya san daga fada suke, tsoronsa daya kar ace wani laifi ya sake aikatawa, dan baya tunanin Nana zata aiko masa wannan tawagar.

“Lafiya dai?”

“Lafiya kalau dan talakawa? Kai ne Sardauna?”

“Aa yayana ne, me ya faru?”

Ya amsa da sauri numfashinsa har gargada yake tsabar tsoro.

“Daga masarauta ake nemansa, ka kira shi a duk inda yake yanzu nan”

“A gaskiya baya garin nan, ya tafi nijar gurin nema”

“Babu ta inda za a iya samunsa?”

“Gaskiya a yanzu dai baya nan, amman lafiya dai?”

Ba su ce masa komai ba suka juya, sai da suka kusa kai wa gurin motarsu sai zuciyarsa ta raya masa ba lallai ne dan wahala da yi kiransa ta sake kiransa ba, idan kama sa za ayi ai da Police za a zo ba da dogarawa ba, idan kuma rabo ne yak kiransa ya ki amsawa ba, what if wani samu ne yake kwankwaso masa kofa yaki budewa.

“Kai ku dakata ni ne Sardauna”

Kusan a tare suka juyo suna kallonsa da mamaki.

“Ban san ku ba ne shiyasa na boye ina fatar dai ba wani laifin ba ne”

“Kasan daga inda aka aiko mu kiranka har kake mana karya?”

Dayan su ya fada yana nuna shi.

“Ayi hakuri dan Allah, ka san duniyar ce yanzu sai da haka”

“Kai dan talakawa ka shiga hankalinka ba ayi ma gidan sarauta karya, yanzu nan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login