Showing 30001 words to 33000 words out of 286946 words
“Wallahi da na san haka abun zai zama da ban fada maka ba, wannan abu be min dadi ba ni Ramatu”
Bata iya ji yo komai amman tana gani ganin yadda bakinta ke motsi ta san da kuma kukan murnafurcin da take, ta san ta shirya komai ne. Daker Falmata ta hade abun da ya tsaya mata a wuya sannan ta nufi kofar fita tana jin kamar ta mutu a yau ta huta, taya zata rayu a idan ubanta kuma ace ba zata ci abincin gidan ba? Miyasa Tumba zata mata haka? Me tai mata? Saboda ta fadi gaskiya? Mi ya kaita fada mata gaskiyar? Miyasa ma yasa ta aikata tun farko? Tana tafiya tana tambayar kanta tambayar da bata da amsa hawaye sai aikinsu suke a fuskarta.
Gidansu kawarta Khadija ta nufa, sa same a tsakar gidan tana wanki kasancewar yau assabar babu school, Khadija na ganin Falmata hankalinta yai mugun tashin.
“Innalillahi ke lafiya me ya same ki?”
Bata ji abunda Khadija tace ba amman tabbas ta ga bakinta na motsi. Hakan yasa Falmata ta fashe da kuka, ta sani an nakasata kenan.
“Khadija Umma ta min shari ta ce Baba ta ga namiji yana taba ni, Baba ya min mari biyu kuma ya doke ni, ya ce kar a sake bani abincinsa, Khadija bana iya ji yanzu sai an yi magana da karfi na shiga uku”
Wani irin rirrike Khadijar take tana fadin kukan kan ya samu hanyarsa, a take Khadija ita ma ta fashe da kuka ita da kawarta aka rasa nai rarrashi wani. Mahaifiyar Khadija ta saki tsintsiyar hannunta tana hawaye.
“Wai me kika tarewa matar nan ne? Wani irin zallumci ne wannan?”
“Allah ya isar miki Falmata Allah ya saka miki”
Khadija ta fada cikin kuka, kamin ta kama kawar tata su nufi baranda su zauna. A gidan Falmata tai wuni Maman Khadija da Khadija suka kitsa mata idan ta koma ta ce wa Falmata taje gurin aikin ta ba su hakuri sun maida ta.
“Kullun idan ta tura ki aiki ki dawo nan ki zauna sai lokacin komawarki gida yayi sannan ki koma, abinci kuma ki zo nan ki rika ci kullum”
Maman Khadija ta fada mata a kunne cike da tausayawa, domin idan bata mata rada ba ba zata ji abunda tace ba. Falmata ta gyada kai.
“Na gode”
“Babu komai ai yiwa kaine, wannan rashin imani na Tumba yayi yawa, ko dan tana ganin bata haifa ba ne take haka? Wannan wace irin zuciyata ce?”
“Allah zai saka mata In-Sha-Allah”
Khadija ta fada tana sharewa Falmata hawayenta. Sai da Falmata ta auna lokacin komawarta sannan ta fita daga gidansu Khadija ta kama hanyar gida tana ta jin tsoro domin gani take kamar asirinta zai tonu Umma ta gano bata je aikin ba.
AA POV.
Tun shekaranjiya da yai hadari da Nana be sake fita aiki ba, ba dan kuma baya iya fitar ba, sai yai amfanin da accident din da yai yace musu ba shi da lafiya zai dauki sati yana jinya, tsoro ya cika masa ciki yana ganin kamar idan yaje zai iya haduwa da Nana ta kira wani tace gashi nan a kama shi wata kila ma Babanta Soja ne ko Alkali a masa daurin goro. Anti Rabi kam ba a magana domin ko kofar gidan aka taba sai ta ji kamar zuwa za ayi a tafi da ita da AA.
“Babu irin gargadin da ban maka ba, amman baka ji ba, gashi nan ka je ka kwaso mana abu kai baka cikin natsuwa ni bana ciki”
Kallon Anty Rabi yai yana murmushi, duk irin tsoro da fargabar da yake idan ya tuna Nana da yadda take wasu dabi'un sai ya samu kansa da annashuwa, ba laifi tana da wauta and he likes that ko dan kudin da take sake masa.
“Babu fa wani abu Anti, da za su kamamu ai da ba za su kai yanzu ba a nemo inda nake ba, ina tunanin bata fada ba ne saboda ita ma bata da gaskiya ai”
“Hmm ka sani ko ana can ana nemanka?”
“Idan nemana ake ai ta san gidan nan, kuma ta san inda na ke aiki”
Ya fada har lokacin murmushi yake.
“Maybe yar farin ce tana da wauta sosai”
Ya fada a fili sannan ya mike tsaye, da gaske he miss her, Allah ka dai ya san irin karyar da tai, da kuma irin sakin da za tayi, no wait ta ma isa gida? What if inda ya barta wani abun ya same ta? Ko ta bi wani kamar yadda ta bishi, ai ba kowa ne na gari ba right? Idan ta nunawa wani kudi zai ma iya kidnapped dinta. A take hankalinsa yai mugun tashi wayarsa dake aljihunsa ya ciro ya chiga contacts sai a lokacin ya tuna ai shi ya bata number sa kuma bata kira shi ba.
Gaba daya sai ya ji ba shi da natsuwa tunaninsa be kawo masa haka ba sai yanzu, and if wani abu ya same ta shi ne sanadi, domin shi ya barta a gurin kuma ya san abunda yai be kyauta ba. Gaba daya sai ya ji hankalinsa yai mugun tashi, be bari Anti Rabi ta fahimci komai ba ya shiga dakinsa ya cire vest din jikinsa ya dauki wata bakar t shirt ya saka ya fito.
“Anti bari na leka nan waje”
“To Allah dai ya tsare idan ka ji baka natsu ba ka dawo gida dan Allah”
“Okay In-Sha-Allah”
Sai da yai addu'ar fita daga gida sannan ya fita gidan. Kai tsaye gurin aikinsa ya nufa duk da ya san ba lallai ne ya ganta ba, sai dai sanin cewa tana yawan zuwa gurin wata kila ma an zo nemansa.
SHATTIMA POV.
Ya saba every end of the week yana ziyartar dakin motsa jiki, but wannan karon sati biyu be je ba saboda be samu zama ba. Hakan yasa yake jin jikin kamar ba nasa ba, tafiya yake a hankali kamar wanda baya son taka kasa da daidaiya yake bin ko'ina da kallo har ya shigo bangaren mahaifiyarsa.
A falo ya tararda yaransa, Iya na zaune kusa da su tana musu wasa sai dai gaba dayansu wani laye suke kamar basu jin bachi.
“Babban Mutum an shigo?”
Iya ta fada baki har kunne.
“Eh Iya ya gidan?”
Ya amsa mata yana leka yaransa.
“Gashi nan fa sun sha ado, yanzu na gama gyara dakinsu”
Da mamaki ya kalleta.
“Mai gyaran bata zo ba ne?”
Iya ta tabe baki tana mikewa tsaye.
“Wannan yarinyar, bata zo ba, wata kila sai gobe ko jibi”
Shattima be ce komai ba, but maybe dan ta kamata tana yi ma yaransa addu'a ne yasa ta ji tsoro ta ki dawowa.
“Karka damu ba dole sai an kawo wata ba, ni kaina zan iya kula da su da dakinsu”
Dan murmushi yai.
“Haba Iya ai ba girmanki ba ne, idan bata dawo ba dai za mu samu wata”
Iya ta yi murmushi tana kallonsa.
“Haka ne Allah ya taimaka, bari na maida su dakinsu”
“Amman a samo wacce zata tsaya da su bana son a na barinsu su kadai”
“An gama Babban Mutum”
Ta amsa masa har da dan risinawa, shi kuma ya wuce dakin mahaifiyarsa. Kwance ya same ta waya a hannunta tana latsawa, sai da ya zauna sannan ya mika mata gaisuwa. Sai ta dago ta kalleshi.
“Lafiya Kalau Shattima”
“Ammy ina tunanin gobe zan koma”
Bata ce masa komai a har na tsawon minti uku. Hakan yasa ya sake cewa.
“Amman ba zan yi dadewar wacan lokacin ba zan dawo”
“Ya dai kamata ka nemi transfer gaskiya, ka fi kowa sanin halin da mahaifinka yake ciki”
Kwankwaso kofar dakin da akai ne ya hana shi cewa komai, be kuma dago ta kalli kofar ba, sanin wanda ya shigo dakin ba bayan Ammy ta ba shi umarni, kamshin turaren kadai ya isa ya sanar nasa cewer Sirleem ne domin ya san kalar turarensa kamar yadda Sirleem din ma ya san na Shattima. A kasa ya zauna yana mikawa Ammy gaisuwa sai ta amsa masa da murmushi tana kokarin tashi daga kwancen da take.
“Ya gida ya aiki?”
“Alhamdulillah, dazu Hajiya ke Fada min Nana ta samu accident”
“Eh amman da sauki sosai”
“Allah ya tsare gaba”
“Amin”
After some minutes ya mike tsaye yana mata sallama.
“Shattima ba ku gaisa ba”
Daga shi har Shattiman ba su dadin maganar Hajiya ba. Domin kowa jin kansa yake ba ma kamar Shattima, ko da wasa Shattima be dago ya kalli Hajiya ba gudun kar ta masa umarni da ido cewar ya gaisa da Sirleem domin shi ya cancanci Sirleem ya gaushe shi ko dan neman auren kanwarsa da yake. Sirleem ya kasara inda Shattima yake zaune ya mika masa hannu sanin cewar idan za a shekara dari a haka Shattima ba zai ce masa uffan ba.
“Shattiman ai ban kura da kai ba sai yanzu”
Sirleem ya fada yana mika masa hannu. Hannun kawai Shattima ya mika masa suka gaisa ba tare da ya kalli Sirleem ba balle har wata kalma ta fito daga bakin Shattima. Sai da Sirleem ya nufi kofa sannan Shattima ya daga kai ya kalleshi, sai kuma ya dauke kai ya kalli mahaifiyarsa wace ke kallonsa tun lokacin da Sirleem ya mika masa hannun.
Sam Sirleem be jidadin abunda Shattima yai masa ba, ya sani ba tun yau Shattima ya saba nuna masa cewar shi ne dan masu gida shi kuma agola, ba shi kadai ba har Zainab wacce kusan matsayinsu daya da shi haka take nuna masa isa tana takama.
Kamin ya karasa fita falon Nana ta kira shi.
“Ya Sirleem”
Juyowa yai ya kalleta be ce komai ba, sai da ta kalli kofar corridor dakin Ammy sannan ta karaso inda yake.
“Ya jikin na ki?”
“Na ji sauki, Ya Sirleem ban karya ba”
“Why?”
Ya tambaya cike da mamaki ganin har 5pm ta kusa ace bata karya ba. Sai da ta sake kallon corridor sannan ta ce.
“Dan Allah zaka kai ni restaurant na ci abinci? Amman karka tambayi Ammy?”
Ya kalli inda take kallo sai kuma ya kalleta kamar ya musa mata sai kuma wata zuciyar ta hana shi.
“Alright muje”
“Kaje can bangarenku ka jira ni, bari na dauko mayafina”
Har ta juya sai ya kira ta ta juyo.
“Nana... An hana ki fita da ni ne ko me?”
“Zan fada maka a mota kaje can ka jira ni”
Bata tsaya jiran abunda zai ce ba ta koma dakin ta dauko kudin da Hajiya ta bata 20k ta saka a cikin skirt dinta sannan ta saka wani karamin veil ta fito da gudu kamar ba ita ce ke ciwon kafa ba. Kamar wacce tai wani kaifi take tsoron a ji haka ta sauka stairs din ta nufi bangarensu Hajiya gabanta sai faduwa yake kar tai arba da Shattima ko Zainab ko wani wanda zai fadawa Ammy ta fita tare da Sirleem.
Can bangaren Hajiya ta nufa sai dai bata shiga ciki ba ta nufi gurin da motocin gidan suke, tun kan ta karasa ya bude mata front seat tana shiga ta rufe motar da sauri.
“X&Y restaurant za mu je, kuma ba fita za ka yi ba, ni zanje nai mana takeaway Please”
Jinginar da kansa yai jikin motar yana kallonta. Can kuma ya tashi motar suka fara tafiya.
“Waya hana ki fita da ni hala?”
“Babu”
Da bashi amsa tana taba kudin da ta boye jikinta dan ta tabbatar idan suna nan.
*🐄🐄 FULANI 🐄🐄*
By Khadeeja Candy
*9*
Har suka isa be ce mata komai ba ita ba ce masa ba. Haka yake a duk lokacin da suka hadu sai ya rasa abunda zai ce mata, na daya dai yana ganinta yarinya kuma yana ganin kamar akwai kurciya a cikinta sosai wanda be dace ya fara firan soyayyah da ita ba, na biyu kuma baya jin yana mata son da ya wuce na gida daya wanda kusan sun zama yan'uwan juna. Ya rasa yadda zai yi Hajiya ta fahimce shi ya rasa da wane baki zai mata magana ta fahimci yarensa, idan ma bata son Mansura zai iya hakura da ita ya auri wata amman why Nana? Why? Har yanzu ya rasa dalilin Hajiya na son ya auri Nana.
Yana fakin ya bude inda yake ajiyar kudi a mota ta dauko 5k ya mika mata, sai ta bude motar da sauri ta fita.
“Ka jira ni a nan”
Shi dai kallonta kawai yai, daman can ya dade da ayyanawa a ransa Nana bata da hankali kamar sauran mutane wata kila kuma gata ne yai mata yawa. Jinginar da kansa yai jikin kujerar motar ya ciro wayarsa ya kamo hoton Mansura yana kallo.
Murmushi yai yana yinta sosai musamman idan ya tuna irin yadda suke mu'alama da kuma yadda take son shige masa jiki, yadda take yabon daukakarsa da kyausa, gashi ta iya drees tana son duk wani abu da yake so, tana gudun bacin ransa, idan wani abun ya same shi hankalinta zai tashi sosai, duk inda yake tana nan manne da shi, wannan dalilin yasa mutane da yawa suka san alakarsu, kasancewar fitattacen mawaki kuma mai tashe duk wani motsi nasa yan media da yan jaridu sun saka masa ido.
Cikin jindadi Nana ta shiga cikin restaurant din, kai tsaye ta wuce reception sai rabon ido take ko zata ga AA. Tsaye tai tana a gurin ta rasa abun da zata ce.
“Hajiya me kike so?”
“Wannan yaron nake nema, wani yaro fari dogo ba sosai ba be da jiki ana mishi lakani da Sardauna”
“Okay kwana biyu be zo ba, ya samu hadari ne ”
Ta dan yi shiru kamin ta sake kallon mai bata amsar ta ce.
“Dan Allah kana da number shi ka kira shi?”
“Okay”
“Yauwa Thank You”
A take ya ciro wayarsa yai dialing number AA ba da wani dade tana ringing ba yai picking.
“Hello Jafar”
“Sardauna wata yarinya ce ta zo nemanka yanzu”
Saurdauna ya tsaya daga tafiyar da yake yana mamaki gabansa kuma na mugun faduwa.
“Wata yarinya? Wacece?”
Jafar ya mika mata wayar.
“Hello”
Yana jin muryarta ya gane ta.
“Nana”
“Na'am na zo baka nan, kana ina ne?”
“Miyasa kika tambaya? Kama ni za ayi?”
“A a ba abunda za a maka, kawai na zo na ji ya jikinka ne, kuma na kawo maka kudi”
“Kudi....”
Dan murmushi yai sai yaji wani karfi da kuzari suna ratsarsa, sai dai tunawa da wani abu yasa tsoro ya kama shi, what if plan ne?
“Nana bana kusa na je Kano, amman idan da gaske kike ki bawa Jafar kudin ya saka min a account”
“To amman yaushe zaka dawo?”
“Sai next week”
“To zan karbi number ka na kira ka da wayar Hajiya Karama ko wata”
“A a ban yarda ba”
Ji yake kamar zata yi amfanin da number na sa ne a gano shi.
“To ka dawo da wuri ka ji”
“To”
“Zan aje wayar kuma zan bashi kudi ya saka maka a account 20k ne”
“Na gode”
Ya mikawa Jafar wayar.
“Jafar zata baka 20 ka saka min account 18k sai ka dauki 2k din”
“Ok ba matsala na gode”
Ta ciro kudin a cikin skirt dinta ta mika masa, sannan ta ba shi 5k din hannunta.
“Ka saka mishi wannan, wannan ka hada min takeaway ka dauki canjin”
Da mamaki ya karbi kudin ta dayan bangaren kuma yana jindadin canjin da tace ya dauka. Cikin sauri ya hada mata komai jalof da naman kaza da lemu da ruwa ya saka mata a leda ya mika mata.
“Please ka ce ya dawo soon ka ji?”
“To zan fada masa na gode Allah ya tsare”
Kai ta gyada masa ta fice cikin rashin jindadin ganin AA da ba tai ba. Sirleem na zaune cikin motar yana jiranta har ta iso ta bude motar ta shiga. Gaba jin tai kamar ta fasa kuka, yana ganinta ya san yanayinta ya canja gashi ta dade a ciki, sai dai be damu ya tambaye ta yai reverse suka dauki hanyar gida.
Da farko AA yai nufi zuwa restaurant din daga can ya tambayi ko ta zo nemansa, sai dai ganin kiranta da wayar abokinsa yasa ya fasa zuwa kuma ya ji duk be da natsuwa, hakan yasa na koma gida jikinsa na ta fada masa plan aka shirya masa wata kila ma za a fara bibiyar line.
Sai da Jafar ya tashi daga aikin sannan ya bawa mai POS din daje kusa da restaurant din ya saka ma AA 18k a account dinsa, AA na zaune yana wanki trouser dinsa wayarsa tai kara ta sauri ya dauka ya duba dan tun dazun yake jiran yaji kudin idan har da gaske ne zai ga kudin, idan kuma plan ne zai gane. Ganin kudin yasa shi murmushi a dubiya be da abun so kamar kudi, ko da Plan ne ake hada masa tun da kudin sun shigo shi be da matsala. Wani irin farinciki ne ya baibaiye shi kamar an masa albishir da gafara. Yana son ya kira Jafar din yai masa tambayoyi kuma tana jin tsoron kar ya kira a bibiyi line sa.
Kamar yadda suka zo dazu, haka ma gurin komawa babu wanda yace da wani uffan, Nana gaba daya mood dinta ya canja titi kawai take kallo, Sirleem kuma driving yake yana ta tunanin yadda zai kwashe da Mansura idan Hajiya ta hana shi aurenta, bayan irin alkawarin da yai mata. Yana ji a jikinsa Hajiya ba zata yarda ya aureta ba ko da bayan ya auri Nana saboda ta tsani Mansura sosai.
After yayi parking Nana ta bude motar ta fita, Bangaren Hajiya ta nufa ta shiga har cikin falon ta bata yi magana da kowa ba ta bude takeaway ta fara ci. Su ma yayyenta kuma kanen Sirleem babu wanda yace da ita komai tun da suka kalleta suka dauke kai ba su sake kallon inda take ba sai da Sirleem ya shigo. Yana kallon Nana ya dauke kai ya nufi corridor da zai sada shi da bangaren Hajiya.
“Bana son duk wani abu da za ace sai an ci, kin san yanzu wani babban aiki ne na ce zan shirya wani abu kuma na basu shi ya ci, ade samu samu wata hanyar, ki mayar masa da abunsa, ke fada masa yai masa wani abun da zai iya samunsa a can inda yake ba wai sai ya ci ba”
“To za ayi haka ranki ya dade, to shi na Mai Martaba fa?”
“Shi be da matsala zan iya dafa wani abun ya saka masa”
“To Hajiya, amman Hajiya zai na ke ganin kamar Talba be da farin jini a masautar nan kamar