Showing 258001 words to 261000 words out of 286946 words
tai bakinciki ba, baka taba ba nuna min banbanci tsakanina da Hajiya ba, Allah ya maka albarka”
“Amin na gode, ni zan tafi a tashi lafiya”
Ya fada sannan ya mike tsaye da zimmar lafiyar sai Ammy ta kira shi.
“Sirleem”
“Na'am”
Ya amsa tare da juyowa ya, sai ta nuna masa gurin zama, komawa yai ya zauna.
“Kar abun ya faru ya saka ka ji wani iri! Har yau har gobe har a bada mi mahaifiyarka ce, kuma Mai Martaba mahaifinka ne, bana son na ga wani canji ko rashin sakewa, kuma kar wannan abun ya saka wata matsala ko rashin jituwa ya shiga tsakaninka da Nana! Ka ji ko?”
Ya dan dago kadan
“Ammy, maganar gaskiya ni a yanzu ba ni da ra'ayin auren Nana, daman can ra'ayin na Hajiya ne ba nawa ba, kuma a halin da ake ciki a yanzu ina da aure...”
Ammy ta masa wani kallo na ban mamaki tana gyara zamanta.
“Na yi aure few days ago ba tare da kowa ya sani ba, kuma na yi hakan ne saboda na ceto rayuwar yarinyar da na aura duk da na san Hajiya ba ta son ta...”
“Ban gane wannan maganar taka ba Sirleem ka yi aure kamar yaya? Kai kake ka haifi kanka balle kai aure ba tare da sanin mu ba? Hajiya ma bata sani ba kenan balle dangin mahaifinki wane irin aure ne wannan?”
Sosai Ammy ta rufe shi da fada, domin hakan da yai ba karamin bata mata rai yai ba, tana masa fada ne a matsayinta na babba kuma mahaifiyarta wanda ko da ace Shattima ne ya aikata haka irin fadan da zata masa kenan.
“Amin aikin gafara Ammy, na san ban yi daidai ba, amman ba ni da yadda zan yi ne saboda....”
Tsinta tsinta ya labartawa Ammy halin da Falmata take ciki da kuma yadda akai aure har ma da yadda Hajiya ta san komai.
“Ba dan aure yana da girma da kima kuma sunna ce mai karfi ba, da sai na saka ka saki yarinyar ba dan komai ba sai dan ka san cewa abun da ka aikata laifi ne babba, amman ba zan yi hakan ba saboda rayuwarka da tata, kuma abun da kai abu ne mai kyau sai dai ka yi kuskure babba gurin aikata hakan”
Sirleem yayi shiru yana sauraren Ammy dake nuna masa bacin ranta.
“Bangaren mahaifinka ka bar mana wannan mu za mu sanar da su, saboda kar abun yai maka yawa, kai kuma ka je kai ta neman yafiyar Hajiya, saboda ba a son bacin rai mahaifiya, Allah ya baka ikon rike matarka da amana kuma ya hada kanku”
“Amin Ammy na gode sosai, Allah ya faranta ranki”
“Idan ka gama boyun sai ka kawo mana ita mu gani, hakika yi dacen mata mai hakuri da tarbiya ga karatun addini na yaba da yarinyar sosai”
“Inshallahu Ammy”
Ya fada sannan ya dan risina mata alamar girmamawa ya mike tsaye ya fice yana mata a tashi lafiya. Sai da ya fito zai shiga motar ya ji wani iri b dan komai ba sai dan tunawa da ada ne sai dai ya nufi bangaren mahaifiyarsa, amman a yau kam sai dai ya bar gidan zuwa na sa gidan..
Cikin damuwa ya isa gidansa, ya dade a motarsa kamin ya fito ya nufi kofar falon, da key din hannunsa yai amfani ya bude kofar falon ya saka kafarsa kamar wani marar lafiya kana ganinsa kasan yana cikin damuwa, kicin ya fara lekawa a zatonta Falmata na ciki, ganin bata nan yasa ya nufi upstairs kai tsaye, dakinta ya fara turawa ya shiga sai ya same ta tsaye tana duba rigar jikinta da alama wanka ta fito take shiryawa cikin rigar da skirt din yan kanti. Tana dagowa sai ta hangeshi ta cikin nadurbi yana takowa zuwa inda take, juyowa tai tana kallonsa.
“Sannu da zuwa”
Be amsa mata ba ya sakar mata murmushi.
“Shiryawa kika?”
“Eh”
“Juya na saka miki zip”
Ta juya kamar yadda ya bukata, amaimakon ya karasa saka mata zip din da ta fara sakawa sai ya zoke shi kasa ya saka hannyensa yana shafa bayanta kamin ya ganganra da su zuwa ya cika hannayen nasa da kirjinta ya lumshe ido ya kai bakinsa ya sumbanci wuyanta, sai ya ji kamar an yaye masa damuwarsa gaba daya a duniyar nan.
“I love you...”
Ya furta mata murya can kasa kamar mai rada. Shiruuuuu tai tana sauraren yadda ta aiki da kirjinta idonta a cikin na shi suna kallon juna ta madubin da ke gabansu. Wani irin bugun kofa da karar bell suka ji lokaci daya, ba kara ta hankali ba, zare hannunsa yai daga jikinta yana motsar lips dinsa, sannan ya juya ya fita, sai ta maida zip dinta ta biyo bayansa ko da ta sauko har ya kai gurin kofar ya bude.
“Mansura... Me kike yi a nan?”
“Dole ka ce me na ke yi a nan tun da ka yi aure macuci mayaudari”
Ta fada cikin kuka sannan ta kutsa ta shigo cikin falon ta kalli Falmata dake tsaye gefen kujera.
“Ai daman na sani, wannan yarinyar ko? Wallahi ka ja mata matsifa kuma ka ja kanka, Wallahi yau har Hajiya sai ta ji maganar nan, kuma wallahi ba zan kyale ta ba”
Falmata ta yi baya baya cikin tsoro idonta na cika da hawaye, Mansura kuma sai yin cikinta take kamar zata riko ta ta doketa.
“Shiiiiiiiiiiiii”
Sirleem ya fadawa Falmata ganin tana son yin kuka. Sannan ya kalli Mansura.
“Ji yadda kika tsoratata, miyasa ba ki yin komai cikin natsuwa ne Mansura”
Mansura ta nuna kanta sannan ta nuna Falmata.
“Saboda wannan shegiyar yarinyar zaka fada min haka?”
“Kar bakinki ya sake furta mata irin wannan kalmar, ba zan lamunta ba get out of my house”
Sirleem ya fada a fusace sannan ya matsa kusa da Falmata ya ja matarsa ya rumgume.
“Ni ni ni ka yi kuskure Sirleem, sai na illataka na illata matarka mark my word”
“Za ki maimaita wannan maganar a kotu, kuma duk abun da ya samu matata ke ce”
Tafi tai tana dariya.
“Eyyyy heyyyy Onídàrúdàpọ̀, apẹ̀yìndà, atannijẹ, daman hausawa ba su iya komai ba sai cin amana, kuma Wallahi i swear to God sai ka san ka taba Yoruba, jẹ itiju, oleshiiiiii oooooooo”
Ta fada cikin daga murya tana masa ihu, ya kyaleta ne saboda ba ya fada da mata a rayuwarsa balle kuma ita da ya san tana cikin jin haushi.
“Fita ki bar min gida ko na saka a wulakanta ki yanzu nan”
“Zan fita ba gida ba ne, zan fita ku kuma zai gagareku zama tun da kuka taba Yoruba kuma yarinyar sai da ya gama cin duwawuya tukuna ya auro ki..... Heeeeeee”
Ta murguda ma Falmata mazaunanta cikin haushi sannan ta nufi kofar falon ta bude ta da karfi ta buga kofar sannan ta fice. Sakin Falmata yai ya karata har gate sannan ya gargadi mai gadin cewar kar ya sake bari ta shigo masa gida, ko da ya dawo cikin falon ya samu Falmata zaune tana kallon kofar cikin tsoro, domin ita dai bata taba shiga wani abu tashin hankali akan namiji ba sai yanzu.
“Ta tafi?”
Yayi murmushi yana zaunawa kusa da ita.
“Ba dole ta tafi ba tun da ba gidanta ba ne, duk wannan iskanci da take tana yi saboda tana ganin kamar ba zan iya mata komai ba, amman zan yi magana da lauyana, za a mana tsakani da ita, domin ba zan yarda tai miki wani abun ba, ke kuma sai ki dage da addu'a”
“Daman bana wasa da addu'a, kuma bana jin wani abu nata zai same ta indai na tsafi ne, ni da Umma take ba ni magani da rubutu na sha, amman addu'ar da nake bata bar komai na ta yayi aiki a kaina ba, na yarda da Allah Sirleem babu abun da zai same ni”
Murmushi yai yana kallon kyakyawar fuskarta.
“Come here”
Ya jata jikinsa ya rumgume tsantsan kamar za a kwace masa ita.
FADIME POV.
maimakon fada ko duka da Fadime za ta sha a gurin Bappa sai ya tarbeta da soyayya da kauna, ya kuma bi ta da addu'ar Allah ya shirya, mutanen gari kuma sai shigowa suke suna yi ma Inna da Bappa barka da arziki, yan rugar sai zuwa ganin Fadime ake tana burge su, a nan dadi ya kumeta tana jin ta samu abun da take so. Babu wanda ya san da labarin wayar da Shattima ya bata sai kawarta Ma'u, bata yarda ta fadawa Inna ba balle Bappa balle kuma har ta kai ga ta nuna musu, kullum wayar na cikin jikinta, bata tabawa sai idan ta shiga bukka ko bandaki, wani lokacin kuma sai ta fakaici idon Inna ta ga ba ya kanta sannan ta dauke ta hoto tana dariya ta boye. Sati daya da faruwar haka Bappa ya kira Shattima akan maganar gidan da Shattima yace ya siya masa. Shattima da kansa ya aiko aka dauki Bappa tare da wasu yan'uwansa Fulani har su uku aka ta fi da su Katsina Ra'ees ya kai shi gidan da aka siya masa, kana ana hannata masa takardun gidan da makullin, take Bappa ya fadi yai ma Allah sujidar godiya yana kuka da hawayensa, yadda yake ma Ra'ees godiya sai ka rantse da Allah shi ya bashi kyautar gidan, Shattima ma kan kasa yi masa magana yai sai da yan'uwansa suka karba su kai wa Shattima godiya sosai su kai masa addu'a da yaren fulatanci kana suka karasa da hausa, ba Bapppa kadai ba ko Inna kasa bachi tai a ranar duk da kasancewar bata ga gidan ba sai ayyana shi take a ranta.
Washe gari Inna da Fadime na zaune waje Inna na zancen gidan da take ganin siyarwa ya kamata Bappa yai wai ya dawo nan ya siya katuwar kona sauran kuma ya siye shanu, Fadime ta turo baki gaba.
“Haba Inna ke ba ki je bunni kin ga yadda suke rayuwa ba, lokacin da n dawo nan ma sai na rika ganin kamar a daji na ke, gaskiya dai mu koma bunni mu ma mu rika cin kaza da kayan dadi”
Inna ta yi magana wayar dake jikin Fadime tai ringing, tun da Shattima ya bata wayar be taba kiranta ba kuma bata san numberta, balle kuma ta shi balle tace ta kira shi kiran ma bata san yadda zata daga ba idan an kirata, arzikinta daya tana gane abun da aka rubuta. Wani irin zillo zuciyarta tai tsabar dadin kiran sai dai bata isa da daga ba a gaban Inna, sai tai zaune tana kallon Inna ko motsi bata yi.
“Kamar waya?”
“Ba waya ba ce”
“Minene?”
Inna ta tambaya cikin mamaki bayan ga karar abu tana ji.
“Memory ne na hade”
Cewar Fadime tana mitsika idon na rashin gaskiya.
“Ina na taba jin memory na waka a cikin mutum? Ina kika gan shi?”
“A lokacin da na je can birni na tsince shi sai na hade da ruwa, shiyasa yake waka yanzu”
“Kuma be tashi waka ba sai a yanzu? Fulani ba za ki daina halinki ba ko?”
Kyalkyalewa tai da dariya ta fiddo wayar da har ta gaji da ringing ta tsinke.
“Na san ba ku iya karbewa ko kuma ku yi min fada shiyasa na boye ta, Shattima ne ya ba ni ita”
Inna ta buge mata baki kamar wanda tai sabo.
“Ke ki rika cewa ranka ya dade, Fulani ba ki da natsuwa”
“To ranka ya dade ne ya ba ni wayar”
Tana cikin fadin haka wayar ta sake ringing, tashi tai da sauri tana kallo red da green din toch din dayan ansa saka received dayan kuma hang up sai ta taba green din tana kallon yadda call din ya fara tafiya sannan ta kai a kunnenta.
“Hello”
Inna ta kura mata ido tana ta kallonta cike da burgewa. Ita kuma ta nufi gurin da aka daure shannun tana ta hello hello ba a amsa mata ba, sai ta sauke wayar ta kalli kiran ta ga yana tafiya sai ta maida wayar a kunnenta.
“Hello Wasim....”
Ta fada tana fatar ta ji muryarsa ya amsa mata, sai ta ji muryar Shattima.
“Wasim ya ce zai kira ki ne?”
“Aa ni ban ma sake ganinsa ba, amman ai zai iya ganin an ba ni waya ya kirani tun da yana tsafi”
“Wato ba ki cire shi a ranki ba ko?”
Ta yi shiru idonta na cika da kwalla.
“Ina son Wasim, ba zan iya cire shi a raina ba, yana da kirki sosai”
Shattima ya katse kiran gaba daya yana jin kamar ta soma masa mashi a kirji, kiran da yai mata na albishir ne sai dai abun da ta fada masa yasa ya ji baya bukatar cigaba da waya da ita, tsaye tai da wayar a kunne hawaye na sauko mata.
“Hello.... Hello... Assalamu Alaikum....”
Tun tana hello har ta gaji ta fara sallama, jin shiru yasa ta sauke wayar tana kallon awarwaron da ya saka mata, sai kawai ta fashe da kuka.
ZAINAB POV.
Tsaye take gaban wani karamun zafi dake ta kwarar da ruwa, lokaci lokaci take kai hannu ta share hawayen da suke cika mata ido tana rumgume da hannayenta, sai kallon ruwa take. Duk abun da take Wasim na zaune saman wani dutse yana kallonta, tausayinta ya cika masa zuciya sosai, he know how hard it's ka bar komai na ka ka dawo rayuwa inda baka saba ba, kuma da mutanen da baka saba ba, cikin wani addini na dabam da al'adar da baka saba gani ba, saukowa yai ya ta ko zuwa inda take tsaye ya tsaya gefenta yana kallon ruwan da take kallo.
“Akwai ciwo ko? Kina jin wani yanayi na dabam, hmm haka na ke ji saboda rabuwa da Fatime, amman na fi jin tausayanki, saboda ke kin rasa komai ni kuwa wanda na ke kawai na rasa”
Ta kalleshi shi kuma yana ta kallon ruwa, ya cigaba ba tare da ya kalleta ba.
“Wani lokacin be kama mu dauki komai mu rike shi a rai ba, komai mai wucewa ne, ina jin yadda kike ji saboda ina jin kamar wani bangare na rayuwata, kuma ina jin kamar zan iya zama silar farincikin idan kin ba ni dama”
Ta sauke kai kasa a yayinda shi kuma yake kallon fuskarta.
“Za mu bar garin nan saboda ki samu farinciki kuma ki sake, ki cigaba da rayuwa kamar yadda kike saba”
Ta kalleshi tana murmushi idonta kuma na zub da hawaye.
“Har da kai?”
“Eh, to me zan yi idan na zauna a garin? A duk lokacin da na tuna abun da suka min akan Fatime zai na ji bana bukatar zama garin, kamar yadda ke ma na san garin ba dadi yake miki ba”
“Bana jindadi, amman ina kokarin kafa rayuwata a nan ne saboda mahaifiyata tana nan, babu inda ya fi min dangina”
“Ba tafiya zaki yi ki barsu har a bada ba, zaki rika zuwa kina dubasu a duk lokacin da bukatar hakan ta taso, ko ba komai za ki fi jindadin rayuwa a inda nutane masu irin addininki suke rayuwa sama da nan, maganar mahaifiyarta ki kuma ki barta”
“Saboda me?”
Shiru yai yana kallonta kamar mai fargabar abun da zai fada mata, sai ya mika mata hannunsa.
“Ina son ki yarda da ni Zainab, ina son ki aminta da ni, ki ba ni dama kuma ki sake jikinki da ni, ta yadda zan iya yakar kucin dake zuciyarki, ina son na shimfida miki wata sabuwar rayuwa wanda ni da ke zamu manta da komai mu yi farinciki kamar kowa...”
Hannunsa ta kalla sannan ta kalleshi gabanta na bugawa da mugun karfi da kuma sauri a lokaci daya.
“Me ya faru da Iya?”
Sai da ya hade yawun bakinsa sannan ya ce.
“Iya ta mutu tun a ranar da na rabo ta da ke, cikinta ya kumbura sosai muna isowa nan sai ya fashe saboda kankarun maitar dake ciki”
Baya baya tai wasu zafafan hawaye na sauko mata, saurin rikota yai ganin zata fada a cikin zafin ruwan, sai ta durkushe a masa jikinta na rawa ta rike warkin dake jikinsa da karfi kamar zata yagashi ta fashe da kuka mai karfi.
“Kenan na rasa kowa... Na rasa kowa.... Na rasa kowa...”
Ta maimaita har sau uku muryarta na rawa, hawaye na sauko mata kamar ba gobe, lokaci daya idon Wasim ya cika da hawaye.
“Ba ki rasa kowa ba Zainab ina tare da ke har abada”
Ya fada tare da dukawa ya rumgumeta sosai ta yadda zata yarda har a yanzu akwai wanda ya damu da ita kuma yake tare da ita.
_________
Ina mata matan kwalisa Matan da suka ansa sunansu na Mata? Ina wadanda ke cewa mun yi mun yi bamu ga amfaninshiba? Hmmm to ku zo ga Yar gidan Maifata ta zo maku da Al ajabu, dan tsugunno, gumba da tsimi da Zuma daban daban, maganin sanyi na maza da Mata. Ga kuma garurruka irinsu mallakau sabuzu kuwa, sa bahaushe saibi, Dan hubbare kafi malam aiki, ke kadai ke da miji, dahuwar kaza, tattabara, ciccibi da dai sauransu. Ba anan kayanmu suka tsaya ba, muna hadin amare na musamman turaren sutura turaren tsugunno turaren wanka da na daki da na jiki duka 4amare nasu na musamman ne, amma ga tsuhuwar da ke son komawa yarinya itama zata iya zuwa ahadata kai abundai sai wanda ya gani, dan haka karkubari abaku labari, domin neman karin bayani zaku iua nemana ta wannan number 09029891757 ko 08169311410, muna aikawa ko'ina a fadin kasar nan har waje kasar nan muna aika kaya.
Address: Nasarawa Samaru Area gurin masallacin mai sola Gusau Zamfara state Nigeria.
63
*Khadeeja Candy*
*Littafin nan na kudi ne biya ki karanta cikin aminci. Pay 300 to 2451879008 Hadiza Abubakar Zenith bank, then send the evidence via 08036126660*
3 MONTHS LATER...
Fadime na tsaye bakin bukkarta dafe da waya a kunnenta sai faman dariya take. Yadda dariyar take isa a kunnen Shattima sai ta saukar masa da natsuwa har ya samu damar murmushi.
“To yanzu fada me nake yi?”
Yayi shiru yana kamar mai tunani.
“Kina tsaye bakin kofar bukkarku”
Ta wara ido tana dariya.
“Wallahi ka canka daidai, dan Allah waya koya maka?”
“Wasim”
Ta sake yin dariya.
“Wallahi Wasim be ko ya maka ba, ai baka san shi ba baka taba ganinsa ba”
“Na hadu da shi ban fada miki ba ne kawai, kuma yace kar na fadawa kowa wannan lakanin”
“Hahaha ban yarda ba, sai na ganka a gabana”
“Rufe idonki”
Ta rufe kamar yadda ya bukata, sai ya mike tsaye daga kan kujerar