Showing 285001 words to 286946 words out of 286946 words
wata kungiya mai taimakawa musulmai haka a garin sokoto? Wasu suka fada mata hukumar zakka dawakafi sai dai yadda aka labarta mata Famwan da irin ayukansu sai ta ji hankalinta ya fi kwanaciya ta da ita, sai da tai magana da Wasim ta fada masa zata je ta dawo sannan ta karbi addiress din inda cibiyar kungiyar take, ta yi sa'a a lokacin shugabar na nan, da ta fadi dalilinta na zuwa sai sukai mata maraba suka karbeta hannu biyu suka gabatar mata da komai cikin har da yadda zata agabarta komai kamar yadda shari'a ta tanada, kana suka jinjina mata, sai dai ta nuna musu bata son kowa ya san abun kasancewar sananniya ce a media.
Duk wani abu da ya kamata kungiyar ta yi mata, aka hada Wasim da manyan malamai da suka gabatar masa da komai na musulunci ya karbi kalmar shahada kuma suka karanta masa cewa ba a hada Allah da wani abu gurim bauta kamar tsafi ko kuma wani ubangijin na dabam. Shi kansa a lokacin sai da yaji wata rahama da natsuwa ta lullube shi da be taba jin irinta ba, natsuwar ruhi da jiki da kamala ta addinin musulunci.
Ita da kanta ta bukaci mutanen da za a hada ta da su ta siya makanta gida a cikin garin albarka garin sokoto, sai suka hada ta da adalilan dillalai akai ta nuna mata gidaje har ta samu wanda ya kwanta mata a unguwar Clapperto road, ta siya gida mai kyau kusan 50million.
Kungiyar ta dauki kudi mai kauri ta bata, da shi Zainab ta kara ta saka duk wani abu da zata bukata a gidan daidai karfinta, washe garin ranar aka daura musu aure a babban masallacin jumma'a na isa talatar mafara. Tun daga lokacin sai Zainab ta koma da zama a gurin daya daga cikin matan da suke fanwan din saboda kula da ita, sun yi mata duk wani hallaci da ya kamata, ciki har da alkawarin samawa Wasim sana'a kasancewar be yi karatu ba.
After a month sa tarewarta ta koma Yola ta saida gidanta ta dauko motarta ta dawo sokoto ta bude shagon kasuwanci na siyarda tufafi da duk wani abu na sakawa kama daga na zama har na mata, katuwar plaza ce ta kama haya ta cika ta da komai na kawa, kuma ta cigaba da sana'arta ta daukar hoto da karbar tallar kamfanona har tai nasara kamfanin Glo suka bata ambassador.
Sannu a hankali Wasim yake koyon komai na addinin, tun yana jin wuyar wasu abubuwan har ya soma sabawa, sunansa ma da ake kiran da shi Muhammad tun a lokacin da ya musulunta sai daga baya ya soma sabawa da shi, da fari idan an kirashi haka baya amsawa sai ya ji kamar ba shi aka kira ba. Sai dai yawan zama da yake a shagon Zainab da ke gawon Nama yasa ya soma sabawa da sunan da kuma mutanen dake kula da shagon, shi kuma yana a matsayin manager ta.
Ba shi kadai rayuwarsa ta canja ba, har da Zainab domin a yanzu ta daina shigar banza da take da magana any how, ga sa'ido akan Wasim da take sosai saboda yadda yan mata suke kawo masa hari idan ya fita, kasancewarsa mai jini a jika gashi kyakkyawa kamar shi yai kansa fari kamar a zaga jini ya fito, sai wani kara fresh yake saboda yana samun hutu da jindadi a yanzu ga safiyayyen gurin bachi da abinci mai kyau ga sutura idan ya saka ya fito sai yai kamar wani balarabe.
Shi kansa yana kishinta kuma yana tayata kare mutumcinta, musamman a yanzu da take kokarin zama uwa, wani abun har shi zai tuna mata cewar addinin musulunci ya hana, domin yana yawan sauraren wa'azi an every night sai ta tafi masallacin dake can kusa da gidan sidi mamman gurin karatu, yana koyar komai a hankali duk da kasancewar ba komai yake ganewa ba, musamman idam yace zai hada harufan arabi ya karanta sai ya ji abu ya masa nauyi but Alhamdulillah tun da yana fahimtar addinsa.
*AFTER FIVE YEARS...*
Hakika rayuwar dan'adam tana cike da kalubale na rayuwa kala kala, wala'alan kana cikin jindadi ne ko akasin haka, dole ne akwai daci akwai bakinciki a wata rana, sai dai idan an yi hakuri da sannu komai yake wucewa, kuma duk abun da yai farko dole ne cilas tai karshe, sai dai be zama lallai karshen yai dadi ba, kuma ba dole ne karshen ya kasance marar dadi ba. Waya tsammaci rayuwa zata kawo Zainab da Wasim a haka? Balle Falmata da Sirleem? Haka ma Shattima da Fadime? Ba su kadai ba har Aliyu da Ataa Muhseem da matarsa suna gurin, Mama Fulani ma tana cikin yan'uwanta.
Babu wanda yai tsammanin wata rana zata zo da sukansu za su hadu akan abu daya, ita kanta Zainab ta cire rai daga waiwayar rayuwar Shattima da Ammy, sai dai yadda suka samu labarinta suka kira a waya suka nuna mata nuna tare da ita har yanzu sai ya sa ta ji sanyi ta wani bangaren, shi kansa Wasim be tsammaci wata rana biki zai hada shi har ya ga Fadime da yaranta ba, ita ta ganshi da yayansa har biyu, kamar yadda bata tsammaci wata rana zata zauna a kujera kusa da kusa ba ita da Falmata. Dukamsu sun ci ado kamar ba a mutuwa, kallo daya za ka musu ka san suna cikin farinciki da kaunar junansu, gaba dayansu hankalinsu ya tafi gurin tafin da ake sakamakon fitowar amarya da ango cikin takun kasaita, Nana ce tana sanye da doguwar riga da farin mayafi dan karami kamar yadda rigar jikimta ma take fara sol. Sardauna kuma na sanye da tsadaddiyar shadda sky blue wanda ta karbe shi ta fito da kyaunsa, tsakanin shi da Nana sai ka rasa waya fi wani kyau da murmushi. Tafiya suke kamar wadanda basa son taka kasa, har suka isa gurin da aka tanadar musu suka zauna. Sannan kowa ya mike tsaye har su akai national anthem, kana Mai Martaba ya fara zaunawa Ammy na gefensa, gefenta kuma matar gobna ce, sai Governor da kansa a gefen matarsa, sai kuma manyan mutane da wakilansu.
Mc ya mike tsaye yana ta gabatar da komai, ba ayi wata riya ba, sai dai bikin ya kayatar domin ayi gayyato masu nishadantar kala kala suka kayatar da bikin. Sai kusan 11 aka rufe taron da addu'a sannan kowa ya nufi gida wadanda aka tanadarwa masarauki kuma suka sauka a masaraukansu.
Washe garin ranar ya kama Sunday ranar za a kai Amarya Nana dakin angonta Sardauna, daman sun Friday aka daura auren Saturday akai Walimar dare bayan ayi sauran bukuwan da mata suke yi kuma bukukuwan al'ada.
A hankali take saukowa da shirinta tana kallon mijinta dake dafe da waya a kunne yana dariya, kana gani kasan yana cikin nishadi.
“Da wa kake waya?”
Ta tambaya bayan ta zauna kusa da shi, a lokacin da ya gama wayar.
“Mansura..”
Dassss ta ji gabanta ya fadi.
“Mansura fa ka ce?”
“Yes”
Ya fada try to kiss her neck sai ta ture shi.
“Miye hadinka da ita?”
“Easy easy Mom Nu'ayn ta fa yi aure har ta haihuwa”
“Yaushe?”
“An dade tun a lokacin da na haihu ta ce ta fahimci da gaske ba zan aureta ba, maybe ta yi duk abun da zata yi ta kasa ne, yanzu haka tana garinsu ma”
“Amman kake waya da ita kasan matar wani ce? Amman ni nan har fada min kake ko malamai na baka yarda nai musu magana ba sai da babban dalili, ashe ba dadi”
Yayi dariya yana rungumota.
“Eh kuma kika wasa sai na hana karatun gaba daya, dan ba zan yarda ana kalle min mata ba ana magana da ita ana jin zakin muryarta”
“Amman kai kake yi da matar wani?”
“Wallahi ban taba kiranta ba ita take kirana, kuma zan daina dauka daga yau inshallahu”
“Da dai yafi maka”
Ta fada a fusace tana jin wani bakin kishi na turniketa. Sai ya riketa yana dariya ya rumgume.
“Kin yi kyau, jiya kin ga yadda ake kallonki wai? Gaskiya idan za'ayi bikin su Kausar Hijabi za ki saka”
Ta watsa masa harara.
“Amman kai da akai bikin Rima da yan mata suna kallonka ai zuwa kai ka fada min wai yan mata sai kallonka suke”
Ya saka dariya yana kara rike a kokarin da take na ta zame daga jikinsa.
“To ai ni namiji ne, hudu aka ce na yi, ke kuma kin auru”
“Au haka ma zaka ce? Shikenan bari Allah ya kai mu bikin kaga yadda zan yi ado, ai yanzu Aymana da Nu'ayn suna gurin Momy ba mi case ko gyale ba zan saka ba, kuma duk wanda ya tare ni tsayawa zan yi”
“Aiko da da an yi bu**uba... Ni din za a tari matata a kwana lafiya a Yola?”
Ta yi dariya tana Kwantowa jikinsa kamar yadda shi ma yake dariyar.
END....!
Ni kuma na yi murmushi na ce Alhamdulillah da Allah ya nuna min farkon da kuma karshen littafin Fulani lafiya, Allah ya yafe min kuraren da nai darasin dake ciki Allah ya ba mu ikon amfana da shi.
Na sadaukar da littafin nan ga mutane uku masu daraja.
Safiyya Dan Jumma (Ummul Falsak)
Asma'u Badamasi (My Asmee)
Salma Gidado (Salwees)
Ina sonku ina kaunarku har cikina raina, Allah bar mu tare har aljanna, kada Allah ya ba shaidan damar shiga tsakaninmu.
Ba zan manta da ku ba, Mama Aisha Samaru uwata ta kaina uwata maganin kukana i love you. Mamana
Maman Hafiz, Mama Hajiya Zainab Kano, Aisha Maccido, Hadiza Mai Fata. Rahama Kabir, Mrs J Moon (Mu ne yan uku lol).
Godiya ta musamman gare ku wadanda suka siya littafin nan, har muka kawo yanzu i love you irin sosai din nan idan babu ku babu ni.
Sai kuma idan mun sake tarayya da ku a littafi na gaba, idan mai komai mai kowa ya yarje mana mai suna BAƘAR WASIƘA. ina rokon yafiyar wanda na batawa rai cikin ganganci ko rashin sani, ayi hakuri a yafewa Candy dan'adam ajizi ne.
*** *** ***
*BAƘAR WASIƘA...!*
_Mai farin rubutu_
Ban ce tafiyar mai sauki ba ce.
Ban muku alkawarin zallar soyayya ba.
Ban ce babu farincikin ba.
Kunci, bakinciki da damuwa, sune abubuwan da suka taru suka tare farincikin AMINATU, kalubalen rayuwa bayan wata rayuwar, tabbas akwai kuka akwai damuwa da bakinciki.
Labarin Tafida, Rafi'a, Laila Sudais da kuma Aminatu. Labarin BAKAR WASIKA, labari ne da zai tabo wani bangare na rayuwar mace, kuma wani bangare na rayuwar al'ummarta da iyayenta...
Ina fatar zaku karbe shi kamar sauran, duk na san ba lallai ne yai muku dadi ba domin ba soyayya ce zalla ba, kalubalen rayuwa ne da fadi tashin yar gudun hijira!
A ina zata kwana? Wa zai bata masauki? Taya za a fahimce ta har a nade mata damuwarta? Wa zata kaiwa kukanta iyeyenta ko al'ummarta? Ta ina mafarkinta ke tabbatuwa? Ashe bayan wuya akwai wata wuyar, bayan dadi ma akwai wata wuyar, bayan wuya kuma akwai dadi.
Tabbas akwai ciwo a rayuwar da baka san karshenta ba, akwai tsoro a mafarkin da ka gagara farkawa! Ta ina lamarin ya fara? Ina tsakiyarsa da karshe? Yaushe damuwar zata wuce? yaushe bakincikin zai gushe? Sai yaushe hawayen zasu tsaya? Zuwa yaushe ne kuncin zai yanke?
Ashe a cikin rayuwa akwai wata rayuwa? A cikin rayuwar ma akwai mutuwa?
BAKAR WASIKA...
1ST JUANURY 2022
In-Sha-Allah
BEST REGARDS ❤❤❤
Khadeeja Candy ce👌💞