Showing 111001 words to 114000 words out of 286946 words
waje a bar wannan maganar”
Shattima ya dago ya kalleshi.
“Saboda me? Ba san inda za a dace ba Mai Martaba duk fata muke yi”
“Hakan yasa nake son maka wata wasiya, na san matsalar auren nan yana damunka, ina son nai maka wasiya cewar kai ta aure ko da kuwa yau zaka aura gobe ta mutu, to jibi ma ka sake auren wata, a koda yaushe ina maka kallon babba a cikin iyalina, ina jin dadi da alfaharin da Allah ya bani kai a matsayin da, Omar ina maka wasiya da ka ji tsoron Allah, kuma ka rike yan'uwanka tsakani da Allah babu banbanci ko nunawa wani ya fi wani...”
A take jikin Shattima yai sanyi, sai ya ji kamar Mai Martaba na masa wasiyar bankwana ne. Shiru mai Mai Martaba yai na dan lokaci sannan ya cigaba.
“Rayuwa a gida da Family irin wannan akwai wahala, amman idan ka jure Allah zai taimakeka, bana son ko bayan raina a samu rabuwar kai a tsakaninku, bana son tsabani ko kiyayya ta shiga tsakaninku, ka yi kowa biyayya ka bawa kowa hakkinsa...”
Mai Martaba bai karasa ba Shattima ya katse shi jin kamar kunnuwansa da zuciyarsa ba za su iya daukar abubuwan da Mai Martaba yake fada masa ba.
“Inshallahu zaka samu sauki Mai Martaba”
Mai Martaba ya gyada kai.
“Sauki yana tafe da yarda Allah, amman sauki na har abada, sauki wanda daga shi babu wani ciwon Inshallahu, ni kadai na san me nake ji akan ciwon nan Omar, bayan ciwon jiki a nake kwana da shi kullum na tashi da shi, ga ciwon tsoron rabar mutane da tunani, na yarda wannan jarabawa ce, babban Sarki kamar ni ace bana iya shiga cikin mutane, bana iya sauraren al'ummata, ina jin tsoron abun da zan fadawa Ubangijina, ina jin kamar sauka ta cancance ni wata zuciyar kuma na raya min idan nai hakuri nan ba da jimawa ba zan tafi na bar Sarautar, ba barin sarautar ce tashin hankalina ba, yadda zan tafi n bar ku, rashin hadin kanku da irin matsalolin da kuke samu tun a yanzu da nake raye, babu uban da zai so ya tafi ya bar iyalansa a watse kansu a rarrabe, kai ne babba Omar dan Allah ka kula da yan'uwanka, na san na dora maka abu mai nauyi, amman Allah zai taya ka, ka bi Hajiya Bilki kamar Ammy, kuma kai ta hakuri da yan'uwanka, musamman Mama Aisha (Nana) ita ce karama a cikinku ita ce kadai ta tashi bata san gata da dadin uba, bata san ta rabe ni ba saboda lalurata, ka kyautata mata ka zame mata uba, kuma kai hakuri da halayenta akwai kurciya a tare da ita, sannan ka saka ido akan tarbiyar Karima, ka bi kanen mahaifinka kamar ni.... Kuma kai ta hakuri da rayuwa”
Shattima ya rufe idonsa da suka gama cika da hawaye.
“Inshallah zaka same ni mai cika umarninka Mai Martaba”
“Allah ya maka albarka”
“Amin”
Ya amsa yana jin kamar ya fashe da kuka.
“Anjima idan Ammy ta shigo, zan sa ta duba maka takardun wasu filaye da gidajen da baka san da su ba, akwai kuma takardar da nai rubutu na wadanda nake bi bashi da kuma wadanda kasuwanci ya hada mu, zan hannata maka su ka aje inshallah”
Uffan Shattima be ce zai iya kara cewa ba ya mike tsaye.
“A tashi lafiya Mai Martaba”
Ya fice daga falon da sauri kamar zai tashi sama, be taba daukar haka wasiya take da nauyi ba sai a yau. Gaba daya jin yake duniyar na juya masa, ta ina zai fara ina zai sauke why mai martaba yai masa wannan wasiyar a yanzu.? Why him? Har ya iso bangaren Ammy kirjinsa be daina nauyi ba, ga zuciyarsa sai bugawa take kamar zata fito, nauyin ba kirjinsa kadai yake ba har a kansa ji yake kamar Mai Martaba ya dauki wani katon dutse ya dora masa a kai. Sai ya samu kansa a falon Ammy sannan ya soma tambayar kansa abun da ya kawo shi a falon, but he need to see his mother maybe ko zai samu saukin abun da yake ji. Hakan yasa ya nufi dakin yana kokarin tura kofar dakin ya shiga ya ji muryar Nana.
“Ni sai na tafi”
“Nana kina ganin rashin kunyar da kika min zai barki ki rayu in peace, kina min tsawa your own biological mother”
Tsaye yai jikin kofar yana kallon Ammy dake zaune kasa ta jingina da gadonta tana kallon Nana kamar Nana ce uwar ita ce yar.
“What is happening?”
Nana kamar mai jira ta juyo gurinsa da sauri ta soma masa bayani kamar zata yi kuka.
“Ya wai bikin yar Farin gida da ake wai Ammy ba zan je ba, kuma Amal kawata ce ita ce ta gayyace ni ita kanwar Amarya ce class din mu daya”
“Yaushe ake bikin?”
“Yau ake budar kan Amarya, kuma ba cikin manyan zan tsaya ba, ni gurin su Amal zan tsaya”
“Shikenan je ki fara shiri tun yanzu, zaki je anjima”
Da sauri ta rumgume shi tana murna.
“Thank Youu Ya I love you”
Ta sake shi sannan ta fice daga dakin cikin murna ranta fes tun da Shattima yace zata je. Sai da ta fice sannan ya nufi inda Ammy take ya zauna gefenta sai shi akan gadonta ya zauna tsabanin ita data ke kasa zaune.
“Ammy why kika hana ta zuwa?”
“Bata son makaranta, duk abun da aka ce tai ba zata yi ba, sai kuma a rika bin ra'ayinta ana mata yadda take so?”
Shiru yai yana kallon yadda idon Ammy ya cika da hawaye, sai ya ji tausayinta ya rufe masa zuciya.
“Amman idan kina irin kalaman nan marar dadi a gareta wani abu zai iya samunta, kuma still mu ne zamu shiga matsala, she's still young”
“Like a baby?”
Ta tambaya hawaye na sauko mata.
“Ina jin kamar ace Nana tana da wata uwar ba ni ba, da yanzu na maida ta hannun mahaifiyarta na gaji da wanne zan ji”
Ta fashe da kuka. Hakan yasa Shattima yaji damuwarsa ta karu, ya mike tsaye jiki ba kwari ya fice daga dakin domin ko kadan baya son jin kukan mahaifiyarsa. Dakin yaransa ya nufa or maybe zai samu peace of mind a can, Luma kadai ya samu a dakin tana ta bachi, kusa da ita ya zauna ya shafa fuskarta a hankali yadda ba zata tashi ba, sannan ya mike tsaye yana sauke ajiyar zuciya ya nufi gurin windows dakin wanda ke saiti da Garden din bangaren Ammy, tsaye yai jikin window yana kallon itacen dake garden din wani iska mai dadi yana bugunsa, hannayensa ya dora jikin window wanda hakan ya bashi damar hango Falmata dake zaune a garden din tana ta kallon wani gurin na dabam kamar mai tunani. A inda take tsaye na kasa baya iya hango na sama sai dai na sama ya hango na kasa.
Hango Sirleem da tai tafe yasa ta mike tsaye tana jiran ya karaso kusa da ita, tun daga nesa yake sakar mata murmushi har ya karaso.
“Naje daukarki Momy tace tasa Ameer ya kawo ki, na shiga bangarenku n karbi takardar maganin wata hadima tace min kina Garden”
“Eh ta bani maganin ma”
“Oh Momy akwai karamci sai da ta siya maganin ma”
Ya fada yana murmushi domin kadan daga halin Momy ne taimako da karamci ga tausayi da son mutane.
Ya kai hannu ya karbi maganin yana dubawa.
“Ta fada miki yadda za ki yi amfani da shi?”
“Eh ina son sai na je gida sai na fara idan zan kwanta”
“Amman dai yau ba zaki kai dare kamar jiya ba ko?”
“Sai yaran sun yi bachi tukuna”
Ya mika mata ledar maganin yana fadin.
“To ya kamata ki samu Mai Napep din da zai rika kai ki ya dawo dake, zan biya shi”
Kallonsa kawai take baki sake tana mamakin yadda yake da karamcin da son taimako har haka. Kamin tace komai yace.
“Ba ki ba ni labarinki ba fa”
Ta yi kasa da kanta, ba dan bata ji domin duk maganar da yake mata yan mata ne cikin daga muryar ta yadda zata ji, ba ita kadai ba har wanda ke kusa da su ma zai iya ji.
“Hey....”
Ya fada yana leken fuskarta. Sai ta dago ta kalleshi, ta sake maida kanta kasa.
HAJIYA BILKI POV.
Hajiya Bilki ta sauke ajiyar zuciya jin abun da Aminiyarta kuma matar Waziri wato Hajiya Talatu take fada.
“Wallahi kuwa”
“Ki ce kina cikin tashin hankali, to wai Waziri lafiya yake kuwa?”
“Ni ina na sani, sai wani fadar yake duk na sake yi ma dan da'uwansa kazafi a bakin aurena, ina zaman zamana zai dauko min wata masifar, wannan duk na Ammy na na sani, shi kuma baya iya musa mata tun da ta shanye shi, daga ni har Maijidda jiya ba mu runtsa ba, kuka kawai take”
“Ai dole tai kuka za akai ta ga halaka, yarinya tana zamanta za a aura mata mutuwa, Wallahi ki tashi tsaye karki yarda sam a kai ki a baro”
“Ai ba zan yarda ba, sai dai ayi wacce za ayi, amman ba zan Waziri ya aurawa Shattima yata ba, ko ana zaune kalar ai ba zan yarda ba balle kuma mutum ya zama maye, idan dama ta ki hagu zan koma, idan ta gwada be yarda ba be janye maganar ba, garin su mutanen nan zanje ayi masa asiri ya janye”
“Ai haka ya dace gaskiya, sai muje tare, kaji min tashin hankali”
“Wai sai fdar yake indai ba Shattima ya fasa ba Wallahi ba za a fasa auren ba, so yake yana aura masa ita ta mutu, waya sani ma ko Ammy ce take cinye masa mata, ko kuma can garin tsafe tsafensu suka kwaso wani mugun abu”
Hajiya ta dade tana magana da Hajiya Talatu kamin ta katse wayar shi M saboda shigowar Nana.
NANA POV.
Tana Fita daga dakin Ammy ta nufi bangaren Hajiya. Tana tura kofar dakin ta shiga sai Hajiya tai wa Hajiya Talatu sallama ta kalli Nana tana murmushi.
“Daughter”
“Na'am Hajiya dan Allah wayarki zaki ara min na kira driver na”
“To gashi”
Ta mika mata wayar, Nana ta kai hannu ta karba ta fice daga dakin tana nemo line AA call list din Hajiya domin bata yi saving number ba. Bugu daya ya dauka.
“Hello”
“Sardauna”
“Na'am”
“Ka shirya anjima da 8 ka zo ka kai ni gurin budar kan Amarya”
“Okay”
“Karka wuce 8pm”
“Okay”
**
Ya amsa mata tare da sauke wayar tare da saka ta aljihu sannan, ya marasa cikin gidan yana nade wandonsa.
“Anti wanki da yamman nan”
“To kayan sun yi datti, kai kuma ba zama kake ba”
Hannayensa ya jefa cikin ruwan ya soma taya ta wankin, daman can idan tana wanki ya kan taya ta ko kuma yai mata, kayan su Khaleel da Aymana duk shi yake wanke wa, har girma yana mata idan yan kwarai na saman kai, ko kuma ya mata rabin girkin ita kuma ta karasa. Sai da ya fara dauraye tufafin yana shanyawa sannan ya dauko mata wani labarin.
“Anti ina tunanin komawa makaranta fa”
“Makarantar lafiya? Ni ba ni da kudin biya maka makaranta yanzu, kai kuma ba aikin wahala kake so ba balle ka taimaki kanka”
“Ai wani aikin zan samu mai soka soon, zan gyara gidan nan na masa fenti na saka masa tayis na siyo miki gas, ke har makka sai na kai ki na siya miki mota, su Khaleet na saka su makarantar kudi, komai zai zama normal...”
Kallonsa tai.
“AA baka rabu da yarinyar nan ba ko? So kake ka jefa kanka a matsala ko?”
“Ni fa na rabu da ita bana tare da Ita sam sam sam”
“Ya dai kamata ace idan nai maka magana ka ji, idan na ce ka bari ka bari, ba ka da wanda ta fini a yanzu, baka da gata sai ni, kasan bamu da kowa sai Allah, idan ka shiga wani hali aka kama ban san ya zan yi ba, aje min wankina”
Ya kalleta a sanyeye.
“Ba maganar yarinyar nan ba ne Anti”
“Ni dai ka aje min wankina”
Ya cire hannunsa ganin da gaske take domin babu alamar wasa a maganar ta balle kuma a fuskarta. Wannan abun yake tsoro ya dade yana son labarta mata ko kuma sammata wani abu amman yana tsoron abun da zata fada, domin shi kansa ya san ba shi da gatan daya wuce Antinsa a yanzu, ita ce uwarsa ita ce ubansa ita ce komai nasa.
“Ka rika taka tsantsa da rayuwa AA, neman kudi ba hauka ba ne bana son ka jefa kanka a matsala, na rasa uwa n hakura, na rasa uba na hakura, na rasa miji na hakura, yanzu kam bana jin idan na rasa ka zan iya rayuwa, kai kadai ka rage min, ni ma ni kadai na rage maka, ya kamata ace idan na maka magana ka ji, ka san irin wahalar da muka sha kamin mu kawo yanzu, kasan irin fadi tashin da nai kamin na samu na gina kaina, muna zaune cikin rufin asiri kana kokarin jefa mu a hadari?”
“Idan akan yarinyar nan Allah ya min arziki, ba fa akanta ba ne”
Uffan Anti bata sake ce masa ba, ta san akanta ne tun da har yai ma kansa addu'ar arziki. Ganin yadda ranta ya bace yasa ya tashi ya nufi gindin murhu ya fara saka itace zai hura mata wuta.
“Karka kunna wutar nan”
“Girki zan dora miki”
“Ba mu da abun dafawa kwado zan yi”
Ya kai hannunsa ya taba aljihun wandonsa, yana da kudi amman ba damar ya bata tace ina ya samo ko kuma tace ba zata karba ba. Mikewa yai tsaye ya dawo bakin kofar dakinsa ya zauna yana kallonta, har ga Allah be jidadin yadda ya ga ranta ya bace ba, domin Anti Rabi ita ce a matsayin uwa a gareshi duk wani abu da uwa take yi ma da, Anti Rabi ce tai masa lokuta da dama zata hanawa yaranta abu ta bashi, babu abun da zai nema ta ki yi masa sai idan bata da hali
“Da kin aje wanki gobe na karasa miki”
Ta masa banza, sosai ranta ya bace ta san yadda AA yake da shegen son kudi, ba zai yi sata ba amman yadda ya lakewa yarinyar nan tana tsoro kar ya janyo musu abun da yafi karfinsu. Mikewa yai tsaye ya shige cikin dakinsa ya bude akwatinsa yana duba kayan da suka fi fitar da shi.
“Yarinyar nan ma da safe bata bar ni naje gidansu ba balle na kara samo wani abu”
Ya fada cikin jin haushi yana tuna kiran da tai masa dazu da safe ta sanar masa cewar ba zata je makaranta ba.
Ina mata matan kwalisa Matan da suka ansa sunansu na Mata? Ina wadanda ke cewa mun yi mun yi bamu ga amfaninshiba? Hmmm to ku zo ga Yar gidan Maifata ta zo maku da Al ajabu, dan tsugunno, gumba da tsimi da Zuma daban daban, maganin sanyi na maza da Mata. Ga kuma garurruka irinsu mallakau sabuzu kuwa, sa bahaushe saibi, Dan hubbare kafi malam aiki, ke kadai ke da miji, dahuwar kaza, tattabara, ciccibi da dai sauransu. Ba anan kayanmu suka tsaya ba, muna hadin amare na musamman turaren sutura turaren tsugunno turaren wanka da na daki da na jiki duka 4amare nasu na musamman ne, amma ga tsuhuwar da ke son komawa yarinya itama zata iya zuwa ahadata kai abundai sai wanda ya gani, dan haka karkubari abaku labari, domin neman karin bayani zaku iua nemana ta wannan number 09029891757 ko 08169311410, muna aikawa ko'ina a fadin kasar nan har waje kasar nan muna aika kaya.
Address: Nasarawa Samaru Area gurin masallacin mai sola Gusau Zamfara state Nigeria.
29
*Littafin nan na kudi ne biya ki karanta cikin aminci. Pay 300 to 0314795884 Abubakar Hadiza Gt bank, then send the evidence to 08036126660*
FADIME POV.
Zainab ta daga kai da sauri, domin ba karamin tsorata tai da tsawar da Wasim ya daka mata ba.
“Okay”
Ya matsa kusa da Fadime.
“Za ki jira ni nan zan je na dauko muku tufafin da za ku saka da abun hawa saboda akwai nisa daga nan zuwa can”
“Ba zaka dade ba?”
Ya daga mata kai alamar Eh.
“Ku sauko ta nan kasa”
Ba musu ta bi bayansa, Zainab kuma ta bi bayan Fadime suka sauka ta dayan gefen dutsen Inda babu wanda zai gansu. Sai da suka sauko sannan ya kalli Zainab ya ce.
“Ki boye camera ki da wayarki, karki yarda a san kina daukar hoto”
“Okay”
Ta amsa masa tana sauke jakar da camera take ciki.
“Amman idan aka gane za a mana wani abu ko?”
Fadime ta tambaya tana jin tsoron a ranta. Sai ya rage tsawo ya dawo daidai ita.
“Ba zan bari a taba ki ba”
“To ai kai ma za a iya maka wani abu saboda ka saba musu doka”
“Wa zai tana dan sarki? Sai dai Sarkin da kansa, amman bayan shi babu wanda ya isa ya taba Wasim a duniyar nan, idan kuma ina nan babu wanda ya isa ya taba ki”
Ba baki kadai Fadime ta bude ba har da ido da kunne da hanci, bata taba jin Wasim ya burge ta irin yau, tsabar mamaki har da hannu ta kai ta taba kirjinsa.
“Ashe kai dan sarki ne... Laaaaa.. Laaaa. Laaaaa”
Tana ta maimaita tana kallonsa, wani irin burge ta yai zuciyarta na raya mata shikenan ita kam kakarta ta yanke saka tun da Wasim Sarki ne ita kuma matarsa.
“Shikenan ma”
Ta furta sai kuma tai shiru bata karasa ba, Zainab dai sai kallon Wasim take, yadda yake kallon Fadime kadai da irin tattausan murmushin da yake mata kadai ya isa ya sanar mata cewar son Fadime yake.
“Zan dawo yanzu”
Be jira cewarta ba ya nufi wata karamar hanya, ya fara tafiya da sauri-sauri tun suna hangoshi har suka daina. Fadime ta zauna a gurin tana ta tunanin tafiya, tabbas tana son ganin garinsu Wasim amman tsoron da take ji yana kokarin hanata sukuni, ga shi yamma sai kara yi take. Zainab kam aikin gyara camera take ta yadda haske ba zai fita ba balle a gane tana dauka hoto, sai da ta gama da camera sannan ta dauko wayarta number Auwal tai dialing sai ta ji ta a kashe, sosai gabanta ya fadi, sai ta ji wani abu marar dadi yana ziyartarta. A hankali ta sauke ajiyar zzuciya, ta kashe wayar tana kallon sararin samaniya. Be yi 20 minutes ba suka hango shi tafe da