Showing 228001 words to 231000 words out of 286946 words
motar ya fice daga gidan yana tukin kamar wanda baya son tafiyar.
Tsakanin gidansa da masarautar tafiya ce mai dan nisa amman sai dai a yau sai ya ji tafiyar ta masa sauri sosai, a maimakon yai fakin a inda ya saba sai yai fakin daga bakin gate din kamar wani bako ya fito yana tafiya gumi na keto masa kamar wanda yai sata, sai a yanzu yake jin cewar ya aikata wa Hajiya Babba laifi, sai dai ya san ida ya fada mata ba zata amince ba, a ganinsa shi mijin mace hudu ne zai iya auren Nana da wata ma.
Kamar wani marar gaskiya haka ya shigo cikin katon falon na Hajiya, idanuwansa duk sun wani fito kamar wanda aka ciro daga rame, ganin babu kowa falon yasa ya nufi dakin Hajiya Babba, yana turawa sai ya samu Karima da Kausar a zaune saman kujera sun kurawa Hajiya Babba ido. Ita kuma tana zaune saman gadonta har lokacin tana yafe da mayafinta da jakar da ta fita da ita duk suna hannunta har talkamin ba ta cire ba, Wardrobe dinta kawai take kallo, ko kyabta idon ma sai an dade take yi. Sirleem ya karasa kusa da ita ya duka a kasa, Kausar da Rima kan kallon mamaki kawai suke masa, Rima ba dan ta ji da kunnenta ba kuma ta gani da idonta ba da ba zata yarda ba ko waye zai fada mata haka karyatawa za ta yi.
“Hajiya....”
Sirleem ya kirata sai ta juyo a hankali ta kalleshi. Shi kuma ya sunkuyar da kai ya rasa abun da zai fada mata.
“Yaya ba a yanzu ya kamata ace ka gane ka aikata kuskure ba, tun kamin ka aikata ya kamata ace ka gane kuskure ne kake kokarin aikatawa, fisabilillahi me zaka yi da yarinya kamar wacan? Kuma ka san Hajiya ta zaba maka Nana a matsayin matar aure? Ko da baka son Nana be kamata kai aure a boye ba, mahaifiyarka tana raye mu ma kanenka muma nan danginka kowa yana nan...”
Karima ta fada cike da jin zafin abun da dan'uwanta ya aikata. Sirleem dai be ce komai ba kuma be dago kansa ba, gaba daya ya rasa abun da zai yi. Murmushi Hajiya Babba tai irin murmushin da kana ganinsa ka san ba na farinciki ba ne, wasa wasa ya kwashe kusan 3 hours a dakin, tun yana jin nauyi da kunyar yi mata magana har ya kai yana rokon tai magana.
“Hajiya ki ce wani abu mana, ki furta wani abun, na san ban yi daidai ba ki fada min ki ce Sirleem baka kyau ba”
Ya fada idonsa cike da hawaye domin har ga Allah ya san ya saka mahaifiyarsa a damuwa. Haka ya gaji da rokomta ya gaji da magiya ya mike tsaye ya fice tana ta innalillahi.
Cikin motarsa ya koma ya zauna ya dafe kansa ya rasa abun da zai yi, ya rasa inda zai saka ransa ya ji, ya rasa abun da zai yi ya samu sassauci. Kunna motar yai ya juya kanta ya fice daga gidan gaba daya.
Sai da ya fita sannan Hajiya Babba ta tashi ta fito daga dakinta ta zauna a falo, ta maida hankalinta gurin tv tana kallo, ba dan babu plasma a dakinta ba, sai dan jin da tai dakin ma ta fita daga kanta gaba daya, gashi ta kasa cire talkaminta ta kasa aje jakar balle kuma mayafi komai da ta fita da shi yana nan jikinta.
Plasma take kallo sai dai ina damuwar da take ciki ta hana ta gane mutane ne a tv ko aljanu ko kuma cartoon? Kallo kawai take saboda ta gusar da abun da ya tsaya mata a zuciya, amman ta kasa abun ya shiga zuciyarta sosai ya danne mata komai ciki har da kalamai da take jin kamar ta kai wa'adinsu.
“Hajiya ga ruwa”
Kausar ta mika mata ruwa a kofi cike da damuwa. Hannu Hajiya ya mika ta karbi ruwan ta kai bakinta kwarara ruwan tai cikin bakinta da zimmar sha sai ta gagara hadewa tana zubawa a bakin suna dawo mata suna jika tufafinta.
“Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un Anty Karima zo..”
Kausar ta fada tana fashewa da kuka. Sai Hajiya ta kalleta irin duban nan na me ya faru? Is like kamar bata san ta yi ba. Karima ta karaso gurin da sauri tana kallon Hajiya.
“Me ya faru?”
“Ruwa na bata ta sha yadda ta sha haka yake dawowa a jikinta”
Kausar ta fada cikin kuka da tashin hankali.
“Innalillahi Hajiya”
Hajiya ta kalli Karima amman ta kasa amsawa.
“Taso mu je daki”
Karima ta rika hannunta sai Hajiya Babba ta mike tsaye kamar wata yar yarinya ta bi Karima zuwa dakinta, Karima ta zaunar da ita saman gadonta ta cire mata takalmin yayinda Kausar ta karbi jakarta ta da mayafinta ta aje a muhallinsu.
“Hajiya ki kwanta”
Da sauri Hajiya ta kwanta kamar mai jiran umarni. Karima ya fito cikin tashin hankali ta nufi dakinta ta dauko wayarta ta kira yar'uwarta Jurry ta fada mata abun da ya faru, cikin mintunan da ba su fi talatin ba Jurry ta iso gidan sai wani huci take tama fusata tana karawa.
“Haba ai dole Hajiya ki shiga wannan yanayin, yanzu fisabillahi Ya Sirleem da kansa zai dauki wuka ya daba miki? Da kansa zai jefe ki a wannan halin”
Jurry ta fada tana zaune kusa da Hajiya, Kausar kam sai rusar kuka take, Karima ce mai gaya ta ita ma tana hawaye.
“Wallahi Ya Sirleem be kyauta ba, yanzu ai ya ji dadi mahaifiyarsa tana cikin damuwa, ban san abun da suka gani a jikin yarinyar ba, kuma ko zai aureta ai ya kamata ya fadawa Hajiya ni na san ba zata hana shi ba”
Jurry ta juya ta kalli mahaifiyarta.
“Hajiya ta shi ki ji”
Hajiya ta tashi zaune kamar mai jiran umarni. Hakan da tai ba karamin mamaki ya ba yayanta ba.
“Hajiya karki sa wannan abun a ranki, ki kyale shi ki cire shi daga jerin yayanki, ki manta da rayuwarsa, ki na da mu kuma mun isheki da yardar Allah, na san dole za ki shiga damuwa ace danka ne zai maka haka”
Jurry ta fada hawaye na cika idonta, Hajiya ta kalleta har lokacin bata iya cewa komai bakin ya mata nauyi a gurin kalami, ko numfashi da ace ta baki take yinsa da bata samu damar fitar da shi ba.
FALMATA POV.
Karasawa tai gaban hoton ta kai hannu ta ta shafa fuskar matar da ke jikin hoton idanuwanta na cika da kwalla, sai kuma ta juyo tama karewa dakin kallo, can kuma ta sake maida dubanta gurin hoton hawaye na sauko mata, miya kawo hoton mahaifiyarta a nan? Ta tambayi kanta tambayar da bata da amsar ta, mikewa tai tsaye wanda hakan yai daidai da shigowar Momy a dakin cike da tunani kala, domin ta kasa natsuwa tana son ta ji abun da yake faruwa, hakan yasa ta zabi tambayar Falmata, domin zuciyarta na raya mata ba a daura auren ba Sirleem. Maida kofar dakin tai ta rufe da makulli. Falmata ta juyo tana kallonta hawaye na mata zuba.
“Wai me ya faru ne? Su waye za su zo da Sirleem yace idan sun zo kar na bada ke?”
Falmata ta nuna hoton mahaifiyarta tana hawaye.
“Waye kawo hoton nan a nan?”
Momy ta dan leka bayan Falmata ta hango hoton.
“Me ya faru?”
“Mahaifiyata ce”
“Ma ma..ma...Mahaifiyarki?”
“Mahaifiyarki?”
Momy ta sake maimaitawa.
“Duba hoton dai da kyau ki gani”
“Mama ta ce Momy, babu inda zan ga mahaifiyata ban gane ta ba, ni ma ina da irin hoto”
“Anya dai? Mahaifiyarki Falmata ko dai kamanni? Wannan ai Safiyya ce”
Falmata ta daga kai tana hawaye.
“Eh ita ce... Mamata ce”
Momy ta sake kallon Falmata da duba na mamaki da al'ajab.
“Wannan fa mahaifiyar Ameer ce... Dan mijina, wannna matar mijina ce ta biyu wanda ya aura tun da dadewa su ka rabu....”
Falmata ta lumshe ido hawaye na sauko mata. Momy ta karaso kusa da ita ta da fa kafadunta tana girgiza ta.
“Ta ya zan yarda da ke? Ta ya zan yarda mahaifiyarki ce?”
“Sunan da kika fadi sunanta ne, kuma ina da irin wacan hoton, mahaifiyata ta ce ta ba ni, ta ce tun tana budurwa ta dauki hoton, a lokacin da samari su ke bawa yan mata kudi su ce su je su yi hoto, ta fada min hoton guda gudu ne wanda ya saka ta dauki hoton mijinta ne na farko ya rike biyu ya bata biyu, kuma tabbas mahaifiyata ta auri wani namijin kamin ta auri Babana, har ta haifi yara biyu da shi mace da namiji macen Maryam da sai namijin Usman wanda ya bata, Maryam din kuma ta rasu...”
Falmata ta fada idonta a rufe cikin kuka mai karfi, lokaci daya Momy ta dauke hannayenta daga jikin Falmata tai baya baya tana kallonta kamar wanda tai arba da wani abun tsoro, tabbas abubuwan da Falmata ta fada haka ne, domin mijinta ya fada mata ya haifi yara biyu da ita dayar ta rasu kuma sunanta Maryam kuma ya fadawa Ameer yadda aka dauki hoton a lokacin da Ameer yake tambayarsa wacece ta jikin hoton da mahaifinsa ya ba Momy yace ta aje masa, sanadin hakan yai kai aka kara gyara masa hoton aka maida shi babba ya saka a dakinsa.
“Hakan na nufin ke da Ameer ....”
Momy ta kasa karasawa sai nuna Falmata take, jin hakan ya sa Falmata ta bude idonta da su kai ja saboda kuka ta kalli Momy.
“Wane Ameer din?”
“Dan...dan...mijina... Allah sarki Ameer... Ashe baka da rabon ganin mahaifiyarka a fili?”
Falmata ta dafa zuciyarta tana tuna waye Ameer din, the first thing da ya fara zuwa mata after tuna shi shi ne lokacin da zai je makaranta ita kuma Sirleem ya shigo da ita cikin gidan, irin maganar da yai mata da kuma yadda ya labarta mata batan mahaifiyarsa da fatan ganinta da yake. Sauri daga kai tai tana kallon katon hotonsa da ke manne a bango ta saka dayan hannu ta rufe bakinta da sauri hawaye na sauko mata. Momy ma hawayen take sai ta juya dafe da zuciyarta ta fice daga dakin, Falmata kan kurawa hotonsa ido tai sosai yayi murmushi yana sanye da suit red, sai a yanzu take ganin kamanin mahaifiyarta a fuskarsa da bakin fatarsa wanda ita ma shi ya haska fatarta.
Tana tsaye a dakin Sirleem ya shigo, yadda yake tafiya kadai da yanayin fuskarsa ya isa ya sanar maka cewar a yau kam ya amsa sunansa na maraya. Karaso yai kusa da Falmata ya saka hannayensa ya jata jikinsa ya rumgume, sai ta fashe da wani irin kuka mai ban tausayi jikinta na karkarwa, abubuwa biyu sun zo mata a lokaci daya, shi ma lumshe ido yai yana maida numfashi a hankali sai hawaye masu zafi suka sauko masa.
IYA POV.
Ganin tai kamar be kamata ta aikatawar da wannan aikin a yanzu ba, bata da tabbacin burinta zai cika ko aa, idan har Shattima be auri Zainab ba ko da ya zama sarki aikin banza ne a gurinta domin ba zata mori komai ba gashi yanzu ma ta bar gidan.
Daukar zare tai ta nade kurwar ta dukawa ta maida kurwar cikin kwaryar ta sannan ta maida kwaryar karkashin gado, ta gyara komai yadda yake, kana ta dauki kuwarwar Maijidda ta fito da ita daga dakin, kicin ta shiga ta dauko wata robar ta saka ta tabarar a ciki ta fara fige gashin jikin tantabarar da hanunta, bayan ta gama ta kunna risho domin ta fi gane yin girki da shi sama da gas.
Sai da ta yanka naman tantabarar sannan ta zuba shi a tukunya ta zuba mai kadan ta dora tukunyar a risho, bayan yayi zafi ta soma soyawa, sai da ta soye abun ta rumus yadda take son naman sannan ta kwashe ta sauke tukunyar ta kashe rishon ta dauko namanta ta zuba a wata kula ta rufe ta dawo dakinta ta boyeshi a karkashin gado. Sannan ta koma kicin din ta juye man da tai soyar da shi a wani karamin roba ta gyara kicin din ta wanke komai kamar bata taba ba. Kwankwasar kofar falon da ta ji ana yi ne yasa tai saurin fitowa daga kicin din ta je dakinta ta boye man sannan ta fito ta bude kofar, ganin Zainab ba karamin mamaki tai ba.
“Kin dawo kuma?”
Zainab bata ce mata komai ba ta raba gefenta ta wuce cikin falon, Iya ta rufe kofar ta juyo tana fadin.
“Ya akai wai miyasa ya aka rike ki?”
Sai da Zainab ta isa bakin kofar dakinta sannan ta juyo ta kalli Iya a jigace.
“Saboda ke ne, duk abun da ya faru da halin da na ke ciki saboda ke ne Iya, saboda zargin da Shattima yake yi akan mu ya rufe mu a dakin horo, dakin da ko dabba ba zata iya zama a ciki ba, haka na kwana cikin sauro babu abun shimfida balle na rufi, ban taba tunanin zan wulakanta kamar haka ba, ban taba tunani wata rana zata zo da rayuwa zata zame min haka ba, a yau na yi nadamar haihuwata da kika yi, ba ni da dangi, ba ni da kowa ba uba, ga uwa ta zame min wata kala, da wanne zan ji?”
“Ce masa akai ke kika dauki yarinyar nan?”
Zainab ta share hawayenta ba tare da tace komai ba ta wuce dakinta wasu hawayen na sauko mata. Ko kadan Iya bata jidadin abun da Shattima yai ma yarsa ta, cikin bacin rai da tunanin irin abun da za ta yi masa ta shiga nata dakin ta zauna bakin gado tana mamakin yadda Shattima da kansa zai taba mata ya, duk abun da take yi bata taba tunanin taba shi ba, bata taba tunanin yi masa komai ba sai dai taba matansa ko yaya saboda tana masa fatan samun Zainab amman a yanzu ta kaita karshe shi da Ammy, domin a yadda ta fahimta abu ne mai wahala wata mu'alama mai karfi ma ta sake shiga tsakanin Zainab da Shattima, ita kuma a yanzu zama a masarauta yayi mata wahala, ba m masarautar ba har mutanen cikinta a yanzu dole wadanda suka san sirrinta su yi mesa da ita, hakan na nufi ita da Zainab din ba su da makoma. Sauko tai kasa ta zauna ta janyo kular namanta ta bude ta fara ci.
“Shegiyar kurwa ko mai babu”
Ta fada tana cin nama cike da jin haushi, bata tashi ba sai da tai ma naman kat ta cinye komai..
HAJIYA TALATU POV.
Maijidda ta shari bachi iya bachi bata barka ba sai kusan asuba, kamin ayi sallah ta shiga bandakin dake asibitin tai fitsari tai alwala ta fito ta zauna bakin gadonta. Hajiya Talatu sai murmushi take mata tana jindadin lafiyar da ta samu duk kuwa da kasancewar bata da wani sukuni sosai.
“Ya jikin na ki?”
“Alhamdullah na ji sauki”
“Allah kara lafiya, ni ai da farko na tsorata sosai Wallahi, ko da muka kawo ki asbitin nan ba ki san inda kan ki yake ba”
Ta dan yi murmushi tana kallon yatsun hannunta. Hajiya Talatu da kanta ta tashi ta hada mata tea da kayan tea da aka kawo mata tun da dare, ka dan ta sha ta zauna jiran sallati, ana yin kira ta karbi hijabin Hajiya Talatu ta saka ta gabatar da sallah azuba, bayan ta gama ta mikawa Hajiya Talatu sai ita ma ta gabatar da tata sallah. Misalin takwas aka kawo musu abun karyawa, a nan Hajiya ce tai hidimar zuba mata ta bata a plate sai tea a wani karamin kofi ta mika mata. Gaba daya sai ta Maijidda ta ji komai ya fita a ranta dan kwan kawai ta ci ta sha ruwan shayi kadan ta aje.
“Lafiya? Ko wani abun kike so a girka miki”
Hajiya Talatu ta tambaya
“Aa bana jin cin abinci ne, jikina ina jinsa kamar ba nawa ba”
“Ciwo kike ji?”
“Bana jin ciwo komai kawai dai ina ta jin wani yanayi na dabam”
Hajiya Talatu ta aje kofin shayin da ke hannunta.
“Kamar ya?”
“Ban san ya zan misalta ba, ina ta jin kewarku Momy, ina ta jin kamar zan tafi na barku”
Ta fada idonta na cika da hawaye har wani ya fara sauko mata, bata taba jin irin yanayin da take ji a yanzu ba bata taba jin kewar kowa kamar yanzu ba, gashi ta rasa yadda zata misalta yanayin da shi ba na ciwo ba ba kuma na lafiya ba, ba na dadi ba ba kuma na bakinciki ba.
“Kin gani Jidda bana son maganganun nan na banza, daga ciwo sai ki fara wani zancen mutuwa wane irin magana ne wannan dan Allah?”
“Wallahi Momy ina jin wani yanayi na dabam, ni dai dan Allah ki yafe min ko da na mutu”
“Ba ma za ki mutu ba, sai kin yi aure kin haifi yayanki na gani da yardar Allah, Allah dai ya baki lafiya ya yaye miki ko minenen”
“Ameen”
Ta amsa tana kwantawa saman gadon sai kallon dakin take, ta yi shiru kamar ba ita ba, motsin ac da hayaniyar mutane da take ji a waje sai ya zo mata a wani yanayi na dabam, can kuma ta juyo ta kurawa Hajiya Talatu ido tana ta kallonta irin kallon na bankwana, irin kallon nan da kake ji kamar kar ka tafi ta bar komai na ka. Hajiya Talatu kam hankali ya tafi gurin wayar da take sai dariya take.
Misalin 9am da yan mintuna Hajiya Talatu ta fita waje saboda masu gyara dakin da suka shigo su yi mopping, kamar fitar Hajiya Talatu ake jira sai wani bachi mai dadi ya fara kewayar Maijidda tun tana hamma har ta fara jin jikinta ya zama very weak ko hannunta ta gagara dagawa, nan da nan bachi yai gaba da ita bachin da babu farkawa, bachinta na karshe a idan duniya, bachin daga shi zata farka ta ji a dakinta na gaskiya.
Mai shara ta yi tai gama tai mopping ta fita ta rufe dakin, Hajiya Talatu bata dawo dakin ba sai da Haroon ya shigo tare kanwarsa.
“Bachi take”
Hajiya Talatu ta fada ganin tana jan numfashi tana maidawa a hankali, har zata tashe ta sai Haroon ya hana ta.
“Ki kyaleta kawai idan na shigo anjima sai na dubata”
“Tau ba matsala”
Sama sama su kai fira da Hajiya sannan ya fice ya bar kanwarsa Hajiya na Fadin.
“Allah yasa da sun zo su