Showing 252001 words to 255000 words out of 286946 words
ta ya zata iya rayuwa garin da bata san kowa a can ba, kuma bata saba ba, gashi ba su yarda da komai na zamani ba balle cigaba? How? Ji tai ita kan ba zata iya bin Wasim ba hakan yasa ta juya da sauri ta fice daga dakin zuwa dakin Iya da zimmar yi masa magana sai ta tararda dakin babu kowa a ciki sai ko matsan kayan Iya. Juyowa tai ta fito ta koma dakinta ya shiga bathroom ta hada ma kanta ruwan wanka ta watsa a jikinta ta fito kamar wata marar lafiya, wardrobe dinta ta nufa ta dauko wani yadi marar nauyi ta saka bata shafa komai a jikinta ko turaren da take so a yau sai ta ji bata bukatarsa abubuwa da yawa sun taru sun mata tsaye a rai, idan ta fara tunaninsu sai ta ji kamar ta kashe kanta ta huta. Tana cikin dakin ta ji sallamar Mai gadinta, ba karamin faduwa gabanta yai ba, domin a yanzu tsoron komai take ciki har da sautin mutane. Haka nan dai ta unkura ta tashi ta fita cikin rashin kuzari, sai ta same shi tsaye jikin kofa yana matsar kwalla.
“Hajiya yanzu aka kirani daga kauye wai Mahaifiyata ta rasu”
Ya fada mata karyar da ya ke ta tsarawa tun dazun, bayan mahaifiyarsa ta dade da rasuwa, kawai ya zabi yai haka ne domin ya tsorota da jin cewar mayu ne kuma ya zai iya tafiya ya bar hakkinsa ba. Zainab ta yi murmushin bakinciki domin ta san karya yake yayi hakan ne kawai saboda ya tsiratar da rayuwarsa.
“Ina zuwa”
Ta fada sannan ta juya ta koma ciki, albashinsa na watan gaba daya ta dauko ta ba mika masa.
“Kana da gaskiya, dole ne zaka tsorata kuma ban ga laifinka ba na gode”
Ta fada masa haka a yayinda yake karbar kudin, shi kam godiya kawai yai ya fice daga falon, sai ta juya ta koma ciki ta dauko babbar jakarta ta dauki wasu tufafin ta zuba a ciki da kuma wadansu abubuwan da zata iya bukata, sannan ta dauko wata karamar jakar ta zuba tarkacenta ta fito rike da makullin gidan a hannunta, sauran tufafinsa duk a ciki ta bar su sai da ita gurin motarta ta saka jakar sannan ta dawonta rufe ko'ina na gidan, sai kuma tai baya baya tana kallon gidan hawaye na sauko mata.
“Allah duk yadda ka tsara a gareni haka zai kasance, Allah ka min mafita ka yaye min damuwata ka shiga cikin lamarina”
Ta saka hannunta ta share hwayenta sannan ta juya ta nufi gate ta bude ma kanta ta dawonta shiga motarta ta fita da ita sannan ta sake dawowa ta rufe gate din ta saka masa key, har ta juya sai kuma ta juyo ta kai hannu ta taba gate din, sannan ta koma cikin motarta ta ja motar bata tsaya ko'ina ba sai gidansu kawarta Amina, duk da wani shiri suke irin sosai ba but ta san Amina mace ce mai amana kuma mai sanin ya kamata. Amina ta yi mamakin ganinta a irin wannan lokacin da ake ta kira kiren sallah magariba. Bayan sun gaisa Zainab ta kama hannunta ta danka mata keys din motarta da na gidanta, Amina ta kalli keys din da mamaki sannan ta kalleta.
“Na meye?”
“Na motata ne da na gidana, na yarda ke shiyasa na baki ajiyar wannan, kuma dan Allah a rika kula min da gidana”
“Miya faru?”
“Ba komai kawai zan bar garin nan ne, na wani lokaci ke kadai na yarda da ke a duk kawayena”
Amina ta mike tsaye tana kallon yadda hawaye ke saukowa a idon Zainab.
“Dan Allah ki fada min idan wata matsala ce”
“Zan kira ki a waya anjima, na baki mana, idan kuma kika ga na dauki lokaci ban dawo ba ki siyar da komai ki min sadaka”
“Wannan wace irin magana ce Lafiya kike Zainab?”
“Lafiya kalau na ke Amina”
Ta fashe da kuka, tare da saurin mikewa tsaye domin bata son mijinta ya dawo ya tararda ita a gidan.
“Amman zan fada wa Mai gidana, idan be aminta ba zan hannata fada miki a waya sai ki fadi wanda a hannatawa abun”
“Ba matsala na gode”
“Allah yai miki mafita ya yaye miki ko miye a ranki”
“Amin sai wata rana”
Zainab ta fada cikin kuka sannan ta juya ta fice da sauri, daman ta cire akwatinta a wajen motar sai ta karasa ta ja shi zuwa gate Amina ta fito ta tsaya bakin kofar falonta tana kallon Zainab hawaye na sauko mata. A Hotel Zainab ta kwana tun a dare ta siye ticket din zuwa Katsina, washe gari ta shirya ta nufi airport cikin shiga ta doguwar rigar atamfa da mask sai dan karamin mayafi da kwatinta sai yar karamar jakar hannunta.
Karfe goma daidai jirginsu ya daga zuwa Katsina, sai a lokacin ne ta ji wani irin kewa da tausayin kanta ya kara kamata.
<<<<<<<<
Da 9pm zan turo wani Inshallah, jiya ban samu na yi ba saboda ba nepa.
_________
Ina mata matan kwalisa Matan da suka ansa sunansu na Mata? Ina wadanda ke cewa mun yi mun yi bamu ga amfaninshiba? Hmmm to ku zo ga Yar gidan Maifata ta zo maku da Al ajabu, dan tsugunno, gumba da tsimi da Zuma daban daban, maganin sanyi na maza da Mata. Ga kuma garurruka irinsu mallakau sabuzu kuwa, sa bahaushe saibi, Dan hubbare kafi malam aiki, ke kadai ke da miji, dahuwar kaza, tattabara, ciccibi da dai sauransu. Ba anan kayanmu suka tsaya ba, muna hadin amare na musamman turaren sutura turaren tsugunno turaren wanka da na daki da na jiki duka 4amare nasu na musamman ne, amma ga tsuhuwar da ke son komawa yarinya itama zata iya zuwa ahadata kai abundai sai wanda ya gani, dan haka karkubari abaku labari, domin neman karin bayani zaku iua nemana ta wannan number 09029891757 ko 08169311410, muna aikawa ko'ina a fadin kasar nan har waje kasar nan muna aika kaya.
Address: Nasarawa Samaru Area gurin masallacin mai sola Gusau Zamfara state Nigeria.
61
*Khadeeja Candy*
*Littafin nan na kudi ne biya ki karanta cikin aminci. Pay 300 to 2451879008 Hadiza Abubakar Zenith bank, then send the evidence via 08036126660*
Kamar wacan lafiyar da su kai da Fadime, haka ta sauka garin Katsina kai tsaye ta nufi tashar ta samu motar da zata kaita garin bayan ta yi jinga da direban, shi kuma ya fada mata ya san garin amman zai kaita bakin kofar garin ne kawai ya dawo, tace masa ta aminta. Sai ta shiga motar ita kadai, suka dauka zuwa garin. Tana cikin motar shiru sai kallon hanya take, a duk lokacin da tai yunkurin kuka sai ta kasa, sai dai abun ya shiga zuciyarta ya zauna sosai ta yadda ko numfashi tai da karfi sai ta ji kirjinta yayi ciwo.
Kamar yadda ya fada nesa da kofar garin ya sauke ta daman tun a tasha ta biya shi kudinshi sai ta bude motar ta fita ta fara takawa da kafa tana tuna zuwansu na baya da Fadime, a lokacin da ta zo a boye kuma cikin rashin sani, tsabanin yanzu da ita kanta ta kawo kanta domin ta san zata gina rayuwarta a nan ne, garin da babu network babu tv babu mota balle wani abu na cigaban zamani. Tun kan ta karasa bakin kofar garin ta hango Wasim tsaye yana jiran isowarta hakan na nufin ya san da zuwanta kenan ko kuma an sanar masa. Sai da ta kai daf da shi sannan ta tsaya ita da shi suna facing din juna, ta kasa ce masa komai shi ma haka sai karantar damuwarta yake zuciyarsa na cika da tausayinta. Can kuma sai ya sakar mata murmushi ya kai hannu ya karbi akwatinta ta juya ya fara tafiya sai ta daga kai tana kallon kofar garin kamin ta juya ta kalli hanyar da ta biyo tana tunawa da Yola. Sai kuma ta juyo ta ni bayan Wasim har suka isa gurin da farin dokinsa yake ya taimaka mata ta hau ya dora akwatinta a sama, shi kuma ya rike linzamin dokin a hannu dayan hannunsa yana tafiya a kasa, kallon garin take da mutanen cikinsa kamar yadda su ma suke kallonta ganin tufafin jikinta dabam kuma ta hau dokin Wasim da kansa yana jan dokin. Tafiya su kai mai dan nisa sannan suka isa masarautar su Wasim, a nan ma shi ya taimaka mata ta sauko sannan yai gaba ta bi bayansa tana tafe tana kallon mutanen dake cikin masarautar da su ma kallonta suke suna saurin kawar da ido saboda Wasim. Banbanci wacan tafiyar da wannan wacan ta yi ta ne a cikin tsoro da zullum tsabanin wannan da bata jin komai ko da ace tana zuwa kasheta za su yi ta riga ta goge komai a zuciyarta. Wata matar ce mai kama da hadiman masarautar tai saurin zuwa ta karbi jakar da Wasim yake roko ta Zainab, shi kuma ya nufi cikin masarautar sai ta biyo bayansa suka shiga har ciki. Abun da ba ta yi zato ba ta samu daga sarki wato tarba da murmushi ya kuma ware mata hannayensa alamar ta karaso gareshi. Sai ta tsaya can bakin kofar fadar idonta ya cika da hawaye.
“Karaso gareni Yata...”
Sarkin ya fada da murmushi a fuskarsa, daman can babu wanda ya kai yan garin Garuk son yan'uwansu balle kuma Sarkin da ya san cewar Zainab jininsu ce, hannu ta saka a share hawayenta sannan ta karasa inda yake ta rumgume shi kamar yadda ya bukata sai duk sauran yan fadar suka duka kasa suna kai mata gaisuwa, ko da ba mutanen kwarai ba ne at least ita dai tana da yan'uwa da za su iya karbarta a lokacin da duniya ta tsane ta.
“Na gode”
Ta fadawa Wasim tana kallonsa, sai ya sakar mata murmushi da bukarsa da tunanin rabuwa da Fadime yasa ta zurma ta haifar masa da rama sosai. Shugaba da kansa ya nuna mata inda zata zauna a kujerar dake kusa da ta shi, sannan ya gabatar musu da ita cikin farinciki duk da bata jin abun da yake fada sai dai tana kallon fuskarsa ta san farinciki yake. Bayan sarkin ya gama Wasim ya shiga yi masa magana da yarensu.
“Sai dai ita tana kan addini ne na dabam tsabanin wanda mu kai ba, ina fatar ba za a hanata ibadar ta ba”
“In har zata zabi dawowa gida cikin yan'uwa da dangin mahaifiyarta me zai hana ta watsar da komai ta rike na mu”
Wasim ya kalleta.
“Kina da ra'ayin barin addininki ne Zainab?”
“Har a bada, ba zan taba barin musulunci ba, ko da kuwa hakan na nufin mutuwa ta ne”
Ya juya ya kalli Sarki yana mayar masa da amsa da yarensu sannan ya dora da.
“Be kamata a hana kowa yin abun da yake so ba, musamman mutane irina irinta wandanda su ka bar kasar nan su ka bar garin nan su ka shiga duniya su ga cigaban da duniya ta samu, an cigaba an wuce wannan babin”
“Ba ma ra'ayin addininta”
“Idan har ba ku ra'ayin addininta hakan na nufi ba ku ra'ayinta, ni kuma zan iya daukarta mu bar garin nan, ba zai yiyu a kara mana wani bakinciki ba ni da ita”
Ya fada da yarensu sannan ya kalli Zainab.
“Ta so muje”
Zainab ta mike tsaye ta bi bayan Wasim. Sai ya shiga da ita can cikin masarautar a inda mata da yaya suke da kuma dakuna gwanin sha'awa, daki daya ya ware mata a matsayin nata sannan ya kawo mata uku wadanda zasu rika yi mata hidima. Wannan furucin da Wasim yai ya saka ba su hana Zainab yin sallah ko saka kalar tufafin da take so ba, hakan kuma da take sai ya burge mutanen garin musamman ganin tufafinta na zamani ne gashi idan ta saka za su rufe mata jiki har kasa, sai dai su matse ta kasancewar duk tufafinta haka suke mata. Idan ta fito waje tana sallah wani lokacin sai su yi taro suna kallonta, alwalar da take ma kallonta suke suna ganin ta yi wani abu na dabam da ba su saba gani ba, gashi bata jin yaren mutanen garin idan tana son magana da su sai ta sha wahala sosai, abinci ma bata iya cin komai sai yayan itutuwa saboda tana jin launin abinci gurin dadi da kala ba irin nata ba, ganin hakan yasa Wasim yake zuwa yana siyo mata abincin irin an yan birni, and haka zai zo ya zauna yana fira da ita duk da kasancewar shi kansa baya cikin sakewar zuciya sai dai a kokarinsa na ganin ya faranta mata rai sai ya samu kansa cikin faranta nasa ran, idan tana sallah kuma sai yai ta kallonta yana tunawa da Fadime. Yau ma kamar kullum yana zaune bakin kofar dakin yana kallon yadda take sallah a kusa da shi saboda zafin dakin yasa ta fito waje tana sallah. Bayan ta gama ta yi addu'a ya kalli kyakyawar fuskarta mai dauke da karamin baki da kuma fararen idanuwa ya ce.
“Wai ku ba ku gajiya da yin wannan abun kullum?”
Kallonsa tai.
“Ka taba ganin mutum ya gaji da ibadarsa? Wannan sallah da kake ganin duk musulmi kwarai ba ya yarda lokacinta ya fita be yi ta ba, hakan yasa ka ga ina kwatantan lokacin ta sai na yi, yin ta tana sakarwa mutun da natsuwa da kwanciyar hankali kuma yana kara kusantar da bawa ga ubangijinsa, sannan ibada ce da ake bawa mutun lada mai yawa a lokacin da yayi ta”
Yayi murmushi ba dan ya gane wani bangare na bayaninta ba. Shiru ne ya biyo baya kamin ta kalleshi ta ce.
“Tun da na zo garin nan ina kokari na koyawa kaina zama da mutanen cikinta da yin rayuwata irin na mutanen garin nan amman na kasa, ina ta kokari na cire Iya a raina amman na kasa, har so nai na yi ma kaina alkawarin ba zan taba tambayar inda take ba, ashe ba zan iya ba saboda soyayyar uwa ta fi gaban wasa, komai zata bata maka rai wata rana sai ka ji kana bukatarta a kusa da kai”
Wasim ya yi shiru yana kallonta sai hawaye take.
“Be zama lallai ki yi rayuwa tare da mu ba, zan tsaya miki ki samu irin rayuwar da kike so a lokacin da kike so, ko da kuwa kasar nan za ki bari gaba daya”
Kallonsa ta sake yi.
“Bana son wani ya sake aikata wani kuskuren saboda da ni, ka fada min ina Iya take?”
Mikewa yai tsaye yana kokarin kawar da maganarta ta biyu.
“Ba zan yarda na sake aikata wani kuskuren ba, dukan abun da zan aikata a yanzu Zabin Raina ne kuma ya zama dole ni ma a ba ni damar rayuwa kamar kowa”
Yana kawai nan ya fara tafiya ba tare da ya bata amsar tambayart ta biyu ba, binsa tai da kallo zuciyarta na hararo mata abun da take jin kamar ba ta shirya masa a yanzu ba.
FADIME POV.
Duk Yadda Shattima ya so ta sake ranta ta koma rayuwa kamar da, a duk lokacin da tunarabuwarta da Wasim maganar da yai mata cewar ba zai sake dawowa ba, idan ta tuna kalmar sai ta ji kamar zata mutu, gaba daya ko abincin kirki bata iya ci, har sai da Shattima ya kebe da ita a wani karamin falon Ammy ya saka gaba da rarrashi da komai sannan ta ci kadan, ko nama domin kazar da ya saka aka soya mata na musamman bata wani ci ba, a daren ranar ma sai da yai mata karatu kamar jiya, sannan tai bachi shi kuma ya tsareta da idonsa yana ta kallonta sai jin yake kamar ya dauke ta ya bude cikinsa ya saka a ciki ya rufe. Washe gari ta farka da wuri saboda tun a daren da zata kwanta Shattima yayi mata albishir da maganar zuwa gida Katsina. Ba laifi ta dan sake saboda tana marmarin ganin iyayenta, a dinning ma da aka kira a karya ta dan ci abinci da yawa, tana ta daukin cin abinci a dinning kasancewar jiya a dakin Nana aka kai mata komai a yau kuma sai Ammy ta aika aka kirata ta fito aka karya tare da Nana da Mama Fulani, daman Aliyu da Muhseen tun ranar da su kai gaisuwa suka juya a mota suka koma Abuja.
“Fulani a saka mata ido, Shattima ya ce bata cin abinci”
Ammy ta fada tana murmushi domin ya jadadda mata cewar ta kula da abinci Fadime baya son ta tafi gida da yunwa shi kuma ba zai samu shigowa gidan ba sai da suna kusan tafiya. A duk lokacin da Ammy ta kira Mama Fulani sai Fadime ta amsa tana ganin kamar da ita ake domin ita ma ta saba a gidan Inna da Bappa suna kiranta da Fulani. Shattima be kira Bappa ya fada masa halin da ake ciki na Fadime ba, shi ma kuma be kira wayarsa ya tambaye shi ba har yau. Ammy da kanta ta shigar da Fadime bangaren Mai Martaba suka gaisa, sannan yai mata goma ta arziki bayan ya tabbatar mata cewar tare da Baba Waziri zata je kuma idan zun tafi Katsina za su sauka a masarautar Katsina ne a hada tawagar da za su mata rakiya har gida, saboda ta jaddadawa Ammy abun da take tsoron Bappa yai mata wato duka ko ma ya koreta gaba daya, ita kuma Ammy tana ganin ko da ba zai mata komai ba ta cancanci karramawa mai girma daga gurinsu.
Cikin wani irin farinciki marar misaltuwa ta fito bangaren Mai Martaba, ba ta sha wahala gurin gane hanyar dawowa ba ta hanyar kwaliyar da aka kawata corridor da zai sada mutum da bangaren Mai Martaba da akai, ta cikin gidan matansa bayan wacan komar mai gate nata na musamman da baki suke zuwa ta can, ga kuma fadarsa a can gefe daya.
Ko da ta shigo falon sai ta samu Shattima shi kadai zaune rike da cup din ruwan sanyi, sabar murna da farinciki ya saka ta manta da ko shi waye da kuma inda take ta soma aro kadan daga halinta na baya tana yafawa.
“Yaro ya...”
Sai kuma tai saurin rufe baki tana kallonsa,