Showing 21001 words to 24000 words out of 286946 words

Chapter 8 - Fulani Book 1 Hausa Novel Complete

20 Dec 2024

894

tai ta fice tana kuka kamar gaske.

“Zainab ki daina biye Nana kuna kara lalata, duk abunda take da gangan take dadi ne yake mata yawa”

Ammy ta fada ba tare da ta kalleta ba, domin har cikin ranta bata jindadin yadda Hajiya Karama, Shattima da Hajiya Babba suke yi ma Nana. Hajiya Karama ta yi murmushi tana mikewa tsaye.

“Ai mun kusa bar miki gidanki Ammy, ina yin aure zan dauke Nana mu tare a can”

“Auren da babu rana”

Ammy ta fada tana tabe baki, sai Hajiya Karama tasa dariya.

“No very soon Ammy, domin na samu wanda na ke so”

Ammy ta kalleta.

“Da gaske?”

“Wallahi Ammy, yana da mata daya yara uku ban dai san real name dinsa ba amman dai ya min, ban fada masa ba but very soon zan sanar da shi ina son shi kuma zan aure shi da gaske”

Magana Zainab take kamar abunda take fada ba komai ba ne. Ammy ta kalleta irin kallon nan na mamaki da tunani.

“Ke za ki ce kina son shi? Ban gane ba”

“Yeah normal ne ai Ammy”

Tana fadar hakan ta nufi hanyar sauka downstairs dake dinning, bata son tsayawa kar Ammy ta fara karanta mata wasu haruffan da ba zata iya hadasu ta tada ba.

Tana saukowa, ta nufi dayan stairs din da zai sadata da bangarenta ita da mahaifiyarta, kamar ta wuce dakinta sai kuma ta nufi dakin mahaifiyar ta ta. Zaune ta same ta hannunta rike da wuri, sai dai ganin Zainab din yasa tai yi saurin boye wurin a bayanta ta kalli yarta ta manya idanuwanta da suka rine su kai ja kamar barkono.

“Na fada miki ki daina shigo min daki babu sallama”

“Na manta ne”

Ta fadi hakan bayan ta zauna kusa da ita, sannan ta bude wayarta ta shiga gallery ta kamo hoton mijin kawarta ta nuna mata.

“Iya kin ga surukinki”

A razane Iya ta kalleta kamin dubanta ya kai gurin hotonta sai da ta kare masa kallo sannan ta dauke kai ta hade rai.

“Shi kika zabo bana?”

“Yes kuma wannan karon da gaske aurenshi zan yi, mijin kawata ne, thought dai ban fada masa ina son sa ba amman zan fada masa soon”

“Zainab kenan, kin san miyasa ake kira da Hajiya?”

Iya ta tambaya tana kare mata kallo, kamin Zainab tace komai Iya ta bata amsa.

“Saboda ina son ki zama isashiya, tun da aka haife ki na saka mahaifinki da kansa ya rada miki sunan Zainab uwargidan Mai Martaba, ni da kaina nai miki lakani da Hajiya sai dai ganin akwai wata Hajiyar matar Mai Martaba ta biyu yasa ake kiranki da Hajiya Karama, so a komai ki isa, kuma ki amsa sunanki yadda Mahaifiyar Shattima take matar Sarki kuma uwar Yarima da Gimbiya ke ma ki taka wannan matsayin”

Zainab ta tsotsa mintin dake bakinta tana jin maganar Iya na wuce mata ta bayan kunne.

“Iya ba mu da gadon Sarautar nan fa karki manta, kuma ni bana son wani an mutu an dawo, finally dai na samu miji kuma shi zan aura that's all”

Tana gama fadar hakan ta mike tsaye ta fice daga dakin dan ba gane yaren mahaifiyarta take ba. Iya ta bita da kallo har ta fice sannan tai murmushi ta fiddo wurin dake boye a bayanta.

“Ba ki da miji a waje Zainab, mijinki a cikin masarautar nan yake, idan ba mu da gadon sarauta to ya kamata jikokin mu su gaji sarauta.....”

Ta karasa tana daga wani bakin kullin da aka nade da zare kamar laya ta matsashi.

“Mai Martaba ko kuma Labib?”

Ta tambayi kanta tambayar da ita kadai ta san amsarta tana lasar bakinta.





FALMATA POV.

“Sallamu Alaikum wai an ce ana sallama da Falmata a waje”

Almajirin ya fada yana tsaye daga bakin kofar gidan.

“Falmata aka ce ko dai Naja?”

“Falmata”

Ya amsa mata, sai da tai kamar tace aje ace tace ba zata zo ba, sai kuma ta tuna da yan kudin da take shigo mata da su na zance.

“Tashi ki tafi”

Falmata kamar tana jira ana fadar hakam tai saurin mikewa ta saka Hijabinta ta fice, Tumba taja tsaki.

“Ni wannan abun mamaki yake ba ni, kamar a kasa nake zubarwa, a maimakon abu ya ragu sai karuwa yake na Naja na raguwa?”

Ta fada slowly tana mamakin lamarin Falmata. Da mugun far'a Falmata ta fito dan ta san mai kiran nata Maniru ne, har zumudin zuwansa take saboda yana kunna mata wakar Sirleem M2 audio da video, wannan ya saka duk a cikin samarinta ta fi kaunarsa.
Sai da ta fara masa sallama ya amsa mata da murmushi suka gaisa sannan ya zauna a dakalin dake kofar gidan suka dasa hira, can kuma ya kunna mata wani sabon video da M2 ya fitar, tsabar zumudi da farinciki sai ta ji kamar ta rumgume shi. Bayan sun gama zance ne ya bada dari uku da lemun yanka a leda, cikin kunya ta karba domim har ga Allah bata son karbar abu a hannun wani sai dai ta sani idan ya koma cikin gidan ba tare da komai baa Tumba za ta iya mata fada ko ma ta doke ta.
Cikin natsuwa ta shigo cikin gidan ta nufi inda Tumba take ta aje mata ledar lemun a gabanta sannan ta mike mata kudin da hannu biyu.

“Gashi ya ba ni”

Kallonta kawai Tumba take irin kallon na mamakin yadda take tsallake duk wani abu da take mata.

“Umma”

Falmata ta kira sunanta ganin kamar bata san ma tana mika mata kudin ba, sai a lokacin ta dawo hayyacinta ta sauke ajiyar zuciya sannan ta karbi kudin ta kuma kalli Ledar.

“Dauki daya”

Cikin ladabi Falmata ta saka hannu ta dauki lemun daya kamar yadda ta bata umarni ta nufi dakinsu, tana shiga tai shirin bachi babu komai a fuskarta sai murmushi yau kam ranta fes ta ga sabon video M2, har ta kwanta sai kuma ta tashi tana rare wakarsa a hankali tana rawa tana kallon inuwarta wacce kyandir ya haska, sai ka rantse da Allah ba Falmata bace yarinyar da ko a hanya ka hadu da ita ba zaka taba saka ran tana magana ba. Sai da taji motsin shigowar Naja sannan ta yi addu'ar bachi ta kwanta.

Washe gari ma kamar ko yaushe, sai da ta gama komai sannan ta shiga tai wanka ta saka wasu tufafin ta fito ta sha kokon da Tumba ta dama, kamin ta sake mika mata wani rubutun ta karba ta sha da Bismillah. Sannan ta fito ta kama hanyar zuwa gurin aikinta tana tafiya a natse, kana kallonta ka ga natsantsiyar yarinya mai kamala da tarbiya.
Ba ta yi mamakin sake karo da Iya a Harabar gidan ba, domin kusan kullum sai ta ganta a gidan duk da bata san aikinta ko alakarta da masarautar ba, amman ta tabbatar da ita din wata babba ce a ciki. Ta gaishe ta kamar yadda ta saba sai dai Iya bata amsa mata ba yau kam ko kallon inda Falmata take Iya bata son yi. Sai dai gaishe da kowa sannan ta wuce cikin gidan, a tsanake ta hau stairs din ke sada mutum da falon Ammy sannan ta danna door bell. after like 5 minutes Shattima ya bude mata kofar, wani irin jan numfashin Falmata tai ta yi mutuwar tsaye a gurin tana kallon Shattima idonta a waje kamar irin ka ga wanda ka dade ba ka hadu da shi ba ko kuma kake mafarkin gani, ba ido kadai ba har bakinta a bude yake a wannan lokacin. Shattima kan sakin kofar yai ya dawo falo ya zauna yana taba wayarsa daman indai shi zai ce mata ta shigo ko ya tambaye abunda take so sai dai ta shekara a gurin, budewar ma ta yi sa'a yana tsaye jikin kofar ne. Na so kafarta tai ta shigo cikin falon tana cigaba da kallonsa kamin idonta ya sauka a gurin Hajiya Karama wacce ke kallonta, wani irin kallonsu take kamar bata taba ganin mutane ba, ita a rayuwarta bata tana ganin fararen mutane da farinsu ke haskawa sosai kamar Shattima ba, gaba daya kallon Balarabe take masa sam bata yarda bafullanin mutum ne take kallo ba, ta kallin fatar jikinta da take baka ta sake kallon Shattima, ba farin ba ko gashin kansa da ke a gyare abun kallo ne, ga wani dogon hanci kamar biro kai ko cikin larabawan wannan na musamman ne. Shi ne abunda zuciyarta take raya mata.

“Me kike so?”

Hajiya Karama ta tambaya, a lokacin ne Falmata ta kara rikicewa, ta sara abunda zata ce, gaishe su zata fara yi ko fada musu aikin da ya kawo ta, tun da take zuwa gidan bata saba karo da daya daga cikinsu ba sai yau, sai dai jiya ta hango Zainab a stairs sai dai bata dauka a kusa kyauta yayi haka ba sai yau.

“Me kike so?”

Zainab ta daka mata tsawa, a take jikim Falmata ya hau rawa sai ta fashe da kuka domin ba karamin tsorata tai ba.

“Easy mana”

Shattima ya fada yana kallon Hajiya Karama.

“To ana mata magana sai tai ma mutane shiru, kuma sai kallonmu take kamar mayya i hate nonsense”

Ta karasa tana mikewa tsaye ta fice daga falon tana wani yatsinar fuska kamar ta ga abun kazanta.

“Baaba ware”

Shattima ya kira taohuwar yana kallon inda take tsaye rike da turaren wuta, sai a lokacin Falmata ta lura da ita da wasu masu aikin da ke can gaban Plasma suna gogewa. Da gudu Baaba ta karaso gabansa.

“Allah ya kara maka lafiya”

“A tambaye ta me take so”

Ya fada kamar baya son magana. Baaba ta kalli Falmata da har lokacin kuka take tana shasshekar kuka ta ce.

“Ke yar talakawa fadi ki yi kwashi gaisuwa kuma ki bude baki ki fadi abunda kike so”

Falmata na jin haka ta fadi kwance a gurin rib kamar an jefar da ita cikin muryar kuka ta ce.

“Ina kwana”

Da ace shi kadai ne adakin da Allah kadai yasan kalar dariyar da zai yi, domin ba karamar dariya ta ba shi ba, sai dai ko da wasa be nuna hakan ba sabanin hakan ma sai ya kara hade rai.

“Wacece ita?”

“Allah ya baka yawan rai ita ce mai gyara dakin yan uku”

Baaba ta fada tana daga masa hannun kamar mai gaisuwa, ya kalli Falmata daga inda take kwance ya kare mata kallo sannan yai mata alama da ta mike tsaye da hannunsa, da sauri ta tashi ta share hawayen idonta tana jiran wani umarnin. Da ido yai mata alama da ta wuce dakin tai aikinta, da sauri ta wuce, cikin rashin natsuwa tai aikin ta fito kamar wacce ta saci wani abu haka ta rika leken falon da babu kowa sannan ta fice.



AA POV.

Be yarda ya fadawa Anti Rabi cewar bayan kudin da Nana ta bata ba ta sake ba shi wasu, sai dai ya sha fada kuma ya sha gargadi akan cewar kar ya sake kula ta.

“Kai ko kallon inda take kar ka sake yi”

“To ai ba za a koma ba”

Ya fada ne kawai amman wani bangare na zuciyarsa na kara raya masa yadda zai sake samun wasu kudin haduwarsu ta gaba, tun da ta karbi lambarsa yake jiran kiranta.

“Wallahi Allah ne ya ji tausayi na ya kawo min yarinyar nan, Allah kadai ya san me babanta ke yi”

Ya fada a ranshi yana aikin saka talkaminsa, sai da yai ma Anti sallama sannan ya fice daga gidan, kamin ya isa gurin aikin nasa har addu'a yake Allah yasa yau ma ta zo, ya kuwa taki sa'a domin ya tarrarda ita zaune a gurin tana ta boye fuskarta kamar yadda ta saba, wannan karon be tsaya komai ba ya nufi inda take, Nana na ganinshi ta fara dariya.

“Tun dazun na zo”

“Muje waje mu yi magana”

Ya fada yana kallon daidaikun mutanen da ke wajen, domin safiya ce ba kamar da rana ba ko dare da ake taruwa sosai a restaurant din. Mikewa tai tsaye ta riga shi fita sannan ya fito ya same ta tsaye a inda ta tsaya jiya.

“Kin samo min aikin driver?”

Ta bata fuska kamar za ta yi kuka.

“A a ta hana”

“Daman karya kike yi”

“Da gaske ne mana”

Shiru ne ya biyo baya na tsawon lokaci, sannan ya sake kallonta ya ce.

“Yau ma kina son na kai ki wani guri ki boya?”

Da sauri ta daga kai.

“Eh Eh”

“To kawo kudi na karbo babur din, amman yau ya ce sai an bashi 4k”

Bata tsaya komai ba ta bude jakar ta dauko kudin ta mika masa.

“Na je can waje na jira ka kamar jiya?”

“Eh”

Ta nufi hanyar fita shi kuma ya koma ciki gurin abokinsa Bashi, ba laifi yau ya manna masa 500 sannan ya karbi key babur din ya fito ya kunna ya hau ya fito da shi waje, yana isowa bata tsaya komai ba ta hau ya boye fuskarta, sai da ya su kai nisa sannan ya fara tunanin inda zai kai ta, ya san zai ba zai sake kaita gidan Anti Rabi ba, bayan dazun da safen nan ma sai da tai masa gargadi, to ina zan kaita? Ko ya kaita gidan Gwaggonshi? Ko gidan Kawu Bala? Kuma idan na kaita suka gano abunda cewar boyeta na yi za su min fada? Sai tambayar kansa yake yana neman mafita, be an karo ba yaji kamar an bugu babur din da suke kai yana kokarin saita babur din suka fadi kasa daga shi har ita, babur din ya haye shi ita kuma ta mulmula ta fada kwalbati.

Kamar ita ta fi kowa ihu a duniya haka ta kwala ihu ta fashe kuka na gaske tana duba hannunta da yaji rauni da kafarta, daman can ko allura aka ce za a mata sai anyi da gaske take tsayawa balle kuma wannan da ta gurje a hannu da kafa da gefen fuska.

“Wayyo Allah Wallahi sai na fadawa kowa, sai an kashe ka yau Wallahi kai ne ka ji min rauni kai ne ka fadar da ni da babur, sai na fadawa kowa yau sai an kashe ka”

Cikin wani irin kuka da tsoro take fadar hakan tana kallon jikinta, AA na jin haka ya manta da nasa ciwon ya taso ya nufo ta ya daga ta, mutane sai sannu suke musu, ganin yana jan kafar wani yace

“Zaka iya jan babur din kuwa”

“Eh zan iya ku taimaka ku dora min ita dan Allah”

Sai da ya hau sannan suka dora masa Nana dake ta ihu tana fadin sai ta fada a gidansu. A hankali ya fara tafiya gabansa na mugun bugawa kamar zai fito, sai da ya samu wani mai chemist sannan ya faka babur dinsa a gurin ya sauko ya rikota ta sauko ya shiga da ita cikin chemist din, zaunar da ita yai sannan ya ce.

“Bari na gyara fakin din babur di na”

Bata ko kula shi ba tana ta kuka da duba kafarta domin har a cinya ta ji ciwo. AA na isa ya haye babur din ya auna a guje be be nufi ko'ina ba sai unguwarsu, kamin ya isa har wani zazzabi ya rufe shi babu muryar da yake ji sai ta Nana tana fadin sai ta fadawa yan gidansu yau ko sai an kashe shi, laifi goma da ashiri, ga boyon da yake mata ga na fadar da ita akan babur dinsa dan ya san yarinyar yar masu abu ce wata kila ma ita kadai iyayenta suka haifa ya san kuma ba za su kyale ba.

Kamar wani mahaukaci haka ya shigo gida hannunsa na ta jini sai dingishi yake. Anti na ganinshi gabanta ya fadi.

“Lafiya AA”

Kasa ce mata komai yai ya zauna bakin kofar dakinta ya dafe kanshi.

“Lafiya hadari kai?”

“Eh yarinyar ce ta roki na kawo ta nan shine na sake aro babur, muna tahowa sai wani mai Napep ya kade ni muka fadi ta ji ciwo ni ma na ji”

Anti Rabi ta daki kirji.

“Me? La'ilaha illallahu Muhammadu Rasulullah Sallalahu Alaihi Wassalam”

AA ya kalleta a tsora ce ya soma magana gumi na karyo masa.

“Kuma Wallahi na ji tana cewa sai ta fadawa duk yan gidansu, wai yau sai an kashe ni tun da na fadar da ita akan babur”

A take cikin Anti Rabi ya murda, ta dora hannu aka ta fashe da kuka.

“Ka gani ko? Sai da na gargade ka amman baka ji ba, Allah kadai ya san waye ubanta mun shiga uku, ina yarinyar take?”

“Na barta a can wani chemist na gudo”

“Kai Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un, mun shiga shida”

Ta fada tana nufar butar da ke tsakar gida ta dauka ta nufi bandaki. Mikewa tsaye AA yai ya fice daga gidan, chemist din unguwarsu ya nufa yana isa be ko tsaya gaisawa da abokin nasa ba ya ce.

“Dan Allah Ilya kai min treatment din ciwon nan kuma ka min allurar malaria, ina jin zazzabin malaria na ta so min”





_________________

Waye zai zo ya cece AA 🤣😂
Me iya take kullawa? 🤔
Anya dai Hajiya Karama mace ta tana neman miji da kanta kamar yadda kike?😥
Wai me Falmata ta tarewa Tumba ne?😭🤧
*🐄🐄 FULANI 🐄🐄*


By Khadeeja Candy


*6*

HAJIYA BABBA POV.

“Jarma har yanzu ban ga komai ba”

Ta fada tana karewa Jarma dake zaune a gabanta sanye da babbar riga, kansa kuma da rawani.

“Kina gaggawa ne kawai Hajiya, ba gashi mun fara ganin haske ba? Komai a sannu ake binsa”

Ya dauke kai tana kallon wani bangare na dakin.

“Ba Mai Martaba nake magana ba, Shattima shine matsalata a yanzu”

“Da Shattiman za mu fara kamin Mai Martaba ya biyo shi, idan mu ka yi gaggawa to kamar muna fallasa sirrinmu ne, ya kamata mu bi komai a sannu”

“A sannu na ke bin komai Jarma, domin burina dole ne ya tabbata, Talba kadai na ke son ya yi mulkin garin nan, so na ke na ga Ammy na zubar da hawayen bakinciki, shekarun da ta saka na yi a damuwa so na ke ta ninka a cikin bakinciki, na san a yanzu tana farinciki da ciwon Mai Martaba saboda tana ganin Shattima ne zai gaje shi ko? Hmmmm”

Ta karasa tana murmushin gefen baki. Jarma ma murmushin yake yana kallonta zuciyarsa na saka masa burinsa.

‘Za mu kawar da Shattima da Mai Martaba, amman dan ki ba zai yi milkim garin nan ba, indai ina raye’

A zahiri kuma sai ya gyara babbar rigarsa ya ce.

“Da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login