Showing 249001 words to 252000 words out of 286946 words
ta kwana bangaren Mai Martaba da tunani kala kala a ranta,sai da ta gama azkar dinta sannan ta dawo bangarenta domin hada masa abun karyawa, ko da ta shigo sai ta samu Shattima zaune a dakinta yana latsa wayarsa, ganinta yasa ya dago yana mika mata gaisuwa. Sai ta amsa da murmushi tana kara jin son danta a ranta, lallai ta yarda idan ba kai cuta ba Allah ba zai bari a cutar da kai ba, idan an samu nasara to kadan ne wanda zata zo da jarabawa.
“Tun da sassafe haka ko nan ka kwana?”
“Aa yanzu na iso”
“Lafiya Kalau”
Ya amsa yana murmushi, sai ta zauna tana kallonsa.
“Shattima ka dage da addu'a, na san kana yi amman ka kara”
“Inshallah, mi ya faru?”
“Komai ai ya faru, lamarin na Iya kadai abun mamaki wanda na san ba dan addu'a ba da a yau ba mu kai haka ba, kuma bayan lamarin Hajiya Babba abun mamaki ne matuka”
“Me ya faru da ita?”
Sai da ta sauke ajiyar zuciya sannan ta labarta masa abun da ya faru da kuma irin kalaman da Hajiya Babba take ta fada mata a lokacin da ta je ganinta.
“Hajiya Babba ba ta ba ni mamaki ba kamar Jurry, mahaifinta? Kuma ni ma dan'uwanta ne, wace irin zuciya ne wannan?”
Ta fada cikin tsananin mamaki marar misaltuwa. Ammy da idonta ya cika da kwalla ta ce.
“Shiyasa ake son addu'a kana rokon Allah ya baka zuri'a ta gari mai tausayinka da kaunarka kuma wanda zata amfani al'ummar musulmi kuma Annabi yai alfahari da ita”
“Allah sarki Mai Martaba bayan duk dawainiyar da yai da ita tana jin ta kai matsayin da take ganin ya kamata a kawar da shi? Ai ko ba amana bata kama su yanzu ba, ba za su taba samun salama a cikin rayuwarsu ba, ko da ko abun da suke da buri ya kasance”
Cewar Shattima yana jinjina lamarin da yake jinsa kamar ba gaske ba. At the same time ya ji wani irin kaunar Fadime ta kara shiga ransa, domin dukan abubuwan da ta fada sun tabba hakan na nufi ba karya tai ba, kuma ta taimaki rayuwarsu, a lokacin da yan'uwa na jini da kuma irin su Iya suke so ganin bayansu. Samun kansa yai da murmushi duk da irin hali yake ciki na mamaki da alajabin abun da Ammy ta fada masa.
“Smiling...?”
Ammy ta tambaya tana kallonsa da dan mamaki, sai yai sauri kallonta domin be san yana murmushin a fili a tunaninsa iya cikin zuciyarsa ne yake.
“Ah Amman Mai Martaba ya san da wannan magana?”
“Bana son tada masa da hankali, ya zai ji ace matarka da Yarka suna kokarin ganin bayanka? Ga kuma Iya a gefe?”
“Yeah amman dole ne zai sani, and the most important thing is komai ya bayyana a yanzu, and Inshallah zan sake sakawa a yi masa saukar kur'ane duk da an sha yi masa a baya, amman hakan ba zai haka mu kara ba, Ammy kuma ki kara tunatar da shi addu'a ya rike ta sosai”
“Shattima kenan, ni zan baka wannan shaidar da baya addu'a wata kila ta yanzu an manta da labarinsa, kuma duk da hakan zan saka a rubuta masa bismillah guda dubu ya sha, domin ita ma tsari ce sosai daga komai”
“Allah ya kara tsarewa, ni fa daman ina tunanin Sirleem ba son Nana yake ba kamar hadinta ne...”
Shattima na kai Aya Nana na turo kofar dakin ta shigo.
“Ammy ina kwana, Ya Shattima Good morning”
“Morning dear”
Shattima ya amsa mata Ammy kuma ta sakar mata murmushi.
“Ammy har yanzu shiru”
Nana ta fada tana zaunawa kusa da ita, sai Ammy ta kai hannu tana shafa kanta murmushi kwance a fuskarta ko bata fada ba ta san abun da take nufi.
“Already na yi magana da wanda zai masa komai, so idan ya gama zai neme ni ni kuma zan masa magana, ai ni na ce zan yi ko?”
“To maganar gidan fa?”
“Hankalinmu ne ba a kwance ba, kwana biyun nan kin sani, bana son na yi ma Mai Martaba magana shi kuma yai ma Waziri da maganar a yanzu, ki bari nan da sati daya idan komai ya daidaita sai mu ga abun da Allah zai yi”
“Okay Ammy wace makarantar kike ce a sama mishi?”
“Ban sani ba tukunan, ya fada min dai engineering yake son yi, kuma na fadawa Prof a sama masa makaranta mai kyau mai tsada”
Wata kalar dariyar jindadi Nana tai.
“Thank Youuu Ammy...”
“Ki karbi account dinsa a saka masa 1million ya siye tufafin tafiya”
Shattima ya fada, sai Nana ta ware ido da karfi ta dawo kusa da shi ta rumgume shi tana murna.
“Thank Youuu so much Yaya wow....”
Sai kuma ta dawo gurin Ammy.
“Ammy ara phone din pls”
Bata ko tsaya jiran umarni ba ta dauki wayar ta fice da sauri tana murna. Bayan fitar Ammy ma ta kintse ta nufi kicin domin ita da kanta take shiryawa Mai Martaba abun da zai ci. Kamar fitarta Shattima ke jira ya aikawa Ra'ees da kira. Sai da tai ringing tana daf da tsinkewa sannan yai picking da muryar da ke nuna yanzu ya tashi daga bachi.
“Ra'ees”
“Na'am barka da asuba”
“Gida na ke son a nemo min within Katsina and Kaita gida mai kyau”
“Kai zaka zauna?”
“No kyauta zan yi”
Raees yayi hamma sannan ya karasa tashi zaune.
“Okay amman wanda zaka bawa kyauta babba mutum ne ko karami”
Shattima ya san dalilin tambayarsa da yake saboda ya san irin gidan da zai samo masa ne.
“A samo mai kyau dai karka damu da ko nawa yake, ina sonsa cikin kwana biyun nan pls”
“Okay”
Ya amsa sannan ya kashe wayar, Shattima ya jingina da kujerar da yake zaune yana murmushi tunawa da lokacin da ya taba kade Fadime.
***
Karfe goma da yan mintuna direba da ya dauko Mama Fulani da Shattima da Aliyu da kuma Fadime ya faka harabar masarautar. A nan kallo ya koma sama gurin Fadime, girman masarautar da kyauta har tsoro ya bata ba dan ta san masarauta ba ce ita kan sai tai zaton unguwa ce mai zaman kanta ko wani babban kamfani. Yawan hadiman da suke ta harkokin gabansu ma kadai abun kallo ne, tafe take idonta na kalle kalle duk da kasancewar bata cikin farinciki da walwala saboda Wasim. Ita kadai aka bari baya tuni Aliyu da Muhseen sun wuce gaba sai Mama Fulani da ke binsu, sai da ta shiga bangaren Ammy ta gane bata ga komai a waje ba, domin tsaruwar falon da yadda aka kawata shi ya wuce misali, ko'ina kallo take tana bawa ido hakkinsu, sai a yanzu ta yarda wata sarautar ta fi wata lallai wani dan sarki ya fi gaban wani sarki, kamar wata kurma haka ta shiga cikin dakin Ammy sai kalle kalle take, idonta na sauka akan Ammy sai ta ji wani irin kwarjininta ya cika mata ido, gurin haske da gashin gira iri daya ne da na Shattima, sai dai Shattima ya fi ta kyau nesa ba kusa ba, zaunawa tai a kasa tana ta kallon tsadadden lace din dake jikin Ammy da ke gaisawa da Mama Fulani, jin an taba kofar dakin yasa ta juyo sai tai arba da Shattima da ya shigo sanye da farar shadda mai wani irin haske da daukar ido, bakar hular kansa ta saka fuskarsa har wani annuri take, ga dogon hancinsa ya kara fitowa kamar an ja shi, farar fatarsa ma sai shining take kamar wani balarabe, murmushin da ya yafawa fuskarsa sai ya kara fito da saka siffar zatinsa da kwarjinin da ya cika idon Fadime har ta mike tsaye tana kallonsa, gaba daya ya canja mata kamar ba shi ba, wata kila ba dan tana da tabbacin fuskarsa a wayar da tai da shi ba sai ta rantse da Allah ba shi ba ne.
“Zauna...”
Ya fada yana nuna mata gurin zaman a dai dai lokacin da kamshin turarensa ya kai mata hari a hanci. Zaunawa tai ba tare da ta dauke idonta daga gareshi ba shi kuma ya wuce inda take yana yi ma Mama Fulani sannu da zuwa.
“Mama barka da sauka”
Sai da ya gama gaisawa da ita sannan ya kalli Fadime ya sakar mata murmushi.
“Tashi ki zauna akan kujera mana”
Bata motsa ba balle tai alamar tashin sai kallonsa take tana jin zuciyarta na bugawa da mugun karfi.
“Wacan akwai rigima tun jiya kuka take ban san abun da akai mata ba, na yi tambayarta har na gaji, yau kuma da ta tashi ba ta yi ma kowa magana ba”
Mama Fulani ta fada, sai Ammy ta kalleta
“Ko bata da lafiya ne?”
“Lafiyarta kalau”
Shattima ya amsa yana kallon da tai masa mugun kyau kasancewar a cikin bakar abaya, irin kyau nan na fulanin asali masu haiba da daukar hankalin namiji.
“Ina Muhseen?”
Ya tambaya ba tare da ya dauke idonsa daga barin kallon Fadime ba, kamar yadda ita ma ta kasa dauke nata idon, sai sakwanni suke turawa junansu.
“Sun fa riga ni shigowa, na dauka ma nan suka shigo ai, maybe sun wuce gurin Mai Martaba ne, na ji Aliyu na fadin ma zai koma yau”
“Hmm dan wajen Fulani ba a son shiga mutane sai dole”
Ammy ta fada, sai Shattima ya mike tsaye.
“Fateema ya hanya? Za ki ba ni labarin jirgi dai ko?”
Ta kasa cewa komai kamar ba ita ba sai kallonsa take, daman tun a jiya bakinta ya mutu saboda Wasim, yanzu kuma da ta zo nan ta ga wata sabuwar duniya sai ta raina kanta bakin ya kara mutuwa mututus. Murmushi ya sake sakar ya kanne mata ido daya for the first time, hakan ya saka ta hade yawu da karfi ta cigaba da kallonsa har ya fice daga dakin, sannan ta kai hannu ta dafa zuciyarta.
Ta inda Mama Fulani take shiga ba nan take fita ba, ta rufe Ammy da fada kan shirun da tai bayan sanin komai, bata kara sanin Annabi a faku ba sai da Ammy ta labarta mata abun da Hajiya Babba take, kamin a jera musu abun ci da na sha ta dauki wayarsa ta kira Baba Waziri ta sanar masa sun iso kuma tana son ganinsa kamin ta iso gidansa, bata kashe wayar ba sai da ta soma lasa masa zumar abun da ya faru, ko awa daya ba kara ba sai ga Baba Waziri a gidan cikin tashin hankali, a nan Mama Fulani ta zazzage masa komai na abun da ya faru kana Ammy ta dora da nata. Ba karamin baci ran Baba Waziri yai ba kuma be ga laifin kowa ba sai Ammy.
“Amman kin ba ni mamaki Ammy, ni yar'uwa na daukeki ba matar dan'uwa ba, ta ya za a hada kai da matata a cutar da dan'uwana kuma kin sani ki kyale ba ki fada min ba? Ta ya matar dan'uwana za ta so kasheshi kuma ki zuba ido kina fadin baki da hujja, kin san abun da ake nufi da makiyi kuwa? Ashe baki dauki ran yayanki da kuma Mai Martaba a bakin komai ba kenan”
“Ato ni ma abun da na gani kenan, kasan wannan har zaka boye yanzu hakaabun da take fada min wai bata labartawa Mai Martaba abun da Hajiya Babba take ba, ta dai fada masa an kaita asibiti bata da lafiya”
Baba Waziri ya jinjina lamari.
“Ni na yi mamakin irin abun da Hajiya Talatu take yi, na san tana son Maijidda amman ba irin son da zai sakata shiga wannan halin ba saboda mutuwarta, shiyasa da aka kaita asibiti likitocin suka ce ba su ga komai ba kwakwalwarta lafiya kalau take, kuma sai sunayenku take ambata”
“Ni ma na yi mamaki sai dai na yi zaton ko saboda mutuwar ne”
Cewar Ammy tana sauke ajiyar zuciya.
“Dole ne Mai Martaba ya san da wannan maganar, kuma har abada Juwairiyya ba zata taba yin albarka ba har abada”
Baba Waziri ya fada cikin wani irin bakinciki da bacin rai marar misaltuwa.
“Kar a tsine mata abun da ta aikata kadai ya isheta”
Ammy ta fada sai Mama Fulani tai mata wani kallo.
“Allah ya tsine mata albarka, yarinya tai yi kokarin kashe mahaifinta kuma ki ce kar a tsine mata, Allah ya kwashe mata albarka ita da uwarta”
Ammy ta runtse ido tana girgiza kai ko kadan bata son abun da ya shafi tsinuwa domin ta san yadda take cin jiki da dukiyar mutum.
***
Sai dare Shattima ya sake saka Fadime a idonsa, fitar da yai dazun daga dakin Ammy gurin gaisuwa yaje be tashi ba azahar daga can kuma ya wuce asibiti zuwansa na farko tun bayan da akai masa transfer, guri shugaban asibiti ya fara zuwa suka gaisa da shi daman sun san juna yai masa maraba sannan yasa akai masa iso zuwa office dinsa, ko da isa ya samu office dinsa da komai a kintse, takardunsa da komai na sa da yake can Ra'ees ya turo masa su a nan kuma an jera masa sa komai, kwalayen da ke aje gefe ya rika budewa yana dauko abubuwan da ke ciki tare da dorasu a muhallin da yake so, a kwali na uku yai arba da littafin Fadime, murmushi yai ya zauna a saman kujerarsa yana karantawa tana da good handwriting domin duk abun da ta rubuta babu wanda be gane ba, gurin dariya sai yai murmushi, labarinta ne tun daga kan mafarkin da take har zuwa haduwarta da Wasim da abubuwan da suka faru har zuwa kadeta da Shattima yai da neman aurenta da Ra'ees yai komai sai da ta rubuta kadan ya rage littafi ya cika, samun kansa yai da dariya sosai a gurin da yake karanta karyar da yi ma su Bappa da kuma gurin da Wasim yake mata dabon maciji.
“Wow...”
Ya furta yana jinsa cikin nishadi marar misaltuwa, har ga Allah yana son Fadime ta dayan bangaren kuma yana jin dadin rabuwar da Wasim yai da ita. Ya wuni a asibiti har biyar na yamma sannan ya nufi gidansa, a nan ma sai ya rika tuna irin abubuwan da suka yi ta faruwa a lokacin da ya kawo ta gidan.
“Ko miyasa ta zama shiru yanzu”
Ya tambayi kansa yana daura tawul.
‘Maybe saboda ta rabu da Wasim’
Wani bangare na zuciyarsa ya ba shi amsa, sai ya kai hannunsa ya tura kofa bandakinsa ya shiga ya tsaya gaban madubi yana kallon kansa.
“Yes no one can take my place, ke dai kin jin kewa yarinya amman ba rabuwar kauna ba, ai ke ba ki san so ba, yanzu dai za ki sani”
Ya fada with smiling yana kallon kyakkyawar kirar mazantakan da Allah yai masa. Ya shafa kansa yana murmushi tunawa da lokacin da take cewa ina ruwanta da ko shi waye, and the time da ta rike masa kafa akan ba zai tafi ya barta a gidan Zainab ba, da kuma lokacin da take fada masa Jekadiya ta zaunar da ita a kasa.
“I like her”
Ya furta yana cire tawul din ya aje muhallinsa, sannan ya sakarwa kansa shawa ya lumshe ido yana maida numfashi a hankali. Bayan ya gama ya fito daure da tawul din ya shiga kicin cup ya dauko ya matsa lemun tsami a ciki ya saka kanwa ya zuba ruwa kadan a ciki ya sha.
Be bar gidan ba sai da akai magariba, a masallacin da ke unguwar yai sallah magariba sannan ya karasa masarautar yai isha'i a can, daman tun shigowarsa dakin Ammy ya lura Fadime bata ciki sai ya sulale ya nufi dakin Nana, duk da ba shi da tabbacin tana ciki, tura kofar dakin yai ya shiga, sai ya samu Fadime kwance a kasa gefen gadon Nana, tana ganinshi sai tai saurin tashi tana share hawaye. Karaso yai kusa da ita ta duka gabanta.
“Miyasa kika kwanta kasa”
“Gadon na Gimbiya ne ai, be kamata na hau ba”
Ta fada tana murza ido, kallon gadon yai sai kuma ya kalleta.
“No ke ma ai sarauniya ce karki sake zama kasa”
Ya zauna a gabanta yana kallon yadda bakinta ke motsawa.
“Kin ci abinci?”
Ta daga masa kai alamar eh.
“Me kika ci?”
“Shimkafa da kaza”
“Eyyy kaza dai?”
Shiru tai bata ce komai ba.
“Ni dai zaka saka a kai ni gida gobe?”
“Why gobe? Kin gaji da ni ne?”
“Ina son na ga Bappana da Inna...”
Ta fada idonta na cika da kwalla, sai yai murmushi.
“Duk wannan saboda Wasim ne ko?”
Kamar yace bude baki yi kuka, sai kawai ta fashe da kuka. Ido ya sakar mata hakan nan kawai ya ji cewar ba zai iya rarrashinta ba, tun tana kuka a hankali har ta fara yi da karfi.
“Ba zaka ce na yi hakuri ba, ba za ka ce na yi shiru ba?”
Ya kalleta yana kallon yadda kuka yana mata kyau.
“Kin min kyau da kike kukan nan”
Ta saka hannu ta dafe kirjinsa domin har ga Allah tana jin zafi a zuciyarta irin zafin da ba zata msaltashi a siffa ba balle har ta fadi yadda kirjinta yake mata. Mikewa yai tsaye ya isa guri tissue dake dakin Nana ya dauko box din gaba daya ya zo gabanta ya zauna ya cire tissue din ya kama kanta ya rike ya goge mata fuska ya gyara mata hancinta kamar wata yar yarinya.
“Tashi ki hau gado ki kwanta”
Ta make kafada alamar ba zata hau ba, sai ta kwanta a kasa. Mikewa yai tsaye ya dauko filo ya daga kanta dora mata kanta akan filon sannan ya janyo bedsheet din dake kan gadon ya lullube ta, haka nan kuma sai ya ji duk ya damu da rashin sakewarta kukan da tai sai ya dawo a ransa ya tsaya. Kwantowa yai kadan ya saita bakinsa saitin kunnenta ya soma karanta mata zuciyar kur'ane wato Yasin, cikin kira'a mai dadin saurararo da kwantar da hankali, lamo tai tana ta sauraren yadda zakin muryarsa ke ratsa kunnenta yana isarwa zuciuayrta da sassan jikinta, can kuma ta lumshe ido tana maida numfashi a hankali. Be kai karshen ayar ba bachi mai dadi yai gaba da ita.
ZAINAB POV.
Sai da ta ci kukan ta koshi sannan ta fito ta baro dakin zuwa dakinta, sai kuma ta rasa abun da za tai a dakin kamar wanda ta manta komai haka ta zama sai safa da marwa take a dakin tana tunanin abun da za ta yi. Sake fashewa tai da kuka, tana jin cewar mutuwa zata yi idan ta bar garin Yola,