Showing 237001 words to 240000 words out of 286946 words
ta mike tsaye ba. Hannunta ta kai ta bude rigarta tana duba cikin.
“Aa wai ya haka ne?”
Ta tambayi kanta tambayar da bata da amsa, sai kuma ta rufe cikin ta sake mika dukan karfinta ta yunkura ta tashi nan ma ta kasa, ta sake yunkurawa a karo na hudu nan ma dai ta kasa tashin.
“Ma ke faru da ni?”
Ta sake tambayar kanta, kamin ta sake yunkurawa sai ta ji nauyin ya sake karuwa fiye da dazun ma, shiru tai tana ta tunanin dalilin faruwar hakan a gareta bayan taba taba hakan ba, sam ba ta kawo cewar saboda ta ci kurwar Maijidda ba ne, har sai da ta ji kankarun dake cikinta na maita sun fara mata motsi, a firgice ta kai hannu ta dafa cikin tana zaro ido.
“Miye haka kuma? Miyasa na ke jin haka yanzu yanzu?”
Kadan kadan suke motsa mata sai kuma su tsaya, sau uku suna mata wasa a ciki sannan ta ji abun ya tsaya mata, a nan ta sake yunkurawa da dukan karfinta sai gata ta mike a tsaye nauyin da take ji duk ya daina ta koma normal kamar da, sai dai mamaki be bar ta domin bata taba yin haka ba kuma bata yi tunanin akwai wani abu da zai saka ta tai haka ba.
Kwantawa tai saman gadon tana ta tunani kala kala, wata zuciyar na raya mata wata kila iyayen Maijidda sun bata magani mai karfi ne ta sha bayan ta kama kurwarta shiyasa ta ji haka, wata kila kuma wani izon ne akai mata, da wannan tunanin bachi yai gaba da ita, ta kwashi bachinta mai dadi har sai da ta hatse bata barka ba sai kusan la'asar, kamar wanda ta tuna wani abu haka ta sauko saman gadon da sauri.
Bandaki ta shiga tai wanka da ruwan sanyi duk da kasancewar akwai sanyi sanyin hadari a garin, tana fitowa bata ko tsaya shafa komai bata saka wasu tufafin ta dauki tsohon gyalenta ta yafa ta saka talkami ta fito ta shiga dakin Zainab. Kwance ta same ta ruf da ciki tana ta aikin kuka.
“Wai ke yaushe za ki daina kukan nan ne?”
Zainab ta dago ta juyo tana kallonta da idanuwanta da sukai ja sosai saboda kuka.
“Babu rana, domin babu ranar da bakincikin nan nawa zai gushe, dan haka babu ranar da wadannan hawayen za su tsaya”
Iya ta tabe baki tana mamakin yadda Zainab take son wahalar da kanta.
“To idan kin gama kuka sai ki ta tafi gidan Waziri ayi gaisuwa da ke”
Zainab ta tashi zaune da sauri tana kallon Iya cike da mamaki.
“Waya rasu?”
“Maijidda yar wajen Hajiya Talatu”
Baki sake Zainab take kallon.
“Maijidda matar za a aurawa Shattima? Yar wajen Baba Waziri?”
“Ita fa, rai yai halinsa kin san kowa da lokacinsa”
“Waya fada miki ta rasu?”
Iya ta dauke kai ta juya ta fita ba tare da tace komai ba. Zainab na ganin hakan tai saurin saukowa saman gadon ta biyo bayanta
“Hakan na nufin ke kika kasheta kenan?”
Iya ta juyo ta kalleta.
“Duk abun da zuciyarki ta raya miki ki dauka shi din ne, domin ba zan iya wanke kaina daga zarginki ba”
“Ba zargi na ke ba, na san ai ke ce, amman ban yi tsammanin za ki sake aikata irin wannan abun ba, ko dan halin da na shiga, ammn hakan be dame ki ba, bayan duk zargi da kyamar da aka fara nuna mana? Kuma yanzu duk wannan be dame ki ba? Har zaki iya takawa ki je musu gaisuwa? Iya ke wace irin halittace?”
Zainab ta karasa cikin kuka.
“Idan ban tafi ba ai su ma sai su zarge ni kamar ke, kara na shiga ayi komai da ni, na watsar da komai nawa yanzu babu ruwana da wani Shattima balle danginsa har ta kai ga matar da zai aura, idan kim ga dama ke ma ki zo ki musu gaisuwa, domin babu ruwan Hajiya Talatu da abubuwan da suka faru bata mana komai ba”
Zainab ta share hawayenta cikin wani irin bakinciki da takaici marar misaltuwa.
“Ba zan zo ba, kuma ba za ki dawo ki same ni ba”
Tana kaiwa nan ta juya ta shige dakinta, Iya kam bata ce komai ba ta saka kafata ta fice daga gidan, a tunaninta Zainab ta yi hakan ne kawai saboda ta hana ta tafiya. Jikin window Zainab ta tsaya tana kallon Iya har ta fice daga gate din da mai gadin ya bude mata.
“Ya isa haka yanzu kan, komai ya kare”
Ta juya cikin damuwa ta fice daga dakin ta shiga dakin Iya, wardrobe dinta ta bude ta soma bincikar kayanta har ta kai gurin atamfar da ta nade tukunyar tsafinta ciki, dauko dankwalin tai ta bude ta fiddo tukunyar tana kallo jikinta sai rawa yake, sai da ta hade yawu sannan ta dora tukunyar a saman gadon Iya tana ta jin tsoro. Can kuma ta tashi ta nufi wardrobe din tana ta kara dubawa ko zata ga wani abun, sai da ta zazzage komai na ciki ta duba bata ga komai ba, sai ta koma gurin da take yan komatsanta wato karkashin gadonta ta soma janyo abubuwan da suke nan, yawanci duk kayan cin abinci ne sai yan ledodi da talkalmi, mikewa tai tsaye ta dage katifar ta yadda zata ga komai, sannan ta dawo tana ta bude bude kwanonon, har ta bude kwanon da Iya ta zuba naman Maijidda a ciki, ganin maskin yasa ta dauka ta shinshina tana mamakin na inda ta samu nama domin ita har yau bata san ta kan maitar ba balle ta san Iya na cin kurwa ne, a tunaninta kashewa kawai take. Aje kwanon tai ta bude wani babu komai a ciki ta sake budewa shi ma wayam, hka ta rika budewa duk wani abu mai murfi ta kai ga kitsen da iya ta aje, shi ma shinshinawa tai ta aje tana mamakin inda ta samu nama ta soya ta cinye ba ta bata ba, bayan bata saba mata haka ba. Hannunta ta kai ta bude kwaryar dake rufe da faifai sai tai arba da aci balbal a ciki na gwangwani sai tsohuwar kaya da allurar, allurar ta fara dauka ta duba zuciyarta na raya mata cewar wata kila iya na tsafi da ita ne, sannan ta dauko kayar ita ma ta duba har ta yi baki sabar tsufan da tai.
“Me take da wannan abubuwan kuma?”
Ta tambayi kanta tana kallon kayar cike da kyankyami, daukarsu tai ta je ta shiga bandakin Iya ta jefasu a ciki, sannan ta fito ta dauki tukunyar dake saman gadon tana dubawa. Tukunyar kasa ce da aka rufe bakinta da jan kyalle, sai da tai kamar ta bude kyalle ta gani ko miye a ciki sai wata zuciyar ta hana ta, daga tukunyar tai sama ta buga ta da kasan tile din iya karfinta. Take rukunyar ta watse kasa sai ga wani dan karamin maciji a ciki mai kai biyu. Wani ihun tsalle Zainab da daka tare da saka ihu ta ta ranta a ana kare sai waje. Mai gadin na ganinta ya mike tsaye da sauri yana tambayar ba'asi.
“Hajiya Lafiya?”
“Maciji dakin Iya”
“Maciji kuma ta ina ya bi”
“Oho je ka kashe shi dan Allah”
“Kai ai sai dai a kira mutane, ina ni ina kashe maciji wani ma aljani ne, ai shiyasa ake cewa kar mu yi saurin kasu su mu hada su da Allah su tafi”
Ko kamin ya gama maganar Zainab ta bude gate din ta fita daga gidan gaba daya, shi ma binta yai gurin neman mutanen da za su kashe macijin, ba su wahalar samun zaratan maza ba domin unguwar akwai manyan samari duk da kasancewarta sabuwar unguwa, har cikin gidan suka shiga Zainab ta tsaya daga waje tana fada musu inda dakin Iya yake, daga bakin kofa suka tsaya suna dubawa ba su koma ba hakan yasa suka fara yamutsa dakin ko za su ga inda macijin ya boya, tun suna yi da dan tsoro tsor har su kao ma dakin daidai ba su ga komai ba, hakan yasa suka fara tunanin ko ya fito falo ne duk da kasancewar falon babu wani guri da zai iya buya, amman a haka suka rika duba ko'ina har kasan kujerun, har cikin kicin ba su ga komai ba. Daya daga cikinsu ya zo yana tambayar Zainab.
“Amman ke kin ga macijin da idonki? Ko kuma tsoro dai kika ji?”
“Na ganshi Wallahi da idona”
“Abun mamaki ni ban ma ta inda zai iya shigowa ba, ko ban dakin ban ga wata hanya da zai iya biyowa ba”
“Wani lokacin a sabon gida ana samun irin haka gaskiya, domin iskokai suna haka, ko a gidansu Najeeb an yi musu haka kamin su samu zama lafiya”
Dayan ya fada, maganar da yai sai ya saka Zainab ta tuna cewar tukunyar da ta fashe ta tsafi ce wata kila macijin aljani ba macijin gaske ba.
“Sai dai idan iskan ne kamar yadda ka fada, amman dai ni na san na ga maciji gaskiya”
“To sai dai ayi ta addu'a Allah ya tsare gaba”
Amin din ma ta ji ba zata iya amsawa ba balle tace musuta gode, haka ta bi su da ido har suka fice sannan ta dawo kusa da dakin mai gadi ta zauna tana ta tunanin yadda zata koma cikin gidan.
********
Kusan kofar gate din gida biyu dake gefen na Baba Waziri dama da hagu fake suke manyan motoci na alfarma saboda rasuwar Maijidda, domin mutuwa mai ban tsaro duk wanda ya ji Maijidda ta rasu sai yayi mamaki domin ba a san ta yi ciwo ba sai idan na kusa da ita ya fada cewar ta kwana a asibiti da zazzabin taifot, hakan yasa har wandanda ba su san ta ba jin cewar budurwa ce suke zuwa gaisuwa, daman kuma Baba Waziri mutumen mutane ne, ta ko'ina zuwa ake masa gaisuwa ga familyn Hajiya Talatu da Hajiya Maryam su ma sai zuwa suke kamar an turosu, yan uwa abokai da suruku kai ma sai zuwa suke.
Sai dai abun da kewa kowa tausayi shi ne Hajiya Talatu da ke ta shikar dariya ta fita hankali, sai kuma ta hada ta waka, duk wani abun da ta gani sai ta fade shi tace na jiya, hakan yasa aka sake maida ita a dakin aka rufe har sai da aka dawo daga kai Maijidda a gidanta na gaskiya, sannan Baba Waziri ya bada izinin a janyo mota a sakata a ciki a kaita asibiti.
Ana fitowa da ita duk abun da ta gani sai ta ce.
“Kai wando na njiya? Ke riga ta jiya? Takalmi na jiya? Hijabi na jiya? Kai mota ta jiya, fulawa ta jiya... Fadime ta jiya, Falmata ma ta jiya, Sardauna ma na jiya, Jarma ma na jiya, Shattima ma na jiya, ga Ammy ta jiya, ga Nana ma ta jiya, kai Jurry ma ta jiya, Mai Martaba na jiya, Hajiya Babba ta jiya...”
Komai ta gani sai ta fada ta ce na jiya, idan kuma bata fadi wani abun ba to zata kama sunanyen mutanen da suke ranta tana fada sai kuma ta bushe da dariya, sai dai babu wanda ya kawo komai a ransa kowa yana tunanin mutuwar Maijidda ne ya taba ta, haka aka sakata a mota aka nufi asibiti da ita yaranta sai kuke suke, ga mutuwar yar'uwa ga rashin lafiyar uwa.
Ana kiraye kirayen sallah la'asar mai napep ya sauke Iya gida na biyu kamin gidan Waziri, sai da ta fito sannan ta ba shi kudinshi tana jin jikinta na wani tsam tsam tsam kamar ba lafiya ba, habar zanenta ta kamo ta kai a idonta tana murzawa saboda ta samu idon yai ja ace ita ma ta yi kuka, domin abu ne mawuyaci ka ga maye na kuka, is hardly, suna da karfi halin bala'i da bushewar zuciya, sai da ta murza idon har ta ji ya dan soma mata ciwo sannan ta nufi gidan tana ta mitsika idon kamar munafuka.
Haka ta ratsa cikin manyan motocin ta shiga cikin gidan, kai tsaye ta nufi bangaren Hajiya Talatu, tun a bakin gate din ta fara hango mutane a harabar wasu akan kujeru wasu akan tabarma wasu akan carpet, cikin karfin hali ta nufi gurin tana isa ta fara musu sallama tana kukan karya.
“Jama'a to sannu mu da wannan rashi”
Mutanen da ke kusa da ita suka masa mata duk da kasancewar ba kowa ya san ta ba a gurin, wadanda ta sani suka santa suna daga can ciki, sai da tai musu gaisuwa sannan ta mike tsaye tana kuka ta fara tsallaka mutane har ta isa bakin kofar falon ta shiga ciki tana fashewa da wani sabon kukan, can ta dago kai ta karewa mutanen da suke cikin falon kallo ka zata ga yaran Hajiya Talatu tai musu gaisuwa ko kuma wanda ta sani sai tai arba da abun da ba tai zato ba balle tsammani, tsaye tai cak lokaci daya ta daina kukan tana kallon ikon Allah. Maijidda take gani tsaye a kofar dakinta tana kallonta fuska babu annuri.
“Ahhh ahh ahh Jama'a ba Maijidda ce ta rasu ba?”
Iya ta tambaya da karfi tana kallon Maijidda da ita kadai take ganinta. Duk mutanen da ke kallon kallonta suke har Ammy dake zaune a one seater rike da carbi da kuma abokiyar zaman Hajiya Talatu wato Hajiya Maryam dake kusa da kujerar Ammy.
“Jama'a ba ku amsa ni ba, ba Maijidda ce ta rasu ba?”
Ta sake tambaya da karfi.
“Ita ce mana”
“To ya nake ganinta gata nan a tsaye tana kallona”
Iya ta fada tana nuna kofar dakin Maijidda, kusan duk wanda ke cikin falon sai da ya juya yana kallon kofar dakinta dake rufe babu wanda ke ganinta sai Iya, sai mutanen da ke kusa da ita suka fara matsawa suna mata kallon tsoro.
“Maijidda...”
Iya ta kira sunanta bata amsa ba, kuma bata motsa ba sai wani mugun kallo iya take ganin Maijidda na mata.
“Ke kika cinyenta kenan shiyasa kike ganinta, ku nemo maza su fitar mana da matar nan a tsareta can waje”
Ammy ta fada daga inda take zaune, da saurin mutanen da ke gabanta suka tashi domin aiwatar da abun da ta fada, Iya kam bata ma san wainar da Ammy take toyawa ba domin hankalinta na gurin zanenta da ta ji ana ja, tana duba kasa sai ta ga Luna Luma da Labib.
“Luma Luna Labib?”
Ta fada tana dukan kirjinta, sai zaro ido take jikinta nata rawa, kamar jira ake ta dago nan ma sai ta soma ganin yayan Ammy da ta cinye da kuma Jakadiya da wata Jekadiya da duk matan da ta ci na Shattima sai da ta fadi sunansa domin ganinsu take ido da ido suna mata mugun kallo.
“Miyasa na ke ta ganin mutanen da na cinye? Miyasa zan yi ta ganinsu bayam na riga na cinye kurwarsu? Ya haka wai haka? Lafiya dai? Me ke faruwa ne?”
A gabar da tai maganar ne mazan da Ammy tace a kira suka shigo sai Ammy ta daga musu hannu alamar su dakata, matan dake jikin kofar kam tuni wasu sun yi waje wasu kuma sun masa can nesa da inda take.
“Miyasa na ke ta ganin mutanen da na ci? Mai Martaba? To ai shi ban ci shi ba, na kurwarsa na nan aje ban cinye ba”
Ta fada tana kallon Mai Martaba dake tsaye gabanta.
“Jama'a ku min rai, ya haka wai?”
Tana kiran jama'a sai kowa ya kara nisantarta, Ammy kuma ta mike tsaye da sauri tana nuna ta.
“Mai Martaba fa kika ambata Iya? Innalillahi Wa'inna Ilaihirraji'un ku kira min Wazari”
Duk wani abun da Ammy take fada da hayaniyar mutane bata jin ko daya gaba daya idonta baya nuna mata komai sai nutanen da ta ambata su kawai take gani. Wani irin zafi ta soma ji a jikinta kamar ana yanka mata reza a fata, can kuma ta soma jin kankarar maitar dake cikin cikinta ta soma motsawa tana mata yawo. Da farko bata ganin kowa yankan kawai take ji ta ko'ina har sai da tai magana.
“Yankana ake fa! A jikina ina jin yakan wuka”
Kamar jira ake tai magana sai ta soma ganin mutane da ta cinye suna yankanta ta ko'ina kamar an aikosu. Mutanen da ke falon kam kowa ya hade waje daya yana kallon yadda take tisge tufafin jikinta tartsatsin wuta na fita a jikinta kamar ana ƙira. Ƙofar Kitchen aka bude mutanen dake cikin falo suka samu fita ta gurin domin Iya na tsaye kusa da kofar falo ne.
SIRLEEM POV.
Cikin gidan ya koma a tunaninsa Hajiya Babba tana ciki kamar yadda ya fita ya barta sai ya samu bangaren Babu kowa sai Hadimai, wayarsa ya ciro ya kira Kausar sai ta dauka tana tana ta kuka ta sanar masa cewar suna asibiti, jikin na rawa ya koma motarsa ya dauki hanyar asibitin, kamin ya isa har ya matsu domin gani yake kamar yana sa za a sanar masa cewar ya rasa Hajiya Babba. A lokacin da ya isa ana cikin gwaje gwajen jininta ne yana gurin aka mata allura ta samu bachi, sai a lokacin ne suka samu labarin rasuwar Maijidda sai ba su da kuzarin zuwa dukansu domin hankalinsu yana gurin mahaifiyarsu. Karima ce ta kira sauran yan'uwa tana sanar musu abun da yake faruwa ita da Kausar, Sirleem dai yana zaune daga waje sai tunanin Falmata yake yana ta motsa hannunsa da ta rike shi da shi a hankali, sai a yanzu ya tabbatar yana sonta, sai dai idan har Hajiya ta zabi ya rabu da ita dole ne ya aikata ko dan samun farincikin mahaifiyarsa
Yana a gurin har la'asar a masallacin dake asibitin yai sallah zahar da la'asar abinci da aka kawo ma kasa ci yai gaba daya ba shi da natsuwa kuma hankalinsa ba zai kwanta ba har sai ya ga Hajiya ta dawo normal.
Jurry kam tun 2pm ta bar asibitin sakamakon wani azababben ciwon kai da ya saka ta gaba kamar kan zai cire har wani abu take ji a ciki kamar gero. A hankali Sirleem ya tura kofar dakin ya shiga sai ya samu Kausar a zaune ta kurawa mahaifiyarta ido, kana ganinta ka san ta yi kuka har ta gaji.
“Sis”
Ta juyo ta kalleshi, sai ta ji tsanarsa cikin ranta saboda tana ganin shine