Showing 189001 words to 192000 words out of 286946 words
na siye aljanunta sannan na samu sa'ar kamata, tana cikin danyen jego dama mu mayu mun fi son saurin kama mai danyen jego ko mai karamin ciki, ina kama kurwarta na yanka, sannan na fara bibiyar yaran da ta bari, ba saboda kowa ba sai dan ke duk ke nake yi ma tanadi... Na boye miki gaskiya ne saboda kar ki bata ranki ko ki nemi komawa garin can da bana kauna...”
Zainab ta lumshe idonta da sukai ja hawaye na sauko mata.
“Kenan! Hakan na nufi ni ba yar kowa ba ce, kuma a tasha aka samu cikina, aka haifeni a kaskance....”
Ta bude idon hawayen na cigaba da sauko mata kamar saboda irin wannan ranar kawai akai mata su.
“Na yarda bun da Fadime ta fada gaskiya ne.....”
Ta mike tsaye jiri na debanta ta fice daga dakin kamar zata fadi tsabar bakinciki.
____________
Ayi min afuwa irin wacce aka saba min🙏 in dai babu uzuri Wallahi babu abun da zai saka ni kin yin typing.
45
*Littafin nan na kudi ne biya ki karanta cikin aminci. Pay 300 to 2451879008 Hadiza Abubakar Zenith bank, then send the evidence via 08036126660*
Ammy ta kofar bathroom din ta rufe sannan nufi gadonta ta zauna tana kallon Shattima, kallom dake nuna alamar ta bashi damar yai mata bayanin abun da ya tambaye shi.
“Sunanta Fadime, i meet her first a Katsina....”
Tun a farkon ganin da yai mata a Katsina har zuwa asibitin da zuwa gidan Iya, sai dai be fadawa Ammy cewar Iya mayya ce ba, ya fada Ammy cewar dai tana tsoron zaman gidan ne shiyasa ta matsa sai ta biyoshi.
“Ban yi zaton zaka dauki kafarka zuwa gidan Iya ba, duk abun ka girmi shi ya kamata ace ka bashi baya.... Matsayinka darajarka ta wuce Iya da Zainab su yi fushi da gidan su bar shi kai kuma ka dauki kafarka ka taka a gidan, me zaka fada musu? Hakuri za ka ba su ko kuma rokonsu zaka yi su dawo nan da zama?”
Shattima yayi shiru for seconds kamin ya hade yawun bakinsa.
“Allah ya taimakeki, agafarce Ammy ban dauka abun zai bata miki rai, Ammy kin sani ni da Zainab akwai kyakkyawar alaka da fahimtar juna a tsakaninmu, na je saboda na yi magana da fahimta da ita, daga baya kuma sai na gane rabon ganin Fadime ne yake kirana shiyasa na tafi amman amin afuwa”
“Shattima kai fa dan Sarki, ba ina fada maka hakan ba ne saboda ya saka ka girmar kan aa, ya kamata ka nisanci wani abu ka fuskancin wanda ya dace”
Fadime ta bude baki jin an ambaci dan sarki.
“Inshallah Ammy, nima ai kin san ba mutum ne mai son irin wannan ba, wannan ma na yarda rabo ne ya kira ni”
Ammy ta maida dubanta gurin Fadime.
“Ita miye alakarta da Iya?”
Fadime na jin haka ta mika hannu ta kama gefen rigar Shattima ta rike, cike da tsoron yadda ta ji yana bawa Ammy girma da ladabi a bayaninsa ta san tsoronta yake balle kuma ita da ya rabo. Ammy ta kalli rikon da tai masa shi ma kuma ya kalli hannunta sai da be janye mata hannun ba.
“I dont know maybe yar'uwarsu ce, ban dai tambaya ba”
A nan bude bakin tai ta zaro ido jin abun da yake fada, gabanta ya fadi kar dai Ammy tai musu dauka daya hakan yasa ta shiga kare kanta.
“Wallahi ba yar'uwar mu bace ai na fada maka komai, Wallahi ajiya aka kawo ni gurinta”
Shattima ya saka kafarsa ya taki kafarta kadan.
“Ni ka daina takina idan ban yi magana ba ai sai a dauka ko ni mayya ce kamar su...”
Ta fada tana turo baki tare da saka dayan hannunta ta taba kafar. Ammy ta kalli kafar sannan ta kalli Shattima da ya rasa inda zai saka kansa, ko kadan baya son Ammy ta ji zancen nan har sai ya gama bincikensa, gashi kuma ta fada a gaban Ammy bayan ta dauko masa wani labari da be san inda ta same shi ba.
“Ban fada miki wacece Ammy?”
Be karasa ba ta tari numfashinsa.
“Ka fada min kace matar sarki ce”
Shattima yayi shiru be sake cewa komai ba tsabar haushi, shi kansa ya san da ba ita ba ce a yau tai masa haka da ba zata sake kai labari ba.
“Ya sunanki?”
Ammy ta tambaya tana tattara hankalinta gaba daya ta maida a kanta.
Wannan karon sai Fadime ta juya gefen Shattima tana tambayarsa.
“Na yi magana?”
“Na yi magana?”
Ta sake tambaya jin ya shareta.
“Ban sani ba”
Ya fada yana watsa mata harara kamar tana ganinsa. Aiko Fadime ta kame bakinta tai gum kamar ba ita ba, ala dole sai Shattima ya bata umarni.
“Da alama dai akwai abun da kake boye min, wanda baka son na sani”
“Babu komai Ammy, gata nan ai aku...”
“Umarninka take jira ai”
Ammy ta fada sai Shattima yai murmushi.
“Ba ta ga damar magana ba ne dai, Fadime ba ki ji Ammy tana tambayarki ba?”
“Ai kai kace idan nai mata surutu da yawa zata iya dukana, shiyasa nake tsoron magana, Sunana Fateema amman a kauye ana ce min Fadime, a birni kuma Fateema”
“Me na ji kina fada dazun?”
“Yaushe?”
“Akan Hajiya Babba da Nana”
Fadime ta gyara zama tana jin an tabo mata inda yake mata kaikayi.
“Eh Eh, a lokacin da najr garin su Wasim to a garin daman garin matsafa ne, to kakansa babban boka ne, yana bada magani kuma yana tsafi sosai, shine wata rana wasu mutane suka zo neman magani gurinsa wasu hajiya biyu dayar ce Hajiya Babba sai wata Hajiya na manta sunanta, sai wani namiji daya sunanshi Jarumi, da wata budurwa, har ina boya bayan Wasim sai na ji tana cewa wai ayi mata magani Nana ta so wani mutum, kuma ta fadi sunan Shattima da wata Fadime har tana cewa a fada mata Fadimen, kuma tace tana son a daure bakin Nana kar ta fadi magana, kuma wai a kashe Sarki a kashe dan sarkin wai kuma a kare aiki da Ammy ta yi wai tana son ta mallake komai, labarin yana da yawa da yawa ne kuma shi bokan ya bawa Hajiyar da suke tare wani magani yace a daba a nama a bawa wata ta ci, yawwa na tuni ita wannan guntuwar Hajiyar tace wai tana son a lalata auren da za ayi da yarta da wani, kuma yace musu akwai tafiyar da babu dawowa, kuma tace wai a raba wani ko waye? Na manta sunanshi da Falmata, Wallahi zan iya fada ko a gaban waye, kuma idan Wasim ya zo a tambaye aji”
Gaba daya jikin Ammy sai yai sanyi, zuciyarta ta shiga bugawa da mugun karfi, Shattima ma shuru yai yana mamaki, ya san Fadime ba zata shirya karya ba, domin bata san zata hadu da shi ba, kuma abun da ta fada yayi daidai da wasu abubuwan.
“Jarumi ko kuma Jarma?”
Ammy ta tambaya tana ta tunanin maganar.
“Ko ma dai waye ne, sunan da J yake farawa, har da wata yar lauka lauka marar jiki, ko ni na fita albarka, na tuna har da cewa tai tana son asa Nana ta lalace kuma wai a saka ta ta zo wani, kuma wai a taba Falmata da wani mutum, kuma akwai Sardauna a labarin, har yace ta yi latti kuma Wallahi a kira matar agabanta ma zai maimaita haka”
Shattima ya kalleta.
“Ke kin san inda kike kuwa? Kin san wacece Hajiya Babba?”
“To ina ruwana, ai gaskiya ce ko a kotu zan fadi haka, idan ba ku yarda ba ku ba ni qur'ane na rantse”
“Bayan wannan kin san wani abu?”
Ammy ta tambaya
“Aa ban san komai ba”
“Idan kika min zan saka ayi miki mummunan hukunci”
Take hantar cikin fadimr ta kada hankalinta ya tashi, ta fara lalaben inda zata samu hannun Shattima ta rike.
“Wallahi ban miki karya ba, gaskiya na fada Allah shine shaidata, ko Shattima?”
Shattima ya kasa ce mata komai sai tunani yake, shi kansa ya tsorata da labarin bare kuma Ammy da ta kasa boye tashin hankalinta.
“Bayan shi fa?”
Fadime ta yi shiru tana nazari abun da zata fada jin ance za a yi mata mummunan hukunci.
“Akan Hajiya Babba ko akan Iya?”
Ta tambaya gudun kar ta dauko wani zance ta saba.
“Me Iya tai?”
Ammy ta tambaya daman bata manta zancen na dazun ba da take fadar wai kar a dauka ita ma mayya ce kamar iya.
“Iya ita kuma mayya ce, kuma ita uwar Wasim ce”
“Ya akai kika san Iya mayya ce?”
“Shi Wasim din daya kawo ni sai yacw ga ajiya nan na kawo miki idan kin ga dama ki cinye idan kin ga dama ki aje, kin ga kenan Mayya ce ko? Kuma yace kin ki amayar da kankarar maita kina cin mutane sai tace har yanzu bata ci kowa ba sai wanda ya shiga gabanta ya hana ta cikar burinta, tace wani mutu take bibiya ta cinye Matansa yanzu kuma yayansa take bibiya, har tana ta jin tsoro tana cewa an min aike ne yace a a, kuma har da wannan muguwar yarta tare suke maitar, kuma fa wannan Zainab din ashe ita ce na kai garin su Wasim, ta dauko hotuna saboda ita na makance fa, amman Wallahi Ammy baki ga wulakancin da take min ba”
“Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un, Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un”
Shine abun da Ammy take ta fada tana dafe da kirjinta sai Fadime ta kara rike kame rigar Shattima ta rike. Ammy za ta yi magana Shattima yai mata alama da tai shiru da hannunsa sannan ya rika hannun Fadime.
“Tashi muje n kai ki gurin Jekadiya ta kula da ke zamu yi magana da Ammy”
“Ita ta kwarai ce, tsoro nake ji dan Allah karka kai ni inda zan cutu kaji?”
“Ta kwarai ce na santa na san halinta”
Yaja hannunta suka fita, falo ya fito da ita.
“Jekadiya”
Jekadiya ta mike tsaye da sauri ta nufo inda yake.
“Ga bakuwa ku zauna da ita a nan a kula da ita, duk abun da take so ayi mata”
“An gama toron giwa, Allah kara maka lafiya da imani”
Ta kama hannunta, Fadime ba dan ta gamsu da ita ba ta sake ta sai dan babu yadda za ta yi. Juyawa yai ya koma ciki, wannan karon a tsaye ya samu Ammy hawaye a sauko mata a ido.
“Shattima yarinyar nan mutum ce?”
“Mutum ce Ammy, zaki iya tuna lokacin da kika fadawa Ra'ees ya nemo min mata?”
“Ita ce yarinyar, ni ma ban san haka ba sai a haduwar ta farko, Ra'ees ya fada min ke kuma kika kara fada min”
Ammy ta zauna bakin gado tana kallon danta.
“Shattima muna cikin makiya, Me ka fahimta game da abun da take fada?”
“A zancen Iya yayi daidai da labarina mutumen da take bibiya wata kila ni ne”
“Ba wata kila Shattima kai ne ma, shiyasa ta tallata maka yarta, saboda ta san ita take cinye maka mata? Kenan ita ta cinye su Luma? Amman matar nan bata da imani”
Ammy ta lumshe ido sai ga hawaye ya sauko mata, daman gudun shiga irin wannan halin yasa shi boye mata sai gashi Fadime ta tono komai.
“Ashe akwai abun da Allah ya gani ya hana zuciyata natsuwa da ita, shiyasa tun farkon zuwanta na kasa samun kwanciyar da ita...”
Hawaye Ammy take babu kakkautawa, Shattima ya dawo kusa da ita ya zauna.
“Gudun sakawa kanki damuwa yasa ban so kika ji maganar nan ba”
“Irin wannan abun ba a boyewa Shattima saboda abu ne na daukar mataki, kana tunanin ido za a zuba mata tana cinye matanka da yayanka a kyaleta?”
“Hukunta ta zaki yi Ammy? Kina da wata shaida ne akan hakan? Maganar Fadime kadai bata isa hujja ba, kiran dana ayi ma Falmata ma ina son na kara bincikarta ne, idan ta tabbata hakan na san irin hukuncin da zan dauka ta cikin ruwan sanyi”
“Muna zagaye da makiya, daga kai sai Nana Allah ya ba ni, kuma ake son a hana mu samun farinciki a kawarmin da kai alala rayuwar Nana mi nai wa Hajiya Babba? Me na tsare mata? Miyasa zata min haka? Ba ni kadai ba har da Mai Martaba? Mijinta uban yayanta?”
“Nana ta fada jiya, a lokacin da aka rufe Sardauna ita sa aka juya case din zuwa kisan kai, Nana tace ta ji tana waya tana fadar sai kin shiga damuwa kuma sai rayuwarta ta lalace ba sata ba har abun da yafi sata sai ta yi”
Ammy ta kalli Shattima cikin tashin hankali tana jin kamar kanta ba zai Iya daukar maganar ba.
“Nana bata fada min wannan ba...!”
“Ta ce baki saurarenta ba kina cikin fushi da ita saboda abun da ya faru, wannan kadai ya isa ya saka na yarda da maganar Fadime, tana son a rufewa Nana baki saboda kar ta fadi maganar ne, wata kila kila kuma Sirleem ne take son a saka mata soyayyarsa, ni daman na gani kuma zuciyata ta ayyana min Sirleem ba son Nana yake ba, domin baya bata irin kular da ta dace”
“Allah sarki Yata... Ina ta tsanarta ina jin kamar nai mata baki, saboda irin abubuwan da take, ashe ba yin kanta ba ne, ban taba mata uzuri ba, saboda tana bata min rai...!”
Ammy ta fada hawaye na sauko mata, tana tuna lokacin da Nana take fada mata ta yi satar sarka kuma bata san dalilin daya saka tai ba, ta san be dace tai ba, hannunta ne yake mata kaikayi.
“Tana nuna mata so kamar uwa, har Nana tana ganin kamar tafi sonta fiye da ni... Muna cikin makiya, ina tunani da addu'ar Mai Martaba ya samu sauki amman Hajiya Balki nema masa mutuwa take tare da kai? Ban taba tunanin Hajiya zata iya haka ba, na san bata so, saboda kishi gaskiya ne, nima ina kishinta, amman Wallahi babu hassadarta a raina, ban taba jin kyashinta ba, ban taba mata fatan mugun abu ba, shiyasa ban kyamace ta ba a lokacin da danta ya nemi auren Nana wata kila da wata manufar ne”
Ammy ta dantse bakinta saboda kukan da yake son subuce mata.
“Shiyasa tai wa yarinyar Falmata sheri? Ashe wata manufar ne? Mutum abun tsoro, ita kanta Hajiya Talatu ban zata za ta iya haka ba, balle Jarma da yake kanensa, ashe zai iya cutarda dan'uwansa har a nemi rayuwarsa saboda abun duniya mai karewa?”
Shattima ya kalleta.
“Ammy dan Allah karki saka damuwa a ranki, Allah yana tare da mu, kuma ya ga zuciyarmu babu wannan cutar a ciki, wata kila shiyasa ya bayyana mana komai cikin sauki kuma ta hanyar da ba mu yi zato ba”
Ta rumtse idonta hawaye na sauko mata, kamar ba gobe. Shattima ya kalli agogon hannunsa.
“Karfe 10 jirginmu zai tashi, ina son na koma Katsina na fadawa iyayenta halin da ake ciki, zan bar ta a nan, Ammy sai kin yi hakuri da halinta kuma Idan aka fadi wata magana a gabanta tana recording ne”
Ammy ta bude idonta ta kalleshi still hawaye sun ki daina sauko mata.
“Allah yai maka albarka Shattima, Allah ya kareku daga dukan shari, yai muku mafita, dan Allah ka tsare addu'a sosai da sosai”
“Da bana addu'a wata kila da ban kawo haka ba, bana wasa da addu'a saboda bana son nai nisa da Ubanjigina, kuma inshallah zan kara dagewa... Ammy kar a gaji da ita tana da yawan requesting”
Ammy ta yi murmushi har lokacin hawaye be daina sauko mata ba.
“Karka damu, ko dan abun da tai mana za a kula da ita, balle kuma na lura tana da muhimmanci a gareka”
Yayi murmush ya mike tsaye, Ammy ta bishi da kallo har ya fice. Sai da ya kawo tsakiyar falon sannan ya kalli Jekadiya ya ce
“Fito da ita”
“To ranka ya dade”
Jekadiya ta riko hannun Fadime suka fito daga falon suka bi bayan Shattima.
“Ina zamu je?”
“Shattima ne yace a fito da ke?”
“Ina zai kai ni?”
“Wallahi ban sani ba, baiwar Allah”
Ta fadar Ammy Shattima ya bi hakam yasa Jekadiya ta bi bayansa har cikin fadar, tsaye ta same shi yana lasa waya da alama su yake jira. Jekadiya ta tsaya nesa da shi ta duka kasa tana jan Fadime ta duka.
“Jekadiya tafi zan kira ki...”
“To ranka ya dade”
Jekadiya ta mike tsaye ta fice da sauri, Sai da Jekafiya ta fice sannan Shattima ya juyo yana kallon Fadime fuskarsa dauke da murmushi.
“Kana nan Shattima?”
Yayi shiru be ce mata komai sai murmushi yake yana kallonta, wani gefen ta tafi tana lalabe sai ya bi bayanta yaja gyalenta sai ta juyo da sauri ta taba shi, hannayenta ta kai har kan fuskarsa tana lalabe, shi dai yana tsaye kamar hoto sai murmushi yake sakar mata kamar tana ganinta. Yatsanta na fada bakinsa ya cigeta kadan.
“Asshhh”
Ta dauke hannun da sauri. Sai ya matsa kusa da ita sosai yana kallon fuskarta.
“Zan tafi yanzu”
“Karka dade ka dawo anjima”
“Dole sai na kai gobe”
Ya fada a hankali yana kallon lips dinta. Kamar ta san yana kallon lips din sai ta mutsa su a hankali.
“Tau idan ka je sai ka dawo ka dauke ni ko ka zo da su ko?”
“Eh”
Ya kai bakinsa gefen fuskarta ya sumbaci kuncinta na baren dama.
“Ba zan yarda Wasim ya dauke min nishadi ba, kin min da abubuwa da yawa”
Yana fadar hakan ya kai hannunsa ya taba tafin hannunta, a take ta sake jin sanyi, da sauri ta janye hannunta tana turo baki gaba.
“Ni Wallahi bana son ka, Wasim nake so”
Yayi murmushi tare da kai hannun ja labban nata.
“You cute ji labbanki”
“Ka daina taba ni ba kyau tana matar wani”
Kansa ya daga sama yai dariya marar sauti sannan ya sauke kai ya kalleta.
“Me kike son na riko miki idan zan dawo?”
“Ni dai kyale ni”
Ta fada hawaye na cika idonta, maganar da yai sai ta ga kamar gaske ne, ita kuma har ga Allah Wasim take so.
Ta juya da sauri ta tana lalabe, sai ya kai hannunsa a hankali ya kama nata ya ja a hankali ya koma da ita hanyar da ta Jekadiya ta fito da ita, sai da suka kusa shiga falon sannan ya tsaya ya saka hannunsa ya share mata hawaye.
“Daina kuka Kanen mahaifina yayi min mata, wasa nake miki”
“Tau...”
Ta fada tana jin sanyi a ranta, sai ya sake murmushi.
“Kurciyarki na burgeni, i like you serious”
Ta yi dariya, da waya ya kira jekadiya ya zo ta kama hannunta. Sai a lokacin ya tuna da zancen Falmata.
“Ina Falmatan take?”
“Tana nan Falo ranka ya dade”
“Je ki kirata, saki wannan”
“To ranka ya dade”
Ta saki Fadime ta wuce da sauri, tsaye yai yana kallon Fadime fuskarsa da