Showing 117001 words to 120000 words out of 286946 words
muku albarka”
Ta kasa karasawa sai fashewa tai da kuka ta duke a gurin tana jin kamar a lokacin ne Mama ta rasu. Sirleem ma dukawa yai gabanta yana kallon fuskarta zuciyarsa ta cika da tausayinta.
“A ranar muka wuni kuka n da ita, sai tace min nai hakuri na yi shiru, na daina kuka, amman ita ba rayuwa za tai ba, ashe da gaske ne ta rasu ranar juma'a kowa na mata kyakkyawan shaida, ta tafi ta bar ni ni kadai, bayan rasuwarta Umma tace ba zata iya rikon kanena ba, sai Baba ya dauke su ya kai su kauye gurin kannen mamana, aka bar ni ni nake aikin komai a gidan, ko ban yi laifi ba zata iya cewa na yi baba ya doke ni, wannan aikin ma saboda na samo mata kudi nake yi, gashi ba a ba ni abincin a gidan saboda Baba ya hana.... Kuma kullum kasa nake zuwa na dawo kasa...”
Ya karasa cikin wani irin kuka mai taba zuciya, mikewa Sirleem yai tsaye ya fice daga garden din wanda hakan ya bawa Falmata damar kuka ta tausayawa kanta. Kara matsawa Shattima yai jikin window yana hango Falmata, he feel her feel shi da Mai Martaba yake masa wasiya ma ya yaji balle ita data rasa uwa at her age ga kuma kuncin rayuwar data fuskanta, wani irin tausayinta ne ya cika masa zuciya.
Sirleem be dade ya dawo gurin rike da tissue da ruwan gora, tissue ya fara mika mata ta karba ta goge idonta ta hancinta sannan ya bude ruwan gorar ya mika mata. Hannu biyu ta saka ta karba ta kai bakinta ta sha.
“Na gode”
Ta furta bayan ta sha ruwa idonta har yayi ja ya soma kumbura.
“Rayuwarki abar tausayi ce Falmata, zan yi magana da Ammy if possible a rage miki time din dadewar da kike, kuma ki samu wani mai napep ki masa magana zan rika biyansa sai ya rika kai ki gida kullum yana dawawa da ke”
Tun da ya soma maganar take masa wani irin kallo mai wuyar fassara.
“Na kasa yarda kai ne Sirleem M2, ni ka gama min komai tun da har ka tausaya min, sai yanzu na yarda ban maka soyayyar banza ba, har yanzu ina ganin kamar mafarki na ke, ban san me zan ce”
Ta karasa tana fashewa da wani sabon kuka, sai yai murmushi ya bude mata hannayensa.
“You deserve a hug”
Shattima na ganin haka ya bar jikin window da sauri.
‘Bad guy’
Ya fada a ransa kamin ya mika hannunsa ya bude kofar dakin ya fita. Jekadiya ya tarar a falon, tana ganisa ta risina tana gaishe shi.
“Jekadiya a fadawa yarinyar can Baba Adamu zai rika kai ta gida kullum kuma ya dauko ta, ki hanzarta kiranta tana Garden”
“An gama ranka ya dade, Allah kara maka lafiya”
Ta mike tsaye da sauri ta nufi kofa, shi kuma ya karasa dakin Ammy ya tura kofar ya shiga da sallama.
“Wa'alaikassalam”
Ammy ta amsa masa tana duba wasu manyan laces dake kasan gadonta.
“Na shiga gurin Mai Martaba ne?”
“Eh mun gaisa”
Daga haka be sake cewa komai ba, Ammy ma bata ce masa komai ba ta cigaba da duba laces din. After like 5 minutes Sirleem yai knocking kofar dakin.
“Ammy”
Jin muryarsa yasa Ammy ta masa izinin shiga, sai ya shigo da kuzarinsa sai dai ganin Shattima hakimce saman kujera ya katse masa hanzari, ko da wasa Shattima be kalli inda Sirleem yake ba, ji yake shi ne gaba da shi saboda yana son Nana ko ba komai dole ya girmama shi. And Sirleem did that ya karasa har inda yake ya mika masa hannu, sai a lokacin Shattima ya kalleshi, ya mika masa nasa hannun suka gaisa, sannan Sirleem ya karasa kusa da Ammy ya zauna, daman can haka yake da ita be taba daukar kansa a matsayin ba dan gidan ba, ko kuma kallonta a matsayin kishiyar uwarsa ba duk kuwa da kasancewar Hajiya Babba bata son haka. Sai da suka gaisa sannan ya gabatar mata da abun da ya kawo shi.
“Ammy akan yarinyar nan ne mai reno, i think tana dare sosai gata mace, why not ta rika zuwa gida 6pm”
Kamin Ammy tace komai Shattima ya kalleshi yace.
“Daga yanzu sai 10 zata rika zuwa gida, kana da matsala da hakan ne?”
Sirleem ya kalleshi kamar zai yi magana sai kuma ya mike tsaye.
“alright All the best, but it's someone's daughter remember!”
Shattima dai be ce masa komai ba, ko inda yake ne sake kallo ba.
“Sirleem you can go zamu duba”
Uffan be sake cewa ba, ya nufi kofa. Shattima ya bishi da kallo zuciyarsa n raya masa yana son yai hakan nan saboda ya samu damar shigewa jikin Falmata da kyau.
_________
Ina mata matan kwalisa Matan da suka ansa sunansu na Mata? Ina wadanda ke cewa mun yi mun yi bamu ga amfaninshiba? Hmmm to ku zo ga Yar gidan Maifata ta zo maku da Al ajabu, dan tsugunno, gumba da tsimi da Zuma daban daban, maganin sanyi na maza da Mata. Ga kuma garurruka irinsu mallakau sabuzu kuwa, sa bahaushe saibi, Dan hubbare kafi malam aiki, ke kadai ke da miji, dahuwar kaza, tattabara, ciccibi da dai sauransu. Ba anan kayanmu suka tsaya ba, muna hadin amare na musamman turaren sutura turaren tsugunno turaren wanka da na daki da na jiki duka 4amare nasu na musamman ne, amma ga tsuhuwar da ke son komawa yarinya itama zata iya zuwa ahadata kai abundai sai wanda ya gani, dan haka karkubari abaku labari, domin neman karin bayani zaku iua nemana ta wannan number 09029891757 ko 08169311410, muna aikawa ko'ina a fadin kasar nan har waje kasar nan muna aika kaya.
Address: Nasarawa Samaru Area gurin masallacin mai sola Gusau Zamfara state Nigeria.
30.
*Littafin nan na kudi ne biya ki karanta cikin aminci. Pay 300 to 0314795884 Abubakar Hadiza Gt bank, then send the evidence via 08036126660*
FADIME POV.
kamin su karaso ya Wasim ya kalli Fadime ya ce.
“Karki yi magana kuma komai aka baki karki ci”
Ta daga masa kai wasu hawaye masu zafi na sauko mata. Ganin hakan yasa ya kai hannunsa ya rika wuyan hannunta. Mutane na karaso kusa da shi suka risina masa alamar girmamawa.
"Erregeak zure ahoarekin ikusi behar du"
_Sarki na bukatar ganin tare da bakinka_
Be ce komai yaja hannun Fadime ya fita daga cikin runfar, Zainab na ganin haka ta bi bayansu da sauri, mutanen da suka zo kiransa suka rufa masa baya. Ta inda mutane suka fito ya nufa rike da hannun Fadime wanda ta kasa daina hawayen da take. Ta bayan wani guri wanda yafi kama da kasuwa suka bullo, duk inda Wasim ya dora kafarsa sai an risina masa an dauke ido daga barin kallonsa alamar girmamawa da biyaya. Sun yi tafiya mai dan nisa a kafa kamin su isa bakin wata babbar kofa ta itace an mata gate har da masu gadinta. Wasim na isowa gurim kofar aka bude masa suna risinawa har sai da ya wuce sannan suka tashi. Hakan yasa Fadime ta ji wani girma ya kamata, ko ba komai ta ci alfarmar Wasim ita ma an risina mata, a nan ta kara yarda babu wanda ya isa ya taba ba, kimar Wasim da sonsa suka kara ninkuwa a ranta. Shiga cikin gurin yasa daga Zainab har Fadime suka manta da abun da ya kawo su gurin, wata sabuwar duniya ce, kuma babbar daula mai zaman kanta, babu komai a dayan bangare sai katuwar gona mai cike da manyan itace wanda har baka iya hango cikinta saboda hudu, ta gafe daya kuma kana jin kwarar ruwa alamar akwai korama a gurin. An bi ko'ina na harabar an haska shi da wutar ice wanda hakan ya bawa Zainab da Fadime damar ganin irin kwaliyar da aka yi ma gurin da koren ganye mai yanayi da ganyen ayaba. Sai da suka isa gaban wata kofa sannan Wasim ya cire talkaminsa na fata, ya nasa kafarsa a gurin, Zainab da Fadime kan daman ba su shigo garin da talkami ba. Wata katuwar fada ce da aka shimfida mata gashin farar damisa, tun daga bakin kofar har zuwa inda Sarkin yake zaune kan wata kasaitacciyar kujera da zaka iya rantsewa ba itace ne aka saffara ba. Daga hannun kujerar har jikinta an masa kwaliya da farar azurfa. Ginin fadar kuma an masa kwaliya da fatar zaki inda Sarkin zai dora kafarsa da hannunsa ma kan Zaki ne a gurin. Tsirarun mutane ne a cikin fadar ciki har da Liya dake tsaye gefen Sarkin dake hakimce saman kujera fuska babu annuri.
Nan da nan jikin Fadime ya fara rawa, kafafauwanta suka fara lankwashewa kamar wata musaka. Nesa da Sarkin Wasim ya tsaya ya saki hannun Fadime ya risina da kafarsa daya ya dukarda kansa ya kwashi gaisuwa.
“Barka da wannan lokacin Shugaba”
Ya fada da yarensu, a maimakon Sarkin ya amsa masa sai wata tsohuwa ce mai bakin zane ta amsa masa tana takowa zuwa inda yake tare da jero masa tambayoyi.
“Su waye wannan Shugabana?”
Wasim ya mike tsaye da kyau yana kallon tsohuwar kamar ba zai amsa mata ba.
“Yan garin nan ne, be zama lallai ki san kowa a garin nan ba”
Ya amsa mata da yarensu, kamin Liya ta nuna Fadime data magana da yaren da su kadai suke ji.
“Na san wacan yarinyar, yana zuwa gurinta, a wani gari da yake yamma da garin nan...”
Fadime ta kara fito da idonta waje, duk da kasancewar bata san me Liya take fada ba amman nuna ta take, gashi ta ga Wasim ma a nan shi ya risina a maimakon a risina masa, take mararta ta kara cika da fitsari, hannunta ta kai ta bugu Wasim yana kallonta ta soma masa magana a cikin ranta.
“Fitsari nake ji fitsari”
Ta fada a ranta tana mutsika masa ido tana masa alamar yadda zai gane. Shi dai kam be fahimci komai ba hakan yasa ya maida hankalinsa gurin Liya.
“Ina magana tana magana saboda an daure mata ta yi yadda take so a masarauta, mi zai saka na fadi abun da ba shi ba a gaban Shugaba? Ya zama lallai sai kun san kowa a garin nan ba, amman lallai ne kowa ya san ku”
Ya fada da yarensu yana watsawa Liya wani mugun kallo. Hannu Sarki ya daga sai tsohuwar taja baya ta nufi wani guri daya fi kama da bukka a cikin fadar, bata dade ba ta fito rike da ture wanda ke dauke da soyayyen nama, ta mikawa Zainab.
“Ci”
Ta fada da yarensu, Zainab ta kai hannu ta dauki yanka daya da sauri ba dan ta san abunda ta fada ba, jiki na rawa ta kai bakinta ta tauna ta hade, daga lokacin ne gaban Liya ya fadi ganin ba tai komai ba. Tsohuwar ta matsa da naman kusa da Fadime.
“Ci”
Tana fadin haka Fadime ta kalli Wasim da sauri, sai ya amsawa tsohuwar da yarensu.
“Bata cin nama”
“Na yau ne kawai, kuma umarnin Shugaba ne, ci”
Ta karasa tana kallon Fadime, da sauri Fadime ta kai hannu ta dauki yanka daya tana kuka ta kai bakinta, bata ko tsaya tauna shi ba ta hadiye. A take ta ji wani abu ya taso mata tun daga cikin cikinta ya nufo makoshinta, wani irin kaikayin bala'i ne ta ji a makoshinta, daga Wasim har tsohuwar da Sarkin da Liya kallonta suke.
“Wacan ta mu ce wacan bare ce”
Tsohuwar ta fada tana nuna Fadime, tana yin baya-baya, wani irin ihu Fadime ta saka ta rike makoshin tana kuka.
“Wayyo kaikayi wayyo Allah kaikayi”
Da sauri Wasim ya maida ita bayansa, yana kallon Mahaifinsa, Zainab kam mutuwar tsaye tai a gurin ganin ita ta ci be mata komai ba, amman ga Fadime rike da makoshi wasu yawu masu yauki na mata zuba kamar kubewa sai kuka take tana wani irin tari, tana yagar wuyanta da yatsun hannunta. Murmushin jindadi ne ya fadada kansa a fuskar Liya tana kallon yadda Fadime ke tari tana susar wuya cike da shauki.
“Errugabea da, nire errua da ez dakiela ezer, tira egin nion”
“Bata da laifi, laifina ne bata san komai ba, ni na janyo ta”
Ya fada yana ta kokarin tare Fadime daga kallon da Sarkin ke mata. Hakan da yai kadai ya isa ya karantar da Sarkin cewar son ta yake.
“WASIM...!”
sarkin ya fada yana gyada kai a hankali tare da kara hade rai kamar bakin hadari, Fadime kam faduwa tai a gurin hankalinta na kokarin bacewa saboda kai kayin bala'i da take ji a makoshinta, Wasim ya duka da sauri ya rike ta. Zainab na tsaye a gurin tana shafa wuyanta ba dan tana jin komai ba sai dan tambayoyin da take da su.
NANA POV.
Wani irin murmushi take tana kallon kanta a madubi, ita kanta ta san ta yi kyau matuka red gown din dake jikinta ta haskata, daman can Nana ba mace ce mai son doguwar kwaliya ba, hoda ce kawai a fuskarta sai jan baki data shafa. Mikewa tai tsaye ta dauki purse dinta ta saka takalminta sannan ta nufi kofa tana takawa kamar wata Amarya. Ko da ta fito babu kowa a falon Ammy hakan kuma ba karamin dadi yai mata ba, sai ta nisa ta hanyar da Ammy take hana ta fita, da sauri sauri ta rika tafiyar gudun kar ta hadu da Ammy ta hana ta zuwa budan kan. Tana isa cikin fadar Ammy ta bude kofar ta baya ta fita. Daidai kofar AA ya faka motar, daman tun 7:40pm ya iso ya aika wata Hadima ta fada mata ya iso sai ta umarce hadimar ta fada masa ya dawo ta kofar fadar Ammy. AA na ganin Nana ya fito daga motar yai tsaye yana kallonta, gaba daya ta sake ta masa mugun kyau kamar ba ita ba, abun ka da marar jiki sai sigar ta kama jikinta kamar wata yar tsana. Ita kanta kallonsa take domin yayi kyau fiye da kullum ba zaka ganshi ka ce direba ba ne dan masu kasa haka ya fito. Murmushi ta sakar masa ganin yadda yake kallonta, sai shi ma ya mayar mata da murmushin ya bude mata gidan baya, saukowa tai a hankali ta shiga motar sai ya rufe ya bude mazaunin direba ya shiga ya zauna, sai ya samu kansa da rashin natsuwa har sai da ya juyo ya kalleta, be taba ganinta da kwaliya ba sai a yau, ashe haka take da kyau? Ya raya a zuciyarsa.
“Kin yi kyau”
Ya furta a fili yana jin wani irin girmanta na kama shi, duk sai yaji ta zame masa kamar ba ita ba ya ji nauyinta na sauko masa.
“Na gode kai ma ai ka yi kyau”
“Thank Youu, ina zamu je?”
“X&L Hotel”
Ya juya yana shakar kamshin turarenta daya cika motar ya bata da na shi karamin turaren. Madubin motar ya saita ya juya ta inda zai rika ganin fuskarta sannan ya kunna wutar motar ya kunna ac. A hankali yake ta tuka motar yana satar kallon Nana ta madubin motar, a duk lokacin da suka hada ido sai ta saka masa murmushi. Daga ita har har shi babu wanda yai wata magana har suka isa.
X&L Hotel babbar Hotel ce a garin Yola, wanda manyan mutane suke zuwa yin taro ko biki ko sauka idan ta kama, ko kuma shakawatawa.
A harabar Hotel din ya faka motarsa sannan ya fito ya bude mata ta fito.
“Zaka shiga ciki?”
“Ana bari a gashi?”
“Yes zan ce kai bodyguard dina ne”
“Okay”
Ya rufe motar yana jindadi, daman can ya dade yana son ya shiga gurin domin ya dade yana jin labarin Hotel din sai dai be taba zuwa. A maimako tai gaba ya bi bayanta sai ta tsaya ta jera tare da shi, yadda ya ci ado ita ma ta ci sai abun ya bada kala kamar saurayi da budurwa, a tare suka doshi wata karamar hanya da aka kawata kamin su karasa wani saurayi ya kira sunan Nana, da sunan da Zainab take kiranta da shi.
“Baby”
Nana ta juyo tana arba da saurayin ta washe hakora ta doshi inda yake, AA kuma ya tsaya a gurin yana kallonsu, side hug tai masa suka gaisa.
“How are you?”
“I'm fine, kai ma ka zo biki”
“Yeah friend din mu ne zai yi aure, amman mu ba ciki zamu shiga ba, waya kawo ki Sirleem?”
Juyawa tai ta kalli AA a ganin be cancanta ta kira direbanta ba a yadda ya ci gayun nan.
“No wani ne”
“Okay sai mun hadu ciki”
Ya fada yana sannan ya nufi hanyar shiga gurin. Ita kuma ta juyo ta dawo gurin AA.
“Mu tafi”
“Ba zamu je din ba”
Ya fada yana watsa mata harara.
“Me akai?”
“Ya zaki rumgume wani kato da ba muharramin ki ba”
“To ai cousin dina ne”
“Ba cousin ba kwarkwata, bari na sake ganin kin rika hannun wani sai na fasa miki kai”
Ya karasa da kwafa ita kuma ta turo baki.
“To Wallahi zan ma koreka daga aikin”
Ya kwaikwayi muryarta yana yatsina fuska.
“To Wallahi zan ma koreka daga aikin”
“Kuma karka bi ni ciki, ba zan shiga ba”
“Wallahi sai na biki, sai na shiga, kuma muna shiga ciki kika ga wani kika masa magana sai na bata miki rai”
Ya fada with serious face, yana kara hade mata rai kamar irin shi ne boss ita take aiki karkashinsa. Tana yin gana ya bi bayanta sai ta juyo tana turo baki.
“Ka daina bina”
“Sai na biki kuma ki kaiwa wani namiji magana sai na bata miki rai”
Wani irin abu taji kamar ta saka kuka, sai kuma ta juya ta cigaba da tafiya yana binta bayanta har suka isa gurin. Bata nuna gate pass din ba sai kawai ta fada masa sunanta.
“Nana Aisha Abdallah Jari”
Da sauri ya bude mata kofar ta wuce AA ya bi bayanta yana fadin shi bodyguard dinta ne. Kato dakin taro ne da aka kawata da ado na zamani ga haske ko'ina kamar rana, mutane ta ko'ina kana ganin bikin kasan na manyan mutane ne. Kusa da kofar AA ya tsaya Nana kuma ta fara raba ido tana kallon mutane, ta nan ta hango Hajiya Babba cikin matan manya sai far'a take ana ta fira, can kuma ta hango kawarta Amal, da sauri ta nufi inda suke Amal din na ganinta ta rumgume ta tana murna kamin ta ja mata kujera ta