Showing 1 words to 3000 words out of 209297 words

Chapter 1 - Akidata Book 2 Hausa Novel Complete

01 Jan 2025

702

a: LITTAFIN KUƊI NE, BA DANNI BA DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH.
LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE, WANNAN NA KUƊI NE
NORMAL GROUP
₦300
VIP ₦500
A TURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN 0009450228
AISHA ADAM
JA'IZ BANK

EVIDENCE OF PAYMENT TA WANNAN LAMBAR 07063065680

46_47




shiru Yusuf yayi yana kallon Widad, yayin da yaji gaba ɗaya hantar cikinsa ta kaɗa jin abunda Widad ɗin ta faɗa, ta kalleshi tace

"Ya naji kayi shiru ne? Akwai matsala ne?"
girgiza mata kai yayi yace
"A'a babu komai" Widad tace

"Shikenan, ga Abinci can, kaci seka sha magungunanka ka kwanta"

Kasa motsawa yayi daga inda yake, balle ya aikata ɗaya daga cikin abunda tace, sake kallonsa tayi tace "wai ko dai jikin ne?"

Girgiza mata kai yayi yace "A'a jikina ai na warke"

" to ai gani nai duk ka wani koma so silent, shiyasa nayi zaton ko jikin ne, ka tashi zan kwanta "

Yusuf ya miƙe, ya bata guri ta gyara shimfiɗar ta ta kwanta, yayin da ya koma gefe yayi jugum kamar wanda aka gayawa saƙon mutuwa.

A ƙoƙarinsa na kaucewa zargi daga Widad, ya miƙe ya ɗakko Abincin da niyyar ya fara ci, Amma gaba ɗaya ya ya kasa, tunani burjik a zuciyar sa, ga labarin da Saleh ya gaya masa, ga kuma itama abunda ta faɗa masa yanzu, ashe dai da daru a gaba, ko wane irin hukunci zata yi masa idan ta gano shi jami'in sirrine? Gashi zuciyarsa ta riga ta gama kamuwa da tsananin ƙaunar Widad, yana matuƙar jin sonta a ransa, a yanzu haka dama yana ɗar ɗar, saboda yasan bashi da tabbacin idan suka koma gida Widad ta cigaba da zama da Auren sa, dukda a yanzu yana ƙoƙarinya jarraba Widad yaga ko tana son shi, a ƙaddara ma ta yadda da Auren, su cigaba da zama tare, waye yasan Aure suka yi, Saleh ne kawai sheda ta yaya zasu fuskanci mutane suyi musu bayanin wannan rikita rikita?.

   Nan da nan wani irin gumi ya shiga tsasttsafowa Yusuf, lallai akwai ƙura a gaba, kasa cin Abincin yayi, dama gashi bakinsa babu ɗanɗano saboda zazzaɓi, dan haka ya ajiye Abincin a gefe ya nemi guri ya kwanta, sedai kamar yadda beyi tsammani ba, bacci ya ƙauracewa idonsa se tunani, yanzu meye mafita? Ta ina ze tunkari Widad yayi mata bayanin waye shi, dan kamata yayi ace shi ya gaya mata ba wani ba.

Haka nan jiki a sanyaye ya cigaba da tunani, ya daɗe a zaune ba tare da ya kwanta ba, yana ta saƙawa yana warwarewa.

Muryar Widad yaji tace "Tunanin Meka ke hakane wai?"

Da sauri ya dawo daga tunanin da yake yace "Babu komai karki damu"

"Ko kana tunanin gidane, da Ummanka?"

Murmushin dole ya ƙaƙalo yace "A'a"

"Nasani dole zakayi tunanin gida, nasan baka jin daɗin zaman garin nan, ko baka faɗa ba zaman garin nan ba daɗi, Amma ni ta wani ɓangaren rahama ne a gare ni, bana fargaba ko tashin hankali saboda maƙiyana, ina matuƙar jin daɗin karamcin da mutanen gidan nan suke min, dukda yadda zaman garin ke bani wahala, amma karamcin su da goyon bayanka na ƙara bani ƙwarin gwiwa, tabbas duk wani motsi da zanyi ina tunanin Daddy, ina tunanin wani hali yake ciki, me yake yi? Nasan ina ransa, sedai ina masa Addu'a zuwa lokacin da Allah ze kawo ƙarshen wannan abun in koma gida, kaima kayi haƙuri nasan duk nice silar shigar ka wannan halin"

Ta ƙarasa maganar cikin damuwa. Yusuf yace "bana dana sanin kasancewa ta dake anan, saboda karamcin mahaifinki da yadda da yayi dani beci ace na bar 'yarsa ɗaya tilo ta shiga wani hali in kasa temaka mata ba, sedai dole inyi kewar Ummana, bata da kowa seni, mahaifina ya rasu, gata marainiya ni kaɗai ne a kusa da ita muke rayuwar mu tare, Allah kaɗai yasan irin damuwar da take ciki, dan tunda na tashi ban taɓa nesa da ita ba, nasan tana cikin damuwa "

Cikin tausayawa Widad tace
"Allah sarki, dole zukatan makusantan mu su shiga damuwa, har gara kai wataƙila bayan mamanka akwai wanda zasu damu da halin da kake ciki na ɓatan da kayi, nikam daga Daddy na se Bulama nasan sukaɗai zasu damu, duk wanda yake tare dani, yana tare dani ne dan wannan dukiyar, nasan da babu ita da bazasu nunamin so ba, kuma nasan zagina suke a bayan idona, shiyasa nake wa mutane wani kallo na daban, a da na zata duk mutane miyagu ne, kuma talakawa zasu iya komai akan kuɗi basu da kirki, sedai wani darasi da nayi shine, shi rashin kirki ba'a talaka ne ko me kuɗi ba, a mutum ne kawai, na samu misali akanka da kuma mutanen ƙauyen nan, basu san koni wace ba, amma suna ta kyautatamin"

Yusuf yace "hakane kam, naga kin sake dasu sosai kamar bake ba, kamar ba kece me wannan AƘIDAR ta ƙin mutane ba, me yiwa mutane kallon miyagu ba"

"Hmm ina da dalilin yin hakan, ka kwanta dare ya fara yi, kaga baka da lafiya akwai buƙatar ka samu isashen bacci"

Yusuf yace "Hakane, kema ki kwanta my queen"

'ba zaka dena faɗar wannan sunan bako? "

"Dama bakya son sunan ne? "

"ban sani ba, ai kasan nace maka bana so"

Yusuf yace "ni gaskiya daɗin sunan nake ji, My Queen, My life, I love you so much My dearest Queen"

Tsaki tayi, ta canza position ɗin da take kwance ta toshe kunne ta, wai danma karta cigaba da jin meze ce"

Yusuf yayi murmushi, ya kwanta sedai fa bacci yaƙi yuwuwa, saboda saƙawa da warwarewa da yayi tayi, akan ya sanar da Widad gaskiya waye shi, kokuma karya gaya mata?


"Barrister Hafiz, kuyi duba a cikin lamarin nan da kyau, ku tsananta tunani kafin yanke hukunci, akwai gwagwaɓar riba da zaku samu idan akayi wannan harƙallar daku, zaku samu alheri fiye da tunaninku, zaku samu arziƙin da baku samu a harkar aiki bama"

Barrister Hafiz ya gyara zama yace "Abunda nake so ku fahimta anan shine, wannan aikin fa hatsari ne dashi, mu sa hannu a siyar da kadarorin Daula, karkuyi mamaki akwai masu bibiyar al'amuran dukiyarsa bamu sani ba, idan abu yazo ya tonu sunanmu ze ɓaci, kuma mu rasa aikin mu, sannan mu fuskanci fushin hukuma"

Alhaji Musa yace "Barrister, sha'anin ƙasar nan tamu yanzu kowa mafita yake nemawa kansa, da kayi ƙaramin laifi a kaika prison a banza, gara kayi gagarumi wanda zaka samu mafita a al'amuranka, kuɗi zaka samu manya ba ƙanana ba, wanda baku taɓa zaton samu ba, kuma a yanzu waye yasan inda Daula yake? Idan abubuwan nan suka samu zaku iya barin ƙasar ma gaba ɗaya, dan haka ku san dabarun da zakuyi, kuyi mana wata takarda da zata nuna yayi holan wasu daga kadarorinsa, a bisa farashi me sauƙi ".

Ya kice gumi Barrister Hafiz yayi yace" Yallaɓai akwai buƙatar a ɗan bamu lokaci, zamuyi shawara tukuna "

"Shikenan, amma bama buƙatar a ɓata dogon lokaci, muna sauraren ku"

"Shikenan yallaɓai, sekun jimu"


Hajiya Sarah ce zaune gefen Bulama, yana shan tea yana karanta jarida, tace

"Yallaɓai, dan Allah ka tausayawa Hajiya Halima, kasa baki a sakar mata ɗanta, gaba ɗaya ta kasa nutsuwa, hankalin ta gaba ɗaya baya jikinta saboda damuwa"

Bulama ya nisa yace "banƙi ta taki ba, amma baki fini son Halima ba, da ina da yadda zanyi da zanyi ƙoƙari in saka a fitar da shi, amma wannan case ɗin ba ƙarami bane, idan na matsa sunana ze iya ɓaci"

"Hakane amma ya kamata kayi wani abu, koda ta ɓangaren kwantar mata da hankali ne, Allah kaɗai yasan halin da take ciki, ba ƙaramin abu bane uwa ta iya jure ɗanta a wani yanayi, idan ka bincika babu lallai ko Abincin kirki tana iya ci"

"Eh to banƙi zancen ki ba, amma Halima mace ce me taurin kai da rashin haƙuri, maimakon tayi haƙuri a bi komai a hankali, amma se azalzala ta take, irin wannan lamarin a hankali ake binsa, amma ita ta fiye garaje, case ɗin nan ba ƙaramin case bane ba, karki manta Daula ne fa aka nema aka rasa, kuma shine yake kula dashi, gaba ɗaya ana saurarar hukuma aji me zasu ce, Amma insha Allah ze fita "

Hajiya Sarah tace " shikenan, Allah yasa amma tana cikin damuwa sosai, Allah ya fitar dashi, dan yaron kirki ne sosai "

Bacci be ɗauki Yusuf ba se wajen Asuba, dan haka da Asuba kasa tashi yayi, Widad ce ta fara tashi taje tayi alwala, ta dawo amma be tashi ba.

Hannu tasa tana ɗan dukan ƙafarsa tace " ka tashi ka makara fa yau "

A hankali Yusuf ya motsa yace
"Subhanallah, kuma shine zaki dinga dukana haka da ƙarfi, sekin jimin ciwo?"

"wannan ɗan dukan ne zan ji maka ciwon?"

"Eh mana duba gurin kiga, har yayi ja fa, kin zage ƙarfinki kina ta faman dukana"

Dagewa tayi ta ƙara masa wani dukan tace "wannan kuma se kace na karya ka ko?"

Yusuf yace "kai, tabbas idan na riƙe ki se na rama, zan rama wannan dukan da kika yi min" yai maganar tare da miƙewa ya fita waje domin yin alwala yazo yayi sallar Asuba.

Da gari ya ƙara haske, Gwaggo ta aiko musu da koko da ƙosai, Widad ta zauna ta dinga tsintar ƙosan ta naci, tace bata shan kokon, shikam Yusuf yaji daɗin yadda ta fara sakewa, yanzu tana iya cin Abincin su, dukda a yanzun ma bakomai take iya ciba, amma tana iya cin wasu abubuwan, yanzu wanke wanke ma, ita take abunta ta wanke banɗaki, wataran kuma Hindu ce ke mata.

Yusuf ya kalleta yace "meyasa ba zaki haɗa da kokon ba?"

"nifa ba son wannan kokon nake ba, wataran ji nake kamar zanyi amai idan na sha"

Yusuf yace "Allah yasa Baba Hari ta jiki, Kisha faɗa da baƙar magana"

Dariya Widad tayi tace "Aikuwa dai, ai gaba ɗaya matar nan comedy ce, komai ta gani se tayi magana, wani abun ina sane nake yi, amma bata ganewa taita faɗa"

Yusuf yace "Hmm Allah ya shiryeki to, aini ban san haka kika iya neman magana ba, ganin cewar a baya ko maganar ma bakya son yi, idan anga fara'arki to da magenki ne roux ko kuma Daddy"

"Allah sarki, harka tunamin da sister roux ɗina, nasan tana missing ɗina, maybe ma yanzu sun barta ta mutu saboda yunwa, nasan bame kulamin da ita, nima haushina suke ji balle magena"

Yusuf yace "Eyya Sorry, Insha Allah bata mutu ba zamu koma ki tarar da ita tana nan"

"Hmm is very hard gaskiya, am missing Home Yoseef, ina tunanin dabbobina gaba ɗaya nasan suna missing ɗina"

"wai me yasa kikafi son dabbobinki akan mutane, kina ƙaunar dabbobi sosai"

Widad tayi ajiyar zuciya tace "labarin yana da tsayi sosai, Amma tabbas dabbobi sun fiyemin mutane, except in some circumstances, duk abu indai dabba ta shaƙu da kai, ba zata yadda a haɗa kai da ita a cutar da kai ba, amma dan adam fa yana iya manta dukkan alkhairinka a hada kai dashi a cuceka, shiyasa na zabi rayuwata a cikin dabbobi”

Yusuf yace “hakane maganarki amma sedai ba duka aka zama daya ba, Amma na Allah  ai basa karewa sannan ba yadda zaai ace mutum yayi rayuwa ba mutane"

Widad tace "kai ka ga haka, nikam nayi, kuma yafi kwanciyar hankali"

Yusuf yace "Ai ba ƙaramin mamaki nayi ba, ranar dana ga kina sukuwa akan doki"

Widad tayi murmushi tace "i miss that Moment, ko a England ina wasan polo, ina son tseren dokuna sosai"

Yusuf yai murmushi yace "ko tsoro ba kya ji"

Daga nan  be kuma cewa komai ba ya maida kai yayi shiru yana da  cin abincin a hankali, widad ta kalleshi tace kamar
" akwai Magana abakinka da kake so ka gayamin,naga jiya tun jiya kana ta yawan kallona"

Yusuf yace aini kullum cikin kallonki nake, babu wani abu da nake son gayamiki

"shikenan tunda kace haka,amma gara inda akwai ka gaggauta gayamin, bazan takuraka seka gayamun ba amma nasan akwai abunda yake damunka”

“kinfara samun ido kenan?”

“ba ido nake samka ba, yanayinka ne ya nuna min, amma shikenan ba ina kokarin matsa maka bane, ko son sanin me kake ciki ba, ni bari in tashi in fita in dan sha iska”

Yususf ya kalleta yace “bana son kifita ki barni,ina jin daɗin hirar nan da muke”

Yamutsa fuska tayi tace  "ni kuma na gaji da zaman dakin, dan haka waje zan fita”

Yusuf yace “shikenan tunda haka kike so,your wish is mine my queen”

“ka ji dashi dai, inka gama karka manta da shan maganinka" daga nan tai waje abunta



Alhaji Haruna ne shida Alhaji Munir suke cigaba da tattaunawa akan al amuransu.

Alhaji Munir yace "‘anya baka ganin ayi kokari a sakarwa matar nan danta, da yasan inda Daula yake iya azabar da aka gana masa ya isa ya fadi inda yake, amma tunda be faɗa ba to tabbas besan inda yake ba, gashi ana batun tafiya kotu, karfa matar nan ta tona mana asiri”

Alhaji Haruna yace “ka kwantar da hankalin ka, hakan ma duk shirine, idan sun tafi kotu, za a dauke hankalin mutane daga wasu abubuwan, da zarar hankali ya dauke ya karkata can, mukuma semu cigaba da barnar mu, kafin a farga mun kwashi abunda muka kwasa koda wancan abubuwan basu samu ba”

“banƙi ta taka ba, amma ka gane wani abu guda daya, mudinga yi muna ankarewa da abunda ze biyo baya, yanzun idan aka shiga kotun nan slide mistake ze iya sakawa asrinmu ya tonu, sannan maganar  da muke har yanzu fa babu wanda yasan inda yaran nan suka shiga, tunda suka gudu har yanzu shiru babu labarinsu, babu labarin inda suka tafi, kuma har yanzu basu dawo garin nan ba, gaba daya a tsorace nake, kuma yakamta ace zuwa yanzu shi wannan yaran da muka sa su sace su me adda yake kowa?, yakamata ace basa raye bekamata abarsu suci bulus ba,suma fa hatsarine as garemu”

Alhaji Haruna yayi murmushi yace “Alhaji Munir ikon Allah, kaikam wasu lokutan akwaika da tsoro, munefa masu kasar nan, ko yaya muka ga wani abu na shirin kawo mana tangarda zamuyi maganinsa, mukeda hukumar tsaro kudi da masu mulki, kai a tunnainka har akwai wani wanda ze kawo mana tarnaki ne? ka sha kuruminka, komai a tsare yake, shekara nawa mukayi ana tafiyar nan, ba tare da an samu mtsala ba? Karka manta Alhaji Bukar ma fa namune, kadai mubi komai sannu”

Alhaji Munir yace “ duk nasan da wanan, amma abunda nake so ka sani shine,wannan mahaukaciyar matar fa zata iya komai idan taji za a kaimata danta prison,bafa zata zuba mana ido tana kallo danta ya tafi prison ba”

“karka damu za a san yadda za ayi da ita”

“shikenan, amma nifa kwanan nan na fuskanci wasu halaye da Musa yake yi, sam na kasa gane kansa fa”

“ba kai kadai ba, nima kallonsa kawai nake, kar ace na fiye matsawa ne ko neman rigima shiyasa kawai nake kyleshi”

Alhaji Munir yace “Banda shi mahaukaci ne, wai takara ze fito, ubanwa ze zabeshi bayan bakin tabon da Daula ya goga masa, ai mutane ba mahaukata bane”

Alhaji Haruna yace “kyaleshi ai ya zata mutane basu da hamnkali, a da alokacin da yayi siyasar ma ai farin jinin Daula ne yasa aka zabeshi, ba wai dann ya cancanta ba, mu zuba masa ido ya cigaba da haukansa tunda bashi da hnakali”

“aikam babu alamar hnakli, gara yaje mutane su cinye ɗan abunda ya tara ɗin ai, se sun talauta shi sannan yazo ya fadi zaben, mutum se taurin kan tsiya, baya ɗaukar shawara sam, indai 'yan siysa ne zasu ziga shine, su cinye komai idan ya fadi su gudu su barshi”

Alhaji Musa yace “:ai shiyasa ban damu da in bashi shawara ba gara yaje suma suci rabon su, daga baya yayi hankali ai”

‘shikenan, ni bari in wuce se munyi waya”

“shikenan,semunyi waya”

Daga na sukayi sallama.

Ganin wucewar Hajiya Halima ne yasa Ramlah bin bayanta zuwa dakinta, tana zuwa tace “Mummylafiya kuwa?”

Zama hajiya Halima tayi tace “ina fa lafiya, wai kotu za akai Anwar kotu fa Ranlah”

“mummy wane irin kotu kuma? Ba za bada belin nas ba ?”

“sun hana , sunce ba zasu bada belinsa ba, kuma wadan nan banzayen sunki suyimin komai akai, sun barni se wahala nake nikadai, nikadai na haifeshi nikadai nake wahala ta, dan san abunda ze biyo baya kenan da ban barin Anwar yaje yana wannan wahalar ba, idan yaso ba zagi ba ko tsinewa ce duniiya sumun baze dameni ba,amma ina kallo akaimin da na prison baze yuwu ba, niba abun  in tona asiri ba, nima zan kwana a ciki, da sedai ayi duk wadda za ayi”

Ramla tace ” mummy kiyi hakuri, ki kwantar da hankalinki, idan kika fallasa ba iya asirinsu ba hatta namu muma ze tonu ne, dan haka kiyi hakuri mubi a hankali”

“wani irin mubi a hankali komai yana lalacewa, in zuba ido akaimin ɗana prison sam baze yuwu ba wallahi, ana shiga kotu nasan prion ne zasuce zasu kaimin shi”

“babu me kaishi prison, kidena damun kanki, Anwar ze fito”

Haka taita kwantar mata da hankali.

Tunda widad ta fice tsakar gida bata sake komawa ɗaki ba, tana maƙale da Gwaggo da Hindu tana koyo aikin gida, yayinda gefe guda sunayi suna faɗa da Hari, yayinda Hanne keta jifanta da bakaken maganganu, wani abun Widad ta gane wani ba zata gane ba, dan wata hussar ina tayi tsauri bata ganewa sam, ita dai tafi maida hankali akan ta koyi aikin,Gwaggo bata hantarar ta idan tayi ba daidai ba seta gyara mata cikin ruwan sanyi.

Saleh ne ya shigo gidan, ya tarar Widad zatayi tatar gasara, tanata kokowa da abun tatar Gwaggo tana gyara mata, gashi ta maida duk hankalinta so take ta koya, gwanin ban dariya da tausayi.

Saleh yace "Ina kwana ranki ya dade?”
Dagowa widad tayi ta kalleshi cikin basarwa tace “lafiya kalau”

Saleh yace  “aiki kike ne?’

Gwaggo tace “aikam aiki muke tayi”

”madallah sannu da kokari Gwaggo, ya me jiki kuma?”

Gwaggo tace “jiki da sauki Alhamdilillah”

“mashaallah, bari inshiga in duba shi”

Widad na jinsu tayi masa banza taki kula shi.

Da sallama Saleh ya shiga dakinsu Widad, ya tarar da Yusuf a zaune yayi shiru yayi zurfi a duniyar tunani, Yusuf ya dago ya amsa.

Saleh yace “ya dai ko jikin ne?”

Yusuf yace “ jiki ai naji sauki Alhamdilillah”

“madallah ai haka ake fata, ai can naga mutuniyar taka a tsakar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login