Showing 15001 words to 18000 words out of 209297 words
da Ameen, ita kuma ta koma ɗakinta.
Nurat ta jashi suka koma harabar gidan, ta kalle shi tace "Yaya Anwar, ya akayi ka fito ne?"
Ya ɗanyi ajiyar zuciya yace "kowa tambayar da yake min kenan, wallahi ban sam waye ya fito dani ba, ban san mutumin ba, na tambaye shi waye shi, yace wai ba'a bashi damar ya sanar dani waye shi ba, amma kin san wani abu?"
Tace "A'a seka faɗa"
Anwar ya ɗan ƙara ƙasa da muryarsa yace "ya cemin Daddy yana gurinsu, shiyasa ma suka sa aka sakeni, amma ban san dalilin da yasa suka sa aka sakeni aka bar Doctor Sufyan ba"
Zaro ido tayi tace "yana gurinsu kuma? To suwaye su? Meyasa suka ɗauke shi?"
"Nima be bani amsa ba Nurat, abun da ya cemin kawai kenan, wallahi gaba ɗaya a cikin damuwa nake, babu Widad babu Daddynta, gashi ranar daza'a ɗauketa kamar tasan abunda ze faru tacemin Anwar ga Amanar Daddy na nan ka kulamin dashi"
Cikin damuwa Nurat tace "kayi haƙuri Yaya Anwar, Allah ya gani kayi iya ƙoƙarinka, amma ƙaddara fa ta riga fata, babu yadda muka iya, sedai muyi ta musu Addu'a Allah yasa suna hannu nagari"
Anwar yace "Ameen, Amma abun da damuwa ace mace kamar Widad a hannun wanda ba'a san ko suwaye ba, akwai tashin hankali sosai Nurat, kin san ku mata kusa a cikin hatsari kuke, daɗina ɗaya tana tare da Yusuf, amma dukda haka abun ba daɗi, mussman shi ƙaddara ta faɗa masa beji ba be gani ba"
Nurat ta ɗanyi shiru tace "hakane kam, ni kaina ina tausayin Yusuf Anwar, amma dan Allah dagaske direban Widad ne?"
Anwar yace "meyasa kika tambaya?"
"bakomai kawai na tambaya ne"
Yace "eh direbanta ne, me kika gani?"
Ɗan girgiza kai tayi tace "yana da kirki sosai, kuma da alama ta yadda dashi sosai, na zata ɗan uwantane"
"Nima na gani, kuma yana ƙoƙari sosai akanta, yana mata biyayya ne sosai, kuma yana da haƙuri shiyasa suke shiri wasu lokutan"
Nurat tace "hakane kam, amma kuwa anje gidan su Yusuf ɗin, 'yan uwansa sun san halin da yake ciki?"
"Aini kinga ban daɗe da dawowa ba, wasu abubuwan duk ban san me ake ciki ba, ban san daga ina yake zuwa ba, sedai zan bincika inji ubangiji Allah ya bayyana mana su gaba ɗaya, amma ina cikin damuwa sosai Nurat, tun Widad na ƙarama nake sonta, ban taɓa furtawa ba, saboda sanin halinta, katsan bayan na dawo naji ance Fahad ɗan gidan Alhaji Bulama zata aura, naita ƙoƙarin in cireta daga raina, sedai ashe ita gaba ɗaya bata da babban maƙiyi a duniyar nan sama da Aure, tana yiwa Aure wani bahagon kallo ne, har a yanzu haka na kasa cireta daga raina, ina jin sonta a zuciyata, ko bacci bana iyayi yadda yakamata, gashi ban san inda take ba gashi na kasa riƙe amanar data barmin"
Wani irin tausayin Anwar ne ya kamata, a ranta tace 'ashe kaima kana cikin damuwar da nake ta soyayya'
A zahiri kuma tace "na tausaya maka Yaya Anwar, ka sawa ranka wannan ɗin Jarrabawa ce, ubangiji Allah yasa mu cinye jarrabawar nan, kasha Lemom mana"
Girgiza mata kai yayi yace "A'a tafiya zanyi nagode sosai Nurat"
Ɓata rai tayi tace "gaskiya idan baka sha ba bazan ji daɗi ba, sekace na baka wani guba, ko kaima Widad ɗinne?"
Murmushi yayi yace "wane ni in zama kamar Gimbiya"
Nan ya buɗe lenon ya tsiyayya yana sha suna cigaba da hira.
Mahaifin Nurat ne ya dawo suna tsaka da hira, ya shigo da motarsa gidan yayi parking, ya fito daga motar yazo ze raɓa su ya wuce, Anwar yace "barka da Rana Yallaɓai"
Ɗan tsayawa yayi ya kalli Anwar yace "wa nake gani haka kamar Anwar?"
"eh nine ranka ya daɗe"
"Allah sarki, ashe ka fito?"
"Eh wallahi Na fito Alhamdilillah"
"to yayi kyau haka ake so ai, har yanzu kuma babu wani labari akan ɓatan Daula ko?"
"Babu har yanzu dai muna sauraren hukuma ne dai"
"Allah sarki, yanzu an fasa kaika kotun kenan?"
"Eh an wankeni, ance bani da laifi shine suka ƙyaleni"
Alhaji Musa yace "gaskiya ne, ai dama bekamata a tsare wanda bashi da laifi ba, hakan ba daidai bane, kuma lawyoyin naku ne suka fitar da kai?"
"A'a su hana su belina akayi, daga baya ma in sunzo hana su ganina ake, wani mutum ne yazo aka fitar dani"
"ikon Allah, shima lawyer ne kokuwa?"
Anwar yace "a'a ban san waye ba gaskiya, dan nima be gayamin ko shi waye ba"
Alhaji Musa yace "Allah sarki, to ubangiji Allah ya tsare"
"Ameen yallaɓai nagode"
Alhaji Musa ya shige cikin gida.
Duk a aikin gida da Widad ke koya bata taɓa attempting zuwa gaban murhu ba, saboda bata son hayaƙi sam, ko menene tana daga gefe.
Tana zaune a ƙarƙashin bishiya tana gyaran wake, Hindu tace "Amarya dan Allah ƙawayena ne suke so suma a dinga koya musu karatu, in basu dameki ba, in baza'a takura miki ba"
Widad ta ɗanyi shiru sannan tace "shikenan tunda ta hanyar ki ne, aini ban isa ince a'a ba, su samo abun rubutu da littafi se mucigaba insha Allah"
Gwaggo tace "Amarya idan da takura fa karkiyi kara, kice musu a'a kawai su haƙura"
"A'a Mama babu takura, bana son mutane ne dai su fiye zuwa inda nake, amma ai bakomai shi ilimin 'ya mace ai abun sone, koba komai zasu amfani al' ummar da suke ciki, suzo zan koya musu Insha Allah"
Gwaggo tace "to Allah ya saka miki da Alkhairi, mu zuwanki garin nan alkhairi ne ai a wajenmu"
Widad tai murmushi tace "bakomai Mama, nima haɗuwata daku alkhairi ne ai".
Hindu tace "lallai su Indo zasuji daɗi, bari inyi sharar nan inje in gaya musu"
Hari tace "wudas dan Allah nima gasu abu na nan a haɗamin dasu dan Allah"
Hararta Widad tayi tace "baza'a koya musu ba ɗin, yaren yahudawan zan koya musu?"
Hari ta wangale baki tace "haba Wudas, dan Allah kiyi haƙuri ki koya musu"
"Anƙi a koya musun" Widad ta bata amsa tare da haɗe rai.
Hari bata kuma yin magana ba, tayi shiru ganin yadda Widad ta haɗe rai, Hanne ce ta fito tana wani yatsine fuska tana harare harare, Hindu ta kalle ta tace "Hanne ke zakiyi wanke wanke fa yau, kin bari ƙudaje se bin kwanukan suke"
Hanne ta galla mata harara tace "bazan ba, inda can ke kike sani inyi, banza uwar shisshigi da sa ido"
Hindu tace "ke kika sani, haka za'a miki auren kije kina ƙazanta, ki bar kwanuka ƙudaje nabi"
"Eh naji gara ni inada mashinshini ma, kefa ba uban wanda yake zuwa gjrinki, aba kamar mujiya aikin banza kawai"
Jikin Hindu ne yayi sanyi, tai shiru gwanin ban tausayi.
Hari se cewa tayi "ni kaina ina mamakin baƙin jini irin na Hindu, ba wanda yake zuwa inda take saboda tsabar girman kanta da baƙin jini"
Shiru Hindu tayi tana goge Hawaye, Gwaggo ce ta janyo Hanne ta dinga kifa mata mari a zuciye.
Widad tace "wai Auren nan dolene? Meye dan mutum bashi da saurayi? Saurayin banza dana wofi, Auren dole ne, itama wannan banzar mata hankali se kace ba sister ɗinki ba, kuna uwa ɗaya kina cin zarafinta"
Hansai tace "ba uwarsu ɗaya ba, Hindu ita kaɗai babarta ta haifa ta rasu, Gwaggo ce ta Riƙeta"
Widad tayi mamaki sosai, dan yadda Gwaggo ke son Hindu seka zata ita ta haife ta.
Widad ta ƙarasa inda Hindu ke tsugune tana kuka, Widad taje ta rugumo Hindu ta dinga rarrashinta tace "kiyi haƙuri kinji Hindu, Allah has a better plan for you kinji Hindu, kiyi haƙuri ki ƙyalesu, ai Aurem ba dole bane"
Gwaggo seda tayiwa Hanne tatas da zagi, ta tsitsstinka mata mari, tazo ta kama hannun Hindu tace "dan Allah kiyi haƙuri kinji Hinduna, muna nan insha Allah miji nagari zezo miki insha Allah"
Ita dai Hindu ba tace komai ba, se goge hawayenta da yake faman yi, tana jin zafin Gorin da akan mata na cewa bata da saurayi, Widad ma abun ba ƙaramin baƙantawa Widad rai yayi ba, dan bata son taga abunda ze taɓa mata Hindu, Allah ya haɗa jininsu sosai.
Widad ta kalli Hari tace "kekam abunda kika yi baki kyauta ba Hari, ke kanki aka bibiya sadakarki aka bawa megari ba dan kina da wani abu da namiji ze kalla ya aureki ba, dan ba kyau kika fi Hindu ba, yakamata ki dinga jan girmanki kema kin haifi mata"
Shiru Hari tayi da yake tasan bata da gaskiya.
Gaba ɗaya ƙarashen wunin nan haka Hindu tayi shi ba walwala, hakan ya shafi Walwalar Widad itama, seta kasa sakewa sukayi jugum jugum.
Nurat suka gama hirarsu da Anwar, tai masa rakiya har mota ya tafi, sannan ta dawo, tana shiga falo ta tarar da mahaifinta a tsaye yana huci, ya kalleta yace "dan ubanki meya haɗaki da wannan yaron?"
Cikin rashin fahimta Nurat tace "Daddy Anwar nefa"
"ina ruwana koma uban waye? Ke yanzu shikenan ban isa in gayamiki kiji ba? Meye haɗinki dashi nace?"
Mahaifiyar Nurat ce ta fito da sauri tace "dan Allah ka saurarawa yarinyar nan, wucewa yazo yi ya tsaya suka gaisa meye abun ɗaga hankali kuma? '
" ke dama ke kike goya mata baya take karyamin doka, ni anya ma kuwa wannan' yata ce"
Cikin mamaki tace "Meka ke nufi da anya kuwa 'yarka ce? Zargina kake kome? Kokuma dan kana abu zata kake kowama haka yake?"
A fusace yace "ni kike gayawa haka?"
"na gaya maka ɗin, ashe ba daɗi nida ka gayamin"
"A gaban' yata kike cewa ina biye biye?"
"to kace ƙaryane mana? Ni zaka kalla kace anya 'yarka ce?"
Aikuwa cike da zuciya yayi kan mahaifiyar Nurat, sedai cikin gaggawa Nurat ta shiga tsakani tana kuka, aikuwa yasa hannu ya shaƙota yayi wurgi gefe ɗaya, bisa tsautsayi tai gware da center table, take ta zube a gurin jini ya shiga zuba a goshinta kamar an buɗe famfo, take suka yi kanta da gudu, sedai ko motsi ba tayi.
Mahaifiyarta ce ta ɗagota a gigice tana kiran sunanta, Alhaji Musa yasa hannu yana ƙoƙarin karɓar Nurat a hannunta amma ta riƙeta gama taƙi sakarmasa ita, cikin kuka tace "ka ƙyalemin 'yata, ai dama kace ba' yarka bace, tunda ka kashemin ita se hankalinka ya kwanta"
Be saurareta ba ya suri Nurat da sauri yayi waje da ita jini yana zuba a goshinta.
Amal kuwa bayan ta shiga gida, Hajiya Halima tace "ina Anwar ɗin?"
"Ya ajiueni ya tafi, wai zashi wani guri ne"
"Nifa bana son yawan yawon nan da yake tafiya, se wani abun ya sameshi tukuna ko? Ze dawo ya sameni ne, ina jinki meyafaru da kukaje gurin Bulama"
Amal tace "ba wani abu bane, dama kawai tambayarsa yayi ya akayi yayi free? Se kuma jaje da yayi masa"
Hajiya Halima tayi tsaki tace "Aikin banza, dana san hakane wallahi ba zashi ba, mutumin banza kawai"
"Mummy kenan ɗan uwankine dai"
"dalla rabu dani, ɗan uwana mara amfani ba"
Amal tai murmushi tace "in an jima zamuga kun jone ai, ba'a shiga faɗanku"
Widad bata wani iya rarrashi ba, dan haka ta kasa saka Hindu farinciki, haka kurum idan ta tuna Gorin da'akayiwa Hindu se taji ta ƙara tsanar Hanne, sam Hanne bata ɗakko halin Gwaggo ba, Gwaggo mace ce me kirki da kawaici, ba zaka taɓa cewa ba ita ta haifi Hindu ba, saboda yadda take nunawa kamar tafi son Hindu ma aka Hanne kai kace gaba ɗaya ita ta haife su, bautar da Hindu take wa Gwaggo Hanne ba tayi, ga shegen som jikin tsiya, shiyasa basa shiri da Gwaggo.
Gwaggo se jan Hindu take da hira, amma taƙi sakin jiki, saboda gaba ɗaya ranta a ɓace yake, haka suka haƙura suka ƙyaleta, sedai hakan ba ƙaramin damun Widad yayi ba.
Yau shiru shiru Yusuf be dawo ba, gashi tun la'asar hadari yake haɗuwa a garin, se cida ake me ƙarfin gaske, kowa ya shige ɗaki ga iska da'ake yi, gaba ɗaya hankalin Widad yaƙi kwanciya, Yusuf be dawo ba ga hadari se cida yake, ga wani irin tsoro da ya baibayeta, lungun kan katifa ta koma tayi shiru tana ta addu'a a ranta.
Har magariba Yusuf be dawo ba, daga bakin ƙofar ɗakinsu tayi alwala, ta rufe ƙofar ta dawo tayi salla, se wata irin walƙiya ake.
Ana idar da la'asar aka kece da ruwan sama kamar da bakin ƙwarya, babu Yusuf babu labarinsa, hakan ba ƙaramin ɗagawa Widad hankali yayi ba, be taɓa yin haka ba se yau.
Tun Widad na tsumayin dawowar Yusuf harta fara cire rai, ga tsoro da ya bai baye ta, take ta fashe da kuka, ta dinga kuka kamar wata ƙaramar yarinya, ga tsoro ga gefe guda tana tunanin ko wani abu ya samu Yusuf ne.
Har wajen ƙarfe goma da rabi na dare, gashi babu alamar za'a tsagaita da ruwan nan, ta dunƙule guri ɗaya tana kuka, ji take tamkar ɗakin nan ze ruso a kanta, dan in akayi cida ji take tamkar ɗakin yana vibrating.
Babu zato ba tsammani taga An turo ƙofar ɗakin, Yusuf ne ya shigo ya jiƙe sharkaf da ruwa se ɗiga yake, jikinsa yana rawar sanyi.
Tana ganinsa maimakon ta tausayawa a halin daya dawo, kawai ta fashe da kuka ta haushi da faɗa
"Ina kaje ka tsaya, kalli agogo ƙarfe nawa? Kawai ka kama ka ɗagamin hankali ga tsoro inaji, ka fita kaje kayi zamanka baka damu da halin da zan shiga ba, wannan wane irin abu ne haka?"
Aikuwa Yusuf ya ƙule, akanta yaje yasha wannan uwar baƙar wahalar, ga ruwan sama yayi masa duka, bata tausaya masa ba se masifa da ta haushi da ita daga shigowarsa, aikuwa ya ajiye kayan hannunsa, yasa hannu a aljihunsa ya ɗakko wata leda ya jefo mata, ya juya ya shiga kokawar canza kayan jikinsa.
Ledar ta ɗauka, taji an nannaɗe leda cikin leda, ga ɗumi a jikin Ledar, se ƙarnin kifi da yake tashi a jiki.
Yadda ya haɗe rai ne yai mata banza yasa ta gane haushi yaji, ya canza kayan jikinsa ya ɗau abun shimfiɗarsa ya shimfiɗa a bakin ƙofa inda yake kwanciya, ga babu abun rufa ga iska da feshin ruwa a gurin.
Gaba ɗaya taji tausayinsa ya kamata, ta ƙarasa kan bargon da yake kwana ta zauna tace
"ka taso mu kwanta akan shimfiɗata, kaga nan ruwa yana jiƙaka"
Banza yayi mata, yaƙi ko motsawa daga inda yake, balle tasa ran ze kulata.
"Yoseef magana fa nake maka" still dai bece komai ba yayi mata banza.
Ta Kai hannunta ta shiga ɗan girgiza shi tana faɗin "dan Allah ka tashi, muje mu kwanta nan akwai sanyi"
A ɗan kausashe yace "malama ki ƙyaleni, tunda bakya tausayina komai nayi abun faɗa ne a gurinki, bana taɓa yi miki abu ki yaba, sedai ki ɓata mini rai, maimakon ki tambayi ya akayi na daɗe haka meya sameni kawai kin hauni da masifa, ni matsa ki ban guri ki dena taɓani"
Se kuma taga tabbas abunda tayi bata kyauta ba.
"Am sorry, ka tashi daga nan karka yi zazzabi"
"ina ruwanki idan nayi, ai ba damuwa kika yi dani ba, ki rabu dani kawai"
Taga dai alamar Yusuf bashi da niyyar tashi, dan haka kawai tayi kwanciyarta a bayansa, sosai ruwa yake feshi yana jiƙasu.
Yusuf yace "ke ki tashi daga gurin nan, wannan ruwan da yake taɓaki ze iya saki mura ko zazzaɓi"
"gara ya samu tare, tunda bazaka tashi ba" tai maganar tana sake maƙalƙaleshi ta baya, Yusuf jiya yi yana nema ya dena fushin da yake, ya maze ya kunna fitilar torchlight ya haskata yace "malama ki cikani kije ki kwanta"
Noƙe masa kafaɗa tayi, Yusuf yace "Shikenan naji, tashi muje mu kwanta a taki shimfiɗar"
Tana jin haka ta miƙe suka nufi katifar, ta gyara musu ita Yusuf ya zauna yace "miƙomin ledar nan" ta juya zata ɗakko akayi wata walƙiya data haske ɗakin gaba ɗaya.
Gaba ɗaya ta afko kan Yusuf, ta riƙe shi gam jikinta yana tsuma, ta runtse ido sosai tana ajiyar zuciya.
Aikuwa akayi wata tsawa me ƙarfin gaske, ruwa ya sake ɓallewa, haska fuskarta yayi yaga yadda jikinta yake tsuma tayi wiƙi wiƙi da ido kamar Agola a rabon gado, yai dariya yace "wai baki iya addu'a bane, se tsoro da kuka?"
Tashi tayi daga jikinsa tana cuna baki gaba, ta miƙo masa ledar kifine a ciki, ya kalle ta yace "wani guri aka kwatantamin, nace bari inje in siyo miki kifi, gurin da nisa ga babu abun hawa a kusa, nayi tafiyar ƙafa sosai, shiyasa kiga na daɗe fa"
Shiru tayi tana kallonsa kamar taga wani sabon abu, ya buɗe ledar kifin, manya manyan gashashiyar tarwaɗa ce da karfashe.
Ya zauna ya dinga cire ƙayar ya ɗakko ya kai bakinta, tasa hannu zata karɓa ya girgiza mata kai yace "karki ɓata hannunki da ƙarni"
Haka ya dinga bata tana ci, can kawai yaga tana hawaye, ya kalleta yace "meyafaru kuma? Yanzu kuma me nayi miki"
Girgiza masa kai tayi alamar bakomai.
"kifin ne ba daɗi" ya kuma tambayarta, nan ma ta girgiza masa kai
"to faɗan da nayi mikine ya saki kuka?"
Nan ma ta girgiza kai, ƙarshe tace "Nagode"
Yusuf yace "da akayi me?"
"Ka siyomin kifi"
"Haba Queen, meye abun kukan kuma? Kukan ki yana ɗagamin hankali sosai, dan Allah kidena kinji, bakomai is my responsibility to make you happy Baby"
Yai maganar yana ɗago haɓarta da hannu ɗaya.
Shiru tayi tana ci gaba da share hawaye, seda ta ƙoshi sannan Yusuf yaje ya wanke hannunsa, ya dawo ya tarar da ita a zaune.
Yazo ya zauna a kusa da ita yace "oya kwanta"
A hankali ta zame jikinta ta kwanta tayi shiru, kamar wadda ruwa ya cinye, shima ya kwanta sedai ko mintuna biyar ba'ayi ba aka sake ƙyallo walƙiya, aikuwa ta kuma cakumo Yusuf kamar jikinsa ya tsage ta shige.
Yusuf yace "Gimbiya addu'a zaki dingayi, kidena tsoro haka"
Ba tace masa komai ba se sake lafewa da tayi a jikinsa, taƙi ko motsawa.
Haka aka cigaba da tafka ruwan sama kamar da bakin ƙwarya.
Shima Yusuf ya rungumeta gam a jikinsa, yana wasa da saman gashinta data ɗaure da ribbon.
A hankali ya kai hannunsa kan ribbon ɗin, saitin kunneta yace "in cire?"
"inka cire min seka gyaramin"
Murmushi yayi, ya zare ribbon ɗin dogon Gashin kanta ya baje akan katifar.
Yusuf ya dinga wasa